← Book details Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 31

Sashe 2

Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayar ce ta soma ruri,sunan aunty Bintu ne taga yana yawo akan fuskar wayar,da sauri ta É—aga da sallamar ta, cikin farin ciki take faÉ—in"aunty Bintu yau a gari?"

Daga ɓangaren aunty Bintu tace "kya tambaya mana,ke da bakya neman mutane"

Tayi Æ´ar dariya tace "ayya!am sorry aunty,yasu ilham da salim?"

Suna nan lafiya,wai da gaske ne kinyi aure?"a cewar aunty Bintu

"Deeja ta ɗan yi shiru na ƴan daƙiƙu kafin tace"haka ne aunty,anyi aure na watanni huɗu baya"

Aunty Bintu tace"Amma da mamaki Deeja,kinyi aure baki sanar dani ba,ko Mima ma baki sanar mata ba?"

"Uhm abinda Yaya fauwaz ya gama ce min kenan, wallahi aunty ba da shiri akayi auren ba,kawai lokaci yazo a haka"

"Haka ne kam!"inji aunty Bintu"shi aure lokaci idan yazo a lokacin shi sai anyi shi ko an shirya ko ba'a shirya ba,fatanmu dai Allah ya baku zaman lafiya ya kaÉ—e fitinar shaiÉ—an"

"Ameen"Deeja ta amsa cikin sanyin Muryar ta

"Kinsan da bikin Yasmin ko?"aunty bilki ta tambaye ta

"Eh na sani,Yasmin da hudan momy Aisha sun kawo min invitation card,Kuma tun kwanaki can ita Yasmeen din ta turo min hoton ankon ta WhatsApp"

"To shikenan,mu ma sun aiko mana da gayyata,don haka zamu zo,itama Mima next week zasu taso daga Malaysia

Cikin É—oki Deeja tace"wayyo daÉ—i!da gaske don Allah aunty?"

"Wallahi kuwa,da jibi zasu taho,wasu uzururruka ne suka tsare su,amma in Sha Allah nan da five days zasu taho"

"To Allah ya kawo su lafiya"

"Ameen,me kika tanadar musu ne?wannan zumuÉ—i haka?"

Ƴar dariya tayi sannan tace"wallahi aunty nayi kewar Mima ba kadan ba,ga yaran ta masu shiga rai musamman ma mei suna na Khadija Mee'ad"

Dariya sosai aunty Bintu tayi tace"lallai,kiji ki da son kai"

"Ba son Kai bane aunty,Ina son yarinyar ne sosai"

"To da kyau,saura ke kema"

"Aunty Bintu lokaci ne,fatan mu Allah ya kawo masu albarka"

"Ameen ya Allah,sai anjuma,ki gaida mai gidan"

"Okay zaiji"daga haka suka ajiye wayar

Farin cikin zuwan su Mima ya danne damuwar da take ciki,don tasan Mima ko banza zata bata shawarwarin da zasu rage mata damuwa,don Mima wayayyiyar gaske ce sosai,kuma tafi Deeja shiga mutane sosai,hakan ya sanya ta karanci dabiun mutane da yawa

Tana jin sanda su Khalees suka fita,sun kwashi a ƙalla mintuna goma da fita,don taji tashin motocin su,sai a lokacin ta fita don kwashe kayan da suka kammala cin abincin,ta kimtsa wajen

Ko da Khalees ya dawo ma bei nuna mata komai ba,itama bata tambaye shi komai ba,don tasan bazai taɓa bata amsa ba

Da daddare tana zaune tana danne danne a laptop,lissafe-lissafe takeyi na kasuwancin ta,na wani babban shopping mall da ta buÉ—e, Khalees ne ya shigo da sallama,ya dube ta da fuska babu annuri yace"gobe su Hajiya zasu zo,don haka ki zama cikin shiri"yana gama magana bai saurari cewar ta ba ya wuce zuwa É—akin shi,a ranta ta furta"oh!wata damuwar dai zan riska na sani"

Washe gari da safe babu aiki,don haka a nutse take gudanar da aikace aikace-aikacen ta,tabi ko'ina ta share tas har É—akin Khalees,batayi tunanin É—ora girki ba,don ta san halin Khalees ba tun yau ba,baayi masa gwanin ta,don sai ta girka yace bazai ci ba,don haka water kettle kawai ta jona ta tafasa tea ta Sha da cake,ta koma kan computer ta cigaba da lissafin ta

**** **** ****

Cikin sauri take shiri don ta bar su salma jira,riga da skirt ta sanya waɗanda suka ji wani matsiyacin ɗinki,gaba daya jikin ta a waje,gaba ɗaya jikin ta a waje,ko budurwar mutunci bazata iya sanya Waɗannan kayan ba ballantana ita matar aure,ko ɗan kwali bata sanya ba sai wani yalolon mayafi da ta sanya kalar atamfar,sannan ta ɗauko purse dinta ta fito,tana rufe ƙofar kira ya shigo wayar ta,da sauri ta duba,kamar yadda tayi tsammani Yaya najeeb ne,tana ɗagawa tace "hello yaya najeeb"

"Haba sister!tun É—azu nake jira,me ya hana ki zuwa ne?"

"I'm sorry bro! wallahi al'amuran bikin Yasmin ne ya sha kanmu shiyasa kaji ni shiru,amma in Sha Allah ko da yamma ne zan leƙo gidan,ba dai Ni nace zan zo ba?"

"So why not bazaki zo yanzu ba?"

"Saboda akwai abubuwan da zamu siyo yanzu mu da su salma,sai anjuma zamu dawo,kai tsaye gida zan wuto in Sha Allah"

"Okay to Allah ya kawo ki lafiya"

"Ameen,bye bye!"ta kashe wayar

A motar afra ta tarar dasu,afra na mazaunin driver sauran kuma suna baya,wato gaba wajen mai zaman banza ya tashi a matsayin mazaunin ta kenan,ta shiga tana fadin "oh sorry na bar ku jira ko?"

Zakiyya ta kalle ta sheƙeƙe gami da taɓe baki,afra kam murmushi tayi tana faɗin"sister kenan,kina wuta"

Tayi wani malalacin murmushi tana cigaba da danna waya,lubaisa kam kasa daure wa tayi,ta dube ta cikin É—aurewar fuska tace
"Amma UMAIMA sai nake ganin kamar wannan shigar bata dace ba a matsayin ki na matar aure ko?"

A watse umaima ta kalle ta,sai dai tun kafin tace komai zakiyya tace "oh lubaisa ina ruwan ki?ita ƙaramar yarinya ce da za'a ce bata san me ya dace ba?"

"Ai kawai tsabar shegen shishishigi ne da hassada"a cewar afra,wadda dama tuntuni basa jituwa da lubaisa

Lubaisa na shirin sake magana nuwaira dake kusa da ita tayi mata nuni da tayi shiru,dole tayi shiru gami da zaro wayar ta ta kunna music ta dasa a kunne,don irin surutan da afra take cigaba da yi

Shopping mall suka nufa inda zasu yi siyayyar bikin,a bakin mall ɗin wayar afra ɗauki ƙara,ta ɗauko ta duba,ganin wadda take kiran nata ne tayi saurin ɗagawa,bayan sun gaisa take sanar da ita cewa ta shirya,sati mai zuwa zata zo don bikin Yasmin,cikin farin ciki afra tace"to ƙawa ta Allah ya kawo ku lafiya,muna waiting"

"Ameen, Sai nazo"sukayi sallama

Afra ta kalli umaima da murmushi a fuskar ta ta tace"umaima be ready,muna da babbar baƙuwa,wannan likitar da nake baki labari mun haɗu daita a ƙasar Lebanon,kin gane ta?"

Umaima tayi murmushi tace"eh na gane ta"

"Yawwa!itace zata zo bikin Yasmin,da alama bikin nan zai yi albarka"

#Nusy_bee

*****Matar Khalees*****

✍️ Nusy bee

Page 3

"Sosai ma kuwa afra,Ni kam zan so in ga wannan matar"a cewar umaima

"She is very nice umaima,ga yaran ta guda biyu masu tsananin kyau,mijin ta kuwa akwai class,ba irin abban haneef ba"

Umaima ta kwashe da dariya,daidai nan afra ta kammala parking suka fito, umaima ta kalle ta tace"a'a afra,ko dai kin ƙyasa ne na fara taya abban haneef kishi?"

Afra tayi ƴar dariya tace"a'a wallahi,shi abban haneef kamar shashasha yake,kowa kawai buɗe masa haƙora yake,ban samu kwanciyar hankali ba sai da na raba shi da Wannan matsiyaciyar yarinyar fa kina gani"

Umaima ta taɓe baki,suka jera suka nufi cikin mall ɗin suna cigaba da hira, afra na koɗa kyau da jan aji na mijin ƙawar ta likita

Sai wajen ƙarfe uku suka gama siyayyar suka ɗauki hanya,amma sai umaima tace a sauke ta a gidan su

Haka kuwa akayi,suka sauke ta sukuma suka wuce gida

Da sallama ta shiga cikin gidan,a falo ta iske su umma,har da najeeb É—in,da sauri najeeb ya taso ya rungume ta yana faÉ—in"lovely sister oyoyo!"

Umma ta kalle su cikin rashin jin daÉ—i tace"haba najeeb!da auren ta fa!"

"No umma!ba Æ´ar uwata bace?"yayi saurin katse ta

Daga haka tayi shiru bata sake magana ba, najeeb ya dubi umaima yace"ki ci abinci zaki raka ni gidan wani aboki na"

"Okay!"ta bashi amsa,ta dubi umma tace"umma akwai abinci ne?"

"Eh akwai,bari in kawo miki"umma ta miƙe ita kuma umaima ta zube akan kujera don hutawa

**** **** ****

Tun azahar ta kammala komai,har abin taryar baƙin nata duk da cewa ba baƙin farin ciki bane,ta gyare gidan tsaf,tunda safe da taga Khalees bata sanya shi a idanun ta ba,hakan bei dame ta ba don ganin nashi babu abinda zai tsinana mata, wataqila ma ta samu ƙarin takaici

Ƙarfe uku da mintuna goma taji ƙarar gate,da alama su hajiyar ne suka iso mei gadi yake ɗage musu gate ɗin,dam!taji gaban ta ya buga,da sauri ta dafe ƙirjin ta tana fadin"allahumma laa sahla illaa maa ja'altuhu sahla wa anta taj'alul hazna izaa shi'ita sahla"

Tana leƙen su ta window,har suka fito daga motar su,su huɗu ne, hajiyar,sai farida da jannat,sai direban su da ya tsaya a wajen malam Audu mei gadi

Da sallama suka shigo cikin gidan,a zaune suka same ta a falon tana jiran isowar su,da sauri ta miƙe tana ta faman fara'a,ta gaishe su ɗaya bayan ɗaya,duk da cewa su jannat ƙannen Khalees ne,kuma ko itama ta girme su,amma hakan bei hana ta gaishe su ba,don ta san cewa su baza su taɓa gaishe ta ba

Hajiyance ta amsa, fuska babu yabo babu fallasa,sai jannat,amma ita Farida kallon ta tayi sheƙeƙe ta maida kai ga wayar hannun ta,da alama chatting takeyi

Bata kula ba,sai ma cima data jere musu a gaban su tana jansu da hira, hajiyance kawai mei amsa wa,sai jannat sama-sama,amma Farida ko uhum bata ce mata ba

Hajiyance ce ta dube ta tace"am dama ba wai zama nazo yi ba,nazo ne in sanar dake cewa jibi in Sha Allah su Farida da zasu dawo gidan nan da zama da zama,don haka sai ki shirya,na riga na sanar da yaron nan (tana nufin Khalees)tuni,don haka sai ki zauna da shiri" ta ƙarasa faɗa tana miƙewa tsaye

Wani irin jiri Deeja ta rinqa ji,amma da yake jarumar mace ce ta dake tace "to Hajiya, Allah ya kaimu jibin"

Hajiya ta amsa da "ameen"

Deeja tace"Hajiya baku ci abincin ba ma"

"A'a mun ƙoshi wallahi,zamu tafi"bata jira cewar Deejan ba tayi gaba,suma yaran suka biyo bayan ta, Deeja bata da zaɓin da ya wuce bin bayan su,ta rako su har bakin motar su

Bayan sun tafi komawa É—akin ta tayi ta É—aga waya ta kira zakiyya,a lokacin dawowarsu kenan daga shopping mall da suka fita, shigowar ta sashen ta kenan,ko zama batayi ba,sai ga wayar Deeja ta shigo

Da sauri ta É—aga tana faÉ—in"Hello! Deeja manya"

Yanayin Muryar Deejan ya fahimtar daita cewa ba lafiya ba,tace"Allah yasa dai lafiya"

"Uhm! aunty kiyya bari kawai,ina cikin damuwa sosai"

"Kina bari na É—an yi uzuri,zan kira daga baya"
Chapter 2 · 0% Book details