Sashe 6
Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yunwa nakeji Ni kam,bazan iya fahimtar zancen ka ba"
"Don Allah ki taimaka min,zan samo ko me kike so ki ci, maganar ba mai tsawo bace"
Zaune ta tashi tana cike da mamakin sauyawar Khalees lokaci É—aya amma har yanzu ta hana hakan bayyana akan fuskar ta
"Khadija me ya sauya ki ne?"me ya sauya min ke ne?me ya same ki ne?"
"Me nayi?"ta faÉ—a cikin É—aure fuska
"Menayi miki da zafi haka kika tsane ni?kike son yi min asarar ɗa na?"ƙwalla ta cika idanun shi
Sai jikin Deeja ya fara rawa, Khalees ya cigaba da cewa"ko da ace wani laifi nayi miki bei kamata ki hukunta Ni ta wannan hanyar ba,balle ma me nayi miki?"
Deeja ta dake tace"haba Khalees!ai girman ƙiyayyar da kakeyi min ta fi ƙarfin wani gama garin laifi,to baka san saniya me zaka yi da ƙahon ta?baka so na me zaka yi da ɗa na?"
Da sauri ya katse ta yana faÉ—in"Khadija wa yace Miki bana son ki?me yasa kika ce haka?kin san yadda nakejin ki a raina kuwa?kwana biyu da kikayi bakya nan kin san a halin kewar da na kasance kuwa?idan kika ce haka bakiyi min adalci ba"
Daga inda take tana iya jin sautin bugun zuciyar shi,hakan ya sanar da ita irin tashin hankalin da yake ciki, cikin sanyin murya tace
"To meyasa baka nuna min so kamar yadda kowaɗanne ma'aurata suke gudanar da rayuwar su?ban taɓa yin abu ka yaba ba,sai dai idan nayi kuskure ka janyo min ɓacin rai, tsakani na da kai kallon banza,tsawa,baƙar magana sai kace baiwa,kayi min adalci saboda Allah?"hawaye suka ciko idanun ta
Ba ƙaramin abu ne yake sanya Deeja kuka ba,ya daɗe da sanin hakan,da sauri ya goge mata hawayen sannan yace
"Khadija, wallahi tallahi ba da nufi nayi miki abinda nayi miki ba,nayi hakane don na nisanta kaina dake kar ki illata ni kamar yadda sauran mata na sukayi min
Khadija! mahaifi na bai taɓa bani damar auren zaɓi na ba, karon farko ya aura min fadila,fadila ta kasance malalaciya,babu abinda ta iya sai rashin wda nuna ita wata ce,gashi a ƙarshe tace bazata haihu yanzu ba don kar ta tsufa,wannan ne yayi sanadin rabuwar mu
Banyi cikakken wata uku ba daddy ya kuma zaɓa min suhaima,ita kam lamarin ta yafi na fadila muni,don kwata kwata bata zaman gida,ga sace sace kamar ɓera,ban isa nayi ajiya a gida ba sai ta ɗauke,na sanar da Daddy Amma sai yake ganin kamar ƙarya nayi,haka nake ta haƙuri daita
Rana tsaka ta tayar da ballin sai na sake ta,na sanarwa Daddy abinda ke faruwa,ya kira mu sa niyyar yayi mana sulhu,amma sai ta baÉ—awa idanun ta toka ta ci masa mutunci,ganin haka Daddy ya bar Ni na sake ta
Bai daddara ba,naje Egypt na dawo bayan naje gaishe shi yake shaida min cewa yayi min aure, hankali na ya tashi,amma hakan na daure na amshi maganar da girmamawa, musamman ma da aka ce min ƙanwa ta ce aka aura min
Labiba,itace ƴar ƙanwar Daddy da aka aura min,itama sam bata da lokaci na,ta sha fita ƙasashen waje batare da sani na ba,da sunan tana zuwa kasuwanci,tun abin na damu na har na cire shi a raina
Baƙar ranar da bazan iya mantawa daita ba itace ranar da na kama labiba da wasu mata suna sheƙe ayar su,abin nan ya gigita Ni sosai,kafin nasan abinyi labiba ta buga min wani abu a kai na da ƙarfi,na daɗi sumamme, ita kuwa ta tattare duk wani abu mai muhimmanci da tasan inayin amfani dashi ta gudu
Sai da nayi kwana biyu a asibiti sannan na samu kaina, mahaifiya ta da sauran ƴan uwana sun shiga matsanancin tashin hankali suka yi ta roƙon mahaifi na akan yayi haƙuri ya bar ni na samu zaɓin raina ko Allah zai sa a dace,amma sai yace har yanzu Ban mallaki hankalin kaina ba,kuma a lokacin ina da shekaru talatin da biyar zuwa da shida
Ganin irin kafiyar shi ya fusata mu,muka ɗauki aniyar duk macen da ya ƙara aura min sai mun matsa mata mun takura mata har ta gudu ta bar mu,cikin ikon Allah sai kika zama mace ta gaba
Wannan shine dalilin da yasa bakya samun afuwa a wajen mu ko, ko ni ko hajiya ko qanne na
Wallahi ba don Bama son ki ba,don uzzurawar daddy,Amma kiyi haquri ki yafe mana,haƙiƙa mun aikata kuskure
Kuka sosai Deeja ta fashe dashi na tausayin mijin nata,ya janyo ta ya rungume ta yana sauke numfashi,da ƙyar ya lallashe ta tayi shiru,sannan ya miƙe ya nufi kitchen don samar mata abinda zata ci
***** ***** *****
Tana kwance jikin kafaÉ—ar shi ta É—ago idanun ta ta kalle shi tace
"Honey!"
Kallon ta yayi batare da ya amsa ba,ta tashi zaune sosai tana fuskantar shi tace"honey tambayar ka nake son yi"
"Okay Ina jin ki, Allah yasa na sani"
"Ranar bikin Yasmeen na ganka tare da wani,wanene shi don Allah?"
"Wa kenan?"ya sake tambayar ta
"Wani kyakkyawa kamar kai,amma da alamu zeiyi jin kai"
#Nusy bee
*****MATAR KHALEES*****
âœï¸Nusy bee
Page 9
Wani mugun kallo ya watsa mata,tayi dariya tace"haba my king, wallahi ka fi dukkan maza a waje na,so nake nasan waye shi?"
"Ban gane shi ba"ya faÉ—a yana sassauta fuska"
"Haba!wani mei shadda sky blue!naga kun fito daga falon Mamie tare"
"Ooooooo! Na gane, engineer abdurrashid kike nufi"
"Yauwa,ƙawa ta Nadiya ce ta ganshi,kuma yayi mata"
Wani watsatstsen kallo ya jefa mata yace"to yana da aure idan baki sani ba"
"And so what?ba namiji bane?ai shi namiji mijin mace huÉ—u ne"
"Eh lallai umaima!to mijin Khadija ne"
Ta É—an bi shi da kallo kafin tace"wacece khadija?"
Ya amsa da cewa"tsohuwar mata ta"
Taɓe baki tayi tace"to wacece ita? sai me?"
"Kinyi silar barin ta gida na,bazan taɓa bari kiyi silar barin kiyi silar barin ta gidan Khalees ba, saboda ta bani farin ciki ta bani walwala a lokacin da na rasa walwala,ta zamar min bango a lokacin da na rasa masafa,ni kuma na kasa yi mata halacci,na baɗa mata ƙasa a ido,na guje ta a lokacin da take buƙatar kulawa,don haka kawai ki bawa ƙawar ki haƙuri"
"Abinda bazei yiwu ba kenan!"a cewar umaima
"Okay!sai kiyi duk abinda kike ganin zaki iya"
"Zanyi kuwa"tana faÉ—a ta fice daga É—akin,ya bi ta da kallo
***** ***** *****
Rayuwar auren Deeja ta sauya,kullum cikin tarairayar ta yake,haka suma dangin shi sun chanja mata sosai,duk wani abin kwaÉ—ayi da take so sukan shirya su kawo mata,nan da nan ta murje tayi kyau,ciwon zuciyar ta ya lafa sosai da sosai,ta kasance cikin farin ciki sosai, yanzu abu É—aya ne yake damun ta in da zata samu yayyen ta guda biyu,nusaiba da Yusuf da ko É—uriyar su bata ji,amma Mima ta kan kwantar da mata da hankali da cewa in Sha Allah suna cikin kwanciyar hankali,kuma zasu waiwaye ta duk daren daÉ—ewa
Hakan ya sanya ta cire damuwar wannan a ranta,ta rungumi mijinta ta cigaba da rainon cikin ta da a yanzu zai kai watanni biyar
***** ***** *****
Nadiya ce zaune ita da umaima a haɗaɗɗen ɗakin umaiman, Nadiya ta kalli umaima tana faɗin"ƙawa ta ya ake ciki ne?Ni fa na damu da batun wannan sweet guy ɗin"
"Sunan shi abdurrashid,kuma tsohon mijin wannan kucakar ne, tsohuwar matar husby"umaima ta faÉ—a zuciyar ta cike da hassada,don dai ta san Deeja tafi gaban a kira ta kucaka,ban da wannan ma,ko a faifai aka ajiye mai kama da ita da mai kama da Deeja sai an riga É—aukar Deejan
"Da kyau,kice zamu gwara kan shegiya mu ga mei tsaya mata,kaf garin nan waye ya isa ya ja damu?"
"Babu kam,yanzu dai mu shirya mu je wajen boka mai gaba ɗaya"babu musu suka miƙe suka ɗau hanya
***** ***** *****
A Æ´an kwanakin nan Deeja ta fara ganin sauyi a wajen Khalees,ya rage zaman gida,ya rage tarairayar ta da kulawa da ita,hakan na damun ta sosai,da ta sanarwa fareeda sai tace suma ya chanja musu,sun kasa gane kanshi, Deeja ce tace zata tambaye shi
Da ya dawo ta same shi a É—akin shi,da ta tambaye shi sai yace ayyuka ne suka sha kanshi,bata yarda ba amma sai ga bar shi a hakan
Har ma'aikatar su Nadiya taje da zummar tana neman wani,anan ta haɗu da Khalees,ai kuwa ya rikice mata sosai,ta rinqa ja masa aji,da ƙyar ta yarda ta bashi number wayar ta
A ranar ta kira umaima ta shaida mata,ihun murna umaima ta rinƙa yi tana godewa bokansu
Allah Sarki!Nana khadija baiwar Allah!!zuwa yanzu Khalees baya samun lokacin ta,sai dai su Farida sukan zo ɗebe mata kewa, hakan yana kawo mata sauƙi
Yau asabar ce,yana gida,akan gado ta riske shi yana waya,ga dukkan alamu da mace yake waya,sai fara'a yakeyi yana kashe murya, gefen gadon ta samu ta zauna,lura da zuwan ta ya sanya shi saurin katse kiran yana kallon ta tare da faÉ—in
"Ya dai?maman twins?"
"Ta zuba masa idanu,tana lura da yanda ya daburce tace"da wa kuke waya haka ne?ko sanin da shigowa ta ma bakayi ba da alamu"ta ƙarashe da ɗan murmushin da za'a iya kiran shi da na yaƙe
Al'adar Khalees bei iya ƙarya ba, balle yaudara,don haka ya gyara zama ya dube ta yana faɗin
"Luvly Deeja,nasan cewa zaki fahimce ni,nasan cewa zaki iya haƙuri dani
Deeja kiyi haƙuri,nan da three days za'a ɗaura aure na"
"Aure fa kace!"ta faÉ—a cikin É—aga murya, hankalin ta a tsananin tashe
"Be calm please! wallahi nima bansan yadda akayi hakan ta faru ba,ban san me ke damu na ba, Please kiyi min uzuri"hawaye suka ciko idanun shi
Babu abinda Deeja keyi sai nanata"innalillahi wa Inna ilayhi rajiun"har taji relief a zuciyar ta,ga kalaman kwantar da hankali da yake mata
Sun kwashi mintuna a haka kafin tace"to naji Khalees,nasan haka zata faru daman, wacece zaka aura É—in?a ina take?"
"Ƙawar matar abokina ce"
Gaban Deeja ya buga tace"wa kenan?"
"Aboki na Imran!"
"What!a cewar Deeja cikin ƙaraji,tayi wani kukan kura ta ci kwalar shi...
#Nusy bee
*****MATAR KHALEES*****
âœï¸Nusy bee
Page 10