Sashe 15
Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Momy bayan kin tafi kin barni ban sake farin ciki ba,ban sake jin daɗin rayuwa ba,bani da abokin hira,Bani da abokin kuka, Hajiya zulfa'u da agololin ta sune kawai suke rayuwar farin ciki a gidan, abinci wannan da zan ci gagara ta yakeyi,ta sanya daddy ya sauya min makaranta mara kyau kuma mai nisa,ta sanya aka sallami driver na,da ƙafa nake zuwa nake dawowa,da na dawo kuma zata fara sanya Ni aikace-aikace,kamar su wanki,wankin mota,share-share da sauran su,sai na gama sannan idan an ga dama a bani abinci,don ma Allah ya sa mama ladi mai aiki tana fakar idanun su ta ɗibar min abincin
Haka na gudanar da rayuwa ta har na kammala primary,sai tace a tura Ni boarding Kar na dame su,haka Daddy ya kaini boarding,tun daga js 1 har ss3,daga nan kuma na samu da ƙyar ta yarda ya biya min kuɗi na karanci medicine a ATBU,shima rayuwar cikin makaranta nayi,don tafi min kwanciyar hankali da zaman lafiya,a wani zuwa weekend da nayi na farka cikin dare naji tana kiran suna na,da na leƙa ta window dai naga tana zuba wani ruwa akanta tana kiran suna na, hankali na ya tashi na tabbatar tsafi takeyi,don haka ko da wasa ban taɓa wasa adduoi ba dare da rana,a ɓangare ɗaya kuma na dage da karatu na wanda nakejin cewa shine gata na,ko ta dalilin shi wataran zan iya haɗuwa da ke
A wannan halin na ƙarasa karatu na na medicine mai wahala a yanayi mai matuƙar wahala,amma alhmdllh takardu na sukayi kyau,a satin da na karɓo takardu na ne ina kwance a ɗaki na sai ga ƙaramar ƴar ta tazo tace na zo na duba yayar ta ameera numfashin ta ne yake ƙoƙarin ɗaukewa,sam banyi tunanin mutanen basa kyautata min ba,iyakar abinda na sani shine profession ɗina,naje Ina ƙoƙarin duba matsalar sai ji nayi uwar ta rafka salati, wai ina ƙoƙarin haiƙewa ƴar ta,sai ga yarinyar ta miƙe tana mitstsika idanu wai bacci takeyi taji kamar an danne ta,abin ya bani mamaki nace ai salma ce tazo kira na tace ameera ba lafiya,salma ta zabga wani ihu tana faɗin"ita wallahi bata fito daga ɗakin ta ba tunda garin Allah ya waye sai yanzu,abin ya bani mamaki na kasa magana,sai ji nayi Daddy yana sauke min maruka hagu da dama,yana faɗin na gado uwa ta na zama mutumin banza,a nan ne naji bazan jure ba nace Ni uwa ta ba mutuniyar banza ce sai dai matar shi da gayyar agololin ta,nan ya hau Ni da duka tamkar ya samu ɓarawo,Ni kam ko ƙoƙarin kare kaina banyi ba sai da ya illata ni,ameera ta miƙe tana hawaye wai sai ta bar gidan tunda na kira ta da agola,buɗar bakin Daddy sai cewa yayi sai dai Ni na bar gidan ba ita ba,don ta fini Amfani,haka inaji ina gani na kama tattara dukkan kaya na zan bar gidan,sai ga Hajiya zulfa'u tazo tana murmushi tana faɗin"nayi ƙoƙarin jefe ka amma hakan bai ci tura ba,to da sauƙi dai tunda na jefe ubanka,kaima gashi ko sisi na batayi ciwon kai ba na kaɗa ka kamar yadda na kaɗa uwar ka, Allah raka taki gona"ban kalle ta ba itama bata damu ba tana gama bayanan ta ta juya ta bar wajen
Shine dalilin da ya sanya ni barin Bauchi na shigo Kano,ranar da nazo Kano a ranar Deeja ta buge Ni a mota, saboda tunanin yadda zanyi da kaina bai bani damar kallon gaba na ba,amma a ƙarshe hakan ya zame min alkhairi tunda gashi na dawo gare ki momy"ya ƙarashe hawaye na zubo masa
Kusan kowa a parlourn hawaye yakeyi, Deeja kamar zata shiɗe duk da kasancewar ta mara saurin kuka da dakiyar zuciya, a hankali momy Aysha ta ƙaraso ta rungume shi tana faɗin"babu komai, ƙaddara ce, alhamdulillahi alaa kulli haalin,nayi farin ciki da rayuwar ka bata lalace ba, Allah yayi maka albarka"shi dai murmushi kawai yakeyi yana goge hawaye
Bayan ta nutsu tace"Imran lokacin da na bar gidan mahaifin ka na bar shi da ciki wata uku,ga abinda na haifa nan"ta nuna masa Ramlah wadda a lokacin zata kai 27-28 years
Murmushi yayi yana kallon Ramlah, Ramlah ta ƙaraso ta rungume shi tana faɗin"yaya momy tana yawan bamu labarin ka,tana nuna mana hotunan ka,munyi missing dinka sosai,yana murmushi yace "nayi missing ɗin ku,amma yanzu alhamdulillahi"
Babu wanda ya kula da sanda Deeja ta zame ta fice daga falon,sai daga baya Imran ya kula,babu ɓata lokaci ya miƙe ya nufi garden din gidan inda suka saba zama suna hirar su,a can ya hango ta ta jingina kanta da kujerar da ta zauna ta lumshe idanu tana ajiyar zuciya,a hankali ya ƙarasa inda take zaune,ƙamshin turaren shi yasa ta buɗe idanu tana kallon shi, yayi murmushi yana faɗin"da tsoro zan baki ai,kuma na manta ashe sister ɗin tawa jaruma ce"
Itama murmushin tayi,ya samu waje ya zauna,ya É—an yi shiru sannan ya fara magana
"Khadijah, I have no enough words da zanyi miki godiya,kinyi min abinda har abada banajin zan manta,kin cika min farin cikin da na rasa tun ina ɗan ƙaramin yaro,bani da bakin yi miki godiya,bani da abinda zan iya biyan ki,fata na Allah ya buɗa miki dukkan alkharin shi duniya da lahira,na gode sosai Deeja"
Deeja ta girgiza kai tace"wannan duk ya wuce ya Imran,yanzu tare zaku koma da momy?"
"A'a,a nan zan zauna,ko don aiki na,amma zan rinƙa kai mata ziyara"tayi murmushi tana faɗin"nima dai Allah yasa Abba ya barni nayi aikin nan,kowa yana aiki ban dani,Mima ma tace ta samu aiki,ga zainab,amma Ni daga ci sai kwanciya kamar wata saniya"ta ƙarasa tana yamutsa fuska
Imran ya fashe da dariya yana faÉ—in"kaji min mata,don kin samu kin zama Æ´ar hutu shine zaki yi mana iyayi?zan zuga Abba ya janye miki tallafi tunda daÉ—in yayi miki yawa"
Ta tura baki gaba tace"Ni da ya daina tura min tallafin ya bar ni nayi aiki nafi son haka,yanzu fa duk na zama malalaciya"ta ƙarashe kamar zatayi kuka
"Common ba wani malalaciya,ke fa jaruma ce,ko baki sani ba?"
"To amma ai rashin aiki zai saka experience É—ina na aiki na aiki ya gudu fa!"
"A haba!babu inda zashi,ki kwantar da hankalin ki, wataran ma Abba da kanshi zai yarda kiyi aiki ki daina saka damuwa a ranki,gata fa Abba yayi miki, common cheer up please!wannan fuskar ko kyau batayi miki ba"da haka ya sanya ta koma yadda take da
#Nusy_bee
*****MATAR KHALEES*****
âœï¸Nusy bee
Page 23
Momy Aysha ta so tafiya da Imran amma sai yayi mata bayanin aikin shi,kuma ma still baya son rabuwa da Deeja, saboda halaccin ta a gare shi,don haka momy Aysha ta bar shi a gidan tayi tafiyar ta Abuja da yaran ta
Shi kam Najeeb shirye-shiryen haɗa Imran da umaima sunyi nisa,don haka ya fara kiran umaiman ta rinƙa kawo musu ziyara,ya rinƙa gabatar da ita a wajen Imran,tun Imran baya damuwa har ya fara ba da kai,umaima fara ce ƙal, kyakkyawa sosai mai gashi har gadon baya,bata da ƙiba kwata-kwata amma ba ramammiya bace,tana da yawan fara'a da iya hira,ga ta da son gayu da kwalliya,ga iyayi,da wannan ta samu ta fara janye shi daga wajen Deeja,wadda shi mu'amalar su a abota ya ɗauke ta da ƴan'uwan taka,da babu soyayya a tsarin shi a yanzu,amma umaima ta tarwatsa komai
Najeeb ne ya rinƙa sukar Deeja a wajen Imran da dabara da wayo,don tuni ya fahimci Imran cewa bashi da wani wayo sosai,a hankali a hankali ya fara cin nasara,dama Najeeb ya kwaɓe shi kar ya kuskura ya bawa Deeja labarin umaima don zata iya raba su,ya nuna masa tun farko ba don Allah ta cece shi ba,ta cece shi ne don taga zai yi mata amfani,har ya ƙara da cewar mata irin su Deeja basa ɓata lokacin su wajen abinda bai shafe su ba,har da misalai,tabbas he is on point,don Deeja bata shiga shirgin da bai shafe ta ba,ko wajen al'ummar gidan bata cika zuwa ba sai wajen shi,yanzun ma takanyi sati bai ganta tazo gidan ba,hakan ya sanya shi yarda da batun Najeeb, zuciyar shi ta cika da haushin Deeja
Rana tsaka Deeja tazo da farin cikin ta wajen Imran tana shaida masa abban ta ya amince tayi aiki a asibitin mijin zee,Amma yadda yayi mata ya sanyaya mata jiki, ko da ta gaya masa baiyi wani appreciating ba sosai, don haka bata wuce minti goma ba ta tafi gida
Daga lokacin ya zamana ba sosai suke haɗuwa ba ma, musamman da ya zamana kowa cikin su aikin shi ya ɗauki zafi,a waya kam sukanyi wata babu wanda ya taɓa wani,tun abin na bawa Deeja mamaki har ta watsar
Shekarar shi guda da zuwa mahaifiyar shi ta bukaci yayi aure a wata ziyara da ya kai mata Abuja,babu ɓata lokaci ya gabatar mata da umaima wadda zuwa yanzu sunyi nisa a soyayya, Deeja kam yanzu sun zama baƙin juna
Ya É—auka momy Aysha zatayi farin ciki amma sai yaga ta É—aure fuska ta fara faÉ—a
"Wacece wata umaima?to ban amince ba, ba da yawu na ba,ga yarinya ƴar mutunci wadda tayi maka halacci amma saboda tsabar butulci ka guje mata,to wallahi dole ka aure ta,zan shigo kanon ma next week, wallahi bazaka mayar dani ƙaramar mutum ba,a cewar momyn cikin faɗa
Shiru yayi cikin ɓacin rai,shi kam duk kusan mutanen da yake tare dasu haushin shi suke ji akan Deeja,a ƙarshe ga mahaifiyar shi ma,take yaji wata tsanar ta ta dirar masa,haka dai yayiwa momyn nashi sallama ya tafi
Kwana biyar da faruwar haka Deeja tazo gidan,a lokacin ma bata san abinda yake faruwa ba,dama wajen su Yasmeen tazo,bayan sun gama hirar su ta fito,har ta nufi parking space ta tuna sun kwana biyu basu gaisa da Imran ba,don haka ta wuce lambun gidan kai tsaye da hope É—in zata same shi
Ilai kuwa yana zaune,sai dai maimakon karatu yadda ya saba yau waya yakeyi yana lumshe idanu yana murmushi da alamu yana jin daÉ—in wayar da yakeyi
Ta nufe shi kai tsaye,a dai-dai lokacin da ya kammala wayar tayi masa sallama,ya amsa fuska a É—aure, bata damu ba ta gaishe shi,nan ma ya amsa ciki-ciki sannan yace "lafiya dai ko?"