← Book details Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 48

Sashe 8

Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wattpad @ouummey Ouummey 003 *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da addarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________ _Free Chapter Three_ Hankali a kwance na tashi aiki tare da tattaro kaya na na fito, tsayawa nayi ina gaisawa da abokiyar aiki na me suna A'isha "Yau ba zaki jira oga ba kenan?". "Ai bana tunanin oga ya shigo yau dan a gida na bar shi". Na bata amsa, akan Salees take magana dan wajen aikin mu daya da shi sai dai ya fi ni matsayi da office uku, mataki na uku yake a ma'aikatar ni ina na bakwai "Eh na manta fa, kin san zasu je meeting a main branch so yau zasu tafi". Da yake na amsa mata dan na manta da batun haka kuma da zan fito be min sallama ze tafi ba, da haka muka rabu na wuce wajen mota na na shiga tare da barin ma'aikatar. Sannu a hankali nake driving zuciya ta cike da tunanika barkatai, wato dai yanzu ban da sauran matsayi a wajen Salees, da ni da banza kwance kusan aya muke, to in ba haka ba ai ya cancanta ya min sallamar ze tafi ko. Wai a duk cikin yanayin da nake sai da wani bangare na zuciya ta ya dinga tursasani yiwa Salees uzuri, ban ja ba na yi masa ta hanyar yin tunanin maybe dan yasan na san zancen ne tun a office. Seda na tsaya a mall nayi siyayyan kaya shafa na da suka yi kasa tare kuma da undies dina da naga kaman sun an yi sanyi, ban fito ba se da na siyowa baby wato Ilham wata gown me kyau da ta burge ni Amir kuma wani takalmi me kyau, wannan sabo na ne bana yin siyayya ban musu tsaraba ba har Salees, Mariya ce dai ban ta orawa kaina yin wannan karyar ba dan ba zan iya ba, shima Salees in daga baya aje wa nayi ganin ba sannu bare na gode. Sai da na adana motar inda ya kamata sannan na kwashi ledoji na zuwa main falon mu, da sallama a baki na na shiga , yuuuu haka Mariya da awayen ta suka zuba min ido kamar sun ga wata sabuwar halitta lamarin da yasa naji na tsargu dan kafin na shigo kaya kaya haka nake jin surutun su. Kadaran kadahan na musu sannu da gida na wuce daki na ina tafe ina jin kaifin idanun su da suka min rakiya da shi, zube ledojin nayi kan bed tare da zama ina aje numfashi, seda na huta sannan na cire kaya tare da shiga toilet na yi wanka. Jakar shopping in su Amir na auka na fita bayan na shirya cikin atamfa ta purple color inkin riga da skirt da suka zauna a jikina suka kuma kama ni wanda yawancin dinkuna na duka haka suke, duk tsadar kaya bana bakin cikin kacaccala shi wajen yin dinkin da nasan zasu zauna a jikina in birge me gida. "Sannun ku fa, maman Ilham ga wannan nasu Amir ne". Na fa a ina aje mata ledar a gaban ta kana na juya zuwa kitchen dan yin girki "Oh mace har mace amma bata da wani amfani, to meye amfanin juya da bata haihuwa?". Kalaman daya daga cikin su da na jiyo dan dama a yadda ta daga sauti take magana ta fa a ne dan naji "Haba ke kuwa Asmah, bana san neman magana, ya muna zaune alau da yar uwa ta kina min irin wannan kalaman?, Gaskiya bana so". Mariya ta fada da murya me kaman tana dariya ne ko kuwa, nidai ban tsaya ba na shige kitchen din na Kai jingine jikin Island da sauri ina sauke numfashi a jere a jere kamar wadda tayi tseren gudu, makogaro na ya bushe kamar wadda ta shekara bata sha ruwa ba, da kyar na iya lakato wani yawu me daci na ha iye ina lumshe ido, a kuma lokacin ruwan hawaye ya fara zarya kan kunci na, halin da na shiga a lokacin ba me bayyanuwa bane. Sanin suna falon yasa na daure zuciya ta na lallashi kaina na hada fruit salad maimakon noodles da na shigo da niyyar yi, juice na auka me sanyi tare da bowl dina na fita cike da fatan kar wata ta kwata fa a min irin maganganun nan dan a yadda nake ji zan iya biye musu muyi duk wadda ta kama. "Auntyn yara angode fa". Yatsu biyu na daga mata batare da nace komai ba na shige aki, da kyar da sidin goshi na sha salad din nan dan wani daci naji yana min a baki. Kuskure baki nayi bayan na gama na ture plates din gefe tare da aukan waya ta ina dubawa wai ko zanga missed call din Salees, sedai ga mamaki na ko text babu balle kira, murmushin takaici nayi tare da kiran shi ni, ta dade tana ringing be dauka ba har ta katse na sake kira shima be auka ba, seda na masa miss call biyar sannan ya turo min short text "Busy". That's all he said, Ina gani na aje wayar jiki a sanyaye, saboda gudun tunanin da ka iya rufe ni na janyo tablet dina na hada mata keyboard na shiga ayyuka a ciki, duk wanda ya ganni kallo aya ze min yasan ina aikin ne kawai amma ba dan jin dadi ba. Dake Allah Alhakeem ne se gashi tashi aya ya aiko min da sanadin farin ciki madaukaki, ba komai bane face karin matsayi da ake shirin yi a ma'aikatar mu, cikin rahamar Ubangiji kuma har da suna na cikin wanda za'a yi reviewing Wanda muna sa rai in mun tsallake review shikenan promotion ya tabbata. Ban yi farin cikin ni ka ai ba na kira Ummi na na fa a mata tare da fatan a taya mu da addu'a ta amsa, yayata Salima na kira itama na sanar da ita, ba tun yau ba na fahimci kunya da nauyi na ta take ji ba sedai ni a raina wani irin girman ta nake gani domin tai min abinda ba kowa ze iya ko kwatanta wa ba. Ta taya ni murna tare da fatan dacewa, tana neman kashe wayar na tare ta da sauri "Ina yaro na?, Shiru baya neman mommy?". "Ba haka bane ba maman Haidar, kin san baban makarantar wuni ya kai shi saboda yaki maida hankali a waccan". "Ayya, dan Allah yaya a kula min da shi sosai, kar a bar min shi da yunwa da damuwa". Daga cikin wayar na jiyo faffa an murmushin da tayi tare da amsa min mukai sallama na kashe wayar sabon zafi na sake hudowa daga kirji na sedai tuni na dakatar dashi saboda bana san abinda ze dinga tuno min da baya, duk da present din ma ba dadi ne dashi ba amma bayan nan akwai ciwo me matukar ra Seda na tabbatar awayen Mariya sun tafi dan gidan yayi shiru ba hayaniyar su kana na dau bowl din da nayi amfani dashi na fita zuwa kitchen. Zama nayi a kujera tare da kunna Tv na shiga kallon wata drama da ake yi a mbc Bollywood, cike da zallar nishadi na kalli abina har aka gama na tashi zuwa daki dan It's evening, akwai bukatar in kwance kai na dan sati na biyu yake ciki. Seda nayi Asr sannan na fara tsifar a falo ina yi ina sauraren wani hirar classmates dina a group da sukai ta hanyar voicenote, a lokacin ne kuma baby ta shigo dan se five ake tashin su, da karfin gwiwar ta ta shigo murya a sama tana ihun kiran sunan uwar ta ita kuma tana saukowa daga sama tana amsawa sedai tashi aya taji dif yarinyar tayi shiru. Wai ashe ni da ta tarar cikin falon ne yasa ta auke wuta jikin ta ya shiga rawa, sam ban ma lura ba ni hankali na na kan abinda nake ji seda naji babar na tambayar ta "Me haka, lafiya na ga jikin ki na rawa?, Me ya faru?". Da mamaki na daga kai ina kallon su, yarinyar ta maza ta fa a jikin mamanta tana zare ido, ko da na gane abinda ke faruwa se kawai na dauke kai na cigaba da abinda nake yi ita kuma taja ta daki tana tambayar ta. Ban san me ta fada wa uwar ba se ganin Mariya nayi a gabana a tsaye kamar wata bishiya "Wane irin rashin imani ne yasa kika yi wa Ilham wannan marin, kin kuwa ga yadda bakin ta ya kumbura?". Kamar kar in tanka se kuma na tan wasa kai na sanin shi bayani yana da dadi kuma rigima sam ba abar so bace musamman gare ni da ba hali na bace, zama da Mariya ne yasa har ban san yaushe na canja ba. "Ilham rashin kunya take koyowa Mariya, wai kamar ni zata kalla ta zaga, imagine fa". "Ban gane zagi ba, kin ga tun kafin raina ya ida aci ki min bayani yadda zan fahimta, Ilham ta zage ki tace miki me ?". "Kin san dai ko ke baki isa in miki karya ba balle aramar yarinya kamar ta, ce min tayi wai Allah yasa tana da iyayen da suka haife ta tun da ba juya bane su". ance ido tayi cikin rashin mamaki balle damuwa "To ai ba karya tayi ba tana da iyaye, shima juyan ai ba sharri tayi ba tunda da juya ne su da basu haife ta ba, shine kawai dan wannan yar maganar zaki nemi lahantata, to wallahi bari uban ta ya dawo dan ba zan yarda ba". Iya ma ura raina ya kai wajen aci dan haka na mike tsaye nima kamar yada take "In Kika yarda ma ba sunan ki Mariya
Chapter 8 · 0% Book details