← Book details Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 31

Sashe 25

Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin duk masu nuna min soyayya da tausayawa sun janye daga gare ni, ba'a maganar dangin mahaifi na da muke rayuwa gida É—aya amma duk da haka abinda zan ci sai sun ga yunwa tana neman kwantar dani suke san min, ba'a yi shekara guda da mutuwar baba ba na daina zuwa kowacce makaranta, don sharaÉ—i Æ´an gidan mu suka saka min, sharaÉ—in cewa sai na É—auki talla tukunna za'a bani abinci,babu musu na amince don bani da wata mafitar bayan wannan

Kusan kowa a gidan nan yana ɗora min talla,masu iymani a cikin su ne ke bani abinci,amma wasu cikin su yadda na siyar na kawo musu kuɗin su haka zasu cafke batare da sun yi min ko godiya ba, ballantana na saka rai da abincin,idan kuwa ƙwandala ta ɓata a kuɗin ina cin mugun duka irin na rashin gata,wasu ma sai suyi ta rantsuwar sai na biya su

Sutura kam idan aka ganni da ita to wasu bayin Allahn ne sukaji tausayi na suka bani kunce,tunda mahaifi na ya rasu ba'a sake yi min sabon ɗinki ba,nayi ƙanƙanta da yawa ballantana nayi tunanin ko da sana'a,Ni ba ƙawaye ko abokan wasa gareni ba,tallar da aka ƙaƙaba min shine aboki na,an sha kawo min farmakin lalata rayuwa ta amma Allah yana tsare Ni

Shekaru na goma sha uku,a lokacin rayuwa tayi min ƙunci sosai, kullum aikin ɗaya ne na ɗauki talla na fita,a lokacin na fara dabarar idan yunwa ta ishe ni na sauke kwanonin abincin na rarrage a leda na samu wanda zanci,har na fara rarrage abincin ina siyarwa ina samun ɗan kuɗin kashewa batare da sanin masu ɗora min talla ba

Ina da shekaru sha biyar muka haɗu da Najeeb,a lokacin sun zo garin nan aiki a wani asibiti, ciwon mara na al'ada ya riƙe Ni a hanyar dawowa ta daga siyar da dambun da nayi

A yashe suka ganni a gefen hanya na dafe ciki ina murƙususu,gefe kuma kwanukan abincin da na siyar ne, Najeeb ne da kanshi ya ɗauke Ni ya saka Ni a Mota muka nufi asibitin da suka kawowa ziyara

Da kanshi ya duba ni ya bani magunguna,da na dawo hayyacina sai na kasa zaman asibitin,nayi ta kuka sai da ya mayar dani gida

Sai dai kafin muje gida ya biya ta shago ya siya min kayan ƙwalam da maƙulashe,da kayan shayi sannan ya bani kuɗin da ban taɓa ganin irin su ba yace na kashe matsalar gaba na

Da farko na tsorata,har na ƙi amsa,amma da ya nuna min shi kawai taimako na yayi sai nayi ta masa godiya,na kwashi kayana na kai ɗaki sannan na mayarwa mai dambu kwanukan ta da kuɗin dambun ta

Daga lokacin na daina talla,dama don abinda zanci ne nakeyi,yanzu kam wannan ya kau,amma ban koma makaranta ba,sai dai na kasa cire wannan saurayin da ya taimake ni a raina

Kusan watanni biyu Najeeb ya dawo,nayi farin ciki sosai,amma sai ya tambaye Ni dalilin talla bana zuwa makaranta ban ɓoye masa komai ba na bashi labarin kaina,ya tausaya min sosai,yace to mai zai hana na bishi ya kaiwa umman shi ni?don bata da ƴa mace,kuma nima ina buƙatar kulawar uwa a shekaru na,sannan zai mayar dani makaranta

FaÉ—ar hakan da yayi yasa ko musu banyi ba na amince,washe gari babu wanda nayiwa sallama na biyo Najeeb muka nufi kano

Babu laifi maman shi ta tarbe ni da kulawa,aka bani É—akin da na ganni tamkar amarya, saboda kyan shi da tsaruwar shi

A gidan su Najeeb na samu Æ´anci sosai,abinda naso shi nake ci,sutura sai wadda na so zan saka,gashi kuma ya sanya Ni a tsadaddiyar makaranta,ya É—aukar min lesson teacher

Ban É—auki lokaci ba nayi wani irin haske,nayi kyau sosai,sau tari haka Najeeb zai yi ta kallo na kamar wani wawa,wani sa'in har kunya yake bani

Shekaru biyu da dawowa ta kano,babu wanda zai ganni yace na taɓa yin rayuwar ƙauye, amma kuma a kullum umarnin Najeeb nake bi,ya hana ni kula ƙawaye,sai Nadiya da aƙalla zata bani shekaru biyar zuwa sama, Nadiyan ce take haɗa ni da ƙawayen ta,ƴan gayu ne sosai, rayuwar su tana matukar burge ni

Rana tsaka Najeeb yace nazo na raka shi unguwa,sai dai maimakon unguwa hotel ya nufa dani,anan yake gaya min manufar shi ta shekara da shekaru,na tsorata sosai,sai dai ya nuna min zaɓi biyu gare ni,ko dai na amince da buƙatar shi ya nuna hidimar da yake min,ko kuma naƙi amincewa ya mayar dani in da ya ɗauko Ni, hankali na ya tashi sosai,ba tsorata matuƙa da makircin Najeeb,yace ya bani nan da gobe na yanke shawara,ko na yarda dashi ko na koma gidanmu,daga nan bai jira komai ba ya ɗauko Ni ya dawo dani gida

Nadiya na kira ina kuka nace don Allah tazo ina son ganin ta, Kasancewar duk wannan abin da akeyi Najeeb ya saka min doka mai tsanani,bana fita sai ya san in da zanje,don haka idan naso ganin Nadiya sai dai na kira ta,ita kuma babu ɓata lokaci tazo,yanzun ma haka akayi,cikin ƴan mintuna tazo

Ɗaki na na ja ta cikin kuka na sanar mata yadda mukayi da Najeeb,ga mamaki na sai naga ta kwashe da dariya,tace"Ni wallahi har kin bani tsoro,yanzu akan wannan minor problem ɗin zaki wani tattago ni?to shikenan kar ki amince,sai ya mayar dake can ƙauyen,a banza za'a yi miki fyaɗe a yasar dake a titi a wulaƙance,kowa yana kallon ki a yatsine,amma idan kika amincewa Najeeb ko babu komai zaki ga tarairaya da kulawa, kuma cikin farin ciki zaki rayu"

Cikin kuka nace"to me zai hana ya aure ni?idan yaso ko ma menene sai yayi dani"wani kallon rainin wayo Nadiya tayi min tace"lallai na yarda yarinta ke damun ki,Malama idan zaki saki jiki ki saki jiki,wanne aure kuma ana zaune ƙalau?ki bar wani batun aure har ki kammala makaranta,amma yanzu kiyi rayuwar ki"haka tayi ta min zuga tana kawo misalai har na yarda na amince"umaiman ta rufe fuskar da tafin hannun ta tana kuka mai soya rai, Afra ma kuka take har da shashsheƙa, Deeja ce dai kukan ya ɗauke sai ajiyar zuciya take saukewa,daidai nan aka tsuge da ruwan sama,da sauri Umaima ta miƙe ta saki asabarin ɗakin da windon ɗakin sannan ta koma ta zauna,sai da ta daidaita nutsuwar ta sannan ta cigaba

"Washegari Najeeb yaje É—auko ni daga makaranta,a hanya yake tambaya ta,me na yanke game da maganar jiya?a sanyaye nace masa na amince,sai naga fuskar shi ta faÉ—aÉ—a da murmushi,yaja hanci na yana min godiya

A taƙaice dai,a ranar Dr Najeeb ya fara sani na ƴa mace,ya gama wulaƙanta rayuwa ta,amma ya kula dani sosai,ya tarairaye ni kamar sabuwar amarya,daga hotel ɗin da ya kai ni ya wuce dani ƙaton store ya siya min sababbin kaya da kayan kwalliya da kayan ƙwalam,ya sake min Sabuwar waya,ya kai ni tsadadden eatry yayi min order na favorite ɗi na, sannan ya mayar dani gida. Ni da ya kamata ace tun biyu da rabi ina gida ban koma ba sai biyar,amma umma ko uffan ba tace min ba, gani na cikin yanayin damuwa ma bai saka ta tambaye ni komai ba"Umaima ta kuma yin shiru tana share hawayen ta

Bayan ƴan sakwanni ta cigaba"duk lokacin da ya kwanta dani yana bani wata ƙwaya, ashe ta hana ɗaukar ciki ce,tun ina jin tsoro ina ɗari-ɗari har na saki jiki,wani lokacin ma nice nake kai kaina gare shi, a haka muke kasance har tsawon shekaru biyu

A lokacin ina da shekaru goma sha tara da haihuwa,a shekarar ne na gama secondary School É—i na,kuma still a shekarar ne Najeeb ya jefa Ni a rayuwar Imran

Da farko bai gaya min shirin shi akan Imran ba,nasan dai yana yawan kira na ko yace nayo girki kala kaza na kawo masa,sai da ya samo kan Imran yake shaida min so yake na aure shi

Da farko ban so ba,amma Najeeb ya nuna min wannan itace mafita dole,da haka ya samu na sauko na fara kula Imran,kuma cikin ɗan ƙanƙanin lokaci Allah ya jarabce ni da son shi

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 35

Komai zanyi sai nayi shawara da Najeeb,da farko naso na auri Imran lokacin da ya aure ki na zauna lafiya da ke,ko babu komai zan samu sauƙi daga Najeeb,don har a lokacin bana ƙaunar yadda yake kwanciya dani,wani lokacin ma a ɗaki na musamman idan mahaifiyar shi bata nan

Amma sai Najeeb yayi ya zuga Ni har naji nima na tsane ki,naji bana buƙatar zama da koma wacece wadda akace Imran ya aura

Ban tashi sanin Najeeb shaiɗani bane sai da aka tashi auren mu da Imran,don zama na musamman yayi dani ya shaida min adadin kuɗaɗen da zan rinƙa tatso masa a hannun Imran,da kuma cewa har gobe duk sanda ya buƙace ni zan zo,na tsorata sosai, kuma na shawarci Nadiya, Nadiya ta nuna min ba wata matsala,kuma hakan ta kasance,duk sanda Najeeb ya neme Ni zan san dabarar da zanyi naje gare shi,gashi kuma har lokacin bai daina bani maganin hana ɗaukar ciki ba

Deeja,abinda baki sani ba shine,bani ce naso Imran ya rabu dake ba,shima Imran bai so rabuwa da ke irin haka ba,duk shirin Najeeb ne,mafi girman laifin Imran shine bakin shi baya shiru, kullum a asibiti bashi da magana sai taki da irin ƙauna da sadaukarwar da kikayi masa,wannan shine dalilin da ya jefa tsanar ki a zuciyar Najeeb, Nadiya ma sai daga baya na gane ƙawar Najeeb ce, saboda tsanar da yayi miki ya tura ta rayuwar ki ta san yadda zatayi ta auri mijin ki Khalees don ta ƙuntata miki

Da farko bansan hanyar wajen boka ba, Amma a sanadin Nadiya na sani,ba don kaina ba sai don buƙatun ta,a tsawon zama na da Imran ban taɓa kai shi wajen boka ba,amma Nadiya ta saka Ni na kai ki, na kai Khalees, na kai mahaifiyar shi da ƴan uwan shi

Bayan Khalees ya sake ki kinyi ɓatan dabo Imran yazo ya tuhume ni,na nuna masa bansan zancen ba,duk da ina zargi biyu a lokacin, ko dai ke kika ɓoye kanki ko kuma Nadiya ta ɓatar dake,don na santa,hatsabibiya ce ta gaske
Chapter 25 · 0% Book details