← Book details Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 31

Sashe 9

Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya waigo yana kallon ta kamar mai yin mamaki,sannan yace"lafiya,bazaki gaida amarya ba?"

Wani watsatstsen kallo tabi amaryar dashi kafin tace"amarya ina gajiya?"

Cikin salon kissa Nadiya tace"gajiya kam babu ita bata da muhalli, saboda na mallaki gwarzon namiji Ni kaÉ—ai,ya zama nawa"

Wani malalacin murmushi Deeja tayi,sannan ta É—aga babban É—an yatsan hannun ta alamar jinjina tace

"Ina taya ki murna,kuma na sara miki babbar mace"tana gama faÉ—in hakan ta É—auki abin da ya kawo ta tayi hanzarin barin kitchen É—in

Abin yazowa nadiya a bazata,don tayi tsammanin zata ƙuntata ran Deejan amma sai taga akasin haka,don haka ta bi ta da ido zuciyar ta cike da ƙunci

Duk da hakan ya ɓata wa Deeja rai amma sai tayi ƙoƙarin dannewa,ta shirya ta karya sannan ta fice zuwa office

Daga office gidan barrister zee ta wuce,zee ta rinƙa tausar ta,tare da ƙara jaddada mata ta riƙi addu'a,kuma sam kada ta daina bawa mijin ta kulawa,anan ta yini har bayan la'asar sannan ta koma gida

A falo ta iske su, Nadiya ta kwanta a jikin shi tana ta zuba masa shagwaɓa,shi kuwa duk yabi ya ruɗe,ta shigo da sallama,amma babu wanda ya amsa,itama sai ta ɗauke kanta da nufin faɗa wa ɗakin ta

"Ke dakata!"a cewar Khalees

Cak ta tsaya batare da ta juyo ba,bai damu ba yace"daga ina kike?"

"Daga office,da na taso sai naga ya kamata na bawa amarya da ango waje su sake,don haka nima nayi nawa wuri"ta bashi amsa

"Tabbas kinyi tunani mai kyau"a cewar Nadiya

Deeja ta kalle ta sannan tace"ai ni koyaushe tunani na mai kyau ne,bana abu mara kyau,ba kamar sauran gama garin mutane nake ba,ina fatan kin gane"bata jira amsar ta ba ta shige É—akin ta

Nadiya tana mamakin Deeja,amma idan ta san wata ai bata san wata ba,dole a haÉ—a da asiri da tuggu don ganin bayan ta,don haka ta É—aga kai ta kalli Khalees cikin kissa tana faÉ—in

"Love da alama gidan ka yafi ƙarfin ka ko?"ya kalle ta cikin kulawa tare da faɗin"me kika gani?"

"Ace kamar ka da kuÉ—in ka da martabar ka amma ace matar ka tana fita aiki?me za'ayi tunani kenan?baka bata abinci kenan fa,wannan ai sai ya zubar maka da mutunci"ta tsare shi da idanu don ganin yanayin shi

Shiru yayi kafin daga bisani ya gyaÉ—a kai yana faÉ—in"zancen ki gaskiya ne love,dole nayiwa tufkar hanci"

Wani sanyin daÉ—i ya ratsa Nadiya,ta sake gyara kwanciyar ta tana faÉ—in"Weldone my love,lallai ka cika jarumin maza"yayi wani murmushin nuna jin daÉ—i yana kallon ta

A É—aki ya samu Deeja tana danne-danne a laptop É—in ta,ganin yadda ya shigo mata fuska babu rahama ya sanya itama ta dake ta sha mur, tun daga amsa sallamar shi bata sake duban inda yake ba,shima bai damu ba ya dube ta yana faÉ—in

"Ban amince miki ki qara fita aiki a gidan nan ba, saboda ba zaman kanki kikeyi ba,da fatan kin gane"yana gama faÉ—in"hakan ya juya ya fice daga É—akin

Ta É—an bi shi da kallo,kafin tayi É—an murmushi,ta sani sarai aikin Nadiya ne,ai kuwa zata basu mamaki

Washegari ta fito cikin shirin riga da zani na lace,ta ɗora ƙaton mayafin ta a kanta, hannun ta rataye da jakar ta

Yau ma kamar kullum a falo ta tarar dasu suna ciyar da junan su abinci,ko kallon banza basu ishe ta ba tayi hanyar fita

"Ke dakata!"taji Muryar Khalees a fusace

Ta juyo fuskar ta babu alamar damuwa,ta zuba masa ido tana jiran mei zai ce

"Ina zakije?"ya tambaye ta

"Idon ta fes cikin nashi ta amsa"in da na saba zuwa,wato wajen aiki"

"To ban bada izini ba"

Ai dama ba kai ka bani izini na fara aikin ba

"To sai ki zaɓi ɗaya,auren ki ko aikin ki?

Maganar ta dake ta sannan ta qara jinjina wa kaidin Nadiya,Amma da yake jaruma ce idanun ta fes cikin nashi kanta tsaye ta amsa"na zaɓi aiki na"

Ba Khalees ba,hatta Nadiya ta tsorata da jin furucin Deeja, Deeja bata kula ba ta juya ta fice daga falon

Da shirin ta ta dawo daga wajen aiki,a nufin ta duk abinda Khalees zai yi mata ta tanadi abinda zata mayar masa,sai dai ko da ya dawo ko kallon sashen É—akin Deejan bai yi ba

A haka rayuwa ta kasance musu har zuwa tsawon sati biyu, Nadiya da umaima babu irin asiri da tuggu da basuyiwa Deeja ba amma a banza,duk da anyi nasarar raba ta da mijin ta, tsakanin ta dashi sai kallo daga nesa,amma Allah ya cire mata damuwar hakan

Da farko su Farida suna kawo mata ziyara suna ɗebe mata kewa,amma sai da Nadiya tayi tuggun da Khalees ya hana su zuwa,hakan bai dame ta ba don sau tari ta kan je gidan hajiyan suyi hira,hajiyar tayi ta mata nasihohi da ƙarfafa mata gwiwa

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 14

A haka har lokacin haihuwar ta yayi,tun safe takejin ciwo,amma hakan bei hana ta fita aiki ba,don ciwon ba sosai yake damun ta ba,sai dai ta sanarwa Aunty Bintu da Aunty kiyya cewa EDD din ta ya cika, kuma ga dukkan alamu zata iya haihuwa yau

Daga wajen aikin ta kai tsaye gidan Aunty Bintu ta wuce,ai kuwa ko mintuna ashirin batayi da zuwa ba ciwo ya buÉ—e mata,aka gaggauta nufar asibiti daita

Sun kai kimanin awa biyar kafin ta haifi sankacecen yaron ta mai tsananin kama da mahaifin shi,sai a sannan hankalin su ya kwanta,Aunty Bintu ta kira kiyya ta sanar da ita,nan da nan tace gasu nan zuwa

Aunty Bintu ta kira Khalees ta sanar masa,amma sai yace bazei samu ɓullo wa ba sai anjuma,yana gama faɗin haka ya kashe wayar

Hakan ya bawa Aunty Bintu mamaki ƙwarai da gaske,sai dai bata sake saurarar shi ba ta zauna jiran su kiyya

Kafin su kiyyan su iso har an shirya baby,ita Kuma Deeja an kai ta ɗakin hutu,su Aunty Bintu suna zaune riƙe da yaron su kiyya suka shigo

Nasir mijin kiyya ne ya kai su,momy Aysha,Mamie babba, nuwaira,lubaisa,sai aunty salma babbar yayar su fauwaz

Nan suka zauna suna kallon baby mai tsananin kama da mahaifin shi,da murmushi a fuskar kiyya tace

"Babyn nan kyakkyawa ne,ya kwaso abban shi da yawa"lubaisa ta leƙa fuskar shi tace"ƙwarai kuwa, Allah ya raya

Basu dauki lokaci ba suka tafi,sai dai sun kawo duk wani abu da suka san mai jego da jariri zasu buƙata

Deeja kam ta sha gata kala-kala,bayan ta nutsu Aunty Bintu ta haÉ—a mata tea ta bata,haka tayi ta kulawa da ita sosai

Sai dai rashin zuwan mijin nata ya ɓata mata rai duk da cewa batayi mamaki ba,amma sai ta bar abin a ranta

Daga asibiti gidan Aunty Bintu suka wuce kai tsaye,har lokacin Khalees bai zo ba,amma hajiyar shi da ƙannen shi sun zo,don a tare suka fito daga asibitin,hajiyance take tausar Deejan,ita kuma Deeja tana nuna mata babu komai

Khalees ko kiran ta a waya baiyi ba sai da ta kwana shida sannan yaje shi da Nadiya,an karɓe su babu yabo babu fallasa ba'a nuna musu wata damuwa ba, Nadiya ta Sha kwalliya amma sai da ta raina kanta da taga su Bintu da su Mima, don itama a lokacin tazo

Mima ce ta kawo musu jaririn,ya ƙura masa idanu yana kallon shi,wata ƙaunar shi tana ratsa shi,a hankali moments da sukayi da Deeja ya fara dawo masa,ya shagala yana ta kallon shi ƙwalla na ƙoƙarin taruwa a kwarmin idanun shi, nadiya tana kallon shi tana ganin ikon Allah,ganin kallon yayi yawa sai nadiya tayi saurin amshe shi tana kallon shi,tace"babyn kyakkyawa kamar baban shi"

Bai fi second goma a hannun ta ba ta miƙawa Mima shi,dama dabarar shi ta raba shi da hannun Khalees

Ya kalli aunty Bintu yace"yanzu sai ayi min list na abubuwan da ake buƙata sai na bayar da kudin ko?"

"Ai ko nawa ka bayar ma yayi"a cewar ta

Sai ya zaro bandir na 50k ya dire mata yana faÉ—in"to ga dubu hamsin"

Abin ya basu mamaki da haushi, amma suka dake,Mima tace"yayi,an gode,sai ka zaɓar wa yaron suna"

Ya miƙe tsaye yana faɗin"ace na bar mata zaɓi,Ni zan wuce, Allah ya raya"

"Ameen,sai anjuma"a cewar Mima suka É—auki kuÉ—in suka fito, suma su Khalees suka biyo bayan su, zuciyar Nadiya kamar ta fashe don baqin ciki,ta so tsiya ta tashi, dama ita ta yanke nawa Khalees É—in zai bayar,amma kuma idan sun san wata basu san wata ba

A cikin mota nadiya ta kalli Khalees tace"honey, gaskiya wadannan mutanen basu da mutunci da alama"

Ya kalle ta yana faɗin"me kika gani?"tace "don Allah kalli abinda sukayi mana,suna magana sai wani ciccin magani sukeyi,ga ƴar wulaqancin ko ƙeyar ta bamu gani ba,kuma ka bayar da kuɗi amma an kasa yi maka godiyar da ta dace, maganar gaskiya bakayi dacen mata ba"

Yayi É—an shiru yana nazari,ganin ya É—auki lokaci baiyi magana ba ya sanya ta faÉ—in"bakace komai ba"

Ya amsa mata da cewa"ai na riga na tanadi hukuncin da zan yanke tuntuni,don ta gama fitar min a rai,gashi ko ke shaida ce bata jin magana ta,kuma kalli irin wulaqancin da tayi mana,ta nunawa duniya Ni ba komai bane a wajen ta,don haka dole nayiwa tufkar hanci"

Wani sanyi ya ratsa Nadiya,amma sai tace"No Kar kayi saurin yanke hukunci,ina da shawara"

Ya kalle ta yana faÉ—in"menene shawarar ki?"

"Why not bazaka saka wa yaron sunan dad ɗi na ba?"ta ƙarashe tana tsare shi da idanu

Batayi mamakin É—an murmushin da yayi ba,yace"good idea,haka za'a yi"

Shiru tayi tana kallon shi fuskar ta É—auke da murmushi,a ranta kuwa yabawa takeyi da aikin bokan ta mai faÉ—a da cikawa

Waya ya ciro ya danna number din Deeja,wadda rabon da ya kira ta har ya manta,a da yayi saving number din da luvly Deeja,amma Nadiya ta mayar da sunan Khadija

Bugu É—aya ta shiga,a lokacin tana zaune tana kallon su Mima da suke ta surutun wulaqancin Khalees ita da intisar da Farida matar yaya Ma'aruf,ta san za'a rina,shiyasa batayi mamaki ba

Wayar ta ce ta soma ruri,ta kai hannu ta É—auka,ganin sunan Khalees ta tsaya tana kallon wayar da mamaki,amma dai sai ta É—aga

"Assalamu alaikum"tayi masa sallama

"Wa'alaykis salam,sannu uwar isassu"

Tayi shiru zuwa can tace"ina wuni!"

"A'a riƙe gaisuwar ki,na gode da wulaqanci,sannan da na bar miki zaɓi,amma yanzu na fasa"
Chapter 9 · 0% Book details