Sashe 5
Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A can bayan sun idar da sallah Mima da zakiyya suka sanya Deeja a tsakiya, Mima ta dube ta cikin damuwa tace"sisto me hakan ke nufi?"kaf family baki da kamar Ni da aunty kiyya Amma auren ki sai ji mukayi a gari,me hakan ke nufi?"
Shiru Deeja tayi zuciyar ta tana suya,da tana da saurin kuka da tayi ta samu sauƙin raɗaɗin da zuciyar ta takeyi,amma ina! bata iya saurin kuka ba,ta dube su tace"aure na da kuke gani ban yi shi a mood na farin ciki ba,asalima har na auri engineer Abdul bansan shi bane,kuma wannan hasarar da kuka san shi da ita bai chanja ta ba,,ga mahaifiyar shi da ƴan'uwan shi da basa so na ko kaɗan,a haka mukayi auren duka duka ko kwana hamsin ban cika ba aka ɗaura mana aure dashi,har kwanan yau daurewa zaman gidanshi nakeyi kawai"
Shiru sukayi suna kallon yanayin ta ya sauya,alamun damuwa sun bayyana akan fuskar ta,Mima ta dafa kafadar ta cikin kwantar da murya tace
"Ki cigaba da haƙuri my Deeja,komai yayi farko zai yi ƙarshe,ki cire duk wata damuwa a ranki komai yayi tsanani yana tare da samu sauƙi in Sha Allah,shi kuma mijin ki ki cigaba da yi masa biyayya in Sha Allah zaki ga ribar abin"
#Nusy bee
*****MATAR KHALEES*****
âœï¸Nusy bee
Page 7
Zakiyya ma ta ƙara da faɗin"in har kika jure kika cigaba da kyautata masa babu dare babu rana ina mei tabbatar miki da cewa shi kanshi ba zei san lokacin da zai fara son ki ba,duk da cewa mijin ki mutum ne mai wani irin ra'ayi, ba'a tantance gaban shi da bayan shi,amma ai mutum ne shi,yana da zuciya,kuma namiji ne ko ba haka ba?
To kamar yadda na sanki baki da saurin fushi ina so ki daure ki cigaba da hakan,wannan shariya da ƙyaliyan ki ajiye su a gefe, Khalees mijin ki ne yayanki ne,ginshiƙin ki ne,kinga yanzu babu in da mama da Abba"
Kalaman kiyya na ƙarshe sunyi matuƙar tasiri wajen karya zuciyar Deeja,wato babu idanun mama da Abba,tunowa da shuɗewar gatan nata ya sanya ta fashewa da kuka cikin tausayawa,su Mima suka rinƙa tausar ta suna bata baki har ta daina kukan
Kasancewar ta tare da Mima da kiyya ya sanya damuwar ta ta kau,ga yusra da Huda ƙannen Imran da suke uwa ɗaya uba ɗaya,su kam suna matukar son ta,har ta kan ji dama ace suma ƴan uwan Khalees haka suke son ta.
Sun haÉ—u da su Imran É—in a falon Mamie babba,bata nuna musu komai ba ta gaishe su cike da girmamawa a matsayin su na yayyen ta,Yaya fauwaz ya kalli Mamie yace"Mamie, Deeja fa wannan abokin Imran É—in ne ya aure ta"
Gaban Deeja ya buga da ƙarfi,abokin Imran?tana jin momy na cewa "wanne abokin nashi?"
"Engineer abdurrashid mana, Khalees,wanda sukayi secondary tare kin gano shi?"
"Au!tooooo!!na gano shi, Allah ya sarki,yaron kirki kuwa,ashe shi ta aura"a cewar Mamie fuskar ta cike da fara'a
"Shi ta aura Mamie"Yaya fauwaz ya tabbatar mata
"To Allah ya sanya alkhairi"
Suka amsa da "ameen"
Miƙewa tayi ta nufi ƙofar fita,cikin rashin sani idanun ta suka sauka akan imran,ai kuwa tayi amfani da wannan damar ta zabga Masa harara,ai kuwa ya sunkuyar da kanshi, fuskar shi ɗauke da alamun damuwa,hakan bai dame ta ba tayi saurin barin falon
Washegari ta kama asabar,a ranar ne aka fara biki, kiyya da Mima da Deeja sun ɗau wanka cikin lace Pink mai ratsin red flowers,wannan tsarabar Mima ce a wani zuwa Switzerland da tayi ta gano su ta siyo har da aunty Bintu da intisar,ai kuwa sunyi matuƙar haskawa a wajen party ɗin
Washe gari ta kama ranar ɗaurin aure,su Deeja ana ta hidima da baƙi,ga wankan da suke ɗauka tamkar amare ita da su Mima,kuma tunda Mee'ad ta ganta ta daina yarda da kowa,gata da farin jini amma ta dage ita sai Deeja kaɗai
Rashin son abincin da yawan kasalar da Deeja ke fama da dashi ne ya sanya zargin ta ƙaruwa,amma bata son tabbatar da hakan saboda bata san da wanne ido zata dubi Khalees da batun cikin ba,tun da a iya sanin ta baya son ta,to ta yaya zai so haɗa zuri'a daita?amma ta yanke shawarar tuntuɓar likitar ta Dr su'ad bayan biki don ta tabbatar cikin ne ko akasin hakan
Su Afra ne ita da umaima da wata ƙawar umaiman nadiya suka jero suka fito falon Mamie
Nadiya ce tayi saurin taɓo umaima tace"umaima!kinga wani handsome guy!da sauri umaima ta ɗago kai don ganin waye
Mutum biyu ta gani,wani guy da bata san waye ba sai mijin ta Imran,nan da nan kishi ya turnuƙe ta tace"to ƙwalelen kare da hantar kura,miji na ne"
Da sauri nadiya ta dafa kafadar ta tace"I'm sorry friend!ba shi ba fa,na kusa da shi"sai a sannan umaima ta ƙare wa na kusa dashi ɗin kallo
Wankan tarwaɗa ne,dogo mai ƙirar ƙarfi, kyakkyawa ne sosai,sai dai da alamu zai yi jin kai yana sanye da shadda,sky blue,ɗinkin yayi matuƙar kyau sosai,ɗan murmushi tayi tace"good,ina taya ki murnar wannan babban kamun,zan Miki hanya daga wajen mai gida na"cikin murna nadiya ke faɗin"na gode sister na"
An kammala biki lafiya,an kai amarya gidan mijin ta lafiya,washe gari ta kama Litinin daga wajen aiki kai tsaye Deeja gida ta wuce, zuciyar ta cike da tsoron wane sakamako zata gani game da zargin da takeyiwa kanta
Bata samu Khalees a gida ba,batayi mamaki ba don tasan bai ci ace ya taso daga wajen aiki ba,don haka wanka tayi ta shirya cikin riga da skirt na atamfa tayi kyau sosai,bata nemi abinci ba duk da yunwar da takeji,don ji tayi tana sha'awar alala,don haka tayi sauri taje inda zata je ta dawo akan kari
Asibitin Dr su'ad ta nufa, cikin Sa'a ta same ta da murmushi akan fuskar Dr su'ad ta dube ta tana faÉ—in"a'a!matan manyan injiniyoyi!kuma manyan akawuntoci,yau kune a asibitin namu?"
Murmushi Deeja tayi tace"mune wallahi,ya akaji da aiki da fama da jama'a?"
"Jiki alhamdulillah!ya ƙarin ƙarfin jikin?"
"Jiki alhamdulillah,mun samu afuwa"a cewar Deeja
"To Allah ya sa dai ba shine ya tashi ba ko?"
Deeja ta girgiza kai tace"ko É—aya, dama suspecting nakeyi, Kamar ciki gare ni shine nazo kiyi mini test"
Cikin farin ciki Dr su'ad tace"Allah ya tabbatar da abinda yafi alkhairi,naga yaran Madam Deeja da angon ta abdurrashid"murmushin yaƙe kawai Deejan tayi
Dr su'ad tayi Æ´an gwaje-gwajen ta inda ta tabbatar wa da Deeja zargin ta, Deejan tayi godiya ta ajiye mata kuÉ—in ta ta tafi
Tana shiga Mota ta kira safeena ƙawar ta, safeena na ɗagawa bata saurari komai ba tace"feena ya ma sunan maganin da kikayi amfani dashi kikayi abortion?"
Cike da mamaki feena tace"abortion kuma? abortion zakiyi ne?haba Deeja,ko nima a lokacin ƙuruciya ce ta ɗebe ni,kuma naga babyn da na haifa baiyi ƙwari ba,shiyasa"
"Wait malama!ba dogon bayani na tambaye ki ba just tell me idan zaki iya"
Cike da mamaki feena ta gaya mata,tana gama faÉ—a mata ta kashe wayar ta nufi chemist
Wani katafaren chemist ta shiga da sallama,mai chemist É—in ya amsa sannan ta tambaye shi maganin,babu musu ya É—auko mata,ta ajiye masa kuÉ—in shi ta É—auki maganin ta juya ta bar chemist É—in
Tana tuƙi kalaman kalaman Dr su'ad nata mata amsa kuwwa"congratulations Mrs Khalees!kina ɗauke da babyn mu na wata biyu da kwanaki shida, Allah ya raba ku da lafiya,sai a kular Mana da baby da kyau"
Dogon tsaki taja tana girgiza kai,a fili,ta furta"abinda bazan iya ba, Deeja bazata iya haifar yaran Khalees ba"
Gida ta koma,a harabar gidan ta iske Khalees yana karatun jarida,bata kula shi ba tayi shigewar ta shi kuma ya bita da kallon mamaki,a ran shi yana ayyana cewa lallai ba lafiya ba
A kan gado ta watsar da komai jakar ta,maganin da ta siyo wanda yazo a hannun ta,mayafin ta da É—ankwalin ta ta É—auki towel ta shiga bayi don zafi takeji
Khalees ne ya shigo ɗakin,gefen gado yayiwa kanshi matsuguni yana jiran ta fito yaji ina taje har zuwa yanzu ƙarfe biyar saura,shi da yace huɗu tayi mata a gida,don masu gadi sun sanar masa dawowarta,kuma ga alamu ya gani,an gyara gidan tas.
Kwalin maganin da ya gani ne yaja hankalin shi kamar bazei duba ba sai dai ya É—auka ya duba
Tashin hankali ne ƙarara a kan fuskar shi mei Deeja zatayi da wannan maganin?"ya tambayi kanshi
Ajiye maganin yayi ya miƙe ya fice daga ɗakin,baiyi cikakken minti guda da fita ba Deeja ta fito, doguwar riga ta sanya,ko mai bata shafa ba ta ɗauko gorar ruwa dake cikin ɗakin nata,ta ɓalli maganin ya zube a ƙasa
Da sauri ta É—ago kanta don ganin me wannan aikin, Khalees ne
#Nusy bee
*****MATAR KHALEES*****
âœï¸Nusy bee
Page 8
Yana tsaye sai huci yakeyi tamkar mayunwacin zaki, kyawawan idanun shi sun rine zuwa jajaye,alamun tashin hankali sun gama bayyana akan fuskar shi
Ita mamaki ya bata ma,amma sai ta ɓoye hakan akan fuskar ta,ta ɗauko maganin da nufin sake ɓalla sai ya fizge,sai taji ya fara bata haushi, cikin ɗaure fuska tace"bani!"
Bai bata ba kuma bai amsa ba,sai girgiza kai kai yakeyi,cikin tsawa tace"ka bani abu na mana!meye hakan?"
Juyawa yayi ya fita, Deeja ta raka shi da ido zuciyar ta nayi mata suya,a haukace ta miƙe ta ɗauki key ɗin motar ta tayo waje,a falo ta same shi ya rafka tagumi,ko kallon shi batayi ba ta ɗauki hanyar fita,sai jin Muryar shi tayi yana cewa
"Idan kika fita a bakin......."da sauri ta juyo tana murmushi tace"Please a bakin igiya nawa?uku?"
"Kar ki fita!"ya faÉ—a cikin wata raunananniyar murya da Deeja bata san yana da ita ba
Jin hakan ya sanya Deejan dawowa tana faÉ—in"to bani magani na"
Shiru yayi zuciyar shi cike da damuwa,ita kuwa ganin bashi da niyyar magana taja ƙafafuwan ta ta shige ɗaki ta faɗa kan gadon ta,ko second talatin batayi ba ya shigo da sallama,ta amsa idanun ta a lumshe,har yanzu yunwa na ƙwarzabar ta,amma damuwa ta hana ta bawa cikin ta haƙƙin shi
Zama yayi a bakin gadon,cikin sanyin murya ya furta"Khadija!"
Zata iya cewa wannan shine karo na farko da ta taɓa jin sunan ta a bakin shi,amma hakan bei hana ta amsawa
"Na'am abdurrashid!"itama ta kira cikakken sunan shi
"Ki tashi zamuyi magana"ya faÉ—a cikin marairaicewa