← Book details Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 31

Sashe 22

Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin tashin hankali Umaima ta miƙe ta fice daga gidan,kai tsaye gidan fauwaz ta nufa, Afra na zaune tana yanke wa haneef farce sai ganin Umaima tayi a kanta,a ɗan tsorace tace"Malama Lafiya?"daga yanayin fuskar ta za'a iya gane haushin da taji na abinda umaiman tayi mata

Amma da yake umaima tana cikin tashin hankali bata kula ba,ta zauna gefen Afra tana faÉ—in"ina fa lafiya Afra, Imran zei iya rabuwa dani,ina cikin tashin hankali"

Afra ta É—an buÉ—a ido da mamaki tace"ikon Allah!to me kikayi masa?"

Umaima ta warware mata labarin kaf tun daga lokacin da nadiya taga Khalees har auren su da sakin Deeja da abinda ya faru yau bata ɓoye mata komai ba

Shiru Afra tayi cike da É—imbin mamaki,zuwa can tace"ya kuke da wannan nadiyar ne?"

"Nima ban sani ba,amma yaya na Najeeb yace cousin ɗin mu ce"wani kallo Afra tayiwa Umaima tace"shine dalilin da yasa kikayi mata hanyar da ta auri engineer ko dai da wata a ƙasa?"Umaima ta sunkuyar da kai ta kasa bata amsa

Afra tayi murmushin takaici tace"uhm!umaima kenan!Ni kishin miji na nakeyi da Deeja, saboda ina da yaƙinin babu wani mai hankalin da zai samu Deeja a matsayin mata yayi wasa da damar shi,tunda na samu labarin auren ta da mijin da yafi nawa komai na zubar da makaman yaƙi na,lubaisa ma haka,amma ke saboda ƙiyayya da hassada ce a ranki sai da kika shigar da wata ƙawar ki kika tarwatsa mata farin ciki da ta ɗauki lokaci mai tsawo tana nema

Mu kanmu son zuciya ne ya rufe mana idanu saboda Imran ɗin nan a wulaƙance ta samo shi ta mayar dashi mutum,amma yau an wayi gari akan wata can da bai san asalin ta ba yayi mata cin mutunci,to Ni dai babu abinda zan iya,kuma wannan haliman da kike magana duk wani rashin mutunci da wata fitsara da kike taƙama da ita ta zarce ki,don haka Ni kar kija min magana,miji na yana nan,tun wuri ki koma gidan ki,nima kar kija yaji aure na ya fara rawa"

"Allah sarki Deeja baiwar Allah!"Muryar fauwaz sukaji,a firgice suka waiga suka kalle shi,yana sanye da jallabiya milk colour yana tsaye fuskar nan babu Rahama

Sai da hantar cikin su ta kaÉ—a,afra ta firgita don tasan itama nata auren zai iya fara rawa

A nutse ya ƙaraso ya samu waje ya zauna sannan ya dube su yace"kun bani mamaki,wannan abu yayi min ciwo sosai, Afra,wallahi ba don kinyi nadamar abinda kukayi ba da yau babu abinda zai hana Ni sakin ki

Ku in banda rashin iymani bakwa ganin cewa Deeja marainiya ce?kuma ita mutum ce da ko magana bata dame ta ba ballantana shiga shirgin wani?to don Allah meyasa zaku matsawa rayuwar ta?

Shi kanshi Dr auren ki da yayi shine sakayyar abinda yayi wa Deeja,don ke dai wallahi ba matar zama bace

Duk halin da kuke ciki da najeeb ina sane"

A tsananin kiɗime umaima ta ɗago ta kalle shi idanun ta a waje, fauwaz yayi murmushi yace"well!you think kuna yin dabara kuna ɓatar da hankalin mutane ke da Najeeb babu wanda ya sani ko?to tun barowar ki garin ku taura,da Abinda yayi silar zuwan ki garin nan na sani,kuma saura ƙiris mijin ki ya sani"

Faɗuwa tayi a gaban shi tana faɗin"don girman Allah ka taimake ni ka rufa min asiri,na roƙe ka"

"Zan rufa miki asiri but in one condition"gyaɗa Kai takeyi tun ma kafin taji sharaɗin,bai damu ba ya cigaba"sai kin datse kowacce alaƙa dashi wanda ya mayar da rayuwar ku kamar waina a tanda daga ke har Imran,idan nace alaƙa ina nufin kowace iriyar alaƙa"da sauri tana share hawayen ta tace"Ni dama don babu yadda zanyi ne,amma na kai watanni biyar ma yanzu ko haɗawa bamuyi ba,nima dama bana son alaƙar"

"Wannan ya rage naki kuma,na biyu kuma wanda shine ma yafi Zama wajibi,ki nemo min Æ´ar'uwa ta"

Umaima kukan ta ya ƙaru,tashin hankali ya mamaye ta,ita ina zata ga Deeja? meyasa ake ɗora mata alhakin ɓatan ta,ko kallon ta fauwaz bai sakeyi ba ya kalli Afra yace

"Ke kuma,duk abinda kikeyi kinayi ne don kinga alamun ina son Deeja ko?to Kar kiji da wai,ina son ta fiye da yadda kike tunani ina son ki,kuma duk ranar da na ganta ki shirya zama daita a matsayin kishiya ko ki bar mata gidan"

"Wallahi abban haneef na amince,na yarda zan zauna daita a matsayin kishiya nayi alƙawari"Afra ta amsa har yanzu zuciyar ta bata daina bugawa ba

Ɗaga kafaɗa yayi gami da taɓe baki alamar bai damu ba,ya fice daga parlourn

Umaima babu shiri ta koma gida,zama tayi tana tunanin mafita,zuwa yanzu kukan ma ya É—auke mata,sai kanta da yake sarawa, abubuwa sun taru sun cunkushe mata

Wayar ta ce ta É—auki ruri,a É—an firgice ta kalli wayar,ta janyo tana duba mai kiran

Ganin Najeeb sai da gaban ta ya faÉ—i,ta daure ta É—aga ta kai kunne,kafin tace komai taji yana faÉ—in

"Malama kina raina min hankali!na buƙaci kuɗi daga gare ki naji shiru,na buƙace ki kina ta min yawo da hankali,to na baki nan da awa uku,ina son ganin ki"

Cikin kuka tace"haba yaya Najeeb!wai me yake damun ka ne?na gaya maka ina cikin damuwa amma maimakon ka tausaya min sai ƙara min wata damuwar kakeyi,ya kake so nayi ne wai?"ta ƙarashe cikin ɗaga murya

"Ke ballagaza!kama kanki!!kar ki sake É—aga min murya,or else na É—auki mummunan mataki akanki,ina ruwa na da wata damuwar ki ta banza? Abinda nace idan bazakiyi ba ki gaya min!"

Cikin kuka tace "bazan yi ba wallahi,na gaji da halin ka,haba!"

Wata dariyar rainin hankali yayi yace"I see,to ko me kika gani kar ki zarge ni,ki zargi kanki"yana kai wa nan ya kashe wayar shi

Takurewa tayi tana zubar da hawaye, rayuwar ta ce ta baya take rotating akan ta,wani irin kuka mai ciwo ya ƙwace mata,amma duk da haka gwara waccan rayuwar akan ƙazamar rayuwar da Najeeb ya jefa ta, mahaifin ta ya faɗo mata a rai, ta sake fashewa da kuka mai ciwo,zuwa yanzu kaso saba'in da biyar cikin ɗari na hope da take dashi a komai ya tafi

To pa 🥺 umaima ya dai??
#Nusy bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 31

Zama tayi dirshan a ƙasa tana tunanin mafita,ji takeyi dama tun farko mutuwa,amma tabbas tayi wauta,tayi tsalle ɗaya mai jefa mutum rijiya yayi dubu bai fito ba,duniya ta ruɗe ta da yawa,ta sake fashewa da kuka tana faɗin

"Ni umaima na cuci kaina,naga ta kaina,nasan abinda nayi ne yake bibiya ta,kaicon rayuwa ta!"

"Ai baki fara kaico ba umaima!munafuka,matsiyaciya, tsinanniya,amma dai bakin uwa ne a kanki ko?dama ke mutuniyar banza ce? dama ke ɗin karuwar Najeeb ce?na godewa Allah da bai bani haihuwa da ke ba annamimiya!"Imran ne mai faɗar wadannan maganganu cikin ɓacin rai da ƙunar zuciya, fuskar shi a matuƙar ɗaure da ɓacin rai da tashin hankali

Wayar shi ya jefa mata a fusace yana faɗin"Umaima!a yau na fahimci kuskure na na auren ki,nayi nadama mara amfani ta auren ki,ashe ragowar wani ƙato ce ko ma nace ƙatti?kuma da auren ki kike fornication?the worst part ma da aboki na?wato da ke dashi dukkan ku mutanen banza ne,Ni zaku cuta Ku ci amana,shine kuka shiga tsakani na da khadija ya cuso ki don ku cuce ni"yayi murmushi mai ciwo yana kallon umaima da ke daskare tana kallon wayar shi da hotunan ta da najeeb suna sheƙe ayar su yake,ya cigaba da cewa

"Nayi miki alƙawarin sai na ganar da ke kuskuren ki daga ke har babban matsiyacin,sannan magana ta ƙarshe,ki nemo min ƴar uwa ta,idan ba haka nima na ɓatar dake"yana kaiwa nan ya ɗauki wayar shi ya take ta ya fice daga ɗakin

Sai a yanzu ta ji wani kukan ya kubce mata,nadama mara amfani ta cika zuciyar ta,a fili ta furta "ya Allah ka taimake ni,Deeja ina kika shiga ne? Allah ka bayyana ta"

*** *** ***

Ita kuwa Nadiya ta kunna ta ƙure volume tana bin waƙar tana rausaya, Khalees ne ya shigo ɗakin kamar an jefo shi,a raine ta kalle shi tace

"Tun É—azu ka fice,ina kaje?"

Wani watsatstsen kallo ya bi ta dashi,sai da taji hantar cikin ta ya kaÉ—a,bai ce mata uffan ba ya wuce closet É—in shi ya fara loda kaya a cikin trolley,yana gamawa ya janyo ya fito,da mamaki ta dube shi tace"ina zaka?"

"Kar ki kuskura ki biyo NI,zakiyi danasani"abinda yace mata kenan ya fice

Mamaki ne ya ƙamar daita,lallai ba shakka aikin ta yayi sanyi,don ita dai a iya sanin ta ko kara ta ajiye Khalees baya iya tsallakewa ballantana har ta kai su ga haka,da sauri ta ɗauki figigin mayafi ta ɗora akan English wears ɗin ta tayi waje,tun kafin ta baro parking lot take zuba mahaukacin horn,bawan Allah jiki na rawa ya buɗe,kafin ta fita sai da ta tsaya ta auna masa zagi da cin mutumci sannan ta fice,tana fita yace"da izinin Ubangijn ka'aba yadda asalin matar gidan nan mutuniyar kirki ta bar gidan nan kema sai kin barshi ita ta dawo,ai Allah nace"ya koma kan benchin shi yana tuna nagarta da halin ƙwarai irin na Deeja

Ita kuwa Nadiya Kai tsaye gidan bokan ta ta nufa,bayan ya gama ƴan dube-duben shi ya kalle ta rai a ɓace yace"kinyi sake mahaifiyar shi ta ɓata mana aiki,yanzu ko da wasa bata sakewa da addu'a,har ƙannen shi ta shi ya sanya sunayi,sannan bata tsaya anan ba,akwai wani abokin aikin shi mijin naki, mahaifiyar shi ta haɗa kai da wannan mutumi tana bashi ruwan addu'a yana bawa mijin ki,aikin mu ya lalace sosai"

"Na shiga uku!"ta faɗi cikin ƙaraji tana dafe kai,"yanzu ya zanyi?"

"Mafita ɗaya ce,ga wannan maganin"ya miƙa mata wani ƙulli yace"ki zuba masa a abinci,ki tabbatar yaci,yana ci shikenan zaki samu kanshi kamar baya ko ma fiye,amma idan bai ci ba za'a iya samun matsala"da rawar jiki ta amshi maganin tana faɗin"zai ci ma,zan tabbatar da yaci"ta ajiye masa kuɗin shi ta fice daga ɗakin nashi
Chapter 22 · 0% Book details