Sashe 21
Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
"Kiyi magana, ki fada min laifi na and we'll sort things out komai ya wuce". "Baka yi min komai ba zuma na". Zuba min ido yayi na tsayin mintina kafin ya sake matsowa kusa na har nunfashin sa na sauka kan fuska ta "No nayi miki, Ina ji a jikina nayi miki laifi, in haka ne meyasa da baki min haka ba se yanzu?, pls ki fada min me nayi miki dan iya tunani na na kasa ganowa". Murmushi nayi jin wai ya kasa gano laifin sa "Ka kwantar da hankalin ka pls, baka min komai ba ni hutu kawai nake bukata, pls ko zaka iya komawa wajen Mariya har zuwa wani dan lokaci?". Izuwa yanzu ina iya hango bacin ran d Salees ke ta kokarin boyewa sedai ko gezau ban ji komai ba a raina akasin da da ban so ko kadan in ga fushi ko damuwa tattare dashi "To kuwa baze yiwu ba, na biki na lallaba ki, na kwantar da kai na sanyayar da murya duk dan mu zauna lafiya amma kin ki bani hadin kai, zama da nine kika gaji ko kuwa wani salon wulakanci ne?". Zare hannyeye na nayi daga nasa na koma na kwanta ina bashi amsa "Babu ko daya cikin biyu kawai dai kamar yadda na fada maka ne ina bukatar hutu, Allah ya bamu alkhairi, pls in zaka fita ka kashe min wutar ka kuma rufe min dakin". Daga haka na ja bargo na lullube afafuwa na tare da kulle ido na, tabdi bala'i ni kaina na san na tsokana masifa sedai sanin na shirya mata yasa nayi banza da duk bala'in da Salees ke yi "Kar ki maida ni wani shashasha mana, bar ganin ina bin ki ina lallaba ki amfada miki tsoranki nake ji, ko kuwa kin fi karfi na ne, to wallahi kyale ki nake yi kawai darajar su Abba, amma ban da haka ke in ance kiyiwa Salees iskanci ba zaki fara ba, wacece ke da za'a dinga bin ki kina wani daukan kai, ban da ma kin kasance butulu duk rufin asirin da nayi kiki baki gani ba, duk suturar da nayi miki amma nine zan zama abin wulakancin ki, to bar ganin ana wani cewa kin raina ni kin mallake ni, wannan duk karya ne dan ba macen da ta isa ta raina ni, ba'a haife ta ba wallahi dan kuwa se ta koma gidan gyatumi tun da babu abinda ya zama dole, kuma wallahi tun muna shaida juna maza ki koma hayyacin ki kafin mu kai ga yin batacciya dan akan haka wallahi komai ze iya faruwa, in nace komai ina nufin komai". Ya sa kai ya fice tare da banging min door din, duk da cikin fadan nasa akwai kalaman da suka zafafa min amma se ban bari sun yi tasiri a raina ba, mafi aala shine na bata masa rai wanda shine aiming dina kuma na ci riba dan haka se na tashi na maida kofa ta na rufe tare da kashe wuta na koma na kwanta tare da rufe ido bayan nayi addu'a, aikuwa ba jimawa bacci yayi awon gaba dani. Washegari tun bakwai saura na fice dan bani ce da girki ba bana kuma bukatar abin karin su, a office na hada tea da heater na dan ina da komai na bukata, na karya a nutse hankali kwance sannan na shiga aiki na raina fes. Karfe tara daidai na kwaso takardu zuwa cikin hall din da zamu yi meeting din ma'aikata gaba daya, a nan naga Salees sedai kallo daya yamin ya dauke kai ni ma kuma ban kuma kallon sa ba muka shiga abin da ya kawo mu, muna gamawa na koma office dina, karfe biyu nayi na tashi aiki, yau kam ban iya dauke ido daga hanyar gidan mu ba duk da zuciya ta na fada min kar nayi amma wata bangaren na tunzura ni kan naje dan ko na tambayi Salees baze bari ni ba, tun bayan auren Mariya ya dauki wata banzar akidar kulle ya orawa kan sa, har gwara ma ni ina zuwa aiki ita Mariya ba inda take zuwa se ta rufe watanni shida bata fita a gida ba, sau in ta yana kai wa iyayen ta ya'yan ita ce dai se sanda ya so sannan ze kai ta da dare, nima haka se dare yake bari na zuwa gida ko ya kai ni, daga baya ne nake takura masa in wuce daga wajen aiki shima ba ko yaushe yake yadda ba. Ajiyar zuciya na sauke bayan na gama daidaita parking a compound din gidan mu kana cike da matsanancin kewa nake bin ko ina da ido ganin an sake gyara shi yayi kyau fiye da da, gwanin sha'awa ko ina ya sha sabon paint ga kuma shuke shuke masu daukan hankali, ba karamin kokari su yayan mu ke yi ba akan gidan mu shiyasa kullum cikin sa albarkar Abba da Ummi suke, gidan mu babban gida ne tun a da dan Abban mu na cikin masu kudin unguwar mu, compound din gidan mu babbane dan yana daukar motoci sama da biyar, a takaice dai ze dauki mota bakwai ko takwas batare da takura ba, sassa uku ne a gidan mu, bangaren samari wanda yanzu duk sun yi aure, bangaren Abban mu se part din Ummin mu inda a nan muka rayu ni da yayata salima. A hankali na bude kofa na fito me gadi ya washe baki yana min sannu da zuwa haka ma sauran ma'aikatan mu, na amsa a mutumce muka gaisa kana na nufi main falo din mu....................... Ouummey Ouummey 08 {5/6/2023 }