← Book details Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 48

Sashe 26

Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da addarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________ _Free Chapter Nine_ Babu dadewa Hajiya Farida ta dawo rike da maganin, kusa da yar uwar ta ta zauna tana mata sannu ganin yadda ta damke cikin tana runtse idanu, da sauri ta balla maganin harira ta miko bottle water ta ha a ta kamo falmatan ta sa mata maganin a baki kana ruwan, da sauri ta hadiye tana dan jujjuya kai na ciwo. Babu dadewa ciwon ya lafa dan maganin babban magani ne haka kuma fast action shiyasa yake da tsada sosai, seda ta dawo hayyacin ta harira ta zuba mata abinci bisa umarnin Hajiya Farida ta karba ta dan ci ta aje ragowa. Ganin yadda hankalin ta ya dawo sosai yasa Farida kasa iya cigaba da rike abinda ke cikin ta "Wai haka zaki yi ta zama da ciwo a ciki sai dai ki sha magani ki kwantar dashi?, Wait taya ma aka yi yau maganin ya yanke miji?". Dan murmushin takaici Falmata tayi "To y azan yi Farida, tun da kaddara ta kenan?, D ana sake wa Alhaji magana yace wai in jira next month yanzu kam dai babu kudi wajen sa, magani kuma yace na bawa Adam kwalin ya siyo, to tun da na bashi ban ma kuma ganin sa ba". Kankance ido Farida tayi cike da mugun mamaki "In ji shi Alhajin yace ki cigaba da zama da ciwo har zuwa karshen wata?, Lallai mutumin nan ya wuce duk yadda nake zato, ke dama kin sa ran ya kawo muku maganin, wannan tambadadden dan da uwar sa ta riga ta gama poisoning mind finishing, ai na fada miki kin ki yadda, wallahi hau da za'a ce kin mutu dukkan su murna zasu yi domin dadadden burin su ne ya cika". "Kuma fa cewa nayi ko a asibitin nan ne ya biya ayi min aikin duk da akwai risk me girma amma na gaji da wahalar da nake sha Farida, wataran har na kan gwammace mutuwa saboda radadi da azabar da ni kadai na san me nake going through, ki dena ce musu tambadaddu, Allah ya shirye su su gane gaskiya ". "Uhm". Kawai Hajiya Farida tace cikin takaicin yar uwar Tata, kalli dai wahala ta gama sha ta sanadin Alhaji da an sa amma wai a daina ce musu tambadaddu, ita ta rasa wace irin zuciya Allah yayi wa Falmata amma komai ya kusa zuwa karshe dan ita ba zata zuba ido ba, dole ta dauki mataki ko dq da ba da sanin Falmata bane. Yin wannan tunanin yasa ta saki ranta ta shiga kwantar wa da yar uwar ta hankali kana ta tashi ta gyaggyara mata daku na inda masu aiki basa shiga mata, se daf da magriba ta yi shirin tafiya bayan ta jaddada wa Falmata cewan ko yaya taji wani ciwo ta kira ta haka kuma ta tambayi Alhaji suje su ga yan uwan su. Da toh Hajiya Falmata ta amsa mata kana suka yi sallama Farida ta wuce. Bedroom din ta ta koma ta yi wanka ta fito ta tsaya gaban mirror dan yin shirin ta sedai se ta bige da kallon kanta cikin madubin. Gaba daya tayi baki ta rame kamar ba ita ba, farar fatar ta me sheki duk ta yi duhu, kyakkyawar fuskar nan duk ta mokade saboda rama, baka ganin komai a fuskar se dogo siririn yancin ta da ya kara tsayi se kuma kodaddun idanun ta da kallo daya zaka musu ka hango rashin lafiya, damuwa, rashin nutsuwa da rashin kwanciyar hankali cikin su. Hannu tasa ta shafo wuyan ta inda kasusuwa suka bayyana kan su a wajen, ta dade ta na shafa wajen cikin tunanin tana hawaye batare da ta san tana yi ba, tsayin lokaci kafin ta farga ta share fuskan ta kana ta karasa gaban bed da ta aje kayan da zata sa ta dauka ta maida wardrobe, a yadda tayi wannan ramar sam ba zata sa kayan mu na al'ada ba dan ba kadan ba zasu bayyana ramar ta kasancewar duk an dinka su ne lokacin da take falmatan ta ba yanzu da se sunan kawai ba. Doguwar riga ta sa kirar Oman kana ta aje dankwalin a gefe ta shiga gyara kan ta wanda shima se d aya samu tangarda saboda halin da take ciki, seda ta tufke jelan sannan ta daura dankwalin kan ta, ba karamin kyau tayi ba duk da kuwa fuskar ta babu komai face kwalli da ta sawa idan ta dan ya rage kodewar da yayi. Kai daga yadda ta daura dankwalin abayar zaka san lallai a da an zuba gayu an kuma kafa dauruka ba kadan ba, ita kan ta murmushi tayi da ta kalli kanta sannan ta kwashi wayoyin ta ta fita falo. Tare da harira suka zauna dan duk cikin masu aikin ta tan matukar kaunar harira haka kuma ba matsayin me aiki take kallon ta ba, kallon yar uwa kuma karamar kanwa take mata dan ta girmewa hariran nesa ba kusa ba, hirar su suke yi suna kallo sama sama abinda yasa zuciyar Falmata dan samun nutsuwa daga tunane tunane. Yadda hankalin su ya dauku yasa har basu ji sallaman Alhajin ba balle shigowar sa seda yayi gyaran murya, da sauri harira ta tashi tayi waje ta kofar baya bayan ta gaida shi, kusa da Hajiya Falmata ya karasa ya zauna inda ita kuma ta tashi zuwa kitchen domin kawo masa ruwa. Kan karamin tray ta dauro bottle water da juice na kwali me dan sanyi kana ta hado da glass cups ta kawo gaban sa ta aje kana ta zuba ruwan ta mika masa ya karba ta kuma shiga zuba juice din. Seda ya karewa juice din kallo kafin yayi bismilla da karfi sannan yasha, ita dai tana kule dashi sedai bata bashi wani muhimmanci ba har ya shanye lemon ya aje. "Wanka zaka fara yi ko abinci zan kawo?". Da sauri kamar wanda tace zata kawowa mugun abu ya shiga kada kai "A'a, a'a ai ba zan ci abincin nan ba, na riga naci abinci a waje cikina a cike yake". Dan tsai tayi tana kare masa kallo kafin kuma ta girgiza kai tana dan murmushin da kan kallo zaka san ba na jin dadi bane "To shikenan, wankan fa?". "Yanzu zan je can part di na nayi, dama dai nace ba wata damuwa ko?" Seda ta dan hadiye miyau kan ta bashi amsa "Maganin da na bawa Adam ne dai har yanzu be kawo ba". "Se fa kina yi wa yaran nan uzuri, yana da harkoki da yawa ne, yanzu haka ya ma tafi can kudu kan kayayyakin mu da ze shigo dasu, amma kiyi min texting sunan maganin se na taho dashi". "Ko kawai ka bawa Bala ya siyo min?". Ta fada sanin in dai shi ze siyo maganin to kuwa har ta mutu be kawo ba. "Shikenan zan bashi kudin ya siyo kawai, shikenan ko?". "Maganar aikin nan alha......". Tun kafin ta karasa ya katse ta yana mikewa tsaye daga zaman da yayi "Ai tuni muka gama magana akan wannan, na fada Miki babu kudi a hannu na yanzu amma watan gaba insha Allah se ayi aikin ko a nan asibitin Shehu ne dan gaskiya fita wata asa ze ci miliyoyin kudade kuma kin ga yadda yanzu harkokin suke se a hankali". Tun d aya fara maganar take kallon shi har ya kai karshe "Allah ya kara budi, gobe ina so inje gida". "Gida kuma, wane gidan kenan?". Ya fada yana bata rai kamar wadda tace masa zata je gidan karuwai ". "Gidan marayu mana, muna da wani gidan da yafi nan ne?". "Ba zaki je ba". Ya fada yana kade babbar rigar sa ya nufi fita waje "A'a Usman ka bar ni kawai dan wallahi goben nan se naje". Ta fada da rawar murya, shima Alhaji tsayawa yayi kana ya juyo cike da mamakin yau Falmata ke ja da hukuncin sa, anya be fara kure hakurin baiwar Allahn nan ba kuwa. "Shikenan kije Allah ya tsare, ki gaida su". Bata amsa masa ba ta zauna tana kallon tv sedai hawaye ke zuba a idanun ta, yana fita itama ta tashi zuwa daki da sauri, kan gadon ta ta fada tana kuka me shiga jiki, wani kuka me tafe da sheshshekar dake fitowa daga can karkashin zuciya, a hankali nunfashin ta ya fara seizing kadan kadan kafin kuma tari ya turnike ta , da sauri ta tashi daga kwancen da take tare d da finciko tissue dake aje kan mirror din ta tasa a bakin ta zuwa hancin ta dan ta ana abinda ze faru gaba. Seda tarin ya tsaya mata da kyar sannan ta zare tissuen dake kan hancin ta ta aje haka ma na bakin ta, gaba dayan su sun aci da jini, wani irin bakin jini me kauri, ganin bata firgita ba yasa nasan ta dade yana ganin hakan kenan. Wata tissuen ta sa ta goge bakin ta sosai kana sa ruwa ta kuskure bakin, ta dauko wani ma ta goge hancin, take fuskan ta yayi tas kamar ba ita ta shiga yanayin ba. Kora tissues din tayi cikin closet ta karawa toilet din spray sannan ga fito, bedside drawer ta bude ta ciro wani tablet guda biyu manya ta sa a baki tare da korawa da ruwa, Wani ta dauko different from the first shima ta sha biyu sannan ta cire doguwar rigan jikin ta tasa na bacci yayi light off tare da kwanciya bayan tayi addu'a. Kashegari da wuri ta shirya, tayi matukar kyau cikin Abayan da tasa kirar Dubai, sosai ramar ta ta buya se wadda ba'a rasa gani ba, sallama tayi da su harira sannan ta fita cikin motar ta
Chapter 26 · 0% Book details