Sashe 28
Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Satin Umaima uku a Kano aka mayar da auren Deeja da Khalees, Deeja ta zama MATAR KHALEES a karo na biyu,ita da Khalees cike suke da farin ciki don wannan shine auren su na farin ciki a iya tsawon rayuwarsu,an sha shagali sosai,su Mima suka miƙa ta sabon gidan mijin ta da ya siya a state road
Satin su biyu da aure suna shan soyayyar su Aunty nusaiba ta dawo musu da Affan,mijin ta da yazo ya saka su gaba ita da yaran ta suka koma US, Deeja tayi kewar su sosai
Watan ta uku da aure tana zaune a parlourn ta tana duba wasu files da zatayi submitting gobe a Company É—in su,don tuni ta koma companyn su ta cigaba da aiki
Ji tayi an rungume ta ta baya,ta san Khalees ne,ta ɗan yi murmushi tana faɗin"sannu dai yallaɓai,ya kamata a rinƙa sallama dai"
"Ke fa ba'a razana ki,na manta"ya faÉ—a yana dungure mata kai"
"Akan me za'a razana ni?ka san dai na fika juriya ko?"ta faÉ—a tana murmushi gami da kashe ido É—aya
Murmushi yayi yana faɗin"to anji"ya dauko hijabin ta da ke gefen ta ya fara ƙoƙarin saka mata,ta kalle shi don neman ƙarin bayani,ya raɗa mata a kunne"we have a visitor, very best friend"karɓar hijabin tayi ta ƙarasa sakawa,shi kuma ya fita ya shigo da baƙon
Mamaki ya kamata ganin Imran,wanda rabon ta da shi ma tun ranar da ta sauka ƙasar ita da su Aunty nusaiba,Amma bata nuna masa komai ba a fuska tayi masa sannu da zuwa,ya amsa da fara'a ya zauna suka gaisa a mutunce,yanayiwa Affan wasa
Deeja ta kawo musu soft drinks sannan ta samu waje ta zauna,Imran yayi É—an murmushi yana faÉ—in"thanks"sannan ya zuba lemon a kofi ya fara sipping a hankali
Ya dubi Deeja cikin sanyin murya yace"Khadijah,zuwa nayi na musamman don neman afuwar inconveniences ɗin mu, I know we did alot to you that I'm sure you will never forget with it,can you find a place in your heart to forgive us please?I regret my evil act definitely and.......wasu abubuwan barin faɗar su inaga yafi amfani,ina roƙon ki yafe mana Ni da Umaima,duk da cewa zuwa yanzu Ni kaina ban san inda take ba"
"I can't get baka san in da umaima take ba"ta faÉ—a tana kallon shi
"Mun rabu ai"
"Na san da haka"shiru yayi yana kallon ta don bai gane abinda take nufi ba
Murmushi yayi tayi tace"duk abinda ya faru ya wuce, abinda baka son faɗa min ma na sani, kuskuren ka baka iya dogon nazari kafin ka aikata abu,da ace kana dogon nazari babu yadda za'a yi Najeeb ya rinƙa juya rayuwar ka har ma da ta matar ka,kuma na biyu,meyasa zaka kori Umaima?ina ce ta gaya maka bata da wajen zuwa? meyasa baka saurari uzurin ta ba,to ka sani duk wani hali da Umaima ta shiga bayan barin ta gidan ka kaine sila"
Mamaki mai tsanani ya ƙamar da Imran,kenan dama Deeja ta san Najeeb ke juya rayuwar su?ya akayi ta san cewa Umaima ba ƙanwar Najeeb bace,amma sai yace"babu abinda nayi Deeja,of course bana buƙatar ta a rayuwa ta anymore,tace zata koma garin su,na bata kuɗin da na tabbatar zai ishe ta kuɗin mota?idan ita marainiya ce bata da iyaye bata da family ne?idan har da gaske take why not ta koma wajen su?me zanyi mata after that? openly ta ci amana ta da aboki na, shiyasa naga gwara na bar masa ita, seems like bata shirya wa zaman aure ba,sai suje su cigaba da abinda sukeyi kawai"daga yadda yake maganar kaɗai ya isa a gane irin raɗaɗin da yake ji a zuciyar shi
Deeja tace"shine kuskuren da ka tafka Dr,baka san wacece umaima ba,baka san komai daga gare ta ba amma ɗauki zafi daita,ba sai na gaya maka ba,ka san na san yadda Umaima take mutuwar son ka,yadda take son ka haka take gudun ɓacin ranka,kasan da haka ko?"
Imran ya É—an yi shiru in confusion yana kallon ta,shi dai Khalees kallon su kawai yakeyi,bayan wasu Æ´an seconds yace"what are trying to say Khadija?"
Wayar ta ta ciro babu ɓata lokaci ta nemo wani hoto ta miƙa masa,ya amsa yana kallo,kallo ɗaya yayiwa hoton gaban shi ya faɗi,shima Khalees kallon babyn yakeyi,da ya kalle ta sai ya kalli Imran,tana zaune akayi mata hoton,sanye take da farar dogon riga mai adon pink flowers,kanta an sanya mata pink ɗin bandana,gashin ta irin na larabawa anyi masa style mai kyau da kayan kitso masu ɗaukar hankali,tana rike da abin wasa tana kallon wani wajen ta ɓangale baki haƙoran ta guda biyu sun fito, Imran ya tsurawa yarinyar idanu ko kiftawa baya yi, Khalees ya ɗago ya kalli Deeja yace"baby luv wannan babyn fa? resemblance ɗin su da Imran is too obvious"
Batare da ɓata lokaci ba tace"ƴar shi ce"a tare suka zaro idanu suna kallon ta a firgice, Deeja tace"yeah, Umaima ta tafi garin su da cikin ka kuma alhamdulillahi ta haihu lafiya,an samu yarinya ta saka mata suna na"ta ƙarashe tana murmushi,daga nan ta basu labarin Umaima,ta ƙara sa cewa"yanzu haka na ɗauko ta,tana nan gida na na Na'ibawa,yanzu zancen da nake ma ta koma makaranta,don na tabbatar da ace Najeeb a hanyar makaranta yaga tayi collapse da bai isa ya wulaƙanta rayuwar ta har haka ba,kuma duk da cewar Mima ta fara min takwara nafi jin na Umaima a raina"
Dukan su shiru sukayi na ƴan daƙiƙu cike da tausayin Umaima,Imran ne yayi gyara murya ya fara magana cikin sanyin murya"ban san komai dangane da rayuwar ta,bata taɓa bani labarin rayuwar ta ba,na ganta tana rayuwar ta comfortably,da farko nayi tsammanin Najeeb yayan ta ne,na shiga shock sosai lokacin da ya tura min hotunan su da videos ɗin su suna baɗalar su,har da ce min gudowa tayi daga garin su ta biyo shi,wai kuma lokacin da zata aure ni tayi masa alƙawarin duk runtsi bazata guje shi ba,amma babu komai,na yafe masa,don yanzu haka fama yake da kanshi,yanzu dai ina rokon ki ki taimaka ki shawo min kan Umaima,tunda kuka fara haka da ita mawuyaci ne ta dawo min, because Umaima is too stubborn"dariyar babu shiri ta ƙwacewa Deeja,tace"wallahi kuwa akwai ta da taurin kai na bala'i ma kuwa,batayiwa ƴan gidan su magana fa,ranar da muka taho fa don na matsa mata ta shiga tayi wa ƴan uwan ta sallama sai ta fashe min da kuka"
Imran yayi murmushi mai sauti yace"of course naji daɗin zama da umaima but ta cika kafiya da taurin kai, shiyasa lokacin da kika ɓace nace tasan in da kike,kuma na matsa mata ta fito dake"
Tunda dai ƴan adawar Umaima suka shirya daita nasan zasu shirya da likita bokan turai,ina nufin jidda da Juliet 😅
Proud of you commentors and likers🥰
#Nusy_bee
*****MATAR KHALEES*****
âœï¸Nusy bee
Post 38
Deeja tayi murmushi tace"zanyi maka ƙoƙari in Sha Allah,duk da stubbornness ɗin ta tana jin magana ta, a matsayi na na babbar yaya
Wani kallo sukayi mata duka su biyun, sannan suka fashe da dariya a tare,buɗa ido tayi sosai tana musu kallon ƙarin bayani, Khalees yana dariya yace"karo na farko a tsawon rayuwa ta da naga babbar yaya da auta sun haɗu waje ɗaya"kawar da kai tayi tana ɗan murmushi,ita fa a tsawon rayuwar ta dama ba wai tana ƙaunar sunan bane,amma bata taɓa jin sunan ya yarfa ta irin yau ba,amma saboda ƙi faɗi sai ta kalli Khalees tace"ai suna ne kawai,a family Mutum nawa na girma?ko baku san ina da ƙani ya rasu ba?idan Dr baka sani ba ai shi abban Affan ya sani"Khalees yana dariya yace"anyi haka,kin girmi mutane na manta,kamar yasmin,kin girmi fadila,kin girmi Mima,kin girmi Mubarak,kin......"
"Aa Ni fa ban ce na girme su ba,kunga a bar maganar kawai"ta faÉ—a tana shan mur
Imran yace"Hajiya Deeja kenan,ko bayan shekaru É—ari kaga mutum ka tambaye shi komai amma banda halin shi,ke kam Allah yayi miki arzikin son girma sai gashi kin zo a kalen hanji"
"Naji nace a bar maganar"ta faÉ—a tana zaro idanu"zanyi magana da umaima,zata dawo in Sha Allah"
"Kiyi mata barazanar yace idan bata amince ba zai amshi Æ´ar shi"a cewar Khalees yana murmushi,
Deeja tace"wa?umaiman?ita da tace na ɗauki yarinyar ta bar mini?amma idan baban ta yana so sai na bashi,tun ma lokacin ko zama batayi,"Imran yayi dariya yace"shiririta!baka san Umaima bane idan ta kafe akan abu,nayi mamakin yadda ta yarda ta biyo Deeja, gaskiya kinyi Sa'a,ko kuma yet she is feeling guilty na abubuwan da tayi miki ne"Deeja tace"whatever,sannan akwai abu ɗaya da nake roƙon ka Please"
Yace"ina jin ki"Deeja tace"ka koma Bauchi ka daidaita da mahaifin ka, it's already time,ko ba komai ka san abinda ya faru ba laifin shi bane,no matter what bazai taɓa juya maka baya ba,kuma for now ka bashi enough space, kusan six years,why not baza kayi letting komai ya wuce ba? I know yadda bai san Aunty Ramlah ba dole zaiyi kewar ka as the only son da ya mallaka"ta ƙarashe tana tsare shi da idanu
Da Imran da Khalees duk kallon ta sukeyi har ta ƙarasa bayani,a hankali Khalees ya mayar da kallon shi ga Imran da ya sunkuyar da kanshi yana tuna baya, Khalees ya dafa kafadar shi yace"all is well friend, Deeja tana da gaskiya, ba'a fushi da iyaye no matter what happen,I know you well friend,nasan ba fushi kayi ba but it's already time ka nemi sasanci da dady,You will never regret it in Sha Allah"Imran ya jinjina kanshi,a sanyaye yayiwa Deeja godiya sosai,yayi mata sallama suka fice shi da Khalees,ya ɗauki Affan da yake ta ƴan wasannin shi suka fita tare
Sati biyu tsakani Deeja, Afra,lubaisa da zakiyya suka ziyarci Umaima a motar Deeja,tana parlour ta goya little Deeja da ke jin rigima sai zaga parlourn takeyi,ta kunna suratul Nur a waya sai bi takeyi,ita kuma mama lami tana kitchen tana dafa musu abincin dare,sai jin sallamar su tayi