← Book details Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 31

Sashe 11

Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har parlour suka shigo suna hira da dariya, Nadiya ta fito da sauri,ganin su Deeja a haka ya tabbatar mata da babu matsala,nan da nan ranta ya ƙara ɓaci,Deeja na kula da ita,amma sai ta nuna tamkar bata ganta ba

Deeja ta cigaba da gudanar da rayuwar ta yanda ya kamata,har zuwa sanda su Aunty Bintu zasu tafi ƙasar Syria,tafiyar ta kama ranar Lahadi,don haka ranar ta kama babu aiki,don haka Deeja taje yi musu sallama

A can ta yini,itace ta kai su airport,a gaban ta akayi komai ƙarfe biyar na yamma jirgin su ya tashi,itama ta juya zuwa gida

A falo ta samu Nadiya da umaima da ƙawar su siyama zaune suna hira,da farko ƙin shiga tayi ta tsaya daga bakin ƙofa don jin mei zasu ce

Umaima taji tana faɗin"ai tunda kin ce aikin baya cin ta na samu wani boka ya bani wani magani tace ayi haƙa a ƙofar ɗakin ta a binne,to tabbas zata gamu da hauka idan ta tsallaka,kinga tana can tana hauka,ga miji ya dawo naki ke kaɗai,yaron kuma zai dawo ƙarƙashin ki,kin ga sai kiyi abin da kika ga dama ko?"

"Kuma nima akwai wani hatsabibin boka da na samo,ya bani siddabaru yace na binne a maƙabarta,hakan zai sanya ya tsane ta har yaji baya ƙaunar ko ganin ta a kusa dashi,kinga dole ta bar gidan ko na uban ta ne"

Nadiya ta amsa"good job! Allah ya bar mu tare,da alama kuna damuwa da al'amura na,idan na gama da ita sai na koma kan waÉ—annan matsiyatan Æ´an uwan nashi,nan gaba ko kallon shi zasu yi sai dai daga nesa

Umaima ta buɗe baki da niyyar yin magana Deeja ta faɗa falon fuskar ta babu alamun damuwa,duk da cewar ta tsorata da lamarin su,ganin ta sai suka sha jinin jikin su,ta ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya a raine,sannan ta ɗauke kanta ta shige ɗakin ta

Sun firgita sosai,don sun ga alamun hirar su,don haka suka chanja hira

Tun daga lokacin ta sake zage dantse ga kulawa da take bawa kanta da yaron ta,a haka har tsawon sati guda

A lokacin ne Khalees ya dawo,a lokacin Deeja bata nan tana wurin aiki,don haka Nadiya ta samu cikakkiyar damar ƙulle ƙullen ta na kissa da kisisina da sharri,shi kuwa Khalees ya bi ya haye kai

Da ta dawo tun a parking space taga motar shi,hakan ya tabbatar mata da dawowar shi,hakan bai dame ta ba,kanta tsaye ta shigo cikin gidan

Bata same su a parlour ba,hakan bai dame ta ba ta shige É—akin ta

Bayan Isha'i tana jin su a parlour suna ta shewar su,ta so ta fito amma sai ta tuna da cewa zai iya yi mata wulaƙanci a gaban Nadiya,don haka tayi zaman ta a cikin ɗakin ta

Washegari sun haÉ—u dasu a kitchen,batare da damuwa ba ta gaishe su,amma ko kallon banza bata samu ba,bata damu ba ta cigaba da harkar gaban ta, Nadiya sai kwarkwasa da kisisina takeyi masa,shi kuwa sai faman tarairayar ta yakeyi,ko kallon su Deeja bata sake yi ba,tayi aikace-aikacen ta ta kammala ta fice daga kitchen É—in

Tsawon kwanaki uku kenan,da dawowar Khalees,amma ko sannu bata haɗa su da Khalees ba,idan tayi masa magana ma baya amsawa, don haka ta haƙura da yi masa magana

Dawowar ta kenan daga Wajen aiki,tana shigowa parlourn taji an bangaje ta,da sauri ta É—ago don ganin waye, Nadiya ce

Ganin Nadiya ce ta san magana take nema,don haka ta mayar da kallon ta kan fuskar wayar ta

Dawowa tayi da baya ta kalli Deejan a ƙasƙance tana faɗin"oh sorry fa!na ɗauka akuya na bangaje shiyasa kika ga ban damu ba"

Wani banzan kallo Deeja ta watsa mata sannan tace"kar ki damu,nima dama sai naji kamar bangazar batayi min kama da da ta mutum ba,nayi tsammanin tinkiya ce ta bangaje ni shiyasa ban kula ba"

A zafafe Nadiya tazo wajen tana yi mata kallon wulaƙanci tace"ke!ki shiga taitayin ki ko kuma jikin ki yayi tsami"

Wani watsatstsen kallo Deeja ta watsa mata na sama da ƙasa sannan tayi wani murmushin rainin hankali tace"haba yarinya!ko wanda ya dire ki bai isa ba ballantana ke!!"

Cikin É—aga murya ta shiga faÉ—in"wanda ya kawo ni fa kika ce, luvly kana jin abinda kike cewa"

FaÉ—ar hakan ya tabbatar wa Deeja cewa Khalees ne ya shigo parlourn,sai ji tayi yace

"Ai tuntuni dama ta nuna tafi ƙarfi na,don haka dole ta bar min gida na"ya ƙaraso inda Deeja take ya zaro takarda a envelope ya miƙa mata yana duban ta a wulaƙance yace"kije na sake ki saki ɗaya,ki tattara ki bar min gida,dama ban ɗora miki idda ba"

Gaban ta ne yayi mummunan faÉ—uwa a ranta ta furta"innalillahi wa Inna ilayhi rajiun"tare da amsar takardar,bata kuma magana ba ta wuce É—aki

Tana jiyo shewa da habaice-habaicen nadiya,tayi mata banza,ta kwashi abubuwan ta masu muhimmanci ta zuba su a mota ta fice daga gidan

Sai da tayi Æ´ar doguwar tafiya sannan tayi parking tana nazarin wajen zuwa,daga bisani ta yanke shawarar wucewa gidan ta da ta gina, saboda dama tuni ta zuba komai

Ƙerarren gida ne dake unguwar Na'ibawa,duk da ƙarami ne amma ya tsaru sosai,ta shigo da motar ta ta rufe gidan ta shiga ciki

Kwanan ta biyu babu wanda ta sanarwa mutuwar auren ta,sai dai akwai abinda ta shirya,don a ganin ta lokaci yayi da ya kamata ta samu farin cikin da ta rasa shekaru masu yawa,don haka ta É—auki hutu a wajen aikin ta,ta soma shirye shiryen barin garin

Satin ta biyu ta gama shirya komai,motar haya ta hau airport,daga nan ta haye jirgin su zuwa in da take fata...

Ayi min afuwa Please

"Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 17

Ƙarfe uku na yamma ta sauka a garin jimeta da ke Adamawa,ta sha wahala sosai kafin ta gano address ɗin gidan da Dr Mahmud ya taɓa bata kafin rasuwar shi saboda bata san garin ba,bata samu kanta a ƙofar gidan ba sai bayan huɗu na yamma

A bakin gidan ta samu wani dattijo,tayi masa sallama ya amsa,ta durƙusa cikin ladabi ta gaishe shi cike da girmamawa,ya amsa yana ƙare mata kallo,bayan sun gaisa ya dube ta yana faɗin

"Yarinya idan na gane ki zan iya cewa autar wajen ZAINABA ce ko?"

Murmushin Deeja ya faÉ—aÉ—a,tace "eh baba,nice autar ta"

"Allah sarki zainab! Allah yayi mata rahama ya kyauta makwanci,ita da mai gidan na ta"

Deeja ta amsa da"ameen cikin sanyin murya"

Yace "ki tashi ki shiga ciki,mariyan tana ciki"Deeja ta miƙe zata shiga,yace "kawo yaron,ko bacci yakeyi?"

Deeja ta amsa da"bacci yakeyi"

"Allah sarki!yaya sunan shi?"

"Sunan mahaifi na ne amma ina kiran shi da Affan"

"Allah sarki! Allah ya raya shi"

Ita dai Deeja tayi shigewar ta gidan

Da sallama ta shiga tana rarraba idanu,wata dattijuwa na zaune tare da samari da ƴan mata a tangamemen tsakar gidan, ƙarƙashin wata ƙatuwar bishiyar mangwaro,sai hira sukeyi,da alamu dai jikokin ta ne,duka suka dawo da hankalin su kanta

Ta É—an daburce kafin daga bisani ta daidaita nutsuwar ta,ta gaishe su sannan ta fara bayani cikin dakiya

"Ni ƴar gidan zainab ce,ƙanwar su nusaiba da Yusuf"

"Ai na ga alamu, Allah yaji ƙan zainaba, Hadiza ce ko?"a cewar dattijuwar

"Eh nice"ta bata amsa kanta a ƙasa

"Masha Allah!ke suwaiba maza kai ta ɗaki tayi sallah ta huce gajiya,ki kai mata abinci maza"kafin ta rufe baki ɗaya daga cikin ƴan matan ta miƙe ta karɓi akwatin Deeja ta jagorance ta zuwa wani ɗaki

Bayan Isha'i Deeja ta kammala komai da komai,ta nufi É—akin Hajiya Mariya,tayi sallama

Hajiya Mariya ta amsa tare da yi mata yi mata izinin shigowa,ta shigowa,ta shiga gami da neman waje ta zauna,Hajiya Mariya ta dube ta cikin kulawa tana faÉ—in"ina mahmudun?"

"Yayi bacci"ta amsa mata

"Da kyau,kinyi masa adduoi kuwa?"

"Ai bana sanya,inayi masa sosai"

"To Allah yayi muku albarka gaba É—aya"

"Ameen Inna"

Hajiya Mariya ta kalle ta sosai tace"da alamu akwai magana a bakin ki ko?"

Deeja ta gyara zama tace"eh Inna,dama Abba ya sanar dani cewa kece kika raini yayye na Nusaiba da Yusuf,shine nazo na gansu, saboda tsawon lokaci ban gansu ba"

Hajiya Mariya tayi murmushi tace"hakane,tabbas Ni na karɓi Yusuf da nusaiba,a gaba na suka tashi,amma daga baya sun koma hannun babban ɗa na dake can ƙasar America dazama,a can sukayi karatu,a can nusaiba tayi aure,shi kuma Yusufu ya matsa sai dai yanzu ban san a in da yake da zama takamaimai ba, kasancewar ba ma a American ya zauna ba"

"Amma ina meyasa aka raba mu?gashi ban shaƙu dasu ba"a cewar Deeja cikin damuwa

"Labari ne mai tsawo Hadiza,idan zaki yi jumuri sai na gaya miki,har da labarin mahaifiyar ki ma"

"Ki bani Inna,dama an ce mahaifiya ta ma tayi haƙuri sosai,zan so na san labarin ta"

Hajiya Mariya tayi murmushi tana kallon Deejan

WAIWAYE............

Malam Ishaq cikakken malami ne mai cikar kamala da sanin ya kamata,yana daga cikin manyan malamai masu karatu da akeji da su a wancan zamanin

Yana da mata ɗaya da yara biyu,matar shi ruƙayya mace ce mai sanyin hali da sanin ya kamata,gata da kirki da mutunci,babu wani wanda zai ce ga abinda tayi masa na ƙuntatawa

Sai dai dangin malam Ishaq sun matsa mata ƙwarai da gaske,a cewar su ta hana shi ya ƙara aure,shi kuma yace aure lokaci ne,idan lokacin ƙarawar yayi ba sai an gaya masa ba

Ismail da sakina yaran su sun taso cikin gata da tarbiyya,sai dai basa iya kaiwa dangin su ziyara saboda tsangwamar da suke sha daga wajen su

Daga baya kuma sai suka dami malam Ishaq da batun ruƙayya bata haihuwa sosai,tun daga kan sakina bata ƙara haihuwa ba,kuma sakinan shekarunta goma sha shida

Rana tsaka malam Ishaq yazo da batun abokin shi ya bashi yarinya,zai ƙara aure,hakan ya tashin hankalin ruƙayya sosai,don tsoro take ji kar ya zamana dangin mijin ta zasuyi amfani da amarya su fitar daita daga gidan,amma sai ta fawwalawa Allah

Anyi auren malam Ishaq da Amina, yarinya ce da bazata wuce sa'ar Isma'il ba,sai dai ga dukkan alamu yarinyar ta samu ingantacciyar tarbiyya,don duk zugar da dangin mijin ta suke mata sai dai ta ji su da kunne,wanda hakan ya dawwamar da zaman lafiya tsakanin ta da ruƙayya,kuma babu wanda ya kai ruƙayyar jin daɗin dacen da tayi na abokiyar zama
Chapter 11 · 0% Book details