Sashe 16
Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɗan murmushin da bai kai zuci ba tayi ta zauna tana faɗin"lafiya ƙalau,dama zuwa nayi wajen Yasmin shine sai na biyo wajen ka mu gaisa"
"To yayi kyau,kina iya tafiya"ya faÉ—a idanun shi a kan wayar shi
Tabbas ranta ya ɓaci amma bata nuna ba,sai tace"wai yaushe momy zata dawo daga China?naji su Yasmin sun ce taje China shekaranjiya"
"Ki tambaye ta,kun fi kusa ai"ya bata amsa idanun shi na kan wayar shi
Ta buÉ—e baki da zummar yin magana ya É—aga mata hannu yace"kinga!tashi kije kawai,kin fiye shishshige min,Ni kuma na tsani mace mai shishshige wa namiji!!"
Tunda take ba'a taɓa furta mata kalmar da tayi mata ciwo ba irin wannan,don haka ta miƙe batare da tace uffan ba ta bar wajen
Kwana goma da faruwar hakan taji Labarin auren ta da Imran a bakin mamie,sai da gaban ta ya faÉ—i don a lokacin ko sannu bata haÉ—a su da Imran,sai dai bata ce komai ba
Kwance tashi har bikin yazo,komai proffesor Isma'il ne yayi mata,ya hana Dr Mahmud komai,an shirya biki na garari an kai amarya gidan mijinta
Kusan lokaci guda akayi bikin su da Mima,sati biyu ne tsakanin su,don haka Mima ta samu halartar auren Deeja,itama Mima ɗin ɗan ƙanin baban ta zata aura,shima ɗan azare ne amma baki ɗaya zaman su da iyayen shi a Malaysia suke,sai dai su auren soyayya zasuyi ba kamar su Deeja ba
To fa!tunda aka kawo Deeja gidan Imran ta gane ainihin kalar shi,babu irin izayar da baya mata da shawarar babban abokin shi Najeeb,wanda ya nuna idan har baiyi yadda zai yi ya kori Deeja ba bazai bashi ƙanwar shi ba,hakan ya tayar da hankalin shi ya dage cikin rufewar idanu ya cigaba da ƙuntatawa Deejan,bata taɓa faɗawa kowa ba duk zuwan da akeyi gidan,sai dai ramar da takeyi tana bawa Kowa mamaki,amma idan an tambaye ta dalili sai dai tace babu komai
Watannin su biyar da aure Imran ya bijiro da maganar umaima bayan ya shawo kan Najeeb da ƙyar,amma momyn shi sam bata bashi goyon baya ba,sai ya tuntuɓi proffesor,shi kam ya wuce gaba,nan da nan akayi komai aka gama aka sanya lokacin aure
Lokacin da momy Aysha taji Labarin tayi baƙin ciki sosai,amma yadda bai same ta da zancen ba itama bata tuntuɓe shi ba
Professor da kanshi ya kira Deeja ya sanar mata maganar auren,ya lallashe ta da kalaman kwantar da hankali,bata nuna masa damuwa ba don ta san hakan zai faru watarana, amma duk da haka hankalin ta ya É—an tashi,sai dai ta fauwalawa Allah komai don ya san shine mai iko a bisa komai
Anyi biki lafiya,anyi sharholiya sosai, amarya ta tare a gidanta
Tunda umaima ta tare Deeja ta fara ganin yadda ake soyayya,sam basa jin kunyar ta,wani abin ma basayi sai sun ga idanun ta a wajen,gashi ta zama tamkar baiwa,duk wasu aikace-aikace na gidan ita takeyi,sai dai bata taɓa nuna damuwa ba duk da abin yana cin ta a zuciya
Makirci kala-kala babu wanda umaima bata taɓa yiwa Deeja,da taimakon Najeeb,Imran kam ya ƙara tsanar ta har ta kai yana dukan ta,ga horon yunwa da yake mata,ta sake lalacewa,da yawan mutane zargi sukeyi kishi ke damun ta
Lokaci ɗaya ta fara wani irin ciwon ƙirji,wani lokacin numfashin ta har ƙoƙarin ɗaukewa yakeyi,ita kaɗai ta san me takeji idan ciwon ya tasar mata,sai dai ta sani bata da Muhimmanci a wajen Imran da zai tsaya ya saurare ta
Zuwan Mima daga Malaysia ya faranta mata rai sosai,a lokacin miman har da ƙaramin ciki,kuma anyi Sa'a lokacin su Imran sunje Abuja gidan momyn shi,don haka suka baje a falo suna hirar yaushe gamo
#Nusy_bee
*****MATAR KHALEES*****
âœï¸ Nusy bee
Page 24
Mima ta ƙare wa Deeja kallo,tace sister deejo,me ya same ki ne naga kin rame haka?ko baki da lafiya ne?"
Deeja ta É—an yi shiru, Mima abokiyar sirrin ta ce,ba don haka ba da baza ta iya sanar da Mima abinda yake damun ta ba,amma saboda muhimmancin Mima sai ta bata labarin irin wahalar da take sha a gidan
Tabbas lamarin ya bawa Mima mamaki da tsoro,kuma ta tausayawa Deeja sosai,tayi shiru cikin alhini tana kallon Deeja,zuwa can tace"amma Imran ya cika butulu,yanzu duk irin soyayyar da kukayi ta zama tarihi saboda ya samu wata?"
Deeja ta girgiza kai tace"ba soyayya mukayi da Imran kamar yadda kukayi tsammani ba,abota ce kawai,kuma shigowar maganar aure ciki ita ta watsa abotar"
Shiru Mima tayi tana jinjina abin,zuwa can tace"gaskiya lamarin da mamaki sister,Imran ya bani mamaki sosai"
Deeja tace"Ni kam sam,don ya gwada min tun Kafin auren"
Mima tace"to Allah ya kyauta,ki cigaba da haƙuri watarana sai labari"Mima dai tayi ta kwantar mata da hankali,duk da cewar abin ya dame ta,kuma abin da ta sani shine da ace itace Imran bazei fara abinda yayi wa Deeja ba
A ranar Mima a gidan ta kwana, Deeja taji daÉ—i sosai, saboda Mima ta É—ebe mata kewa,dama kuma gwanar surutu ce da barkwanci
Washegari Mima ta tafi,Deeja sai taji dama kar ta tafi saboda taji daɗin zuwan ta,kuma a ɗan zaman da sukayi taji sauƙin ciwon kirjin ta
Kwanan Mima biyu da tafiya su Imran suka dawo,ta fuskanci ya ƙaro wulaƙanci, saboda momyn shi tayi masa faɗa sosai akan rashin zuwa da Deeja,sannan batayi wani marari akan umaiman ba,don haka ya ƙudurce a ranshi Deeja sai ta gane kuren ta
Tunda tayi masa sannu da zuwa ya daka mata tsawa ta shige É—aki bata sake yarda sun haÉ—u ba,da sassafe zata fice aikin ta,sai ta kai biyar na yamma bata dawo ba,da zarar ta dawo sai ta rufe kanta a É—aki,haka tayi ta gudanar da rayuwar ta tsawon sati guda
Baƙar rana a gare ta,ranar da baza ta taɓa gogewa a cikin ranta ba,itace wata ranar talata takwas ga watan biyu
Dawowar ta kenan daga aiki,ta jefar da jakar ta akan tiles abinda bata taɓa yi ba,yau tun safe jinta takeyi wani iri kamar ba ita ba,ta rasa me yake damun ta, wanka ta shiga,tana fitowa tayi sallar la'asar da taji ana kira,tana idarwa ta ɗan kwanta don ta huce gajiya,sai bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita
Bata farka ba sai bayan maghriba,tayi matuƙar mamakin baccin da tayi,ta miƙe tayi sallah,haka kawai yaji gaban ta na faɗuwa,ƙirjin ta ya tsananta ciwo,abu ya dame ta,ta ɗan yi shiru,zuwa can ta janyo jakar ta dake yashe akan tiles don ta ɗebe kewa sai taji ta a kashe,abin ya bata mamaki sosai,don ta san wayar ta akwai ragowar chaji,amma hakan bai wani dame ta ba ta sanya ta a chaji,sai bayan ƙarfe tara na dare ta kunna ta
Saƙonni da miscalls ta gani barkatai,da sauri ta fara duba miscalls ɗin,yaya Ma'aruf ta gani
Mamaki ya kamata,indai Ma'aruf da ta sani ne baya kira sama da biyu,amma yau shine mai kira har sha ɗaya,to lafiya?sai taji gaban ta ya faɗi,da sauri ta buɗe saƙonnin don ganin abinda suka ƙunsa
Tashin hankalin da ta gani ne ya sanya ta ƙwala ƙara tana faɗin"innalillahi wa Inna ilayhi rajiun"jikin ta na matsanancin rawa
"Aslm auta,Abba Met with an accident on his way back from Abuja today,and sadly we lost him,I called you several times but you are not picking"
Tashin hankalin hankalin da Deeja ta shiga baya faɗuwa,daga tsaye ta saki wayar tana jan numfashi,amma saboda tsabar ƙarfin hali da tashin hankali haka ta nufi parlourn tana haki,still ta kasa yarda abban ta abin ƙaunar ta ya tafi ya bar ta,kuka take so tayi amma ta gagara,ko a mafarki bata taɓa kawo abban ta zai tafi ya bar ta a wannan halin ba
A parlour ta iske Imran da umaima suna shan soyayyar su hankali kwance, umaima ce ta fara ganin ta,cikin masifa tace"Malama Lafiya,uban me kika zo yi mana?"
"Abba na!yaya Ma'aruf ne yace wai ya tafi ya barni,yaya Ma'aruf yace na rasa Abba na garkuwa na"ta faÉ—a cikin fitar hayyaci lokaci guda kuma tana ficewa daga cikin parlourn
Imran ya bi ta da kallo,karo na farko kenan bayan auren su da yaji tausayin ta,ganin har ta fice daga parlourn cikin sauri ya miƙe ya bi ta,amma kafin ya riske ta a waje ta hau napep ta tafi,bai bi ta ba sai ya dawo gida,duk da ya tausaya mata
Ita kam kai tsaye gidan su ga nufa,tana zuwa ta samu yaya Ma'aruf a harabar gidan da shi da aminin shi na amana Khalees, dukkan su sai sharar ƙwalla sukeyi,ta jefa musu tambaya cikin tashin hankali
"Ina Abba na?"
Bin ta sukayi da kallo,don sun sani sai tafi kowa jin mutuwar,don itace favourite ɗin shi kuma shi kaɗai gare ta a yanzu,gaba ɗaya tausayi take basu,ta ƙanƙame Ma'aruf tana faɗin"yaya Ma'aruf abbana!Abba na kar ya tafi ya bar ni,wallahi ina son shi,idan ta tafi ya zanyi?"
Yana ƙoƙarin kwantar mata da hankali amma ina!kafin ya ankara sai gani yayi ta sulale ƙasa sumammiya
Cikin kuma mai motsa rai Ma'aruf ya durƙusa ya ɗago ta,cikin sauri Khalees ya miƙo masa ruwa ya amsa ya yayyafa mata,ta ja ajiyar zuciya
Zumbur ta miƙe tana zare idanu,sai ta fashe da kuka mai ban tausayi, Ma'aruf ya kama hannun ta suka shiga gidan tana ta sambatu
A ranar babu wanda ya runtsa saboda tashin hankali da suka shiga, Deeja ta gigice sai suma takeyi,tilas aka É—auke ta sai asibitin da suke zuwa wajen likitar ta Dr su'ad
Cikin lokaci ƙanƙani likitoci suka rufu akanta,sun ɗau kimanin awa uku kafin su fito, hankalin Dr su'ad a tashe
Office ta ja Ma'aruf ta sanar dashi cewar zuciyar Deeja ta kamu da ciwo
Hankalin Ma'aruf yayi matuƙar tashi,yace"ciwon zuciya kuma doctor? innalillahi wa Inna ilayhi rajiun! Deejan har nawa take da zata kamu da irin wannan ciwon?"
"Ko kwanan ta ɗaya da haihuwa idan Allah ya ƙaddara sai kaga ta kamu da ciwon, ballantana ma ana haifar jarirai dashi,amma ita nata ta same shi ne due to depression and anxiety,tana cikin tsananin damuwa,why baka san abinda ya janyo ciwon ba a matsayin ka na yayan ta?"
"Dr Ni dai nasan na sanar mata rasuwar mahaifin mu,and I know she is his favorite,and they love each other,but Bana tunanin wannan dalilin can lead Deeja to this stage,ko babu komai itama musulma ce ta yarda da ƙaddara"