Sashe 13
Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kayan sawa ne,sai takalma da kayan ciye-ciye iri-iri, sai ta hau murna da tsalle-tsalle,ta manta da ciwon da ke jikin ta,shima Isma'il sai ya damu kanshi da farin ciki,ya tattare mata kayan sannan ya fita zuwa É—akin luba
Da sallama ya shiga ta amsa da rawar jiki,ya gaishe ta fuska babu yabo babu fallasa,ta amsa tana ta faman wage baki haÉ—e da faÉ—in"Masha Allah ismaila!Yaya karatun?"
"Karatu mun gama alhamdulillahi"
"To Masha Allah!yanzu sai aiki ko?"
Ya ɗan kalle ta a kaikaice ya ƙara ɗauke kanshi yana faɗin"shima an samu"
"To lamari yayi kyau,sai aure ko?"
Kamar yace shima an samu sai yaga kamar tambayoyin nata da rainin wayo a ciki,don haka sai yace"gwaggo bari na leƙa cikin gari"bai jira cewar ta ba ya fice daga ɗakin
Yana fita Luba ta leƙo ɗakin zainaba,a lokacin zainaban ɗin bacci takeyi,a fili ta furta"eh lallai,wato an samu sake har da bacci!to dole ki tashi ki ƙarasa aikin nan,ke zainaba! zainaba!!"ta shiga ƙwalla mata kira
A firgice zainab ta farka, Luba ta tsaya a kanta tana yi mata kallon banza,gaban ta ya faɗi,ta miƙe zaune tana kallon luban,cikin gadara Luba tace"wato don isa da ƙwarewa har da bacci don kinga wancan saƙagon ya dawo ko?to maza ki tashi ki ƙarasa yi min wanki na"
Shiru zainab tayi gami da zuba mata idanu, Luba ta daka mata tsawa har sai da ta firgita,ta miƙe jiki na rawa ta nufi tsakar gidan domin ƙarasa wankin
Tana cikin yin wankin malam Ishaq ya dawo tayi masa sannu da zuwa ya amsa cikin kulawa, cikin farin ciki take shaida masa dawowar Isma'il
Shima ya cika da farin ciki,ya tambaye ta
"Yana ciki?"ta bashi amsa
"A'a ya fita,amma inaga ya kusa dawowa,ka zauna ka jira shi"babu musu malam Ishaq ya shige cikin gidan,ita kuma ta cigaba da aikin ta
Tana cikin yin wankin Isma'il ya dawo,da sallama ya shigo,ta amsa cikin farin ciki,ganin ta tana wankin ya sanya ranshi yayi mummunan ɓaci,cikin fushi yace
"Zainab ba na hana ki wannan wankin ba?"
Tsoro ya kama zainab,ganin shi cikin fushi tace"gwaggo ce tace nayi wallahi"
"To ajiye,wuce mu je"babu musu ta ajiye ya kama hannun ta suka wuce cikin gidan
Jin Muryar malam Ishaq ya wuce ɗakin mahaifinsa,da sallama ya shiga,malam Ishaq na zaune yana cin abinci,yayi matuƙar farin cikin dawowar ɗan nashi,suka zauna suka kama hira,basu ɗau lokaci ba ya sako masa batun zainab
Cikin rashin walwala yace"gaskiya baba ya kamata a tausayawa zainab,don a ƙananun shekarun ta bai kamata ace ana bata ayyuka fiye da ƙima ba,gashi bata da lafiya"
Malam Ishaq ya numfasa yace"wallahi Ni kaina abin yana damu na Isma'il,don dai bani da yadda zanyi ne,amma na bar komai a hannun ka,ka É—auki matakin da ya dace"
Isma'il ya gyara zama yace"na gode baba,yauwa,dama ina so na shaida maka wani Company ya bani ya bani aiki a can san Fransisco É—in,kuma nan da next month zanje na fara yi musu aiki"
"Masha Allah alhamdulillahi! gaskiya nayi farin ciki, Allah ya taimaka"
"Ameen baba, godiya nake"
"To batun aure kuma fa?"ismaila?"a cewar malam Ishaq
Ismail ya ɗan sunkuyar da kanshi cikin jin nauyi yayiwa malam Ishaq bayanin faɗima balarabiyar ƙasar Yemen
Har malam Ishaq ya fara murna sai ya ɗan yi shiru kafin yace"anya ismaila?baka ɗauko fin ƙarfin ka ba kuwa?"
ÆŠan murmushi Isma'il yayi sannan yace"ai tuntuni mun fahimci juna har iyayen ta sun sanni,kuma sunyi na'am da ni"
Murmushin malam Ishaq ya faÉ—aÉ—a yace"to Allah ya sanya albarka, Allah ya kaÉ—e fitina". Isma'il ya amsa da"ameen baba"
Cikin sati biyu zainab tayi kyau ta murje ta maida jikin ta,bata kowane aiki sai wanda baza'a rasa ba,sai wanda Isma'il ya bar ta tayi,abin yana damun Luba sai dai babu yadda zatayi
Ana isaura kwana Shida ya koma san Fransisco ya shawarci malam Ishaq akan cewa yana so ya mayar da zainab gidan sakina,malam Ishaq ya nuna musu babu damuwa,don haka ya sanar da zainab cewa ta shirya kayan ta
Ba ƙaramin murna tayi ba, washegari ya ɗauke ta zuwa azare,sakina tayi matuƙar murnar ganin ƴar'uwar ta, Isma'il ya damƙa ta a hannun sakina tare da yi masa fatan alkhairi
Watannin shi uku da fara aiki a ƙasar America akayi auren shi da faɗima,bayan auren ne ya ɗauki zainab ya tafi da ita,a lokacin ma sakina tana laulayi,yayi matuƙar taya ta murnar samun ƙaruwa,domin zuwa yanzu babu wulaƙanci da gore-goren da bata sha daga wajen dangin miji duk sai akan haihuwa,to yanzu dai ta samu ciki bayan shekaru goma sha biyu da tayi da yin aure
Rayuwar zainab ta chanja a ƙasar US,yanda faɗima take son ta da nuna mata kulawa yana faranta mata,haka shima Isma'il,kuma ya sanya ta a makaranta mai matuƙar tsada, cikin lokaci ƙanƙani ta sauya baki ɗaya
Isma'il bai manta da mahaifin shi da kuma Æ´ar'uwar shi ba,don haka yana kula dasu sosai,da sakina ta haihu faÉ—ima da zainab sun zo suna,sun taho mata da kaya tuli guda, yarinyar ta ci sunan surukar ta hajiya Fatima amma suke kiran yarinyar BINTU
Yau dai na karya record nayi post biyu a rana ɗaya 🤣🙃😅
#Nusy_bee
*****MATAR KHALEES*****
âœï¸ Nusy bee
Page 20
Wannan shafin naku ne matar Khalees fans, readers,more especially likers da commentors, Deeja da Khalees sun ce a gaishe ku🥰
Itama faɗima bata rufa shekara ba ta haifo ƴar ta salma,itama sakina tazo suna,itama sakina tazo suna,kuma ta ga Garba ta mutunci a wajen faɗima da ƴan'uwan ta,babban abin farin cikin ma shine,yanayin da suke zaune da ƙaramar ƙanwar su zainab,hakan ya faranta mata rai sosai
A haka suka cigaba da rayuwa,har zainab ta kammala karatun ta na secondary,kuma ta fara karatun babbar makaranta cike da nasara,a lokacin faɗima na da yara biyar,sakina kuma uku gare ta,akwai shaƙuwa mai tsanani tsakanin zainab da yaran faɗima,salma,nasir,fauwaz,abdallah da Minal,tana kula dasu sosai,Kuma basa rabuwa dare da rana,sai dai makaranta ko bacci
A shekarar ne auren ƙanwar faɗima mai suna AYSHA ya mutu,ta zo ta samu yayar ta ta cikin kuka take shaida mata wulaƙancin da mijin ta yayi mata
"Aure ya ƙara shikenan ya juya min baya,da Ni da IMRAN yanzu bamu da maraba da bola,wani lokacin abinda zamu ci ma gagarar mu yakeyi,duk a tunani na komai zai wuce,kawai shekaranjiya sai gashi ya kawo min takarda,wai ya sake ni saki uku"ta ƙarashe cikin rushewa da kuka
Shiru faɗima tayi tana jin babu daɗi na abinda mijin ƙanwar ta yayi mata,ta san wacece ƙanwar ta Aysha,duk da cewa ɗan adam na iya chanjawa,amma tana yiwa one and only qanwar tata kyakkyawan zato
"Nayi nadamar auren É—an Nigeria wallahi,sun cika son kansu"Aysha ta cigaba
Murmushi faɗima tayi tace"kayya Aysha!Kar ɓacin rai ya sanya ki yanke hukunci cikin fushi,idan mutum yayi miki laifi sai ki yanke hukunci gwargwadon laifin da yayi miki,shine adalci. Amma hukunta wani da laifin wani rashin adalci ne, Aysha Nima ɗan Nigeria nake aure,kuma ina zaune da ƙanwar shi,amma koda yaushe da shi da family ɗin shi ƙoƙarin su su faranta min,rashin dace ne kawai da jarabta daga Allah ya same ki,ki roki Allah ya baki ikon hayewa,sai kiga yayi miki sakayya mai girma"
"Hakane ukhty!da har nace zan zubar da cikin nan nan jiki na amma na fasa,sai dai ina tausayin Imran,don yana da haƙuri da zurfin ciki,ina tsoron kar a cutar min dashi,don matar nan bata da iymani"
"Ki bishi da addu'a,a duk inda kike a faɗin duniya addu'ar ki zata riske shi,kuma addu'ar uwa a kowanne lokaci tana tasiri akan ɗan ta"haka faɗima tayi ta kwantar mata da hankali har ta samu sauƙin damuwa
Akwai wani abokin Isma'il mai suna MAHMUD,likita ne babba,yana aiki a wani asibiti dake cikin san Francisco University inda zainab take karatu,kuma abokin Isma'il ne sosai,yana da mata É—aya hajiya bara'atu,da yara uku,Ma'aruf,Abida da faiza, kwata-kwata bara'atu bata daraja mai gidan nata,yaran duk sun raina shi, Ma'aruf ne kawai ya fita Zakka,domin shi É—abiun mahaifinshi gare shi kuma dama sun fi sabawa dashi,amma matan duka mahaifiyar su suka biyo
Lokacin da yaga zainab ya yaba sosai da nutsuwar ta,don haka ya miƙa tayin shi a wajen Isma'il, Isma'il yaso yi masa musu don yasan halin matar shi,amma haka ya danne,ya bawa Mahmud auren zainab
Ana i saura wata uku biki suka dawo Nigeria gaba ɗaya,suka sauka a tangamemen gidan Isma'il da ke sardauna crescent Nassarawa G.R.A,gida ne ba garari,babu abinda babu a ciki,sannan ya gina parts a ƙalla goma a gidan saboda yace so yake ya haɗe kan yaran shi ko da bayan sunyi aure,ya so malam Ishaq ya dawo gidan amma ya nuna masa a'a,a cewar shi shi da tsufa ya cim masa ma jiran lokaci yakeyi,anan suka cigaba da zama har lokacin biki yayi
Anyi biki lafiya, Isma'il ya nunawa zainab gata sosai,an kai amarya gidan mijinta wanda ke badawa layout, kasancewar shi dama iyalan shi a Nigeria suke zaune ba kasafai suke zuwa US ba
Sai dai tunda ta tare take fuskantar matsaloli daga wajen abokiyar zaman ta,ga yaran ta basu da kunya ko kaÉ—an, Ma'aruf ne kawai mai tausayin ta da girmama ta
Duk abinda akeyi doctor Mahmoud bai sani ba,kuma zainab bata taɓa shaida masa ba,ba shi ba ma,ko ƴan uwan ta bata shaidawa,idan abin ya dame ta sai dai ta shige ɗaki tayi ta kuka
A haka ta kasance har tsawon shekara guda,a lokacin ne ta haifi Æ´ar ta ta farko wato NUSAIBA,a lokacin bayan an kammala suna gida aka maida ita gaban faÉ—ima har ta murmure
Ranar da zata koma tun safe take zullumi,har faɗima ta fahimci halin da take ciki,amma da ta tambaye ta sai tace ba komai,tilas ta ƙyale ta,amma ta rinƙa yi mata nasiha cikin hikima da kara ƙarfafa mata gwiwa
Shekaru biyu tsakani ta kuma haifar ɗan ta YUSUF,a lokacin doctor Mahmoud ya fara gane makircin da bara'atu,ta sha haɗa su faɗa,zainab ta san aikin ta ne amma bata taɓa gaya masa ba sai da ya gane da kanshi,wannan shine dalilin da yasa ya raba musu gida,sai a sannan zainab ta samu kwanciyar hankalin gidan auren ta
Sai da Yusuf ya shekara bakwai sannan zainab ta sake haihuwar Æ´ar ta mace,a lokacin bara'atu Æ´aÆ´an ta bakwai,bayan faiza akwai sadiya,fadila,Mubarak da shukra sadiya sa'ar nusaiba ce,Yusuf ya bawa fadila wata bakwai,Mubarak shekarar shi huÉ—u,ita kuma shukra watan ta tara