← Book details Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 31

Sashe 4

Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basu samu damar zama cin abincin ba sai da sukayi sallar maghriba,suna cin abinci suna hira,anan aunty Bintu ta sanar dasu batun auren Deeja

Cikin madaukakin mamaki Mima tace"kamar a mafarki?Deeja tayi aure kullum mukanyi waya ko chat amma ta kasa sanar dani?"

Aunty Bintu tace"kin santa da zurfin ciki,kuma ina zargin akwai matsala ne,duka duka fa kwananta arba'in da shida da yi mata aikin zuciya akayi mata auren fa"

Hafeez ya gyaÉ—a kai yace"lallai babu mamaki,to ina tsohon mijin nata?"

Aunty Bintu tace'yana nan"

Kuma suna haÉ—uwa dashi?"a cewar Mima tana tsare ta da ido

"Sai dai idan bataje gidan Mamie babba ba,kuma bikin a gidan mamien za'a yi"a cewar aunty Bintu

"Yayi aure ne?"hafeez ya tambaya

"Tun kafin su rabu da Deeja "a cewar Mima"wata fitsararriya mara kunya mara tarbiyya"ta ƙarashe maganar tana yatsina fuska

"Ke Mima!ina raba ki,a ina kika san bata da tarbiyya?"a cewar aunty Bintu

Murmushin takaici miman tayi tace"a bar maganar kawai aunty"daga nan suka sauya wata hirar

A ranar Mima ta kira Deeja ta sanar mata da saukar su,ihun murna ta rinƙa yi,tace"oh!leemo nayi missing ɗinki da yawa,ina my baby Mee'ad?"

"Tana wajen abban su ita da munib"

"Yayi kyau,to yaushe zaki ƙaraso?"

"Oho miki,mara mutunci kawai,kiyi aure amma ki kasa sanar dani?"

"Uhm!"da story sosai Mima,sai mun haÉ—u kawai,yaushe zaki zo?"

"It is better mu haÉ—u a gidan bikin, saboda abban Mee'ad ya matsa min gobe,jirgi zamu bi zuwa azare,don mu gaida ammin su"

"Okay,babu matsala, yaushe zaku dawo?"

"Jibi in Sha Allah,Kuma a gidan bikin zan sauka"

"Okay babu damuwa,Ni da gobe nace zan je,amma yanzu na fasa sai jibin"

"Haba ke kuwa,meyasa?"

"Mu haÉ—u a jibin kawai,da stories"

"Okay Allah ya nuna mana da alkhairi"

"Ameen"sukayi sallama

A ranar Deeja cikin farin ciki ta kwana,walwalar ta ta bawa Khalees mamaki ƙwarai, saboda irin tarin matsaloli da ta tsinci kanta a ciki basa bata damar yin walwala kamar kowanne mutum,amma sai sabgar ta takeyi cikin farin ciki,shi kuma Khalees jin kai irin nashi ya hana shi tambaya

Washe gari da safe daga office Kai tsaye wajen kitso da ƙunshi ta nufa,ai kuwa aka tsantsara mata kitso, dogon baƙin gashin ta ya amshi ƙananan kitson,lalle ja da baƙi ya amshi chaculate fatar ta,tayi kyau sosai ga wani haske da ta ƙara a ƴan kwanakin nan

A ranar bata koma gida ba sai shida saura Æ´an mintuna,tun sanda mai gadi ya wangale gate ta hango khalees yana ta faman Safa da marwa, fuskar shi É—auke da alamun damuwa,amma ganin shigowar motar ta sai ya tsaya cak yana kallon ta batare da yace uffan ba, fuskar shi har yanzu a É—aure take

Kai tsaye parking space É—in gidan ta nufa bayan ta daidaita parking É—in motar ta fito tana É—an satar kallon Khalees É—in,ko uffan ba tace ba tayi nufin wucewa cikin gidan

"Daga ina kike?"

Batare da damuwa ba ta bashi amsa,"naje kitso da ƙunshi ne"

"Shine sai yanzu?"ya faÉ—a da É—an É—aga murya

Ganin hankalin mutanen da suke yiwa gidan hidima ya fara dawowa kansu ya sanya ta furta"I'm sorry"da sauri ta wuce cikin gidan

Ta fito wanka ta ganshi a bakin gado,har yanzu fuskar shi babu walwala,hakan bai dame shi ba,ta zauna a gaban madubi ta fara gyara kanta,sai yanzu Khalees ya ƙare mata kallo ganin tayi kyau sosai,amma duk da haka bai fasa faɗar abinda ya kawo shi ba

"Ban amince ki rinƙa zuwa ko'ina kina haura la'asar a waje ba,idan haka ta kuma faruwa rai zei ɓaci"bei jira amsar ta ba ya miƙe ya fice daga ɗakin

Wayar ta ta É—auko daga jakar ta,miscall shida ta gani,shaf ta manta cewa ta sanya ta a silent,duk misscall shidan Khalees ne,a fili ta furta "oh!wato jin kai bazai bar shi yace"ya kira ni ban amsa ba ko?"

Washe gari ta kama juma'a,kuma a ranar zata tafi gidan bikin,sai zumuÉ—i take tayi,Khalees yana kwance yana kallon yadda take ta farin ciki, gaba É—aya sai yaji ya shiga damuwa,wato farin ciki takeyi Saboda saboda zata nisance shi?"

Da yaga zumuɗin yaƙi ya ƙare sai yace"Malama haukan ya isa haka,idan kika matsa ma wallahi sai na hana ki"

Kallon shi tayi cike da mamaki,ganin ya É—aure fuska ya sanya ta É—auke kanta ta cigaba da abinda takeyi, zuciyar ta cike da mamakin shi

Ƙarfe bakwai da mintuna arba'in ta kammala shirya komai,a lokacin tuni Khalees ya wuce wajen aikin shi,ta loda akwatunan ta a Boot taja motar ta ta nufi wajen aikin ta

Sha ɗaya da minti bakwai wayar ta ta fara ƙara,tana dubawa,sunan Mima ta gani,da sauri ta ɗaga tana faɗin"sister leemo ya?kun sauka lafiya?"

"Lafiya lau sister deejo,mun dawo fa"

"Da gaske don Allah?"a cewar ta cikin farin ciki

"Wallahi kuwa,yanzu haka ma gamu a airport,aunty Bintu zata É—auke mu"

"To Allah ya iso daku lafiya,Ni ina wajen aiki"

"Okay to mu haÉ—u a can É—in kawai"

#Nusy bee
*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 6

Sha biyu daidai Deeja ta tashi daga aiki,kai tsaye sardauna crescent ta nufa cikin unguwar Nassarawa GRA,in da gidan professor Ismail yake, kai tsaye gidan ta nufa,horn ɗaya daya tayi mai gadi ya leƙo yana ganin itace yayi mata sannu da zuwa,suka gaisa cikin mutunci,tayi masa alherin da ta saba yi masa sannan ta shiga cikin gidan

A makeken tempol É—in gidan ta ajiye motar ta cikin jerin tarin motocin da ke cikin tempol É—in,ciki har da motar Imran da Mima,da alamu dukkan su suna nan kenan

Bata damu ba ta nufi sashen Mamie don su gaisa,da sallama ta shiga,su huda da yusra da ke falon suka miƙe suka rungume ta suna murnar ganin ta,da ƙyar suka ƙyale ta,ta gaida da Mamie da kuma mummy Aysha,da fara'a suka amsa mata sannan ta yada zango suka cigaba da hira

** ** **

Ita kuwa Mima aunty Bintu ce ta É—auko su ita da yaran ta,kai tsaye gidan professor Ismail ta kawo su,shi hafeez bai taho ba, Saboda yana da uzururruka a can,sai ranar É—aurin aure zai zo

Bayan sun gaisa da Mamie sai ta kira afra take shaida mata isowar ta,cikin azama afra ta shigo ta rungume ta cikin murna taja su sashen ta,a can ta shirya musu abinci lafiyayye ,sosai Mee'ad da munib suka burge afra,cikin rawar jiki ta kira haneef tana fadin"haneef,zo ga aboki nayi maka"yaron ya shigo falon da sauri yaja munib suka nufi wajen wasan shi

Sun kwashi mintuna suna hira ,a ƴar hirar da sukayi Mima ta fahimci cewa afra mace ce mai surutu da rawar kai,don a hirar su ta fahimci cewa matar yaya fauwaz ce,kuma da alamu akwai aminci mai ƙarfi tsakanin ta da umaima,don haka gaba ɗaya taji batayi mata ba,don haka tace "bari naje mu gaisa da mutanen gidan ko?aunty kiyya tana nan kuwa?"

Sai walwalar Afra ta ɗauke,ta ɗan taɓe baki tace"suna main parlour Ina ga,muje can"Mima batayi musu ba suka wuce zuwa babban falon

A can suka haÉ—u da da su lubaisa,kiyya da nuwaira,sai aunty salma da aunty nafisa,sai minal da itama zuwan ta kenan,sai umaima

Sun gaisa da kowa, cikin mutunci,umaima da kuma suka fara kallon kallo, Afra tace "sisto ga ƙawa ta Dr halima azare"

Murmushi Mima tayi tace "nice to meet you umaima"ta miƙa mata hannu sukayi musabaha

"Na gode,ya gida?"ya mei gida da yara?"inji umaima cikin sanyin jiki

"Kowa lafiya,ya naki mai gidan?"

"Lafiya ƙalau,,a cewar umaima"Mima tace"good haka ake so"bata jira cewar umaima ba ta ja hannun kiyya suka bar falon suka nufi sashen kiyyan

A can Mima ta zube a kan kujera,ta dubi zakiyya tana fadin"aunty kiyya Ina yara na ne?ban gansu ba"

Zakiyya tace"Islam da Hisham suna makaranta,shi kuma Aisar babbar Æ´ar aunty rahama ta É—auke shi"

"Yayi kyau"a cewar Mima,ta É—an yi shiru,zuwa can ta kalle ta tace"aunty kinji sisto tayi aure?"

"Na sani wallahi,amma bamu samu halartar auren ba,wani irin aure ne kamar taron mutuwa"

"Akwai matsala kenan ko?"a cewar Mima

"Babu mamaki,amma sai tazo sai muji ta bakin ta"

"To Allah ya kawo ta lafiya"

"Ameen"

Haka suka cigaba da hira akan Deeja,sun ɗan juma kafin su miƙe su nufi main parlour

Mima na kula da kallon da umaima da lubaisa sukeyi mata lokaci lokaci amma tayi banza dasu, Afra kam sai zaƙewa takeyi akan miman,a ƙoƙarin ta na samun shiga fiye da zakiyya

Deeja ce tayi sallama ta shigo, hankalin su ya koma kanta, Mima tayi tsalle ta rungume ta suka fara ihun murna,zuwa can suka saki juna suna haki da dariya, Deeja ta kalli Mima tana dariyar murna tace"sister leemo! gaskiya Malaysia ta amshe ki,kinga yadda kikayi fresh kika ƙara kyau?ko dai munib ya samu ƙani ko ƙanwa ne?"

Dariya Mima tayi gami dukan kafadar ta tace"ai ke za'a yiwa wannan tambayar sister deejo,don Allah aunty kiyya taya Ni dubawa , yarinyar nan batayi ƙiba da haske ba?da alama engineer Abdul yayi ajiya"

Gaban Deeja ne ya bada dam!har sai da hakan ya so ya bayyana akan fuskar ta,don dama kwanan nan tana zargin hakan saboda rashin ganin al'adar ta,ga yawan kwaÉ—ayi da ta koya,amma da yake jaruma ce ta dake tare da faÉ—in"ji sharri,ko don na rafko ki zaki wayance?"

"Aunty kiyya tace"wane sharri kuma?da gaske take wallahi,ko dai Khalees ya iya kiwo ko kuma yayi ajiya,cikin biyu É—aya"

Dariya sukayi su duka, duk da cewa Deeja ta yaƙe tayi,ta nemi waje ta zauna tana faɗin"ke dai aunty kice ta Baki cin hanci ne kawai"

Su Afra kan mamaki ne ya ƙamar dasu,yaushe Deeja tayi aure?Nuwaira ce ta kasa jurewa ta kalli aunty kiyya tace"Aunty kiyya dama Deeja tayi aure ne?"

Mima da Deeja suka kalli juna a tare da sannan suka kalli nuwairan,Mima ce tayi caraf ta amsa da cewa "eh tayi aure,watanni huÉ—u baya ma,da mamaki ne a cikin ikon Allah? "

Cikin sanyin jiki nuwaira tace"babu kam, Allah ya sanya alkhairi"

"Ameen"in ji aunty kiyya,ita dai Deeja tana jin su,sai ma danne dannen waya da ta fara don ta nuna musu rashin muhimmancin nuwairan a wajen ta

Mima ce ta janye hannun ta tana fadin"zo muje sashen aunty kiyya muyi sallar la'asar, gashi can an fara kira"babu musu ta miƙe,itama Aunty kiyyan ta miƙe suka nufi sashen nata
Chapter 4 · 0% Book details