← Book details Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 31

Sashe 10

Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To ba laifi,wanne suna ka zaɓa masa?"ta tambaye shi babu alamun damuwa a tare da ita

"Sa'eed nake so a saka masa"

"Kamar sunan mahaifin Nadiya"ta faɗa da mamaki da ɓacin rai

"Eh,haka nake buƙata"

"To bazan sanya ba,idan tayi zuciyata haifi nata ta sanya"tana gama faÉ—in hakan ta kashe wayar baki daya tana masifa

Su Mima suka mai da kallon su kanta,ta kalle su tana faÉ—in"kunji wai sunan mahaifin Nadiya zaa saka?"

"Kamar yaya sunan mahaifin Nadiya?ba cewa su Aunty Bintu yayi ki sanya sunan wa yaron ba?"cewar Aunty Farida cikin mamaki

"Ya chanja shawara,wai na saka sunan baban matar shi, saboda ni daga sama na faɗo bani da uba"ta ƙarashe tana watsa hannayen ta a iska

"Kan bala'i!lallai ma wannan mutumin ya cika É—an rainin hankali,to me ya mayar da ke?sokuwa ko me?"a cewar Mima cikin fushi,dama a cikin family É—in su Mima tana daya daga cikin masifaffu

Murmushin takaici kawai Deeja tayi,don tafi zargin akwai abinda Nadiya tayi masa yakeyi mata haka

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy_bee

Page 15

Ranar suna an sha shagali,yaro ya amsa sunan Mahmud,sunan mahaifin Deeja, amma Mima ta ɓoye sunan da Affan,anyi hidima sosai,mai jego ta sha ado cikin manyan kaya kala-kala ita da jaririn ta, wasu ita ta siya,da yawan su kuma siya mata akayi,don daga gidan professor Ismail an kawo mata sama da kala ashirin kayan fitar suna,banda na jaririn ta ma,ga su Aunty Bintu,hidima dai sai son barka

Har da umaima akazo suna,sarai sun gane cewa leƙen asiri tazo yiwa Nadiya,don haka Deeja ta zage gayu da facaka iri iri,mai make-up din da tayi mata lokacin bikin mijin ta da nadiya ita Aunty Bintu ta sake ɗauko mata,ga sutura masu asalin tsada da ɗinki mai kyau,ga adon gold abin sai son barka,ga cima kala-kala sai wanda Mutum ya zaba,ba umaima ba kaɗai,hatta da lubaisa sai da ta raina kanta

Umaima bata wani dade a gidan sunan ba ta tafi gida,tana komawa ta kirawo Nadiya ta shaida mata abinda ya faru a gidan sunan, Nadiya taji takaici sosai don so tayi ace Deeja ta wulaƙanta,amma wai umaima ke sanar mata yadda Deeja ya haska kuma ake tarairayar ta a wajen sunan,don haka tace

"Ƙyale ta umaima, alƙawari fa na ɗauka,sai na rusa mata farin ciki,zata san cewa da ni Nadiya gagari kowa takeyi,sai na nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane,sai na sanya ya ɗora hannu aka na rasa mafita,don wallahi sai na sauke mata wannan ji da kan nata,sai tayi data sanin zuwa duniya"ta ƙarasa cikin ɗaukar alwashi da ɓacin rai

"Wallahi ina bayan ki,ke dai kawai ki shirya,dole mu komawa boka"a cewar umaima

"Ai haka za'ayi kawai,don naga alama tana ɓata min aiki,kuma idan nayi mata baya kama ta"

Umaima ta jinjina kai tana fadin"wannan ai mei sauƙi ne,tunda kin gama da wanda take taƙamar ai shikenan"

"Ke dai bari kawai umaima,duk da na raba su harkar gaban ta kawai takeyi,ko kaɗan bata da damuwa,kuma ya kasa kataɓus akanta"

"Keep on trying, watarana zakiyi nasara"a cewar umaima,tana mai ƙarfafa mata gwiwa"

"Har sai kin faÉ—a?ai na riga na gama yanke abinda zanyi mata na samu ta fita daga rayuwa ta"

"Okay!to Sai na jiki"suka kashe wayar

Taro ya tashi lafiya, hankalin Deeja ya kwanta sosai,don yadda aka tarairaye ta aka nuna musu kulawa ita da jaririn ta ya sanya ta kuma sakin ranta,rashin damuwa da al'amarin ta da Khalees yakeyi kwata-kwata baya danun ta,don ta sani ba yin kanshi bane,kuma bata taɓa fashin saka shi a adduoin ta ba

Gyara sosai aunty Bintu tayi mata,ga ƙara wayar mata da kai da takeyi, kullum cikin tofe ɗan ta da adduoi kala-kala take,kuma dare da rana bata gajiya da yiwa mijin ta addu'a,tare da addu'ar Allah ya bayyana mata yayyen ta,tana son zuwa Yola amma fargaba ta hana ta

Watan ta guda amma har lokacin bata koma gidan auren ta ba,sai dai ta koma bakin aikin ta,Affan kuwa yayi kyau yayi ɓulɓul abin shi,kamannin shi da Khalees sun ƙara fitowa sosai

Zaman Deeja a gidan Aunty Bintu ya taimaka ƙwarai wajen tafiyar da kaso mai yawa na damuwar ta,ta nutsu sosai tana aikin ta,tana son komawa makaranta don ƙaro karatu amma tana tsoron tunkarar Khalees da batun,don haka taga gwara ta haƙura kawai,har sanda al'amura zasu daidaita

Don haka ta cire damuwar komai a ranta,ta riƙi aikin ta da yaron ta sosai

Watanni biyu suka shuÉ—e,Deeja tayi kyau tayi haske sosai,a lokacin sati biyu ya rage su Aunty Bintu su tafi kasar Syria,don haka Deeja ta fara shirin komawa gida

Ranar da zata koma Aunty Bintu ta aika aka gyara mata É—akin ta,nadiya na zaune tana jin kiÉ—a sai ga su intisar sun shigo da sallama

Su shida ne,intisar,ilham ƙawar intisar sai masu aikin Aunty Bintu su huɗu

Sheƙeƙe ta kalle su sannan ta zare airpiece ɗin kunnen ta tana kallon su a wulaƙance,cikin isa da gadara tace "ku kuma fa?daga ina?"

Intisar ta kalle ta sama da ƙasa tace"yi haƙuri,ba wajen ki muka zo ba,kin gane?"tana gama faɗin haka tayi wucewar ta ciki,suma sauran suka biyo bayan ta

Nadiya ce ta biyo bayan su tana faÉ—in"maza maza kuzo ku fice min daga gida,matsiyatan yara kawai"ko kallon ta basuyi ba suka wuce suka kama aikin su

Basu juma sosai ba suka koma gida,suka zayyane wa Auntyn Abinda Nadiya tayi musu amma suka mayar da ita mahaukaciya,sukayi ta dariya

Da yamma su Aunty Bintu suka raka Deeja gidan ta tamkar masu kai amarya, nadiya ta tsorata sosai ganin dawowar Deeja,ganin Deejan babu alamun damuwa a tare da ita ya firgita Nadiyan,amma sai tayi tsammanin ko ta san da tafiyar da Khalees yayi ne, kasancewar Khalees yaje wata seminar a Abuja jiya,Kuma bazai dawo ba sai bayan sati uku

Su Aunty Bintu suka gama abinda ya kawo su suka tafi, Nadiya na ganin sun tafi sai tayi azamar shigowa

Deeja na zaune tana shayar da Affan Nadiya ta shigo,kallo É—aya tayi mata ta É—auke kanta,don ta san ko ma menene ya kawo ta ba na arziki bane,don ko sallama batayi ba. Nadiya ta dube ta a wulakance tace

"Ai dole ki ɗauke kanki,don ni na baki damar shigo min gida har zan shigo in da kike ki ɗauke kai,wato kinji labarin miji na baya nan ko?hakan yayi kyau,amma ki shirya karɓar tanade tanade da nayi miki......."

Karatun Alkur'ani Deeja ta sanya,ta janyo airpiece ta saka a jikin wayar ta toshe kunnuwan ta dashi hakan ne ya tilasta wa nadiya ficewa daga É—akin tana jan tsaki,a ranta tana ayyana ko me zatayi sai tayi don ganin ta kuntatawa Deeja

Daga lokacin ya zamana kowa harkar shi yakeyi,sai dai Nadiya ta tsani ta buÉ—e idanu taga Affan,ta tsani yaron tsana mafi munin,don haka ta sha alwashin sai taga bayan shi,har da uwar tashi ma

Har da zan ɗauki hutun ma'aikata na yau nima,kawai sai nayi tunani na fasa😁😉

Ayi min afuwa biki mukeyi shiyasa akaji ni shiru

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Kwanan nan fa sai ana min uzuri 😅 saboda ciwo na da yake yawan tashi yana buƙatar hutu,still ayyuka sunyi yawa,gashi nan dai gashi nan dai,duk da haka ina godiya kuma at the same time Ina neman afuwa 🙏

Page 16

Sai dai bata samun damar,hakan, saboda Deeja bata taɓa barin Kofar dakin ta a buɗe matuƙar ba fitowa zatayi ba,kuma indai zata fita goya shi takeyi ko ta datse ɗakin

Kwanan ta tara da dawowa da yamma bayan tayi sallar la'asar tana zaune tana gyara kayan Affan a taji ƙaurin miyar da ta ɗora,da sauri ta miƙe ta fito ta gyara miyar sannan ta koma ɗakin ta

Tun kafin ta ƙarasa ɗakin taji Affan ya canyare da kuka,da gudu ta ƙarasa don ta san bacci ta fita ta bar shi yanayi

Abinda ta gani ne yayi matuƙar gigita ta, Nadiya ce take shafawa Affan niƙaƙƙen barkono a fuska,wani ihu Deejan ta saki sannan tayi kan Nadiya, Nadiya ta firgita da zuwan ta amma tayi saurin watso mata ragowar yajin, Deeja ta goce sannan ta hankaɗe Nadiyan ta ɗauke ɗan ta

Kai tsaye banɗaki ta nufa da yaron tayi masa wanka sosai,amma har lokacin bai daina kuka ba,ta fito duk jikin ta rawa yakeyi,a lokacin Nadiya bata ɗakin,ta cire zanin gadon ta sanya wani ta kwantar da yaron tana kallon yadda fuskar shi tayi ja yana ta tsanyara ihu,kamar wadda aka tsikara tayi maza ta ɗauke shi da nufin shayar dashi amma yaƙi kamawa,sai kawai ta fashe da kuka mai motsa rai, hankalin ta ya kai ƙololuwa wajen tashi,tana tunanin mafita amma ta rasa dabara

Wayar ta ta soma ruri,a firgice ta É—auka ko ganin sunan batayi ba ta É—aga

Muryar ƙawa ta safeena taji tana faɗin"Hello! Deeja bakya ji na ne?"

Sabon kuka Deeja ta saki, safeena tace"subhanallahi!ina hanya gani nan zuwa"

A harabar gidan ta samu Deeja tsaye tana jiran ta,ko daidaita parking batayi ba ta fito tana faÉ—in"lafiya dai?"

Deeja bata iya magana ba illa nuno mata Affan da zuwa yanzu ya fara rage kuka,da sauri safina ta amshe shi suka faÉ—a mota suka nufi asibitin doctor su'ad

Tayi masa abinda ya dace,ya samu bacci,sai a lokacin Deeja ta samu nutsuwa,tayi musu cikakken bayanin abinda ya faru

Salati suka sanya suna tafa hannaye, doctor su'ad tace"lallai matar nan bata da ko É—igon iymani, jariri yaron da bazai iya aikatawa kanshi komai ba ballantana ya aikatawa wani me yayi zafi haka za'a yanke masa É—anyen hukuncin da ko babba bazai jura ba?"

"Wanne laifi kuwa?bakin hali ne fa kawai,ke dai Deeja ki ƙara kula da yaron ki kawai"a cewar safeena cikin ɓacin rai

"Ina kula dashi sosai, duk da cewa Allah ne mai tsarewa,yanzun ma Allah ne kaɗai yasan abinda zai faru ya taƙaita mana wahala"a cewar Deeja

Doctor su'ad tace"hakane kam,yanzu dai gashi nan an magance matsalar,a shawarce Kar ki nuna mata damuwa,ki rabu da ita,ki bar ta da halin ta kawai"

Deeja ta girgiza kai tace"Ni dama ko kallo bata ishe ni ba,ko me zatayi bata gaba na,idan tayi min na rabu daita ai idan tayiwa wani bazai ƙyale ta ba ko?"

"Hakane kam, to Allah yasa mu dace"a cewar safeena

Doctor su'ad ta amsa da"ameen

Sun daÉ—e suna hira har maghriba,sukayi sallah sannan safeena ta mayar da Deeja gida
Chapter 10 · 0% Book details