Sashe 26
Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A saboda haka naje gidan Nadiya,Amma sai ta nuna min babu ruwan ta da maganar,ƙarshe ma bamuyi rabuwar daɗi da ita ba,don a lokacin Imran yayi min abinda bai taɓa yi min ba saboda ke,wato mari
Ina cikin wannan tashin hankalin ne Najeeb ya turawa Imran evidence ɗin abinda muke aikatawa, saboda ya neme ni naƙi bashi haɗin kai, daga nan kawai na saddaƙar aure na ya gama mutuwa,gashi Imran sai nanata min yake na nemo ki duk inda na kai ki
Ina cikin wannan mugun halin tsawon kwana huɗu Imran ya zo da ƴan sanda suka kamani ina kukan tashin hankali,sai da suka kaini station naga Ashe har da Nadiya,wadda na firgita sosai da ganin ta yadda ta fice daga hayyacin ta,ƴan sandan nan babu tausayawa suka rinƙa gallaza mana don mu fito dake,amma amsa ɗaya muke nanata musu itace bamu san in da kike ba,kwanan mu shida a hannun su muna shan azaba iri-iri,ƴan uwan Nadiya sukayi bailing ɗin ta da ƙyar,a lokacin na ƙara kukan rashin dangi,don Ni dai nasan babu mai bailing ɗi na
Ilai kuwa babu wanda yazo min,amma bayan kwana uku suka sake ni,kai tsaye gidan su Najeeb naje amma yayi min korar kare,dole na koma gidan Imran,amma tun a compound ya bani takarda ta yace na fice masa daga gida,nayi ta kuka ina roƙon shi kan bani da in da zan je,yace wannan bai dame shi ba,na fice masa daga gida,da yaga naƙi fita ya janyo Ni kamar bola ya jefar dani sannan ya gargaɗi mai gadin kar ya kuma bari na na shiga
Ban daddara ba naje gidan fauwaz,amma abinda Imran yayi min nafila ne,don shi sakawa yayi mai gadin nashi kore ni da bulala,na koma bakin gate ɗin gidan Imran na raɓe,ga dare,ga yanayin sanyi,ga sauro,haka na kwana har asuba,da ya fito zashi sallar asuba ya ganni ranshi ya ɓaci,Ni kuma na fashe da kuka don a lokacin bansan yadda zanyi ba,ya tsallake Ni yayi tafiyar shi masallaci,to bayan ya dawo ne da ya shiga gida ya fito da kuɗi a envelope ya bani yace yayi min iya abinda zai iya,na fita daga rayuwar shi ko ya wulaƙanta ni,nayi ta roƙon shi ya yafe min,amma magana ɗaya yake nanata min,baya son sake gani na a rayuwar shi
Da kuÉ—in da ya bani nayi kuÉ—in mota na dawo garin mu taura,yadda na tafi ba'a sani ba hakanan babu wanda ya damuwa da dawowa ta,na buÉ—e É—akin mahaifiya ta na gyara na shiga,nayi ga jinyar kaina tsawon sati É—aya
Bayan na dawo dai-dai nayi amfani da kuɗin wajen Imran na saro kayan miya da omo da sabulu na fara siyarwa,amma saboda rashin kasuwa yasa na fara fita bakin kasuwa na kasa kayan na siyar,idan nayi ciniki na sayi abinda zan ci,idan banyi ba ciniki ba na zauna da yunwa,don na gwammaci yunwa akan baƙar rayuwar da Najeeb ya jefa Ni a baya,don nayi alƙawarin bazan sake ba
Bayan watanni biyu na fara yawaitar ciwon kai,da kai amai,alamomin ciki masu yawa suka bayyana a tare dani,har a lokacin ban wani gane ba, kasancewar bani da wannan wayewar
Sam ban fahimci ciki gare Ni ba sai da naga ƴan gidan mu suna nuna ni,daga karshe dai wata matar ƙanin baba na tazo ta zage Ni da gori,wai naje nayi karuwanci nazo zan haifa musu shege
Tabbas na tsorata da jin ina da ciki,ba don komai ba sai don bani da ƙarfin gwiwar tunkarar Imran,don dai nasan ba na Najeeb bane,don na kai watanni biyar inayi masa hanya-hanya idan ya neme ni, saboda all of a sudden kawai naji na gaji da rayuwar dabbobin da mukeyi
Nayi laulayi sosai,don sai da ta kai bana iya fita sana'a ta,amma Æ´an gidan mu babu mai zuwa inda nake
Sai da ciki na ya shiga wata na biyar sannan na samu sauƙin laulayi,na cigaba da sana'a ta,haka zan ɗauki kaya,ga nauyin ciki,kuma ko sau ɗaya ban taɓa tunanin zuwa awo ba
Sai da ciki na yayi wata takwas sannan wata dattijuwa maƙwabciyar mu,tace na daina fita zata ɗauki abinci na,nayi ta mata godiya
Ai kuwa ta cika alƙawari,don safe, rana,dare sai ta aiko min da abinci,in da na godewa Allah cikinnawa ba mai tsirfa bane,komai na samu ci nakeyi. Ciki na yana cika lokacin haihuwa na fara yawan ciwon mara akai akai,sai nayi zaton haihuwa ce sai kuma abu ya lafa,sai da nayi kwana tara a haka sannan na fara naƙudar gasken
Na sha wahala sosai,don sai da na fara tunanin ko mutuwa zanyi,amma saboda taurin kai yadda ƴan gidan basu nemi taimaka min ba nima ban nemi taimakon su ba,da dai naga ciwo ya ƙi ci yaƙi cinyewa sai na faki idanun su na kira wani yaro nace ya kira min dattijuwar da ke aiko min abinci Inna laraba,ai kuwa bata juma da zuwa ba na haihu
Tsawon kwanaki bakwai inna itace ke shigowa tayi min wanka ta wanke jaririya,É—an ta ta sanya yayiwa yarinyar huÉ—uba,da aka tambaye Ni suna ke kika zo min rai,don haka nace a sanya mata Khadijah
Inna laraba ta kula dani har nayi kwana talatin da biyar,a lokacin na cigaba da fita sana'a ta Saboda kula da little Deeja
Yanzu watannin Deeja ƙarama huɗu da haihuwa, Allah ya rufa min asiri da ƴar sana'a ta bana rasa ci ko sha,sannan bana fashin yi miki addu'ar Allah ya bayyana ki ya tsare ki a duk inda kike
Rabo na da karatun addini tun bayan rasuwar mahaifi na babu jumawa,don haka lokacin da aka buɗe wata makarantar matan aure banji ƙyashin shiga ba,a lokacin Deeja watannin ta biyu da haihuwa
A haka nake rayuwa har zuwa yau,ko da bana farin ciki amma bana cikin baƙin ciki,kuma ina zaune lafiya da Ni da ƴar jaririya ta
Wannan shine labari na Deeja,haƙiƙa ni ɗin mai kuskure ce,amma kuma na kasa gane wanene silar hakan,mahaifi na da ya kasa mayar da raino na wajen dangin mahaifiya ta,ko dangin mahaifiya ta da suka kasa nema na tsawon shekaru,gashi ni bazan iya kai kaina gare su ba,ko dangin mahaifi na da basu mayar dani dangin uwa ta ba bayan sun san ba riƙe Ni zasuyi ba,ko ma dai menene, alhamdulillahi,na godewa Allah da ya nufe ni da shiriya tun kafin lokaci ya ƙure min"
Menene ra'ayin ku game da labarin Deeja da na Umaima?wannene yafi ban tausayi kuma yafi Zama matsala a cikin al'ummar mu?sai naga ra'ayoyin ku a comment section, Allah ya barmu tare MATAR KHALEES fans 🥰
#Nusy_bee
*****MATAR KHALEES*****
âœï¸Nusy bee
Page 36
Shiru ɗakin ya ɗauka na wasu ƴan mintuna bayan gama labarin Umaima,bakajin komai sai shashsheƙar kukan Afra da Umaima,da ajiyar zuciyar Deeja,kiran sallar la'asar ne da akayi ne ya sanya Umaima miƙewa tana goge kumburarrun idanun ta,a lokacin ruwan yayi sauƙi,ta ɗauki ƴar butar ta guda ɗaya ta zuba ruwa a ciki tace"gashi ku fara yin alwala,akwai makewayi idan kuna buƙatar shiga"Afra ta miƙe ta ɗauki butar batare da tace uffan ba,don har yanzu kuka takeyi
Ita kam Deeja har yanzu idanun ta suna kan little Deeja da ke kwance a jikin ta tana shan baccin ta cikin kwanciyar hankali,ko alamun hawaye babu a idanun ta,amma a zuciyar ta ji takeyi da zata samu tayi hawayen da taji sauƙin raɗaɗi da ciwon da takeji,ta juma bata ji tashin hankali irin wannan ba,shiyasa bahausheyace kai dai kaga mutum,amma bakasan yaya yake gudanar da rayuwar shi ba,baka san kalubalen da yake fuskanta ba, lallai rashin uzuri a rayuwa babbar masifa ce
Afra ce tayi sallama ta shigo tana duban Deeja tace"kije kiyi alwalar Deeja,nayi"sai a sannan Deeja ta kwantar da little Deeja ta miƙe cikin mutuwar jiki ta fice daga ɗakin
Umaima ma ficewa tayi Afra kuma ta tayar da sallah
Bayan sun idar da sallah ma zama sukayi jugum jugum kowa da tunanin da takeyi,don ma ita Umaima ta ji sauƙin nauyin da ke zuciyar ta,a ƙalla tayi magana da waɗanda ta san sun fahimci halin da take ciki,basu daɗe da idar.da sallah ba ruwa ya dawo kamar da bakin ƙwarya,cikin sanyin murya Deeja ta kalli Afra tace"Afra anya kuwa zai yiwu mu koma yau?"kafin Afra tayi magana Umaima tace"mai zai hana ku kwana anan?kunga yadda akayi ruwa hanyar ba lallai tayi daɗin tafiya ba"Afra ta kalli Deeja don jin me zata ce,cikin sanyin murya tace"to Allah ya kaimu goben"
Sosai fara'a ta bayyana a fuskar Umaima,taji daÉ—i sosai,ko babu komai dai yau É—aya zata sake da wasu mutane da ta sani a rayuwar ta,cikin murna tace ameen ya Allah"su dai su Deeja sai kallon ta sukeyi cike da tausayawa
Deeja ta kalli Umaima da ke chanjawa little Deeja kaya tace"yanzu Umaima idan Allah ya fito miki da miji zakiyi aure?"
Umaima tace"ƙwarai kuwa,bayan haihuwa ta wani abokin ƙanin baba na ya nemi aure na,da farko har na amince masa,har Wajen sana'a ta ƴaƴan shi sukaje sukayi min rotse suka watsa min kaya na suna faɗin uban su bazai auri karuwa mai ƴar shege ba, dalilin haka na tsorata na sallame shi"
Daga Afra har Deeja sakin baki sukayi suna kallon ta da mamaki, Deeja tace"saki nawa Imran yayi miki?"
"Saki É—aya ne,takardar ma tana nan har yanzu"
"To shine kike tunanin auren wani bayan Imran?"a cewar Deeja tana kallon ta
Daga Umaima har Afra a firgice suka kalli Deeja, Umaima cikin in Ina tace"I....I... Imran kuma?...yace baya son gani na fa,yace ba fita a rayuwar shi, kuma kema ba sai na gaya miki ba kin san Imran yafi karfi na yanzu"Deeja bata sake magana ba ta amshi little Deeja da take ta kallon ta,don ruwan da akayi da sakin asabarin da Umaima tayi yasa É—akin yayi duhu,sai Deeja ta kunna torch da ke jikin power bank É—in ta,ta haske É—akin tarwai
Murmushi tayi tana kallon ta, itama yarinyar kamar ta sani ta fara ɓangale baki tana dariya, Deeja ta shagala tana mata wasa,dama ita fa tun ganin ta da babyn a farko ta shiga ranta
Umaima ce ta miƙe tsaye tana ɗaukan hijabin da tayi Sallah bayan ruwan ya tsaya,tace"bari naje nayo cefanen girkin dare,biyar ta gota yanzu"itama Deeja ta miƙe tana faɗin"nima dama ina son zaga garin,mu je, Afra ke kam nasan bakya jure wahala zauna ki jira mu"