Sashe 12
Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zama yayi daɗi tsakanin ruƙayya da Amina, Amina na girmama ruƙayya, itama ruƙayya taba mutunta ta, hakan ne ya wanzar da zaman lafiya a gidan
Watan ta shida a gidan ta fara laulayi,duk yadda su dangin Ishaq suka so shiga tsakanin ruƙayya da Amina hakan bai samu ba,tilas suka sanya musu idanu
Sakina ta zamto babbar aminiyar Amina, kullum suna tare,hakan ya sanya suka saba,tun kafin zuwan Amina dama sakina ce nauyin komai a gidan,yanzun ma ita É—in ce maiyin komai a gidan,da kafin Amina ta fara laulayi tare sukeyi,amma yanzu Aminan bata iya yin komai
A haka har lokacin haihuwar Amina yayi,kai tsaye tace a bar ta ta haihu a gida,hakan kuwa akayi,don babu kulawar da bata samu a wajen su sakina,hatta da Isma'il ya kan siyo duk wani abu da yaji tace tana so har ya ishe ta,wannan hadin kan nasu yana matuƙar sanya malam Ishaq cikin farin ciki
A haka har Allah ya sauke ta lafiya ta haifo ƴar ta mace, ruƙayya ce ta karɓi haihuwar ta gyara mai jego da jaririya,nan da nan gida ya cika da mutane,ana ta murnar wannan ƙaruwa
Sai dai Inna Mariya ta katse musu hanzari,don kuwa cewa tayi da ita zata tafi can Adamawa in da take aure,sam hakan baiyi musu daɗi ba,amma tunda malam Ishaq ya amince haka dole suma suka haƙura,don dai ita Amina marainiya ce mahaifiyar ta ta rasu tun tana ƙarama,sannan uwar riƙon ta ko da wasa bata ji daɗin ta ba,dole Inna Mariya ƙanwar mahaifiyar tata itace zata maye gurbin yayar tata
Ranar suna malam Ishaq ya raÉ—awa jaririya suna zainab,an sha shagali sosai, sannan suka shirya suka tafi Adamawa
Mutanen gidan sunyi kewar Amina da zainab ba kaÉ—an ba,su kenan kullum a lissafin kwana nawa ya rage su dawo
Ranar da zasu dawo Mutanen gidan sai É—okin dawowar su sukeyi,aka gyara ko'ina akayi ta dafa abinci kala-kala,duk don dawowar Amina da zainab
Sai dai mummunan labarin da suka ji yayi tsananin tayar musu da hankali, Amina sunyi hatsari ita da waÉ—anda zasu dawo da ita,cikin tsananin tashin hankali gaba dayansu suka nufi asibitin da aka kwantar dasu
#Nusy_bee
*****MATAR KHALEES*****
âœï¸Nusy bee
Page 18
Sai dai a halin da suka same su ya ƙara firgita su,kuka suka rinƙa yi sosai,zainab ta samu karaya shida a hannaye da ƙafafuwan ta,banda manyan raunuka,sauran mata uku da suka rako ta biyu daga cikin su ma rai yayi halin shi,har an kai su mutuary,sai dai wani ikon Allah zainab ko ƙwarzane batayi ba,asalima a lokacin baccin ta takeyi hankali kwance
Amina ta dube su cikin zafin ciwo take faɗin"ga zainab nan,ku kular min daita,Ni bazan rayu ba,na bar amanar ta a hannun ku,don....don....don....."yadda maganar take sarƙewa ya ƙara ba su tsoro,a gigice sakina ta fice da gudu zuwa office ɗin babban likitan
Amma ko da suka dawo gani tayi mahaifiyar su ruƙayya riƙe da hannun Aminan, Isma'il dama bai shigo ba yana daga bakin ward din, ruƙayya sai kuka takeyi,likitan ya duba pulse dinta ya tabbatar musu da Amina tayi tafiya mai nisa,jiri ne ya ɗebi sakina,sai da likitan ya taimaka ya riƙe ta
Basu juma sosai ba aka yi cike ciken da ya dace aka basu gawar Amina,aka sanya ta a ambulance aka tafi daita zuwa ainihin gidan iyayen ta
Tabbas anji mutuwar Amina,don Amina yarinya ce ta gari bata da abokin faÉ—a,gata da girmama na gaba da ita
Baba talatu itace uwar goyon Amina,sai a yau tayi nadamar abubuwan da ta aikatawa Amina ita da yaran ta, domin ko babu komai Amina ta kular mata da yara,amma ita kullum talatu bata da burin da ya wuce ta ci zarafin Amina,yau dai ga Amina ta bar mata duniyar
An yiwa Amina sutura an kai ta gidan ta na gaskiya,su kuma su ruƙayya suka dauko zainab suka dawo gida
Sun daÉ—e sosai kafin mutuwar Amina ta sake su,suka mayar da hankali wajen rainon zainab baiwar Allah
Shekarar zainab ɗaya akayi auren sakina da Kabiru,Kabiru da kowa nashi ƴan garin azare ne,don haka can aka kai su,wannan dalili ya janyo shaƙuwar zainab da sakina tayi rauni
Sai Isma'il ya zamana makaranta ce kawai take raba su da zainab,kuma shima sai anyi mata dabara yake samu ya tafi,idan tayi kukan bai dawo ba sai ta haƙura taje wajen ruƙayya,amma da zarar ya dawo to ta bar wajen ruƙayyan
Sun saba sosai,hakan ya faranta ran malam Ishaq,sakina ma ta kawo musu ziyara sau biyu a tsayin shekaru uku da tayi aure,a lokacin zainab na da shekaru huÉ—u
A lokacin ne ruƙayya ta kama wata iriyar cuta da aka kasa gane kanta,wadda taso tsaidawa da Isma'il karatun shi,amma tawakkali irin nata ya sanya take matsa masa akan yaje makarantar kawai,babu abinda zai same ta
Tun tana kwanciya yau gobe da sauƙi har ciwon ya kwantar da ita gaba ɗaya,sunyi zaryar zuwa asibiti amma an kasa gano kan abin,har ruƙya anyi mata amma duk babu cigaba
Sai da ta shafe shekara biyu tana fama,a lokacin ne Isma'il ya ƙare karatun shi ya dawo don jinyar mahaifiyar shi
Dangin malam Ishaq ganin har lokacin yaƙi aure sai suka rinƙa zuga mahaifiyar shi,ai kuwa tace ko dai ya ƙara aure ko ta tsine masa
Haka dai ba don ya so ba aka aura masa lubabatu, auren luba uku amma bata zama, saboda fitinanniya ce ta gaske,gashi kuma sam sam bata da tarbiyya
Zuwan luba gidan ya haifar da fitina, saboda irin cin zalin da takeyiwa zainab,abinda sam Isma'il da ruƙayya basa jura, shiyasa kullum suke rigima da Isma'il,ƴan uwan mahaifin shi kuwa dama tuntuni sun daɗe da yi masa tambarin rashin tarbiyya,don sam baya ɗaukar shirmen su
Watan luba uku a gidan Allah yayiwa ruƙayya rasuwa,mutuwar ga jijjiga malam Ishaq da Isma'il ƙwarai,ita kanta zainab da bata gama wayo ba amma ta fuskanci anyi musu rashi itama ta sha kuka, hakanan itama sakina da aka sanarwa mutuwar
Sakina ta so tafiya da zainab,don dama ita har yanzu Allah bai bata haihuwa ba, Isma'il yace tayi haƙuri don bazei iya jurar rashin zainab ba
Basu juma sosai ba jarabawar su ta fito,inda tayi kyau sosai,don haka aka bashi scholarship inda zai tafi san Francisco University donyin degree É—in shi na biyu a can
Yayi murna sosai,amma sai ya fara tunanin yadda zai yi rayuwa ba tare da zainab ba, mahaifin shi ya nuna masa kar ya damu,ko shi zai iya kula da ita
To fa!tunda ya bar ƙasar zainab ta fara rayuwar wahala,duka,zagi,cin mutunci,horon yunwa,babu abinda luba bata yiwa zainab,amma ta kaɗa mata warning cewa kar ta sanar da mahaifin ta,idan ta sanar masa sai ta yanka ta,zainab akwai tsoro gashi bata da wayo don haka ko da wasa bata taɓa gigin sanar da malam Ishaq ba
Æangaren abinci kuwa,idan luba ta bata abinci tun safe bazata sake bata ba sai dare,kuma shima ba wanda zata Æ™oshi ba,ga aikin da take sanya ta wanda yafi Æ™arfin shekarunta,idan tayi ba dai-dai ba tayi mata mugun duka,da malam Ishaq ya taÉ“a kama ta ta tula mata wanki ya tambayi ba'asi sai cewa tayi
"Haba malam!idan ban koyawa zainaba aiki yanzu ba sai yaushe?idan ta girma fa ba yi zatayi ba,kuma bazata iya ba,kuma ai abin kunya ne a ce an kai zainaba gidan miji bata iya komai ba,kaga sai a zage mu a duniya a ce don uwar ta bata raye yasa muka kasa koya mata Æ´an aikace-aikacen gida"
Jin hakan ya tilastawa malam Ishaq zuba musu idanu,ƴan'uwan shi suna sane da abin da takeyi mata amma ko a jikin su,sai ma ƙara zuga ta da sukeyi
A haka zainab ta cigaba da rayuwa har Allah ya nufi Isma'il da kammala karatun shi,kuma ya samu nasarori da yawa,juna a can san Francisco Allah ya haɗa shi da faɗima, faɗima dai balarabiyar ƙasar Yemen ce
Sun shaƙu sosai da faɗima,daga mutunci lamarin nasu ya juye zuwa soyayya,amma yawanci hirar su akan zainab ne,take taji tana son yarinyar duk da bata san ta ba,amma kullum sai ta ga hotunan ta,a ƙarshe dai da kanta ta nemi idan Allah yayi sunyi aure ya dawo da ita gaban su su rike ta,yaji daɗin hakan sosai
Zainab na durƙushe tana faman yin wani uban wanki,duk da cewa zazzaɓi ne a jikin ta, sakamakon mahaukacin dukan da luba tayi mata, saboda ta aike ta da kuɗi sun faɗi, dai-dai nan Isma'il yayi sallama ya shigo
Da sauri ta ɗaga kai gami da amsawa,ganin Isma'il sai ta nemi zazzaɓin da takeji ta rasa,da gudu ta nufe shi ta ƙanƙame shi,sai ta fashe da kuka,shima hawaye ya fara cikin tsananin baƙin ciki da mamakin halin da yazo ya same ta a ciki,ya ɗago kanta cikin raunin murya yace
"Zainaba kinyi jinya ne?"
#Nusy_bee
*****MATAR KHALEES*****
âœï¸Nusy bee
Page 19
A hankali ta girgiza masa kai,yace"amma kuma jikin ki da zazzaɓi"ita dai shiru tayi bata ce komai ba
Gefe ya ja ta ya zaunar da ita,sannan ya kalli uban tulin kayan wankin,ya maida kallon shi kanta gami da tambaya
"Waye ya baki wannan wankin?"
Cikin yanayi na ciwo ta amsa"gwaggo ce"
"Ita ta baki wannan uban wankin?"ya tambaya a fusace
A hankali ta É—aga kai
Ya girgiza kai zuciyar shi cike da damuwa, lokaci guda kuma ya miƙe gami da kama hannun ta,suka shiga cikin gidan,ko ta kan kayan da ya shigo dasu bai bi ba
Kai tsaye ɗakin ta ya nufa daita ya kwantar da ita,yana fitowa suka yi kiciɓus da luba,ta firgita ƙwarai da gaske,don tasan waye Isma'il musamman akan ƴar gudaliyar nan zainaba,amma sai ta basar,cike da yaƙe da inda-inda take faɗin
"Ah!mutanen Amurika ne yau a gidan namu?Barka da sauka"
A daƙile batare da ya kalle ta ba yace"Barka"
Bai fi mintuna goma ba suka suka shigo da likita,ya dudduba zainab ya rubuta mata magunguna sannan yace a tabbatar taci abinci kafin ta sha,bayan likitan ya fita Isma'il ya tambaye ta ko ta ci abinci,ya sha mamakin jin cewa bata ci ba,cikin ɓacin rai ya fice daga gidan
Abinci ya samo mata mei rai da lafiya da kanshi ya bata sannan ya bata magani,da yaga ta ɗan dawo hayyacinta sai ya miƙe ya ɗebo kayan da ya shigo da su,ya juye mata tsarabar da yayi mata a gaban ta