Sashe 20
Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babu wanda Deeja ta sanar wa sai Mamie da Aunty kiyya,don ko Aunty Bintu bata sani ba ballantana kuma Mima,a lokacin ma mamien bata nan tana Abuja,momy Aysha bata da lafiya taje dubiyar ta
Ɗaurin aure kawai akayi,don ko walima ba'a yi ba,Deeja sai tarar rabin wanda ta aura takeyi,Aunty kiyya da Aunty Farida ne suke kula da ita,sai zainab ƙawar ta wadda zuwa yanzu ta gama yi mata komai don komawa bakin aiki
Da daddare bayan Isha'i aka kai Deeja gidan ta,sai rarraba idanu take na fargaba,don bata san me zata tarar a wannan auren ba,to Imran ma da ta san shi ta saba dashi ya aka ƙare ballantana wanda ko ganin shi bata taɓa yi ba?
Da wuri suka tafi ya rage saura ita kaÉ—ai, ban da sunan Allah babu abinda bakin ta yake ambato
Sai wajen sha É—aya taji shigowar motar shi,takure kanta tayi a cikin kujerar da take zaune,gaban ta sai dukan uku-uku yakeyi
Da sallama ya shigo,ji tayi kamar ta san muryar,har bata san sanda ta É—aga kanta da sauri don tabbatar da zargin ta ba
Ai kuwa mamaki mai tsanani ya mamaye fuskar ta ta kasa amsa masa sallamar,ba kowa bane face engineer abdurrashid Abubakar Yusuf wanda muka fi sani da KHALEES.
Shima wani kallo ya bi ta dashi alamar mamaki,kafin ya wuce zuwa É—akin shi
Itama a saɓule ta tashi ta wuce ɗakin ta,a ranar dai bata runtsa ba saboda tsananin mamaki da takaicin wannan haɗin,to ya ta ƙare da Imran ma da suke shiri ballantana wannan dimkin ɗin da ta daɗe da daina gaishe shi saboda tsabar rashin amsawa?
"Oh Ni Khadija!"ta faÉ—a a fili"nan kuma rayuwa ta jefo ni?wancan dai ga irin rayuwar da nayi a gidan shi,saura wannan mai fuskar mala'ikan tsaron wutar, kullum fuska a É—aure yana cin magani, ko Ni da na rasa iyaye na duka biyun ai bana daure fuska sai wannan da duka iyayen shi suke raye, Allah ya sani na tsani a É—aure min fuska wallahi idan naga ya cigaba da wannan mugun halin wallahi sai in........."
Maganar ta maƙale tare da hannun ta da take ƙoƙarin cire rantsatstsiyar rigar lace da ke jikin ta,jikin ta ya kama rawa sosai,ta sake murza idanu tana kallon Khalees da ya biyo ta zuwa ɗakin nata,shima dai kallon nata yake cikin idanu, fuskar tashi a ɗaure amma bazata iya cewa ga expression ɗin da yake kai ba
Dama biyo ta yayi ya kawo mata kazar da ya kawo ta al'ada daga nan ya gani ko bata lacking komai,sai yazo ya samu tana kwashe masa albarka
Sunkuyar da kanta tayi ƙirjin ta na dukan uku uku,shi kam ya taɓe baki ya ɗauke kai ya ajiye mata kazar ya fice daga ɗakin
Deeja bata sake tabbatar da baƙin miskilancin Khalees ba sai da zaman su ya miƙa,yayi mamakin samun ta a matsayin cikakkiyar budurwa duk da cewa ta taɓa aure,amma bai nuna ko a fuska ba ballantana har ya tambaye ta
Zaman nasu dai babu yabo babu fallasa,baya zama daita suyi hira,idan tayi kuskure yayi ta faÉ—a da tsawa,baya yaba mata,tun tana tsoron shi har ya zama jiki ta daina
Sai dai yana sauke haƙƙin auratayya da ya rataya akan shi,sannan bata rasa ci ko sha, kazalika yana matuƙar kulawa da ita idan ciwon ta ya so tashi ko wata rashin lafiyar,sannan kuma ya bata dama ta koma aikin ta,don ana i gobe zata koma yayi mata kyautar sabuwar mota
Ƴan uwan shi ma ba wani zuwa sukeyi ba,idan taje kuma bata samun fuska shiyasa take janye jikin ta,kuma tana shakkar shiga cikin su
Wannan shine tarihin Deeja da gwarazan ta Imran da Khalees 🥰
CIGABAN LABARIN.......
Ƙarfe biyar da mintuna biyar haka agogon ƙasar US ya nuna,a hankali take saukowa daga matattakalar jirgin janye da trolley ɗinta,tana rungume da yaron ta Affan, zuciyar ta cike da tunane-tunane,a wani ɓangaren kuma cike da farin cikin haɗuwa da ƴar uwar ta
Sai da ta samu waje ta zauna sannan ta ciro wayar ta tayi activating international mode ta fara kiran number din da Inna Mariya ta bata,bugu biyu aka É—aga
Sai a sannan fargaba ta shige ta,cikin rawar murya tayi sallama,wata murya mai cike da nutsuwa ta amsa,cikin rawar murya take faÉ—in
"Good evening ma!I am Khadija Mahmud,am talking to Dr nusaiba mahmud please?"
Matar tayi dan murmushi tace cikin harshen Hausa"eh nice auta,Inna Mariya ta sanar dani zuwan ki,kin sauka ko?"
Haba!ai Deeja ji tayi kamar an tsunduma ta a aljanna,ta washe baki tana faÉ—in"yeah na sauka few minutes ago"
"Okay!just wait for few minutes, you will be home very soon in Sha Allah"daga nan aka kashe wayar
Cikin farin ciki ta cigaba da kallon masu kaiwa da kawowa a reception na airport É—in, lokaci É—aya kuma zumuÉ—in ta ya É—an ragu tuno Khalees da tayi,ta san duk lokacin da ya dawo hayyacin shi akwai daru,to mutumin da in dai tafiyar kwana ta kama ta ko kwana É—aya ne sai tayi da gaske ballantana wadda ita kanta bata san ranar komawa ba?
Ta sauya layi, kuma babu wanda ta sanarwa tahowar ta sai Mima,wadda ta korawa warning ko da wasa kar ta sanarwa ko Aunty Bintu, ballantana yaya Ma'aruf
Ta kalli ɗan ta wanda babu inda ya baro Mahaifin shi, Allah sarki!a yadda ta san soyayyar yara irin ta Khalees da yanzu tare suke rainon abin su,amma shigowar Nadiya cikin rayuwar su ya tarwatsa musu farin ciki,ta goge ƙwallar idanun ta da sauri tana bin danƙareriyar G-wagon ɗin da ta gani tayi parking ɗan nesa da ita
Wani kyakkyawan matashi da zai iya yin Sa'an ta ne ya fito daga motar,sai sai wasu yara mace da namiji da suka biyo bayan shi
#Nusy_bee
*****MATAR KHALEES*****
âœï¸Nusy bee
Page 29
Macen zata Kai shekaru goma,namijin bai wuce shida ba,kallo ɗaya tayiwa macen gaban ta ya faɗi,don ko ina yarinyar nan ta fito bata da maraba da abban ta,tayi musu kuri har suka ƙaraso in da take zaune da murmushi a fuskar su
Sallama sukayi mata,ta amsa itama fuskar ta a sake,cikin murmushi matashin yace"Deeja, right?"
Gyaɗa Masa kai tayi tana murmushi tace"yeah"yace"wow!very nice!!you are highly welcome, let's go, Aunty nusaiba is waiting for you"ta miƙe tsaye,yarinyar tayi saurin amsar Affan suka wuce suka nufi motar
A motar Æ´ar ta macen ta kalli Deeja tana murmushi tace"Aunty Deeja what's his name?"tana nuno mata Affan
"Mahmud,known as Affan,what about You and your brother?"
"I am ZAINAB known as amra,my brother is Ismail known as ajmal,and this is Uncle safwan"ta ƙarashe tana pointing matashin, murmushin fuskar ta yana nan
Wata ajiyar zuciyar farin ciki tayi tana sake rungume yaran tana jin ƙaunar su a ranta, Safwan da ke gaba yana driving yana kallon su ta madubi yana murmushi
Suna isa bakin tangamemen gate ɗin gidan Dr nusaiba Safwan yayi horn, guard ɗin ƙofar ya ɗage, zumuɗin Deeja ya ƙaru, Allah Allah kawai take ta ganta a gaban sister ɗin ta
A balcony É—in suka tsaya,shi dai Safwan bai ma shigo ba,daga nan fita yayi uzurin gaban shi don ya bawa Æ´an'uwan damar ganawa da junan su sosai
Intercom Amra ta matsa,within some seconds Aunty nusaiba ta bayyana
Fara ce tas kamar abban ta,babu in da tabar shi sai yanayin idanun ta irin na maman su(zainab)doguwa ce mai madaidaicin jiki,ta saki baƙin gashin ta irin na Deeja sak da suka gado daga zainab har gadon bayan ta,alamun hutu da gyara sun gama bayyana a tare da ita,wani idan ya ganta zai ɗauka bata wuce sa'ar Deeja ba
Ba sai ance wa Deeja ga yayar ta ba,babu ɓata lokaci ta faɗa jikin ta ta ƙanƙame ta ta fashe da kuka,ita dai nusaiba murmushi takeyi tana shafa bayan ta,wata nutsuwa ce ta shigi Deeja,don sai ta ji tamkar jikin mahaifiyar ta ne,lallai Bature yayi gaskiya da yace(blood is thicker than water
Sai da Aunty nusaiba ta ja ta zuwa parlourn sannan ta sake rungume ta tana goge mata hawayen tana faɗin"is okay! shikenan,ai kuma kuka ya ƙare,ko nima taɓarar zaki yi min?don ance min dama baba da Abba sun sakalta ki ko?"ta ƙarasa da sigar tsokana tana murmushi
Tura baki Deeja tayi tana faɗin"Ni Allah bani da taɓara"
"Naji,ina su yaya Ma'aruf?"da sauri ta kalle ta ta É—aure fuska tace "bai san nazo ba,bana son ya sani for now please"
Nusaiba ta buÉ—e ido ta kalle ta tace"to ta yaya zai sani?"
Deeja ta juya hannu tana faÉ—in"na sani ko kuna communicating?"
Ƴar dariya nusaiba tayi tana dungure mata kai tana fadin"lallai dai naga autar mamma,babu inda kika bar halin ta Allah yaji ƙan ta,bari nayiwa su Amra magana su kawo babyn nan ku samu ku yi wanka ku ci abinci ku huta"daga nan ta wuce zuwa ɗakin su Amra
***** ***** *****
Cikin shagwaɓa ta kalle shi tana faɗin"haba honey!kana kallo na maƙaryaciya ne?ka duba da kan ka ma ka gani,wallahi abubuwa da yawa sun ƙare,idan baka siya ba wa zei siya min? Please mana my gentle"ta ƙarashe tana kwanciya kan kafaɗar shi
Ya kalle ta cikin ƙosawa da halayen ta yace"umaima!wallahi na gaji,daga Ni sai ke kawai a gida amma ko waɗanda suke rayuwa su goma basu kai mu cin kuɗi ba,yau kwana tara kawai da yin monthly shopping Amma har abubuwa sun ƙare,zubarwa kikeyi ne ko me?naga dai ba ƙananan kuɗi nake kashewa ba amma a banza,to wallahi nan da next one week Kar ki saka ran zan sake siyo ko tsinke"
"Haba my heart,ka daure mana,Ni a gani na duk abinda kayi min ai baka faɗi ba ko?"cikin shagwaɓa da kissa take maganar
Ko kallon ta bai sakeyi baya miƙe yana ƙarasa sanya rigar suit ɗin shi, yana gama shirya wa ya ɗauki briefcase ɗin shi bayan ya saka sau cikin shi ya fice daga ɗakin,ta biyo shi har harabar gidan kamar yadda suka saba
Yana ƙoƙarin buɗe motar shi yaga mai gadin yana ɗage gate ɗin gidan,daga shi har umaima suka bi motar da ta shigo da kallo,wata farar mota ƙirar GMC ce ta shigo cikin gidan,suka bi motar da kallo don ganin waye wannan ya kawo musu ziyara da wannan farar safiyar