← Book details Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 48

Sashe 27

Rashin Haihuwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

wadda bata wata me kyau bace can amma kuma ba wai ba ta da kyau bane. A compound din gidan Hajiya Farida tayi parking ta fito tana sakin murmushi, Farida ce kawai kawar ta ita ce kuma kadai yar uwar ta haka kuma aminiyar ta, gurbin da Farida ta cike mata ba kadan bane haka kuma halaccin ta gare ta me yawa ne duk da dai ita ce ta fara yiwa Faridan amma ba kowa ke iya rama alkhairi ba. Da sallama ya shiga falon, ihu Hassana ta saki tare da tashi ta nufo ta a guje, duk kai kai kai din da Hajiya Farida keyi be sa ta fasa ba se da ta fada jikin falmatan har da wani dan tsalle kafin ta kankame ta, ita ma sa hannu tayi ta sake ri e ta a jikin ta suna dariya Farida kuwa ta soma fada "Ke dai wallahi ban san yaushe zaki yi hankali ba Hassana, ban da rashin mutunci kayar min da ita zaki yi da zaki dane min ita haka bayan kin san ba wani lafiya ne ya ishe ta ba salan ki cuce ni, to Allah ki ka kuma se ran ki ya baci, bana son shashanci, yarinya ga uwar nauyi kaman buhun shinkafa kawai ki nemi illata min yar uwa". Bata fuska Falmata tayi ganin yadda Hassana tayi rau rau da idanu, "Gaskiya ni dai Farida kina min abinda bana so, kawai shikenan se ba zata zo ga uwar ta ba saboda bani da lafiya, ko kuwa ke kadai ce me yar uwa da zaki ce haka, dan ma kin samu ana yin yar uwar ta ki, to ni dai kiji ma ya'ya na are above anyone, maza matso ki sake yi min oyoyo sweetheart ". Ta fada tana sake bu e mata hannu bayan ta matsa nesa da ita daidai lokacin da Hussaina ta fito daga bedroom suka kuwa kwaso da gudu su duka biyun suka fada kan ta gaba daya suka zube kan kujera suna dariya, ita kam Farida bata kuma bi takan su ba ta cigaba da abinda take yi a kitchen jin yadda Falmata ta gwale ta sedai tana jiyo kyakyacin dariyar su daga nan wadda ta manta rabon da taji dariyar Falmata har haka. Wani irin tausayin ta ne ya sake kama Farida tuno yadda Falmata ke masifar son yara tun suna kanana se gashi Allah ya jarraba ta da rashin haihuwan kuma ta bata mamaki dan bata ta a zaton Falmata zata iya karbar wannan kaddarar ba. Seda ta gama aikin ta sannan ta fito ya same su kamar wasu kawaye "Oya aje a fito da komai a shirya kan dining bari nayi wanka nima". Da haka suka tashi zuwa aikin da aka sa su ita kuma ta wuce wanka aikuwa itama Hajiya Falmata ta tashi ta shiga taya su jera abincin, tare suka yi gaba daya sannan suka wuce wanka suma ita kuma ta zauna kallon wata hira da ake yi da wani mawaki a TV. A shirye suka fito dan tare zasu tafi dukan su zuwa gidan marayu wanda nan ne gidan su Farida da Falmata kasancewar marayun da suka tashi suka budi ido a gidan batare da sanin su waye iyayen su ba, hakan yasa suka riki gidan marayun gida duk kuma wanda ke cikin gidan suka dauke su yan uwa kuma dangi, Hajiya Farida bata ta a kunyar nuna wa ya'yan ta gidan matsayin nasu gidan iyayen ba, a kullum tana alfahari da gidan dan acewar ta ba'a yi musu rikon wulakanci ba. Seda suka karya gaba daya har Falmata sannan suka dungu ma zuwa compound suka shiga motar Hajiya Farida leaving behind motar Falmata a gidan. A motar na hirar su suke yi ita da Farida dake tuki yayinda Hassana da Hussaina ke baya suma suna tasu har suka kai gidan, kayayyakin alkhairin da suka saba bayarwa na kayan abinci duk suka dire haka kuma suka dinga zagaye gidan bangare bangare suna gaisawa da jama'a, da suka tashi tafiya wannan karon Hajiya Farida ce kawai ta bada kudi kamar yadda suka saba dan ita Falmata babu kudi hannun ta. Haka suka yi sallama da jama'a suka koma gidan Farida suka sauke yan biyu su kuma suka sake fita domin tafiya meeting din kungiyar su wadda Farida ta shiga ne kawai saboda Falmata dan kungiyar purpose din ta babu irin su Farida ciki. *NATIONAL ASSOCIATION OF INFERTILE WOMENS* Babbar kungiya ce da ta cika ta tunbatsa da Manyan mata iri iri, kungiya ce da aka kafa ta solely dan matan da basa haihuwa, zaka yi mamaki in ka ga dimbin mutanen dake ashin kungiyar domin ta ha a mata kala kala, manyan masu kudi masu rufin asiri kai har ma d talakawa. An kafa wannan babbar ne domin kwantar wa d matan da basa haihuwa hankali, samar musu da aikin yi da kuma kwatar musu yancin su a inda ya dace, haka kuma domin taimaka su a gurin da suke bu atar taimako. Suna yin meeting din wannan ungiya ne annually ma'ana duk shekara, a nan za'a zauna a ji koken juna, me bukatar taimako ayi mata, sababbin members kuma ayi masu rigister tare da councelling kan abubuwan dake jawo rashin haihuwa, in abin me magantuwa ne suna tsayawa kai da fata har se sun ga an ci nasara da izinin Ubangiji batare da duba da ko nawa za'a kashe ba while the treatment........... Ouummey Ouummey 10 {5/9/2023 }
Chapter 27 · 0% Book details