← Book details Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 31

Sashe 17

Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dr su'ad ta girgiza kai tace"ba wannan bane,don da alamu ciwon ya kwana biyu a tare da ita, and it's better a kula da ita yadda ya kamata,gudun samun wata matsalar again"bai sake magana ba ya juya ya fice daga office É—in cikin mutuwar jiki,Dr ta biyo bayan shi

Waje ya samu ya zauna yayi tagumi,ya kai mintuna sha biyar a zaune kafin abokin shi Khalees ya shigo reception É—in

Ya kai mintuna biyar a tsaye a kan shi amma bai san yazo ba,sai da ya taɓa shi sannan yayi firgigit kamar wanda ya tashi daga bacci

Khalees ya samu waje ya zauna kusa da abokin nashi,ya zaro wayar shi daga aljihu ya miƙa masa,ya amshi wayar, cikin nutsuwa Khalees ya kalle shi yace

"Ana ta kiran ka don ayi maka ta'aziyya amma baka tare da wayar ballantana ka É—aga,sai yanzu naje gidan naku Abida ta shaida min abinda yake faruwa ta bani wayar na kawo maka,ya mai jikin?"

"Da sauƙi"ya bashi amsa cikin matsananciyar damuwa

Shiru sukayi su duka, Ma'aruf damuwar da yake ciki ta hana shi magana,shima Khalees duk da cewa akwai damuwar dama can shi ba mai yawan magana bane

Sun kwashi kusan rabin awa kafin Imran ya shigo reception din,yayi musu sallama suka amsa,cikin mamaki Khalees yace"isn't you Imran alƙasim?"

"Yeah abdurrashid Abubakar!dama zan sake ganin ka?many years ahead!"Ma'aruf yana kallon su da mamaki akan fuskar shi, Khalees ya kalli Ma'aruf cikin murmushi yace"he is friend of mine lokacin da nayi boarding school a Bauchi,a good friend of mine"

"Wow!very nice!Ashe kun san juna?"a cewar Ma'aruf da ɗan murmushin yaƙe a fuskar shi,don ya fara zargin kamar Imran ne silar ciwon Deeja

Imran ya gyaɗa kai yana murmushi,sannan ya ɗan kalli Ma'aruf yace"ya ƙarin haƙuri kuma?"Ma'aruf yace"haƙuri mun godewa Allah"

Imran yace"to Allah yaji qan shi yayi masa rahama, Allah ya albarkaci bayan shi ya sada shi da annabin rahama, Allah ya bada haƙurin rashin shi"Khalees da Ma'aruf suka amsa da ameen,Imran ya ƙara cewa "ya mai jikin? fauwaz ya sanar dani tayi collapse tun jiya?"

Ma'aruf ya ja ajiyar zuciya yace"yeah,Amma for now da sauƙi,don ta dawo hayyacinta yanzu ma bacci takeyi".

Imran fa ka tara maƙiya,ya kamata ka kama kan ka,don kowa yace baya yin ka😁

#Nusy bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy_bee

Page 25

"Okay to bari na shiga na ganta"a cewar Imran,bai jira cewar su ba ya shiga don ganin Deeja

Kwanan Deeja shida a asibitin aka sallame ta,,ta rame tayi zuru-zuru,ta sake zama so silent,Wai a haka kullum Ma'aruf,matar shi fareeda da su Aunty Bintu suna kusa da ita suna tausar ta,baba Prof ma sau uku yana zuwa duba ta, mamie kam ita da yaran ta kullum suna hanya,yanzun ma da aka sallame ta kai tsaye Mamie ta wuce da ita can gidan

Ta kai kwana goma kafin ta dawo hayyacinta,su mamie da yaran ta suna tarairayar ta da mantar da ita damuwar ta,hakan ya sa ta fauwalawa Allah komai ta kwantar da hankalin ta

Ta kai kimanin sati uku a gidan bana Prof kafin mamie ta mayar da ita gidan ta,tun a ranar da ta koma umaima ta tare ta da wulaƙanci iri-iri,sam bata gaban ta don yanzu abinda ya dame ta ma dabam, tuni ta kama harkar gaban ta

Cikin lokaci ƙanƙani shima Imran ya dawo da ainihin siffar shi,suka ƙara santa Deeja a gaba da cin mutunci iri-iri

Sai ya zamana idan ta fita aiki bata son dawowa, Saboda Imran ya ƙuntata mata sai ya hana ta zuwa aikin,haka tana ji tana gani ta ajiye aikin ta da take matuƙar so

Yau watan ta biyu da dawowa gidan Imran,da kaɗan kaɗan sai da ciwon ta ya kai ta ga kwanciya,yau kam ta wayi gari da tsanantar ciwon don yadda numfashi yake wahalar daita kamar mai athma,don haka ta yanke shawarar zata je asibiti don gwada lafiyar ta,don haka Imran yana shirin fita ta same shi shi da umaima a bakin motar shi tana zuba masa shagwaɓa

Tayi musu sallama,Imran ya amsa amma fuska a ɗaure,ita kuwa umaima wani kallon banza ta bi ta dashi kafin ta taɓe baki ta ɗauke kai

Cikin sanyin murya ta gaishe shi,ya amsa a daƙile sannan yace"me ya kawo ki?"

"Bana jin daÉ—i ne,ina son zuwa asibiti"ta bashi amsa cikin yanayin ciwo

Ƙare mata kallo yayi daga sama har ƙasa,eh tabbas ga alamu nan ya gani,amma sai yace"sai ki jira,ƙarfe tara zan zo na kai ki asibitin"

Cikin Muryar ciwo ta amsa da cewa to "to na gode, Allah ya dawo da kai lafiya"ta juya ta koma cikin gida,tana jin umaima na jan dogon tsaki,ko kallo bata ishi Deeja ba

Kafin ƙarfe tara fa gama shirya wa duk da bata da lafiya,amma Imran shiru,har goma shiru,da taga sha ɗaya tayi sai ta fara neman shi a waya,amma sai ya rinƙa danna mata busy,ganin hakan bai wani bawa Deeja mamaki sosai ba, instead ma sai ya kira ya'yan ta Ma'aruf ta shaida masa

Shiru yayi cikin mamaki da haushi,can yace"shi Imran É—in ne yace ki jira shi kuma yake katse miki kira?"

Deeja tace "eh"

"Gaskiya Imran ya bani mamaki,ban zaci zai yi haka ba,kar kiyi wasa da lafiyar ki,maza ki shirya kije ki ga doctor su'ad,don kema kin san ciwon ki bana wasa bane"

Ta amsa da"to"sannan ta kashe wayar

Shiryawa tayi cikin ƙarfin hali ta fice zuwa asibitin Dr su'ad, Dr tayi mata gwaje-gwaje ta tabbatar mata dole sai anyi admitting ɗin ta,don babu wani improvement da aka samu yanzu

Deeja Imran ta fara turawa text message ta sanar masa sannan ta turawa Ma'aruf

Ko awa É—aya baayi ba Ma'aruf da Farida suka bayyana, Farida ce ta zauna a wajen Deeja,shi kuma Ma'aruf da ya ga babu matsala ya wuce wajen aikin shi

Wajen ƙarfe uku fareeda na zaune a kujerar da ke gefen gadon da Deeja take kwance,sai kallon ta takeyi tana mamakin yadda ta ƙara ramewa ta lalace,Imran yayi sallama ya shigo

Cikin nutsuwa ta amsa,ya shigo cikin ɗakin,suka gaisa a mutunce ya tambayi ya mai jikin?ta amsa da sauƙi sannan ya dire mata dubunnan kuɗaɗe a matsayin kuɗin magani,sannan ya ɗora wata envelop akai yace

"Kuɗin nan na magani ne,wannan envelop ɗin saƙo ne idan ta tashi ki bata"

Ta amsa da"to shikenan"ya miƙe ya nufi hanyar fita yana faɗin"Allah ya bada lafiya"

Farida ta amsa da"ameen"

Wajejen ƙarfe huɗu da rabi Deeja ta farka,Farida tayi mata sannu,ta haɗa mata ruwan wanka,tayi wanka ta ɗauro alwala tayi sallah,sannan ta gabatar mata da abinci, kaɗan taci saboda gaba ɗaya hankalin ta yana gida

Bayan ta dawo nutsuwar ta fareeda ta bata saƙon mijin ta, kuɗi ne kimanin 500k,sai envelop,ta ajiye kuɗin sannan ta buɗe envelop ɗin

Sai da taji gaban ta ya yanke ya faÉ—i,don haka sai ta fasa warware takardar tayi shiru tana fargabar abinda zata riska

A lokacin Farida bata ward É—in,ta fita zuwa office É—in Dr su'ad

Cikin dakiya ta É—aga takardar ta warware ta a hankali,gaban ta yana dukan uku-uku ta soma karantawa

Assalamu alaikum

Nasan ba za kiyi mamakin ganin saƙo na ba saboda kema kin san me kikayi kuma tun da can ma kin san zaman haƙuri nakeyi da ke, saboda ba son ki nakeyi ba,kullum cikin saɓani da mahaifiya ta nake a dalilin ki,wato yanzu har ta kai zan ce kar kiyi abu,kuma kiyi, gaskiya bazan iya da halayen ki ba

A don haka na yanke duka igiyoyin aure na da ke,inayi miki fatan alkhairi, Allah ya baki wanda ya fi ni"
Imran alƙasim

Bayyana irin tashin hankalin da ta shiga ma ɓata baki ne,ta miƙe a gigice tana furta"innalillahi wa inna ilayhi rajiun"dai-dai nan Farisa da Dr su'ad suka shigo

Da sauri suka ƙaraso suna faɗin"lafiya dai Deeja?me yake faruwa?"bata ƙarasa faɗa ba sai gani sukayi Deeja ta sulale ƙasa,ko alamar motsi babu a tare da ita

A gigice tayi ƙasa ta fara girgiza ta tana ambaton"Deeja! Deeja!!"amma ina babu alamun rai a tare da ita,ita ma dai Dr su'ad a gigicen take, sai dai tayi ƙoƙarin saita kanta ta bata taimakon gaggawa

Hakan yayi matuƙar gigita su ganin still babu wani improvement,Farida tayi waje a matuƙar kiɗime,karo sukayi da Ma'aruf.....

Gaskiya fa ko ni na fara jin tsoron Imran 🥺

#Nusy_bee

****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 26

Zubewa tayi a ƙasa tana haki cikin tashin hankali,da sauri Ma'aruf yaja baya yana faɗin"subhanallahi!me ya faru ne?"

"Deeja!Deejan mu ta mutu"a cewar ta cikin tashin hankali

Cikin sauri ya faÉ—a É—akin,daidai lokacin wasu nurses suka shigo alamun Dr su'ad ta sanar dasu,da sauri aka É—auke ta aka nufi emergency room da ita

An kai kimanin awa biyu kafin a shawo kan matsalar,abin ya ɗagawa kowa hankali, musamman Farida da take ta gursheƙen kuka, saboda ta sani tuntuni kaf ƙannen Ma'aruf da Deeja kaɗai suke shiri saboda su faiza basu da mutunci sam,haka ya janyo musu shaƙuwa,ta sani in dai ta mutu to tabbas zata shiga wani hali

Su kansu likitocin sunyi mamakin abinda ya taɓa ciwon nata lokaci guda,sukayi musu warning akan cewa su kula da duk abinda zai ɓata mata rai

Abin ya bawa Farida mamaki, saboda ta san dai har ta fita babu alamun damuwa a tare da Deeja

A sanyaye ta koma ɗakin da aka kwantar da Deeja,ta fara tattare kwanukan da Deejan ta kammala cin abinci,har ta gama sai ta kula da takardar saƙon Deeja a yashe a ƙasa,kamar kar ta ɗauka sai kuma taga gwara ta ɗauka,ta ɗauka ta buɗe ta karanta

"Innalillahi wa Inna ilayhi rajiun!!!"ta furta cikin ƙaraji

Sai ta zubar da kayan ta ruga wajen da Ma'aruf yake tsaye,cikin kuka ta miƙa masa takardar

Ma'aruf ya girgiza sosai ya gyaÉ—a kai tare da faÉ—in"lallai babu shakka Imran ya cika butulu"

Farida cikin kuka tace"ai wallahi bazai gama da duniya lafiya ba, Allah ya sai ya bi mata haƙƙin ta"

Baƙin ciki da takaici ya hana Ma'aruf sake magana,ita kuwa Farida kuka take tana la'antar Imran

Da Deeja ta dawo hayyacinta Farida ce mai tausar ta tare da bata shawarar ta manta da wani Imran ta cigaba da rayuwar ta,Hajiya mamie tazo,jin abinda Imran yayi ya girgiza ta matuƙa,abin yayi mata ciwo,amma ganin momy Aysha ta fita shiga tashin hankali har da kuka sai ta saukar da nata fushin
Chapter 17 · 0% Book details