Sashe 2
Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Godiya Da sunan Allah me Rahma me jin kai, dukkan Godiya ta tabbata ga Allah SWT Ubangijin talikai, me kowa me komai da ya bani ikon fara rubuta wannan littafi me suna a sama cikin koshin lafiya, ina addu'ar Allah ya bani ikon gama shi kamar yadda na faro ya sa mu amfana da duk wani darisin cikin sa, kuskuren cikin sa kuma Allah ya yafe min. *Jan hankali*. This book is a total work of fiction, suna, gari kasa ko wani abu daga cikin labarin in aka yi rashin Sa'a yayi daidai da naki to fa arashi ne, ban rubuta wannan littafi dan cin mutunci ko wulakanta wani ba face dan ganin yada ce in fito da virtues din matan da rashin haihuwa yasa ake yi wa kallon kaskantattu, wulakantattu ko marasa amfani, a guji yanke wani abu ko juya min labarin ta kowace siga dan tabbatar da zaman lafiya, kamar yadda na fa a wannan labarin irarre ne bisa fasaha da baiwar da Allah ya bani tare da yin duba ga rayuwar mu da abubuwan dake faruwa cikin wasu gidajen auren. *Dedication* *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da addarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sai dan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ______________________________________ ______________________________________ _Free Chapter One_ Tun daga kasa har sama nake karewa kaina kallo ta cikin tafkeken madubin da ke girke a dakin baccin nawa, babu ta inda na hango wata makusa ko kasawa a tattare da ni, hakan be wadatar da ni ba sai da na sake agowa na sake sako duban tun daga kan yalwataccen gashin kai na bakikirin dake kwance kan kafadu na, a hankali na sauke duba na kan matashiyar fuska ta dake cike da tashen kuruciya, ba wai na budurtaka ba a'a na shekarun tashe ga iri na da muke kan wannan mataki, zagayayyar fuskar ta auke take da wadatattun idanun da Allah ya awata ta dasu, farare tas masu haske da matukar daukar hankali, ban tsawaita ba na sauko kan dogon karan hanci na da ya dada wa fuskar kyau bayan idon, hanci na ba siriri bane zut in nan yana da dan fadi kadan da yasa ya zauna das kan fuskar, kyakkyawan aramin baki na me auke da madaidaitan lips da basu cika karanta ba haka kuma ba manya bane, a hankali kuma na lumshe idona na bu e tare da sakin kyakkyawan murmushin da ya bayyana jerarrun ha ora na da basu kasance farare ba sedai milk ne masu kyau da suke samun kula a ko yaushe. Cikin wani irin yanayi na girgiza kai na wani abu na tsirga min cikin raina na sunkuyar dashi kafin cikin karfin halin da na saba yi na bude na cigaba da surveying jikina, a kan cikakken wuya na idanuna suka sauka wanda ke dauke da wasu layi haka ko guru guru zance, cikar kirjina dake fisgar hankali na maida kaina farin ciki na ratsa ni, shafaffen ciki na da bashi da alamar agawa balle in aje tumbin da wasu daga cikin sa'anni na ke korafi dashi suke kuma sha'awar lafewar cikin nawa sai dai gare ni hakan shine ciwo mafi girma ga rayuwa ta dan babban burin na a wannan duniyar be wuce in farka in ga cikina ya tasa kamar kowace mace da Allah ya albarkace ta da arzikin haihuwa ba. Da kyar na ha iye wani mugun miyau ina janye duba na daga wajen na maida kan faffa a kuma cikakken kugu na wanda shine abu mafi daukar hankali a jikina gaba aya, nikaina yana daya daga cikin halitta na da nake alfahari dashi dan shine kadai abu aya da ya rage min da ya ri e ni a gidan aure na ya kuma sa nake da yar ragowar kima a idanun mijina wato surar da Allah ya min, ban tsawaita ba na karasa kan kafafuna dake wadace da jan lalle wanda bana rabo shi, lallen ya zauna daras kamar a kai a aka ire shi, yadda ya haska farar fata ta kuwa abin ba'a ce wa komai. Babbar ajiyar zuciya na sauke dana gama karewa kai na kallo kafin cikin sanyin jiki na dauki kwalbar turaren da tuntuni shi ne zan shafa amma na tsaya kallon kaina kamar bakuwar kan nawa, zazzagwa nayi a hannu na na shiga shafe lallausar fata ta dashi lungu da sa o sannan na aje, wata na kuma auka itama na murza a hannun na shige shafe wasu wurare masu mahimmanci a jikina, ina yi ina yan tunane tunanen da suka zame min jiki a duk lokuta irin wannan. Ringing din wayata dake aje kan bedside drawer yasa na dawo hankali na sosai na shiga shiri da sauri dan nasan ba kowa ke kiran ba se oga, na dade da sanin ya tsani jira musamman daga gare ni kamar yadda yake fa a min times without number sai too ifdai nikuma ya riga ya zame min jiki musamman a kwana kin nan. Kayan bacci na ciro masu kyau, laushi hadi da daukar hankali na zura ina tattare gashi na waje aya na kama shi cikin ribbon, duk da na shafa wasu turaren kafin sa kaya ba hakan ya hanani sake fesa wasu ba wanda suka sa take dakin ya cika da sassanyan kanshi na me ratsa zuciya wanda nake amfani dashi kadai lokacin da zan je ga oga. Waya ta na auka na kashe batare da duba komai ba dan bani da lokacin hakan me ni na can na jira na kuma san tuni ya cika yayi fam se nayi rarrashi. Seda na sawa kofa ta key dan gudun matsala da jan magana sannan na wuce upstairs inda nan ne turakar me gidan take, seda nayi Knocking tare da dan dakatawa sannan na tura ofar a hankali ina me yin sallama cikin daga murya dan ankarar da na cikin dakin cewa gani nan fa tafe. Nasan zaku yi mamakin wai na tsaya knocking ni da dakin mijina da addini ya bawa damar shiga wajen sa duk sanda naso haka kuma ganin sa cikin kowane yanayi halak ne gare ni, to ba komai yasa nayi hakan ba face gujewa haduwa da acin rai, a irin wannan yanayin na kan ci karo da mabanbanta takaicin da kan hanani bacci wasu lokutan yayinda wasu lokutan kuwa nake hana zuciya ta damuwa ko da kuwa taso yin hakan. Ajiyar zuciya nayi hango shi zaune ken bed Yana danna waya, cikin tafiya ta me daukar hankali da kuma karin wasu salo dan sace zuciyar oga na kai gefen mirror in sa na aje yar jakar kayan hannu na sannan na karasa gare sa wanda tun shigowa ta da yayi min kallo aya be sake yi ba. Cikin jikin sa na shige ina manne masa kamar wata cingum na sanyaya murya dan nasan nayi laifi haka kuma na shagwa e fuska cikin fatan samun lagon sa "Am sorry zuma naaa, na tsaya shirya maka kaina ne ta yadda zaka mori daren ka cike da annashuwa da farin ciki, ayi min afuwar dadewar da nayi plsss". Na karasa ina kai hannuna cikin irjin sa ina masa waiwayi cikin salon da nasan baze iya jurewa ba, kamar yadda na sani kuwa lumshe idon sa yayi tare da rike hannun da ke yawo jikin nasa kana ya bude su ya zuba kan fuska ta "Kullum se kince ayi miki hakuri kuma ba haka ze Hana gobe ma ki sake ba, na kasa gane meye matsalar ki Khadijah, ke ba da ba ba jikan da zaki fake da kula da shi ba amma ko mariya dake goyo ba zata fa a miki kawo uzuri ba, Allah ya sani kin fara kaini bango dan na fara gajiya da uzurorin ki marasa kan gado da bakya rasa na bayar wa kullum". Daga jikin nasa da nake kwance na lumshe ido zuciya ta na motsawa, ba se Salees ya tuna min da cewa ban ta a haihuwa ba, ba se Salees ya tunatar da ni bani da tsuntsu bani ga tarko ba dan hakan abu ne da bana ta a mantawa ko da kuwa acikin mafarki ne. Sanin shiru na wata matsalar ze jawo yasa na daure rashin da i na na bar shi iya cikin raina yayinda a zahiri na ago na sumbaci bakin sa ina tabbatar masa insha Allah ba zan kara ba wanda hakan yayi tasiri gare shi dama kuma be fiya riko ba, cikin zakuwa da natsuwa ya shiga birkita nutsuwa ta da salon sa masu tafiya da ruhi na suke kuma karamin kaunar sa a ko da yaushe inda nima tuni na biye masa muka fada cikin wata duniya me wuyar bayyanuwa, seda duk muka sami nutsuwar da ta dace kafin muka shiga wanka dan yin shirin kwanciya. Ko a cikin toilet din ma be bar ni haka ba dan se da yayi neman maganar sa san rai kafin muka wanko jiki muka fito, cikin sanyin jikin gajiyar da ya tara min na maida kayana tare da hayewa kan gado na lafe ina sauke numfashi yayin da gefe aya nake mamakin rashin faruwar lamarin da ya zame mana jiki cikin watanni aya zuwa biyu da suka wuce. Ban kai arshen mamakin ba sautin kukan yaro ya fara ratsa kunne na, tun ina jiyo wa kasa kasa har ya fara arfi alamun ana nufo dakin ne, cike da takaici na tsurawa kofar dakin ido cikin jiran faruwar sabon mu, dukan kofar aka shiga yi kamar a filin yaki wai kuma hakan da sunan knocking ne fa ake yi, daga kwancen da nake ban motsa ba naga tashin sa daga kokarin kwanciyar da yake yi kusa da ni ya bude dakin yana an ha e rai. "Ka gan shi nan yaki yin shiru, nayi nayi wallahi se kuka yake har na rasa