← Book details Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 31

Sashe 18

Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gashi kuma Imran yana sakin Deeja ya É—auki umaiman shi suka wuce US in da fauwaz ya tafi honeymoon da amaryar shi

Satin Deeja uku ta samu sauƙi sosai,mamie da kanta ta ɗauko ta a asibiti,ta dawo da ita gidan baba Prof,cikin ɗan lokacin aka sake mayar mata da matsayin ta na auta, saboda gata da sakalcin da ake mata, tarairaya sai abinda aka manta, yaya abdallah ƙanin fauwaz kullum sai ya fara zuwa wajen ta a falon Mamie yayi ya tsokanar ta sannan yake fita aiki,idan ya dawo kuma ya taho mata da favourite ɗin ta,nan ma su sha hira,hakan yana damun matar shi lubaisa wadda itama ba wani sakewa Deejan take sosai ba,itama Deejan ba shiga sabgar ta takeyi ba

Cikin É—an lokaci Deeja ta mayar da jikin ta tayi kyau,fatar ta tayi fresh asalin chaculate skin É—in ta ta fito,ta cigaba da rayuwar ta cikin farin ciki

Watannin ta uku a gidan su fauwaz suka dawo,shima Imran gidan ya wuto instead of gidan shi da ya saka Deejan da umaima a ciki. Shi kanshi fauwaz bai ji daɗin abinda Imran yayi ba amma ƙarairayin da suka yi ta zuba masa ya sanya shima ya fara ganin laifin Deeja

An tarbe su cikin mutunci,babu wanda ya nuna musu komai,don dai baba Prof yayi warning kan kar a sake tayar da zancen,don haka ko a fuska babu wanda ya nuna musu komai,umaima sai yatsina takeyi

Lokacin da suka dawo ko ƙeyar Deeja basu gani ba,don bata nan ma ta je yiwa yaya Ma'aruf da Aunty Farida sallama da zasu wuce turkey gobe,bata dawo gidan ba sai bayan maghriba,a lokacin dukan su suna zaune a main parlour ana hira cikin raha da farin ciki,tayi sallama da yawan su suka juyo,ciki har da su fauwaz da umaima,shi kam Imran all of a sudden yaji wani guilty conscience ya shige shi,ya kasa ɗaga kai ya kalle ta

Kallo É—aya tayi musu ta É—auke kai ta gaishe su babu yabo babu fallasa,wasu sun amsa,wasu basu amsa ba,ta tsallake su ta wuce part É—in Mamie in da É—akin ta da aka kashe wa kuÉ—i kamar na amarya yake

To fa!ganin Deeja a gidan,gashi Imran da alamu ya dawo gidan shima,sai umaima taji hankalin ta ya tashi,ta samu aminiyar ta afra ta karanta mata komai sannan ta nemi shawarar ta

Itama afra tana tsoron fauwaz zai iya auren Deeja,don tun ba yanzu ba yana yawan ba ta labarin ta,don haka suka fara ƙulle-ƙullen yadda Deeja zata bar gidan,tunda dai ba gidan ubanta bane (a cewar su umaima fa 😁)

Kwanan su biyu da dawowa Imran na zaune a lambun gidan inda ya saba zama yana duba wani littafin su na likitoci anatomy sai sallamar Deeja ya ji,yayi saurin É—ago kanshi yana amsawa,duk da cewar yayi mamakin zuwan nata amma ko a fuska bai nuna ba,don shi dai tun ranar da suka dawo sai dai ya gano ta daga nesa,don ko ya shiga parlourn mamie gaishe ta baya ganin Deejan

Sam bai ji daÉ—in yadda ya ga ta koma so lean ba alamun dai har yanzu ba wani daÉ—in jikin ta takeji ba,ko kuma tana cikin damuwa

"Sannu da hutawa!"ta furta fuskar ta babu yabo babu fallasa

"Sannu Khadijah,mun same ku lafiya?"ya furta da Æ´ar fara'a a fuskar shi

Maimakon ta amsa sai gani yayi ta dire masa kuÉ—i a kan É—an table É—in da ke gaban shi,har yanzu fuskar ta babu yabo babu fallasa ta kalle shi cikin idanu tace

"Wannan kuÉ—in ka ne,kasan a musulunce idan aure ya rabu batare da ma'auratan sunyi wata mu'amalar aure ba namijin yana da rabin sadaki,dama 300k ka bayar ko?to ga 150k É—in ka

Sannan wannan kuma"ta faɗa tana nuna wanda yafi yawa ta cigaba"kuɗin da ka kai asibiti ne,tunda a lokacin da ka bayar auren ya ƙare responsibility na zuwa lafiya ta ya koma kan iyaye na,so shine na dawo maka da kuɗin da ka bayar na asibiti,na gode"tana kai wa nan ta juya ta bar wajen tana yunƙurin ɗaga kiran da akayi mata a waya

Imran da mamaki ya ƙamar dashi ya taso da sauri ya biyo ta da kuɗin duka yana faɗin"haba Deeja!yanzu waɗannan kuɗin zaki dawo min dasu bayan kema kin san ninkin su ma kin fi ƙarfin su a waje na? Please Deeja menene na dawo dashi kuma?"

Fasa ɗagawa wayar tayi ta kalle shi cikin idanu tace"bana buƙata ne,zai fi ka samu waɗanda suke buƙata ka basu zaka fi samun lada,ko ka ganni a buƙace ne?"

"Kin raina kyautar da na miki ko me?"ya faÉ—a zuciyar shi na sake karyewa

Yatsina fuska Deeja tayi tace"bakaji abinda nace bane?bana buƙata,idan ma kace na fi ƙarfin su ne to babu laifi,kyauta kuma bana so,na gode, Allah ya sa ka gane"tana kai wa nan ta juya ta bar wajen tana ɗaga sabon kiran Mima da tayi mata a lokacin

Tabbas idan yace baiyi nadamar sakin Deeja ba yayi ƙarya,bai yarda shi wawa ba ne sai yanzu da har aboki zai shiga rayuwar shi ya tarwatsa masa farin ciki,ya tabbatar yana son umaima Amma Sam baya mata kallon mutum mai ƙima,yasan bayan momyn shi babu wata mace da ta bawa rayuwar shi gudunmawa,ta magance masa damuwa kamar Deeja,amma shi kanshi baya son ma tuna irin abubuwan da yayi mata waɗanda ya san har abada bazata taɓa mantawa ba

Jiki a saɓule ya koma ya zauna yana kallon kuɗin da kawo masa,ba sai an gaya masa ba ya san definitely Deeja ta fi shi kusan komai na rayuwa, musamman gata,duk da cewa a yaran professor ta girmi Yasmin Amma ita yake kira autar shi, ballantana sauran mutane,tana samun gata da kulawa fiye da tunani,kowa son ta yake, saboda tsabar gata da soyayyar da ake mata ma lokacin da ta kammala karatun ta ta dawo Nigeria abba ya hana ta aiki,baba Prof ma ya goyi bayan shi,su a ganin su zata je ta sha wahala,don haka suka yanka mata kuɗi mai kauri a matsayin albashi,kuma ko da ta samu suka bar ta ta fara aikin ma basu daina bata albashin ba,amma duk da haka ya kan tuna duk ƙanƙantar abinda ya bata a lokacin ko ya siyo mata tana karɓa da farin ciki tayi masa godiya,karo na farko da Deeja ta dawo masa da wani abu da ya bata,wanda ba sai an gaya masa dalilin ba

Duk wannan tattaunawa da Deeja da Imran sukayi akan idanun umaima,amma bata jin mei suka ce,ai kuwa ta cika tayi fam tana ta huci,a ranta ayyanawa takeyi dole ma ta ci uban Deeja don ta fara kai ta bango,ta kama ƙugu ta tsaya tana huci,ita kuwa Deeja ko lura ma da ita batayi bata tana magana da miman ta a waya suna dariya,sai kawai ji tayi an damƙar mata wuya

Da sauri ta juya tana kallon umaima,tare da faÉ—in "zan kira ki leemo"ta kashe wayar

Cikin mamaki tace"baiwar Allah lafiya?"

"Oho ban sani ba,meye alaƙar da ta haɗa ki da miji na?wai ma ba an rabu ba?"

Abin ya bawa Deeja haushi,ta kalli umaima da ke girgiza jiki tana ɗaure fuska,tana kuma sake riƙe mata wuyan hijabi

Ta san dai ko dambe zatayi da umaima sai ta karya ta ma umaiman bata mata ko mintsini É—aya ba,ture ta tayi tana faÉ—in"dalla sake ni,har wani miji ke gare ki?me ya shafe Ni dashi?"

"Oho naji,to me ya kai ki wajen shi?"

Deeja ta ja tsaki ta kalle ta cikin idanu tace"shi da kika isa dashi kije ki tambaye shi"daidai nan afra da zakiyya suka iso wajen,zakiyya itace matar Nasir Wanda yake bin salma

Kwata-kwata ba ta shiga shirgin su Afra sai ta kama, saboda ta fuskanci basu da tarbiyya kwata-kwata, musamman afra da umaima,har gwara gwara lubaisa ma,don haka Deeja itace mutuniyar ta

Fuska É—aure ta kalli su Deeja tace"lafiya kuwa?"

Umaima ta kalle ta a yatsine tace"wannan ƙaruwar gidan ta daina bibiyar min miji"

Zakiyya ta kalle ta cikin ɓacin rai tace"karuwa?"

"Eh karuwa!"a cewar afra cikin tsiwa, zakiyya zata sake magana afra tayi mata nuni da tayi shiru,sannan ta ja hannun ta suka bar wajen,tana jin umaima na jan dogon tsaki

Ɗaki suka shiga, zakiyya ta rinƙa tausar ta amma sai Deeja ta nuna mata abin bai dame ta ba, dama kuma bata saka su umaima a layin masu hankali ballantana suyi abu ya dame ta

Umaima da Afra kuwa sashen afra suka wuce suna shawarar yadda zasu ɓullowa Deeja,a ƙarshe dai suka samo hanyar da zasu fara musguna mata,sukayi shewa suka tafa

Kwana biyu tsakani Mamie ta wuce Abuja,wanda daga nan zasu Yemen ita da momy Aysha

Deeja ta shigo main parlour tana tafiya tana chatting da Aunty Bintu,labari take bata cewa yaya Ma'aruf da Aunty Farida zasu dawo next week,dama tafiyar ta yaron su ce Ayman da yake fama da matsalar ciwon ƙoda,amma yanzu da sauƙi sosai,tana cikin karanta amsar Aunty Bintu da take sanar da ita sun yi waya da Aunty Farida ɗin sai kayi taji santsi ya kwashe ta ta tafi luuu ta bugu da ƙasa,sai ji tayi an kwashe da dariya ta rainin hankali,ta kalli ƙasa don ganin abinda ta taka,ɗanyar kuɓewa ce kuma ga dukkan alamu zuba ta akayi,ta kalli masu dariyar, umaima,afra ce da lubaisa

Afra ce ta ƙaraso wajen tana kallon ta a wulaƙance tace"kaɗan kika gani, indai kin nacewa zaman gidan nan,tunda baki da zuciyar da zaki zauna a gidan naki uban

Deeja batayi jinkirin mayar da amsa ba"gaskiyar ki,tunda ko babu komai a gidan naki uban nake da zama"tayi ƴar dariya tace"shashashu"ta miƙe a zafafe ta tsallake kubewar ta bar wajen

Umaima ta ɗura wani ashar ta nufe ta tana huci, lubaisa ta riƙe ta, umaima tana huci tace"sake ni,wannan karyar har ta isa ta zage ni?"

Afra tace"easy sister,rabu daita,kema kin san bazamu ƙyale ta ba"

Kai amma umaima kina da ƙarfin hali😥ko da yake banga laifin ki ba, saboda kinga Imran a mutum,baki ganshi lokacin da yake wulaƙantaccen shi ba

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 27

Tun daga ranar su umaima suka matsa wa Deeja lamba,duk abinda zasuyi don su ɓata mata rai yi sukeyi,kuma ta hanyar da ba kowa ne zai gane ba ballantana a tsawatar musu,bugu da ƙari ma Mamie bata nan, ballantana ta saka idanu
Chapter 18 · 0% Book details