Sashe 8
Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dukan su suka amsa mata,tayi mamakin ganin Deeja,amma sai ta ɓoye,sukayi mata sannu da zuwa,ta amsa da sakin fuska,ta dubi Deeja da sigar tsokana tace
"A'a!mai jegon gobe,yau wacce rana mai girma Khalees ya bamu aron ki?"
Dukan su sukayi Æ´ar dariya, amma Aunty Bintu ta gane dariyar dole Deeja takeyi, saboda alamun damuwa sun bayyana akan fuskar ta
Amma a lokacin Aunty Bintu bata nuna mata komai ba,ko ba komai bai kamata ta sanya ta tona cikin ta a gaban intisar ba
Wajen ƙarfe tara na dare Aunty Bintu suna tare da Deeja a ɗakin Auntyn,in da suka bar intisar da salim da mei bi wa salim sumayya suna kallo a parlour,su Kuma suka zame suka nufi cikin ɗaki
Cikin kulawa Aunty Bintu ta kalli Deeja tace"Deeja,ko baki gaya min ba akwai alamun damuwa a tare da ke,damuwar da ce ta dawo ko wata sabuwa ce?"
Duk abinda ke faruwa zuciyar Deeja a dake take,sai yanzu ta fashe da kuka mei cin rai,sai da tayi mai isar ta,aunty Bintu batayi ƙoƙarin dakatar daita ba,ta kalli aunty Bintu tace
"Aunty Ina cikin wani hali,aunty ina cikin tsaka mai wuyar fita,Aunty Ni dai tawa ta ƙare,Aunty Ni kam......."
"Wait!wait!!yaya kikeyi min wasu zantuka kamar wata jahila?me kike nufi da hakan?ki fito kiyi min bayani sai nafi fahimtar ki,ko sakin ki Khalees É—in yayi?"
Cikin kuka tace"ƙanin saki yayi min aunty,Wai.....Wai kishiya zeiyi min"
Cikin takaici Aunty Bintu ta ja dogon tsaki tace "to sai me?kishiya kan ki aka fara?ko akan ki za'a ƙare?ko a kanki zata zauna?"duk da cewar maganar ta doki ran ta
"Aunty ƙawar matar Imran fa zai aura,,tace wai sai ta raba Ni dashi fa"
"Ƙawar matar Imran kamar yaya?"Aunty Bintu ta tambaya a ɗan firgice
"Wallahi ƙawar matar Imran zai aura,saura kwana uku ɗaurin auren"
Aunty Bintu ta danne damuwar tava matsayin ta na babba tace"to sai me?ya auro ko waye ma?me zai tsorata ki?ke fa jinin ISHAQ ce,kuma kin san mu Bama sanya da addini,don haka kar kiyi wasa da addu'a,idan da nufi akayi auren kina zaune gayyar zata watse,idan ba da nufi bane ma zaki gani,na sanki da dauriya,to ki ƙara daurewa,kiji ki nuna baki ji ba,ki gani ki kauda kai,kar ki kuskura ki nuna musu ɓacin ranki,don zasuyi miki dariya, Allah shine gatan mu baki ɗaya,duk abinda ya samu bawa dama can tun kafin halittar shi Allah ya ƙaddara haka,don haka ki maida dukkan lamuran ki ga Allah"
Kalaman Aunty Bintu sun sanyaya mata jiki,tayi shiru tana nazari, cikin kwantar da murya Aunty Bintu ta ƙara da cewa
"Ki daina saka damuwa irin wannan a ranki, tabbas nasan akwai ciwo amma idan baki ɗauke shi da zafi ba zai zo miki a sauƙaƙe,kinga dai baki da wadatacciyar lafiya,kuma bake kaɗai bace,idan kika yi ganganci da Rayuwar ki har kika mutu mu kikayiwa asara,mijin ki wata zai auro,burin kishiyar taki kenan,to ina ranar wannan abu?"
Likers sa commentors wannan naku neðŸ‘ðŸ‘ðŸ‘🥰
#Nusy_bee
*****MATAR KHALEES*****
âœï¸Nusy bee
Page 12
"Nayi Miki alƙawari in Sha Allah zan bi maganar aunty,bazan Sanya damuwa a raina ba"Deeja ta faɗa tana mai son bawa kanta ƙwarin gwiwa
"Yawwa little sis, Allah ya Miki Albarka, kwanta maza ki huta"Deeja ta kwanta batare da ta sake magana ba
Wajen ƙarfe ɗaya na dare Deeja ta farka tayi ta sallolin nafila tana roƙon Allah ya kawo mata sassauci
Washe gari Aunty Bintu da kanta ta kai ta akayi mata gyaran jiki,sannan aka mata lalle ja da baƙi,ga gyaran gashi,ba don cikin da ke jikin ta ba babu mai cewa tana da aure,ai kuwa Aunty Bintu ta rinƙa koɗa ta har ta saki ranta
Kai tsaye daga nan gidan ta suka wuce,duk dakiyar Deeja sai da tsoro ya É—arsu a ranta,amma dai haka ta cije ko don ganin idon aunty Bintu
A harabar gidan suka samu Khalees,yana ganin ta ya taho da sauri,suka gaisa da Aunty Bintu a Mutunce, fuskar ta babu yabo babu fallasa ta dube shi tace"ga auta nan na dawo maka daita,ni zan wuce, Allah ya sanya alkhairi"tana gama faÉ—ar hakan ta faÉ—a mota
Khalees yazo daidai windon kusa da ita yana faÉ—in"Aunty mun gode Allah ya saka da alkhairi"ta kalle shi tace "a'a babu komai wallahi"
Kuɗi ya zaro masu ɗan yawa ya miƙo mata yana murmushi,amma tace bazata karɓa ba ta gode,ta ja motar ta bar shi nan tsaye
Ya mayar da hankalin shi kan Deeja,a lokacin ma tuni ta shige cikin gidan,don haka shima ya rufa mata baya
A ɗakin ta ya riske ta,tana ƙoƙarin shiga banɗaki,amma shigowar shi bai hana ta shigewar ta ba,don haka bashi da zaɓin da ya wuce ya nemi waje ya zauna
Bata wuce mintuna biyar ba ta fito, yana kallon ta ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa da suka amshi jikin ta,cikin ta ya fito É—as gwanin sha'awa
Ganin tana shirin ficewa ya sanya shi faÉ—in"Deeja zauna muyi magana"
Babu musu ta nemi waje ta zauna, fuskar ta babu alamun damuwa,ta zuba masa idanu jin me zai ce
Cikin taushin murya ya kalle ta yace"Khadija,kin san dai ina son ki ko?"
"Me ya kawo wannan maganar kuma?"ta faÉ—a tana kallon shi
Hannayen ta ya riƙo yace"ga dukkan alamu kina kallo na a macuci, mayaudari,kuma wallahi ba haka bane, maganar aure na dabam matsayin ki a cikin zuciya ta dabam,inayi miki son da ban taɓa jin irin shi akan wata ƴa mace ba,don haka kar kiyi tsammanin na daina son ki,aure na da Nadiya wata ƙaddara ce da bazan iya kauce mata ba,kiyi ta min addu'a kin ji?"ya ƙarashe maganar cikin Muryar tausayi
Shiru ta É—an yi,kafin tace"shikenan Khalees,komai ya wuce, Allah ya sanya alkhairi"
Yayi É—an murmushi yana faÉ—in"ameen na gode my dear wife"
Mima ma babu shiri ta tattaro ta dawo daga Malaysia,Ana igobe ɗaurin aure ta iso,gidan Deeja ta wuni tana ƙara wayar mata da kai tare da jaddada mata ta riƙi addu'a, don itace makami,kuma makari ga mumini
Anyi biki sosai,an sha shagali, Khalees sai faman rawar kai yakeyi,su Mima ne suke nunawa Deeja cewa kar ta damu,idan namiji yayi sabon aure haka yakeyi
Ta É—au wanka kala-kala da kwalliya,mai kwalliya ta musamman Aunty Bintu ta É—auko,sai ta zamo tamkar itace amaryar
Da daddare aka kawo amaryar,a lokacin Aunty Bintu bata É—akin,sai Mima,kiyya da barrister zee da suke tare da Deejan
Jin guɗa da iface-iface ya tayar da hankalin Deejan,ta miƙe tsaye a firgice,zee tayi saurin kamo ta ta zaunar da ita, Mima tace"cool down my sister,ki kwantar da hankalin ki,wannan damuwar ba mafita bace,kuma idan suka gano cewa kin sani sun fara samun lagon ki,don haka ki daure, Allah yana tare dake, Please my sis"da waɗannan kalamai zuciyar Deeja tayi sanyi,ta samu waje ta zauna
Kai tsaye babban falon aka nufo da amarya,suma su Deejan duk a babban falo suka zauna, Deeja tayi kwalliya har ta gaji da kyau
Umaima tana sawun farko a masu shigo da amarya, sukayi wa juna kallon-kallo ita da Deeja,daga bisani tayi mata murmushi mai nuni da zamu ganar da ke kuren ki, Deejan ma murmushin nuna ƙwarin gwiwa tayi sannan ta kawar da kanta
Suka shigo gaba É—aya,har da Afra,su Deeja kam basuyi mamaki ba, Saboda sun san Afra da Deeja jirgi É—aya ya kwaso su suka sauka a tasha É—aya,nan dai aka gabatar da al'ada sannan masu kawo amarya suka juya suna ta habaice-habaice,babu wanda ya tasamma kula su
Umaima da wata ƙawar su mai suna siyama ne suka zauna da amarya,a cewar su suna ɗebe mata kewa,babu wanda ya damu da su,Aunty Bintu, kiyya da zee suka wuce gidajen su,ya zamana saura Mima kaɗai
A zaton su umaima sun É—auka duk sun tafi saura Deeja kaÉ—ai,don haka kai tsaye ta shiga É—akin Deejan a gadarance,ko sallama babu,gashi kuma tayi babbar Sa'a Mima ta shiga banÉ—akin da ke cikin É—akin
A lokacin Deeja ta chanja kayan ta zuwa na bacci,baby Pink,sai wata Æ´ar hula da ta É—ora akan ta, Alqur'ani ne a hannun ta tana karantawa a zuci,sai ganin mutum tayi a gaban ta
Duk da ta É—an tazama hakan bei hana ta É—agowa cikin nutsuwa ba,tana ganin umaima ce ta maida kanta ga abinda takeyi
Umaima ta saki shewa tare da faÉ—in"da kyau MATAR KHALEES ta wucin gadi,ko da yake nayi miki uzuri,da alama giyar soyayya da miji ce take É—iban ki,amma nan gaba idan zaman gidan Khalees ya gagare ki,ko mukayi miki adalci muka maida ki baiwa a nan gidan,nasan dole za'a girmama mu ko?"
"Ke jahila daƙikiya!ke har kin isa ki maida ta baiwa?ke dai ki lallaɓa auren ki da aka samu aka liƙawa saunan mijin ki,amma Deeja tafi gaban bauta ko a gidan ubanki ne,banza mei toshashshiyar ƙwaƙwalwa,kije ki nemo ilmi ko Allah zai sa a rage asara, Deeja tafi gaban bokan ku ko malamin tsibbun ku"Mima dake fitowa daga banɗaki ce ke faɗin haka
A tsorace umaima ta kalle ta,har ga Allah tana tsoron Mima,don da ganin ta bata da mutunci,Mima ta ƙaraso inda umaima take ta nuna mata ƙofa tana faɗin"maza ɓace min da gani tun kafin wannan koɗaɗɗiyar fuskar taki ta yayyage yanzun nan"sum sum sum umaima ta fice daga ɗakin,cikin sanyin jiki
Tana jin Mima na jan dogon tsaki,amma bata da damar magana don duk masifarta mimab ta sha gaban ta
Mima ta dubi Deeja tace"sister sai haquri fa,kar ki tsaya zub da ajin ki akan WaÉ—annan karnukan"
Deeja ta mere baki tace"ai tuntuni na bawa banza ajiyar su,don da alama basu san ƙimar kansu ba"
Ina gaishe ku likers da commentors,kune Æ™warin gwiwa naðŸ˜ðŸ¥°ðŸ˜
#Nusy_bee
*****MATAR KHALEES*****
âœï¸Nusy bee
Page 13
A hargitse umaima ta shiga ɗakin Nadiya tana faɗin"ƙawa!ashe wannan shegiyar likitar tana nan?tsinanniya masifaffiya"
Nadiya tace"rabu da ita,ai dole ta tafi tunda dai ba gidan ubanta bane"
Mima bata juma ba ta wuce gida,tana fita Deeja tayi saurin datse ɗakin ta da makulli,kamar ta sani kuwa,motar Mima na barin gidan su umaima suka zo suka fara buga mata ƙofa,cikin sauri ta ɗauko airpiece ta kunna Suratu Yusuf a wayar ta ta toshe kunnen ta, a haka bacci yayi awon gaba da ita
Washe gari a kitchen ta Samu amarya da ango,cikin shauƙin soyayya suke sarrafa abinda zasu ci,ta sha mamakin ganin Khalees ko kallon ta baiyi ba,amma ta dake tace
"Yallaɓai ina kwana"