Sashe 19
Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai dai Deeja bata taɓa ɗaga kai ta kalle su duk da cewa suna ɓata mata rai,ta cigaba da harkar gaban ta kamar bata san sunayi ba
A lokacin ba ƙaramin kewar aikin ta takeyi ba,da akwai shi yanzu ta san ganin ta ma sai yayi musu wahala ballantana su sanyo ta a gaba,amma yanzu babu aikin,sai dai ranar da ta gaji da zaman gidan ta tafi gidan Aunty Bintu ko gidan zee ƙawar ta,ko safeena,itama ƙawar ta ce tun ta secondary School,dama ita bata tarin ƙawaye
Ganin irin takurawar da sukayi mata ya fara yunƙurin tayar mata da ciwo ya sanya ta ƙuduri aniyar ɗaukar mataki akan su
Tana tsaye daga gefen ƙofar main parlour tana danna waya sai ji tayi an bangaje ta har wayar hannun ta ta faɗi,sai da ta firgita,ta ɗago da sauri tana kallon mai wannan aikin,sai taga Afra
Tsaki ta ja ta sunkuya ta ɗauki wayar ta da har ta ɗan tsage,a zafafe ta furta"ki rinƙa kallon gaban ki idan kina tafiya,idan kuma makancewa kikayi sai kiyi magana a samo miki ɗan jagora"
Kamar jira Afra take tayo baya da sauri tana nuna Deeja da yatsa tana faɗin"ke kama kanki,don dai kin san nafi ƙarfin wata trash ke,kar kiyi min abinda zai ɓata min rai na wulaƙanta ki a gidan nan wallahi"
Deeja na kallon cikin idanun ta har ta kai aya sannan ta amsa mata"mijin naki bai karanta miki cewa ba'a nuna ni da yatsa bane?fara sauke yatsan idan yaso sai nafi fahimtar magana kikeyi"
"An nuna ki da yatsan,kiyi abinda zakiyi,mijina kuma yafi ƙarfin yin magana akan wata kucaka ke"
Deeja tayi wata dariyar rainin wayo sannan ta kewaye afra zata wuce, Afra ta finciko ta baya tana huci,Deeja ta kalle ta a nutse tana ƙoƙarin danne ɓacin ran da ke yunƙuro mata,kamar zatayi magana sai ta fasa tayi gaba
Batayi aune ba sai ji tayi Afra ta ɗauke ta da mari, Deeja tayi stiff a wajen cikin tsananin mamaki da ɓacin rai,don samun waje Afra ta fara zazzaga mata masifa tana nuna ta da yatsa da tayi mata magana
Batayi aune ba sai ji tayi anyi sama da ita an buga da ƙasa,aikin Deeja ne,a cikin tsananin fushi ta rinƙa wanke fuskar ta da maruka hagu da dama,tsabar gigita ma ko kukan afra ta gaza yi,umaima ce ta shigo parlourn ganin halin da Afra take ciki ya sa ta taho da gudu don ƙwatar ta,amma cilli ɗaya tayi daita umaima ta gane wannan ba kalar su bace,wato cika baki ba ƙarfi,da gudu ta kwasa zuwa part din afran,nan ta samu fauwaz ta shaida musu yayi hanzari yazo kar Deeja ta kashe Afra,a bala'in sauri ya ƙaraso wajen,kafin ya ƙaraso ma Deeja ta gama abinda zatayi ta watsar da umaiman can gefe ta ɗauke wayar ta da ta faɗi tana ƙoƙarin barin wajen
Fauwaz ya kalli afra da umaima take taimaka mata ta tashi,ya kalli Deeja da ta sha mur tana ƙoƙarin shigewa ɗakin ta,a fusace yace"Deeja mahaukaciyar ina ce ke da zaki kama mata ta kiyi mata irin wannan dukan sai kace kin samu banza?"
Wani kallon rainin wayo ta watsa masa fuska a É—aure tace"shafa kaji!
Ba fauwaz ba,hatta umaima da afran da ke fama da kanta sai da suka kalli Deeja da sauri saboda tsananin mamakin amsar da ta bawa fauwaz, fauwaz Sarkin zuciya ya kai mata mari,tayi saurin gocewa sannan ta kalle shi cikin idanu tana kaɗa babban yatsan ta da dan tsakiya a fuskar shi tana faɗin"mafi girman kuskuren da zakayi a rayuwar ka shine marin DEEJA! don't attempt it again!"tana kaiwa nan ta samu waje akan two sitter ta zauna don zuwa yanzu ita kaɗai ta san me takeji a ƙirjin ta
"Okay! that's right!tattaro kayan ki ki koma gidan ubanki,wato mugun halin da kikayiwa Imran shi zakiyi mana ko?"
"Imran!"ta maimaita da wani yanayi a fuskar ta,sam korar da fauwaz yayi mata ma bata gaban ta,amma ambatar Imran da fauwaz yayi ya daki ranta,wato sharri ma Imran yayi mata,hawaye Masu zafi suka silalo a fuskar ta, bata sake magana ba ta miƙe ta shiga ɗakin ta ta ɗauko ɗan ƙaramin trolley ɗin ta ta zo ta wuce ta gaban shi,don lokacin afra da umaima basa parlourn,ko kallon tsiya batayi masa ba ta fice daga parlourn
Sai fauwaz yaji babu daÉ—i abinda yayi mata,cikin sanyi jiki ya biyo ta,har ta kai main entrance na gidan yace "Deeja dawo,kar ki fita"
Banza tayi masa ta cigaba da tafiya,ya sake cewa"Deeja bakya jin ina miki magana,i said don't move an inch daga in da kike"
Juyowa tayi ta kalle shi sama da ƙasa tace"kwantar da hankalin ka yaya fauwaz,bari kawai na bar muku gida kuyi sakewar ku yadda kuke so da matan ku,dama Ni na matsa muku"tana kaiwa nan ta sa kai ta cigaba da tafiya
"Deeja nace......"
"Hold it Yaya fauwaz!"ta faÉ—a a É—an tsawace sannan ta juya ta cigaba da tafiya
Kai tsaye gate ta nufa, fauwaz ya ƙwalawa driver din su kira yana bashi umarnin ya ajiye ta a duk inda zataje,ko kallon fauwaz batayi ba cikin ɗan sakin fuska ta kalli driver din tana faɗin"yi zaman ka kawai baba,na gode"ta fice daga gidan
Fauwaz yayi mamaki,ya tsorata sosai da zuciyar Deeja,ko da yake yasan Deeja tana da ɗauke kai akan abubuwa da yawa, kuma sau tari ko da anyi mata abu bata rama ba lokaci take jira,amma tana da uzuri,kuma tana da haƙuri,sai dai yau ga dukkan alamu an ƙure haƙurin ta
A sanyaye ya juyo yana nadamar abinda yayi mata,ya san shi da ya sake samun fuska a wajen ta kamar da sai wani ikon Allah
Ita kuwa Deeja gidan Aunty Bintu ta wuce,ta so tafiya gidan yaya Ma'aruf amma har yanzu basu dawo ƙasar ba,don haka ta wuce gidan Aunty Bintu
Wujiga-wujiga ta shiga parlourn Aunty Bintu,sallama kawai tayi ta shiga, Aunty Bintu ta É—ago da sauri tana kallon ta,bata sake kallon ta ba ta nemi waje ta zauna,Aunty Bintu tayi mata kallon tsaf sannan tace
"Auta lafiya dai?"
Bata tanka ba kuma babu alamun zata tanka ɗin,ganin hakan sai ta ƙyale ta,don kowa ya ga Deeja kallo ɗaya zaiyi mata ya gane da matsala
Ta kai mintuna biyar kafin ta miƙe don yin alwalar sallar la'asar da taji ana kira,sai kawai ta yanke jiki ta faɗi, Aunty Bintu ta rafka salati da ihu, intisar da ke ɗakin ta bata ma san da zuwan da Deeja ba ta rugo a guje, ganin Deeja a kwance a ƙasa ta tafi tana girgiza ta tana kiran sunan ta,ganin ba tashi zatayi ba ta fita compound ɗin gidan tana ihun neman taimako, within few minutes ma'aikatan suka hallara a parlourn
Kai tsaye asibitin Dr su'ad aka wuce da Deeja,sai dai wannan karon abin yafi ƙarfin asibitin,dole Aunty Bintu ta sanar da Ma'aruf da ko cikakken awa uku da sauka a ƙasar basuyi ba,haka ya sake shirya tashin su zuwa ƙasar Spain,don dama ya daɗe yana nema mata damar ganin wani babban likitan zuciya Dr Nicolas Alfred,babu ɓata lokaci kuwa suka wuce zuwa can ƙasar Spain
A ranar ya gayawa Mima,ai kuwa nan da nan ta shirya ta wuce garin Barcelona da ke can ƙasar in da a can Dr Nicolas yake
Awanni biyu da saukar jirgin su Ma'aruf da Farida sai intisar a Barcelona Mima ta sauka a ƙasar,dukan su babu walwala a fuskokin su,a lokacin da Mima taje har an shiga da Deeja observation room
Dama kafin su tafi Ma'aruf ya shaidawa Alhaji Abubakar mahaifin Khalees da baba Prof,dukan su sunyi mata fatan samun lafiya tare da bada kuÉ—i mai yawa na gudunmawa
Binciken Farko likitocin suka gano zuciyar Deeja ta kumbura,tana buƙatar aiki,wanda babu ɓata lokaci Ma'aruf ya saka hannu aka shiga daita theater room
Aikin ya É—auki tsawon awanni shida,su Ma'aruf suna ta addu'ar Allah yasa ayi aikin a Sa'a
Bayan sun fito an tura ta É—akin hutu ba tsawon awanni ashirin da huÉ—u,su ma su Ma'aruf suka koma masaukin su suna jimami
Anan Farida take bawa Mima labarin mutuwar auren Deeja,Deeja ta sha mamaki matuƙa,take tsanar Imran ta sake ninkuwa a ranta, ranar dai Imran ya sha tsinuwa da la'anta da alkaba'i daga wajen Farida da Mima har ma da intisar da bata saka musu baki ba,amma tana aika Tata tsinuwar a ranta
Sai da Deeja ta kwashe watanni biyu aka sallame ta,ta samu kulawa sosai,sau wajen biyar baba Prof yana zuwa duba ta,haka masu mamie da su yaran ta su fauwaz,duk da cewa ko sau ɗaya fauwaz ɗin bai ga haƙorin ta a waje ba kuma ya san dalili
Sosai Deeja ta mayar da jikin ta ta koma walwalar ta,daga Spain Kai tsaye Umrah suka wuce Saudiyya,daga nan suka wuce Malaysia,kwanan su goma suka dawo Nigeria,amma a can suka bar Mima
Kwanan su uku da dawowa Alhaji Abubakar yazo har gidan marigayi Dr Mahmud, kasancewar yanzu Deeja ta koma gidan su da zama,a babban parlourn Dr Mahmud É—in Ma'aruf É—in ya sauke shi da girmamawa,bayan ya gaishe shi ya umarce shi ya kira masa Deeja
Jidda Ahmed,Deeja tace a gaishe ki yadda kike supporting É—in ta da taya ta yaÆ™ar Imran ðŸ˜
#Nusy_bee
*****MATAR KHALEES*****
âœï¸Nusy bee
Page 28
Da sallama ta shigo parlourn,ta durƙusa cikin girmamawa ta gaida shi,ya amsa cikin kulawa yana tambayar ta jiki,ta amsa da alhamdulillah, fuskantar ta yayi sosai sannan yace
"Khadija naji duk abinda ya faru,kar ki sanya hakan a ranki ya dame ki,ki ƙaddara cewa jarrabawar ki kenan,amma in Sha Allah komai yazo ƙarshe yanzu,yau juma'a ko?to in Sha Allah zuwa juma'a mai zuwa da kaina zan aura miki mutumin da ya dace,in Sha Allah hakan zai kawo ƙarshen dukkan matsala"
Kan Deeja a ƙasa tana sauraron aminin mahaifin nata da maganar shi tayi mata gingirin aka,shi kanshi Ma'aruf maganar ta zo masa a bazata,amma duk a cikin su babu mai iya cewa komai,sun daɗe da sanin aminin abban nasu baya magana biyu,kuma ba'a chanja masa magana, Ma'aruf ne yayi ƙarfin halin yin fatan alkhairi,ya miƙe yayi musu sallama, suma sallama sukayi masa suka biyo bayan shi suka nufi cikin gidan suna tunanin wanda za'a bawa Deeja