Sashe 24
Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sunyi matsanancin mamaki da farin cikin ganin Deeja,da alamu ma hankalin ta a kwance yake,ɗan jaririn yaron ta Affan yanzu yawon shi da gudu babu inda baya zuwa,babu abinda baya ci maganar ce dai ba sosai ba,kallo ɗaya Deeja tayi wa Khalees ta fashe da kuka,don yadda ya rame ya lalace abin tsoro,shi kam da sauri ya ƙaraso inda take ya riƙe hannun ta gam yana faɗin"Deeja ina kika shiga? hankalin mu ya tashi sosai,komai ya ƙare min Deeja,komai yayi min duhu saboda babu ke,nayi missing ɗin ki sosai Deeja"
Deeja ta girgiza kai tace"ka yafe min Khalees,na aikata kuskure,nayi abinda bai dace ba,na daga muku hankali,amma komai ya wuce,ga yaron ka nan"ta miƙa masa Affan"shima yayi kewar ka"
Ya ƙanƙame shi yana kallon shi yana murmushi,idanun shi cike da ƙwalla,kusan kowa a parlourn sai da ya jinjina irin soyayyar da sukeyiwa juna, Ma'aruf yace"Weldone auta,mu ba'a ganmu ba ko?"da murmushi ta tashi ta ƙarasa kusa dashi ta rungume shi tace"kaima nayi missing ɗin ka yaya,ina Aunty Farida?"
"Tana gida,ashe all this while gidan nusaiba kika je kika tare kika barmu da tashin hankali?"
Nusaiba tace"yaya Ma'aruf ita tace bata son kowa yasan tazo,shiyasa nima nayi shiru"
"Yanzu fisabilillahi idan tana shirme sai ki biye mata?"
"To yaya Ma'aruf nasan abinda aka mata?"Ma'aruf yayi Æ´ar dariya kawai,ya kama hannun Adnan suka fice daga parlourn
ÆŠaya bayan É—aya Deeja ta gaisa da yayyen nata,suka rungume junan ita da kiyya, Afra ma tazo ta rungume ta cike da farin ciki,daga nan suka ja ta sashen kiyyan,don yanzu ita da lubaisa ne kawai a gidan, fauwaz da Imran kowa ya koma gidanshi
A can taji labarai iri-iri,har da na Umaima,sai taji tausayin ta sosai,har ma tayi alƙawarin zata nemo ta ta taimaka mata jin wacece ita,abin ya bawa su Afra mamaki, Afra ta kasa haƙuri tace
"Gaskiya ke ta dabam ce Deeja,yanzu duk wahalar da Umaima ta baki har zata baki tausayi bayan ta fita daga rayuwar ki ki sake dawo da ita?"
Murmushi Deeja tayi tace"kika sani ko hakan ya zama silar shiryuwar ta,ke ce fa yanzu kika ce min bata da iyaye,Najeeb ya kawo ta kuma yanzu basa tare,kika san a wanne halin rayuwar take?kuma ma Ni sam banga hikima don mutum ya aikata maka sharri ka rama masa da sharri ba"
"Hakane kam, Allah ya sa hakan ya zamo silar shiryuwar ta ta"
"Ameen ya Allah"inji Deeja
Khalees ya nemi izinin tafiya da Affan,don dama Deeja ta yaye shi,babu musu ta haÉ—a masa Æ´an kayayyakin shi,yana ta É—aga mata É—an hannun shi ta rako su har bakin mota,sai da suka tashi sannan ta koma gida
#Nusy_bee
*****MATAR KHALEES*****
âœï¸Nusy bee
Page 33
Kwanan Deeja da dawowa ta ja Afra suka nufi gidan su Umaima ko nace gidan su Najeeb,sun sha mamakin a halin da suka same shi,yayi haÉ—ari ya faÉ—o daga mashin ya gamu da matsalar spinal cord,ko iya tashi bayayi, mahaifiyar shi mai jinyar shi
Da sallama suka shiga parlourn da Afra ta rinƙa bin shi da kallon mamaki ganin yadda ya sauya,suka gaida mahaifiyar tashi,da ke bin su da idanu,ta amsa da fara'a, Deeja ta gaishe da najeeb da ke kwance yana jin jiki,don bayan wannan matsalar har da brain cancer da ta kama shi,ya amsa cikin rawar murya, Afra kam ko kallon banza bai samu daga gare ta ba, Deeja ta kalle shi tace
"Am dama gidansu umaima muke son zuwa,to bamu san address É—in ba,shine nazo idan Allah ya sa ka sani ka sanar mana"
Shiru Najeeb yayi na ƴan sakwanni kamar bazai ce komai ba,ƙwalla ta tarar masa a idanu,cikin karayar zuciya ya fara bayani
"Umaima Æ´ar garin taura ce,tana zaune a wani family house mai suna gidan cheÉ—iya,kaf garin su ansan gidan,sai dai umaima bata ji dadin gidan ba,don haka ko Ni bani da tabbacin zaku same ta ko bazaku same ta ba"
Deeja ta miƙe tana faɗin"zamu jarraba zuwa mu gani,in Sha Allah zamu same ta"daga nan tayi wa mahaifiyar shi sallama ta dire mata kuɗi 20k, mahaifiyar shi sai godiya take kamar zatayi wa Deejan sujjada, shima Najeeb cikin karayar zuciya yace
"Deeja,ki yafe min,kinga yadda rayuwa tayi dani,idan kika haÉ—u da umaima itama kice ta yafe min,don na cutar da rayuwar ta da yawa"
Deeja ta goge ƙwallar idanun ta tace"na yafe maka"sannan ta fice daga parlourn, Afra ta biyo bayan ta
Kai tsaye Deeja ta nufi taura jihar Jigawa,daga ita har Afra suna fatan Allah yasa su ga umaima
Basu wani sha wahalar gano gidan ba,amma da suka tambayi wata mata da ke tatar gasarar koko ina Umaima?sai ta yatsina fuska tace"bata dawo daga kasuwa wajen sana'ar ta ba,sai dai ko ku jira ta ko ku bi ta"Deeja da Afra suka kalli juna suka sake kallon matar,Deeja tace"babu matsala zamu jira ta,inane ɗakin nata?matar ta nuna musu tsohon ɗaki mai tsohon ƙyaure batare da ta sake magana ba
Allah yaso da bishiya a kofar ɗakin umaiman, Deeja ta koma mota ta ɗauko musu babbar dadduma suna hira suna shan iska,babu wanda yayi musu tayin ko ruwan sha,in da Allah ya taimake su suna da ruwan gora a mota,shi suka sha sukayi,Deeja ta ɗauko musu ƙatuwar dadduma sukayi alwalar azahar sukayi sallah. Zaman awa biyu da mintuna sukayi umaima ta dawo, Deeja tana bawa afra labarin Cambridge University ta hango Umaima tana shigowa gidan,shiru tayi tana kallon yadda ta fice a hayyacin ta tayi duhu sosai,tana sanye da atamfa da hijabi da suka ji jiki,amma fes take,fuskar ta ma babu alamun damuwa sam a tare da ita, Afra ma kallon ta takeyi,har taje wajen wata igiya ta kwaso kayan shanya sannan ta nufo ƙofar ɗakin nata
Sam bata kula da wasu a zaune ba sai da ta ƙara matsowa, Deeja ta fara gani,don tafi saitin inda take tahowa,ƙamewa tayi tana kallon Deeja da tunanin ko mafarki takeyi, Deeja tayi murmushi ganin irin shock ɗin da Umaima ta shiga ta miƙe tana murmushi ta rungume ta, Umaima ta ƙanƙame Deeja tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya,afra ma ta miƙe tazo ta rungume ta, Umaima ta haɗa su duka ta rungume tana kuka,sai da ƙyar ta ɗago tana kallon Deeja tana faɗin"Allah Sarki Deeja!ina kika shiga ne?yadda na ɗauke ki ba haka kika ɗauke Ni ba,na shiga tashin hankalin ɓatan ki,ki yafe min Laifuka na Deeja......"maganar Tata ta katse saboda kukan da jaririyar bayan ta ta fara tana mutsu mutsu,wadda Allah bai sa Deeja da Afra sun kula da ita ba
Sakin Deeja tayi ta É—anyi baya tana sauko da babyn,kallo É—aya Deeja tayi wa jaririyar ta waro idanu tana faÉ—in"umaima haihuwa kikayi?"
Murmushi umaima tayi,Deeja ta amshi yarinyar tana ƙara kallon ta,bata da maraba da mahaifin ta Imran, Umaima ta ɗauke daddumar da suka shimfiɗa da suka shimfiɗa ta buɗe ƙofar ɗakin ta suka shiga cikin ɗakin
Siminti ne malale a ɗakin,amma duk ya faffashe,daga gefe kuma yaloluwar katifa ce da aka shimfiɗa mata zanin gadotsoho,sai dai ɗakin ƙal yake,dama umaima ba daga nan ba wajen tsafta
Cikin rawar jiki ta dauko murhun ta na gawayi tana ƙoƙarin hura wuta, Deeja ta dakatar da ita, Umaima tayi murmushi tana kallon Deeja tace"ko dai bazaki iya cin cimar mu ta ƙauye bane?"
Da sauri Afra ta kalle ta,nan da nan hawaye suka ciko idanun ta,tace "Umaima yau ke kike kiran kanki ƴar ƙauye?"
Umaima ta waro idanu tana murmushi tace"to da Ni ɗin ƴar ina ce?nan ce mahaifata,nan ce mahaifar baba na,kinga kuwa bani da inda yafi nan"bata ƙara sauraren su ba ta cigaba da ƙoƙarin hura wutar ta, Deeja tace"mu fa ba yunwa mukeji ba,ki zo mu zauna, magana zamuyi tukunna"Umaima tace"duk da haka dai sai mun ci abinci tukunna"tilas Deeja ta ƙyale ta, Umaima ta ɗora musu faten tsaki da yaji yakuwa da gyaɗa
Bayan ta gama a kwano É—aya ta zuba musu,ta É—ebo musu ruwa a Æ´ar randar ta,suka ci a tare suna hira,bayan sun gama ta kwashe kwanukan don wankewa, Deeja kuma ta gyara wajen, Umaima tana shigowa tace"kai!daga zuwa kawai sai ki fara aiki?"
"Ke dai zauna kawai Umaima"a cewar Deeja,babu musu ta zauna tana fuskantar Deeja
Deeja tace"umaima me ya faru bayan tafiya ta?kuma dama kina da ciki kika taho baki gayawa Imran ba?ya na ganki haka?me yake faruwa ne?"
Murmushi mai ciwo umaima tayi,ta karɓi jaririyar ta daga hannun Afra,ta fara shayar da ita,ta jingina kanta da jikin bango ta fara magana cikin sanyin murya
"Iyaye na dukka biyun na rasa su ina ƙarama, mahaifiya ta ta rasu ina da shekaru biyar, lokacin da ƴan uwan ta suka zo gaisuwa bayan an share makoki sun so tafiya dani,amma mahaifi na yace a'a, tabbas ran ƴan uwan mahaifiya ta ya ɓaci,ƙarshe dai baayi rabuwar daɗi ba,don baba na jadaddawa ya rinka yi ƴa tashi ce babu mai raba su,dangin shi suka shiga maganar suka ƙara dagula lamarin
Haka dangin mahaifiya ta suka koma garin su suka barni a hannun mahaifi na,babu irin gatan da baiyi min ba, makaranta boko da islamiyya da kanshi yake kai ni,ya zauna yayi hira dani,yayi wasa dani,don sam bana iya shiga cikin yara kamar kowa nayi wasa,don haka idan mahaifi na bayan na dawo daga makaranta É—akin mu nake shigewa nayi ta wasanni na da kayan wasan da baya gajiya da siya min
Haka rayuwa ta kasance har tsawon shekaru uku,a lokacin ina da shekaru takwas,a wannan lokacin ne nasan ma'anar rashi duk da ƙarancin shekaru na,don a shekarar ne na rasa mahaifi na bayan rashin lafiya da yayi ta kwana ɗaya"umaima ta kasa cigaba saboda kukan da yafi ƙarfin ta,da alamu har yanzu tana jin zafin mutuwar,su kansu Deeja da Afra kuka sukeyi,Deeja ma mutuwar mahaifin ta ce ke dawo mata
#Nusy_bee
*****MATAR KHALEES*****
âœï¸Nusy bee
Page 34
Umaima ta cigaba"lokacin da mahaifi na ya rasu na samu tausayawar al'umma da dama, musamman ƴan gidan mu,amma abin mamaki wannan karon ko mutum daya daga dangin mahaifiya ta bai zo ba, ina jin ƴan gidan mu suna zunɗen wai dangin mahaifiya ta basu san mutuwa ba,kuma soyayyar ƙarya sukeyi min don babu yadda za'ayi ace basuji mutuwar mahaifi na ba,tun maganar bata wani dame ni ba,amma da aka ɗauki lokaci da mutuwar mahaifi na sai ta dame ni