Sashe 7
Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk yadda yayi ya kwace kanshi yaci tura,ta damƙe shi cikin fitar hayyaci tana faɗin"macuta! azzalumai!!mugaye!!!me nayi muku?dama nasan bazaku ƙyale ni ba,dama nasan sai kunyi min haka, Allah ya fi ku!"haka tayi ta sambatu cikin fitar hayyaci wanda Khalees ba fahimta yakeyi ba, ƙoƙarin shima ya ƙwaci rigar shi da ta cukwikwiye
Allah ya bashi Sa'a,yana ƙwace rigar tashi kuwa yayi harabar gidan a a guje, Deeja kam yaraf ta faɗi ƙasan tiles tana mayar da numfashi,amma har yanzu idanun ta babu hawaye,amma sun tsumu da tashin hankali
Shi kam Khalees cikin azama ya nufi motar shi,yana shiga ya fara yiwa mai gadi horn,cikin azama ya É—aga gate É—in,har yayi gaba ya dawo ya cewa mai gadin
"Ko da yaya kar ka bari matar gidan nan ta fita,idan kayi wannan kuskuren to a bakin aikin ka"yana gama faÉ—ar haka ya ja motar shi ya bar wajen zuciyar shi cike da tashin hankali
Cikin tsananin gigita Deeja ta yunÆ™ura ta miÆ™e zata fice daga É—akin,wayar Khalees tayi Æ™ara,babu dogon tunani ta É—auki wayar ganin sunan my heartbeat da emoji na heart â¤ï¸,tayi gaggawar É—agawa amma bakin ta É—auke da sallama
Daga can ɓangaren taji anyi shewa gami da faɗin"MATAR KHALEES a yanzu"
"Wacece?"Deeja tayi ƙarfin halin tambaya
"Upcoming MATAR KHALEES,don ki sani Khalees nawa ne Ni kaɗai,muddin na shigo gidan nan babu wata mace da ta Isa ta ko da kalle shi ne,amma a yanzu dai na baki aron shi kafin in shigo......"jin bazata iya jurar abinda matar ke faɗi ba ya sanya ta saurin datse kiran,ta miƙe a gigice ta janyo mayafin ta ta yafa,ta nufi harabar gidan ko ganin gaban ta batayi
Sai dai duk yadda taso malam Audu ya bar ta ta fita hakan ya ci tura,nan da nan ta fara wani irin haki wanda sai da ya kai ta ƙasa
Ma'aikatan gidan ne suka nemo Khalees a waya,dama ba nisa yayi ba,ai kuwa sai gashi yazo,cikin sauri ya sanya ta a mota ya umarci driver É—in shi da ya kai su asibitin Dr su'ad
A can asibiti Dr su'ad da wasu manyan likitoci suka rufu akan ta,sun kai awa guda suna abu É—aya, Khalees sai kai wa da kawowa yakeyi cikin tashin hankali da damuwa,ya san zancen auren shi ne ya tayar wa da Deeja hankali har haka, amma bayajin zai iya janye maganar auren,da zai iya da ya janye
Yana tsaye Dr su'ad ta fito fuskar ta babu walwala,yana ganinta sai da yaji gaban shi ya faÉ—i,ta kalle shi tace"engineer Abdul biyo ni"babu musu ya bi ta,amma zuciyar shi cike da taraddadin abinda zata ce,yasan ko menene ba mei daÉ—i bane
Suna shiga ta nemi waje ta zauna, shima ta nuna masa wajen zama,ya zauna yana sauraron abinda zata ce
Ta zare glass É—in idanun ta tana kallon shi tace
"Wato da farko munyi tsammanin ciwon Deeja ya tafi tun bayan dawowar ta daga Spain,duba da cewa zaka kula da lafiyar ta,sai dai kuma abu ya chanja ba kamar yadda muka zata ba,ciwon Deeja yana nema ya dawo sabo,ga cikin ta da yake barazanar fita, gaskiya Khalees idan baka kula ba zaka iya rasa Deeja da abinda yake cikin ta baki ɗaya,don haka ka kula"tana gama faɗin haka ta miƙe ta fice daga office ɗin
Faɗar irin tashin hankali da Khalees ya tsinci kanshi a ciki ma ɓata baki ne,ji yake a ranshi dai da yanda zai yi da yayi ya fasa auren,amma ina!ji yake idan bai auri Nadiya ba zai iya mutuwa,yayi tagumi da hannu bibbiyu yana tunanin mafita
Ganin bai samu komai ba ya tilasta masa miƙewa,jikin shi babu ƙwari ya fito daga office ɗin,yana fitowa wayar shi ta soma ƙara
Da yayi niyyar share ta,amma sai ya É—auko ya duba,fareeda ce
Cikin sanyin jiki ya ɗaga, Farida ce ta soma magana"bros meke faruwa ne?ina ta kiran ka amma kaƙi picking"
Cikin Muryar tashin hankali yace"Farida ina cikin damuwa, luvly Deeja tana kwance a nan asibiti bata san in da kanta yake ba"
"Innalillahi wa Inna ilayhi rajiun!me ya same ta?"a cewar Farida cikin ruÉ—ewa
"Ciwon ta ne ya tashi"a cewar Khalees cikin rawar murya
A gigice Farida tace"wane irin ciwo ne da ita?"
"Heart attack ne"ya bata amsa
"Subhanallahi!gamu nan zuwa"ta kashe wayar
Yana zaune a reception abin duniya ya dame shi suka ƙaraso,har da Hajiya da ƙanwar shi mai bin shi Aunty sameera,suka ƙaraso fuskokinsu babu annuri kowacce ta nemi waje ta zauna
Sun É—an yi shiru na Æ´an sakwanni kafin hajiya ta dubi Khalees cikin É—aurewar fuska tace
"Me nakeji haka ne?wane irin baƙin labari Farida ke sanar dani ne?"
Shiru Khalees yayi,kafin ya fara maganar cikin rawar murya
"Hajiya ciwon ta ne ya tashi"
"Me ya tayar mata da ciwo?"ta faÉ—a tana tsare shi da idanu
"Eh.......to........dama.......dama....zancen a...auren nawa ne"yayi shiru cikin damuwa
"Wai auren dole ne yin shi?"ta faÉ—a cikin É—aga murya
Khalees ya kwantar da murya yace"amma hajiya ya kamata kiyi min uzuri,dukkan ku kun so ace na auri zaɓin raina,amma hakan bei yiwu ba sai yanzu"
Hajiya ta girgiza kai tace"tabbas a da naso ka auri zaɓin ran ka,amma banda yanzu,ko a lokacin da naso ka auri zaɓin ran naka naso hakan ne saboda rashin dacen zaɓa maka mata da abban ku keyi maka,amma yanzu alhamdulillahi,an samu dace,to meye na ƙara auren kuma?"
"Don Allah Hajiya ku taimake ni ku bari nayi auren nan, wallahi idan har banyi ba zan iya mutuwa,ina matuƙar son Nadiya"
Har hajiya ta buÉ—e baki da zummar yin magana sameera ta kaÉ—a mata ido tayi shiru
Sun samu ganin Deeja, hankalin ya tashi ganin yadda ta rame lokaci É—aya,sai É—an cikin ta da shima ya rame,cikin sanyin jiki suka fito suka nufi gida
Suna tafiya akan titi,sameera ce mai tuƙi,sai hajiya a gefen ta,sai Farida da Jannat a baya,sameera ta kalli hajiya tace"hajiya dole fa ki ƙara ƙaimi da addu'a, alamu sun nuna akwai hannu cikin lamarin yaya Khalees"
Hajiya ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tace"Ni kaina zargin da nakeyi kenan surayya,kuma babban abin takaicin da mahaifin shi yaƙi mara masa baya ya nemo matar aure amma yanzu don Allah ji ya amince da wannan auren,kuma wallahi tausayin yarinyar nan nakeyi,don bansan me amaryar nan tazo dashi ba,amma kuma ai akwai Allah"
"Hakane,inji Aunty sameera"Allah ya shige mana gaba"suka amsa da "ameen"
Sai da Deeja ta samu awa shida sannan ta dawo hayyacinta,a firgice ta farka tana ƙoƙarin ficewa daga ɗakin da aka kwantar da ita, Dr su'ad da ta shigo yanzu tayi saurin kwantar da ita tana fadin"Ina zakije ne?"
Ta kalli Dr su'ad da rinannun idanun ta tace"Dr rabu da ni kawai"ta ƙarasa tana ƙoƙarin zame hannayen ta daga na Dr ɗin,kuma a lokaci guda tana ƙoƙarin miƙewa tsaye
"Cool down madam,me yayi zafi haka?don Allah ki bi komai a sannu,komai zei warware in Sha Allah,Amma wannan zafin ran da kike nunawa ai bashi da wani amfani ko?"
Cikin Muryar ɓacin rai tace"Dr duk bayanin da zanyi miki baza ki gane bane,kawai ki bar ni naje in da zanje"
"No bari na sanarwa engineer,don bazan kwana a ciki ba"
#Nusy bee
*****MATAR KHALEES*****
âœï¸ Nusy bee
Page 11
Kafin Deeja ta kuma cewa wani abu ta zaro waya ta fara kiran Khalees,ganin kiran doctor su'ad ya Sanya shi azamar É—aga kiran,yana É—agawa tace"kazo É—akin da aka kwantar da Madam É—in ka"bata jira amsar shi ba ta kashe kiran
Minti biyu tsakani sai gashi ya shigo cikin sauri,ganin ta a zaune yayi saurin nufar ta,amma ta dakatar dashi cikin ƙaraji
"Kar ka ƙaraso in da nake Khalees,kar ka soma, Wallahi na tsane ka macuci, mayaudari, azzalumi,wanda bei san darajar mace ba,wallahi abinda kukayi min sai Allah ya saka min,don bazan taɓa yafe muku ba, munafukai annamimai,kuma na gama auren ka,dole ka sake ni,maƙaryaci kawai"idanun ta sun kaɗa sunyi jawur,amma ko ɗigon hawaye babu,don dama can ita ba mai saurin kuka bace
Ba Khalees ba,itama Dr su'ad abin ya ɗaure mata kai,suka shiga bin ta da kallo, Dr su'ad ta matsa kusa da ita tana faɗin"haba malam!mijin ki ne fa,a ƙalla ya samu wannan alfarmar ko?"ita kanta Dr jikin ta rawa yakeyi, ballantana Khalees da ya shiga mummunan tashin hankali
Deeja ta ƙarasa zare hannun ta gami da faɗin"a da yake amsa sunan miji a waje na,amma a yanzu"ta girgiza kai gami da miƙewa tsaye
Duk yanda suka so Deeja ta saurare su hakan yaci tura,a ranar Khalees yaga ainihin kalar matar shi,dole suna ji suna gani ta fice daga asibitin
Bin ta sukayi da kallo,tana fita Khalees ya lallaɓa ya bi bayan ta,napep ta tsare,ta shiga, shima ya shiga motar shi ya bi su
Kai tsaye gidan Aunty Bintu ta nufa,mai adaidaita sahun yayi parking, wajen mai gadin ta ranci kuÉ—i ta sallami mai adaidaitan,sannan ta shiga cikin gidan
Khalees ne ya fito daga motar shi ya baiwa mai gadin maƙudan kuɗaɗe,mai gadin ya fara godiya,yayi saurin dakatar dashi yace"kuɗin da Deeja ta karɓa a Wajen ka ne,ragowar kuma ka riƙe"yana gama faɗar hakan ya koma cikin motar shi ya tayar ya tafi
Deeja kuwa a hargitse ta shiga cikin gidan,intisar tana zaune a falo tana buga game a wata Deeja ta shigo
Cikin tsoro da mamaki intisar ta tare ta tana faÉ—in"sannu da zuwa,lafiya Aunty Deeja?"don ta san Deeja da nutsuwa
Deeja ta kalle ta da rinannun idanun ta tace"ina Aunty Bintu?"
"Ta tafi dubiya,ɗan wata ƙawar ta aka kwantar a asibiti"
Deeja ta nemi waje ta zauna tana sauke ajiyar zuciya,ita dai intisar kallon ta kawai takeyi a É—imauce,zuwa can Deeja ta kalli intisar tace
"Kina da É—ari biyar?"
"Eh,amma dubu É—aya ce"
"Babu laifi,kai wa baba mai gadi ki ce ya ɗauki kuɗin shi"babu musu intisar ta miƙe ta nufi harabar gidan,jim kaɗan ta dawo ta shaidawa Deeja cewa baba mai gadi yace wani ya biya kuɗin
Sai da gaban Deeja ya faÉ—i,don bata raba É—ayan biyu Khalees ne, saboda tayi zargin ya biyo ta,amma sai bata nuna ba,sai ma kwanciya da tayi tana tunanin mafita
Intisar bata sakeyi mata Magana ba,ta koma kan computer ta cigaba da danne-dannen ta
A haka suka kasance har sanda aunty Bintu ta dawo,da sallama ta shigo falon