Sashe 29
Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri ta leƙo,tana ganin Deeja ta tafi da gudu ta rungume ta tana dariya,duk da cewa kiyya ta san labarin komai amma tayi mamakin chanjin da ta gani a wajen umaiman,gashi yanzu asalin farin ta ya dawo,tayi fes da ita, dama umaima akwai gayu da iya kwalliya, yanzun ma tana sanye da English wears riga da wando pink colour,ta ɗauke gashin ta da baƙin ribbom. Afra tana kallon ta tace"lallai umaima!wato mu duk baki ganmu ba ko?"da sauri ta saki Deeja ta rungume su ɗaya bayan ɗaya tana murmushi,ta ja su suka shiga parlourn, kiyya ta amshi little Deeja tana kallon ta
Nan da nan ta kawo musu drinks da snacks tana faɗin"yau anyi surprising ɗina"lubaisa tace"sistern ki ce ta tattago mu"Umaima tayi murmushi ta kalli Deeja da take danna waya tana murmushi itama, kiyya tace"Ni kam ban ma san sanda aka tambayi abban su ba,sai ce min yayi wai khadija tace zamu fita"Afra tana dariya tace"ballantana kuma abban haneef,jira yakeyi auta tace ayi yace an gama"da tsokana ta faɗa tasan Deeja bata ƙaunar,ai kuwa ta ɗago ta zabga mata harara,duk suka kama dariya
Sun ɗan taɓa hira da raha, Deeja ta tambaye ta game da karatu,cikin zumuɗi take sanar mata da cigaban da ta samu,yanzu haka tayi wajen izu ashirin da biyar,ga litattafai na addini,game da institution kuwata fara lecture a MAAUN in da take karantar business administration,su kansu su Afra ba ƙaramin burge su Deeja tayi ba,a hankali Deeja ta shigo da maganar Imran
Ɗif umaima tayi bata sake magana ba,suka haɗu suna ta roƙon ta ta koma, Afra tana murmushi tace"nayi missing ɗinki sosai sister,gidanmu ma yayi missing ɗinki,kuma Dr ma yayi missing ɗinki sosai"Deeja tace"kuma ko ba don shi ba ki taimaka ki koma don takwara ta,she will be very happy ace ta tashi gaban iyayen ta duka biyun,sai ta fi jin dadin tarairayar da zaku mata"kiyya tace"seriously Umaima ko da nasan da Bama shiri ranar da Imran ya sake ki da abban su Aisar ya sanar min komai game da ke banyi bacci ba,I wish kin koma ɗakin ki,mu haɗa kanmu gaba ɗaya"ta ƙarashe tana murmushi, lubaisa ma tace"indai kika ƙi komawa Dr Imran to daga yau na daina yarda da love,indai naku ya mutu to I'm very sure namu Ni da ya abdallah yana mutuary"sukayi ƴar dariya,cikin sanyin murya Umaima tace"zan koma,ko don yarinya ta,i still remember Imran yayi min komai"shewa suka saka dukan su kamar ƙananan yara suna tafi
Baayi cikakken wata guda ba aka mayar da auren Umaima da Imran,har taura Imran yaje ya nemi auren ta,bayan sati uku kuma ya mayar da ita can ya sasanta tsakanin ta dasu,daga can suka wuce Bauchi
A Bauchi ya gamu da abin mamaki,don mahaifin shi kuka ya rinƙa yi yana neman yafiyar shi da mahaifiyar shi,ya sanar masa Zulfa'u ta haukace tun sanda aka samu ƙaramar ƴar ta da salma da ciki,ita kuma Ameera da cutar AIDS,shi kuma ya tattara yaran ya mayar da su wajen mahaifinsu ita kuma ya sake ta
Imran ya sha mamaki sosai,ya jinjina ikon Allah,ya gabatar da Umaima a matsayin ta na matar shi, Alhaji alƙasim ya sa musu albarka sosai
Imran ya bawa mahaifin shi labarin ƙanwar shi Ramla da mahaifiyar shi ta haifa,tayi aure itama a Abuja,har da yaran ta uku,dady yace"Allah sarki Aysha,don Allah ka nemar min yafiyar ta"
Kwanan su shida a Bauchi yau,sosai Umaima take girmama dady, kullum cikin yi masa hidima take,don sai taga kamar nata mahaifin
Deeja ce ta kira ta tace ta tambayi Imran zata je bikin ƙanwar Mima idan ya amince su tafi tare,tunda Deeja ta ambaci Mima gaban ta ya faɗi,don Allah shaida tana mugun tsoron Mima,gashi yanzu zata je gidan su,kuma bazata iya yiwa Deeja musu ba
Wajen ƙarfe biyar suka sauka gidan su Mima a azare,Mima bata wulaƙanta umaima ba,amma ko kaɗan bata sake mata ba,suna zaune a ɗakin miman suna hira, Mima na bawa Deeja labarin zuwan inna haleema takwarar ta gobe, wadda ta kasance ƙanwar mahaifin su ce
Mima tace"Allah ya kaimu goben,kice gobe da shafta,mama bilki fa?"
"Mama bilki maybe itama tazo goben, maybe kuma sai jibi"
"Allah ya kaimu"a cewar Deeja,suka cigaba da hirar su
Ita dai Umaima tana takure a gefen gado tana kallon yadda suke yin hira,sai su koma musu,sai su fara zagin juna sai su cigaba da shewa,a hankali ta goge hawayen ta tana jin kewar Æ´an uwa,don ba wai sun saba da dangin ta bane har yanzu
Gashi tsoron maman su Mima ya kama ta ganin irin kallon da take bin ta dashi, shiyasa ma tunda ta rakuɓe a ɗaki bata fita ko'ina ba
Mima ta shiga É—akin mahaifiyar su da sallama,mama sakina ta amsa, Mima ta samu waje ta zauna tace"gani mama"
Mama sakina tace"Mima wacece wannan wadda Deeja tazo tare da ita"
Mima ta taɓe baki tace"oho,kwashe kwashen auta ne,amma wai naji ance surukar ƙanwar Mamie babba ce"
"A ina take?"a cewar mama tana kallon ta
"Nace miki ban sani ba fa,ki tambayi Deeja"mama bata sake magana ba, Mima ta fice ya koma É—akin ta
Bata samu Deeja a É—akin ba sai Umaima da babyn ta take ta kuka,dama bata saka ran samun Deejan ba saboda zataje gidan Aunty Aziza,wadda itace immidiates É—in Aunty Bintu,ko kallon Umaima da ke fama da little Deeja batayi ba,ta faÉ—a toilet don yin wanka
Umaima ta san matsalar little Deeja,bata bacci sai anyi mata wanka,gashi ita dai bazata iya tambayar ruwan wanka ba,dama dai Deeja tana nan ne,kuma mugun tsoron Mima takeji,haka ta miƙe tana ta jijjiga little Deeja da take sake mimmiƙewa tana tsala ihu
Sai da Mima ta gama shirya wa,ganin abin na little ba na ƙare bane ta kalli Umaima fuska babu yabo babu fallasa tace"ko bata da lafiya ne?"umaima ta girgiza kai,Mima tace"to lafiya take irin wannan kukan?"
"Ina ga ko wanka take buƙata"Umaima ta bata amsa
"Ko an saba mata wankan kafin tayi bacci?"Umaima ta gyaÉ—a kai
"Ikon Allah!shine bazakice a baki ruwa kiyi mata wanka ba?"bata jira cewar umaima ba ta fice daga É—akin,bayan Æ´an mintuna da dawo da baho da ruwan zafi,da kanta ta daidaita ruwan ,ta amshi little tayi mata wanka ta shirya ta,tun kafin ta gama little tayi bacci,ta kwantar da ita a hankali,tayi mata addu'a ta tofa mata,batare da ta kalli Umaima ba ta fice daga É—akin, umaima sai bin ta takeyi da kallo,tana fita tayi murmushi ta koma kusa da Æ´ar ta ta kwanta itama
Sai wajen ƙarfe tara Deeja ta dawo,a parlour ta samu Mima tana yiwa Mee'ad kitso, ta sauke Affan da yake bacci ta kwantar da shi a kan kujera tana faɗin"wash Allah na"
"Gantali daÉ—i,sai yanzu?"a cewar Mima, Deeja ta harare ta tace "sai dai uwar gantali daÉ—i"Mima tace"seriously Baki da kirki Deejo,kin bar matar mutane kin tsallake kinyi tafiyar ki"
"Ayya!wallahi nayi mata tayin zuwa, tace a'a naje na dawo"Mima ta taɓe baki tace"ƴar ta sai kuka takeyi,wai ashe wanka take buƙata,tsabar sokwanci ta kasa tambayar ruwan wanka"Deeja ta kwashe da dariya tace"tsoron ki take ji ne, kullum kina haɗe mata rai kina mata tsawa,gashi don wulaƙanci kika je har gidan mijin ta a gaban mijin ta kika faffalla mata mari, leemo Allah ya shirya min ke"Mima tayi ɗan murmushi tana taɓe baki tace"ai kuwa ta haɗu da wahala"Deeja tayi dariya ta miƙe ta shige ɗakin da Umaima take
Washe gari Æ´an biki suka fara halarta, kasancewar yau za'ayi event na Farko, Umaima dai ba don Deeja ba da tuni ta koma gida saboda har yanzu tana da tsoron shiga mutane,tana lafe a É—akin Mima,daga ita sai wayar ta,don little ma Deeja ta amshe ta suna tsakar gida ana raha,bayan la'asar inna haleema da mama bilki suka iso kusan a tare,Mima sai raha da wasa da dariya sukeyi,bayan sun gaisa da mama sakina suka wuce É—akin Mima inda Umaima ke zaune tana chatting da mijin ta
Sai da suka zauna sannan umaima ta gaishe su cikin girmamawa,bin ta sukayi da kallo suna amsawa,É—auke kanta tayi ya cigaba da danna wayar ta,mama bilki ta kalli Mima tace"Mima ina kuka samo Æ´ar INNALE?"
Mima ta É—ago kanta cikin mamaki tace"wacce innale kike magana akai mama?kuma wacece Æ´ar tata?"daidai nan Deeja ta shigo da sallama
Inna halima tace"nima Ina ganin ta innale kawai na gani a tare da ita"
Mima ta kalli Umaima da tun ambaton innale na farko ɗago kanta a firgice tana kallon su inna haleema,mama bilki ta ciro wayar ta ta fito da hoton innale, wadda asalin sunan ta maimunatu ta miƙawa Mima
To pa 🥺me yake shirin faruwa ne?
#Nusy_bee
*****MATAR KHALEES*****
âœï¸Nusy bee
Page 39
Mima ta kalli hoton sannan ta kalli Umaima da ke kallon su idanu waje,tabbas basu da maraba, Deeja ma ta kalli hoton ta kalle ta,ta kalli su inna haleema tace"inna wacece innale?"
"Autar mu ce,asalin sunan ta maimunatu,ta rasu shekaru wajen ashirin baya, shiyasa baki santa ba,amma takwara ke zaki iya tuna ta ko?"Mima tace"sosai ma kuwa,kin manta na santa?mama tace Kafin auren ta tayi raino na sosai, lokacin da ta rasu ma da wayo na,na kai shekaru tara ma"
"Kin tuna lokacin da tazo zuwan ta na ƙarshe da ƴar yarinya ko?"a cewar mama bilki
Mima ta ɗan yi shiru,can tace"tabbas anyi haka,wai ma ni tunda ta rasu ban sake jin labarin yarinyar ba,gabanin rasuwar yadikko(kakar su)na taɓa tambayar ta ina ƴar innale amma bata bani wata gamshashshiyar amsa ba,Ni kuma tun daga sannan na watsar"
"Ai kuwa dai babu wanda ya sake bi ta kan yarinyar saboda wulaƙancin da mijin innalen yayi mana a lokacin da muka so amsar yarinyar"a cewar Inna haleema
Deeja da tun fara maganar su bin su take da kallo tace"inna a wane garin tayi aure ne?"
"Inna haleema tace"a jahar Jigawa ne,wani ƙauye taura"gaban Deeja ya buga,ta daure ta sake cewa"yaya sunan yarinyar ta ta?"
Inna haleema tayi ƴar dariya tace"nan fa ɗaya,wani sunan iyayi ta sa mata,duk sanda tazo ba wani iya faɗa mukeyi ba,Ni na manta sunan ma,sai dai ko yaya"Mima dai sai binsu da kallo take tana mamakin waɗannan tambayoyin na Deeja,don ta san halin ta kamar yadda ta san yunwar cikin ta,bata taɓa abu a banza