Sashe 3
Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Okay I'm waiting"daga haka komawa tayi ta kwanta a rigingine,zuciyar ta nayi mata zafi,ta lumshe idon ta,ta kai mintuna goma sha biyar a haka kafin taji kuwwar wayar ta,ta buɗe idanun ta ta miƙa hannun ta a kasalance ta janyo wayar,ta ɗaga
"Hello ina jin ki"
Deeja tayi ajiyar zuciya sannan tace"bari kawai aunty kiyya,ina cikin tashin hankali da taraddadi"
"Me ya faru kuma?"kiyya ta tambaya tana gyara zama
A hankali ta warwarewa zakiyya komai, cikin mamaki da kaÉ—uwa zakiyya take gyaÉ—a kai,zuwa can tace
"Deeja,ki cigaba da haƙuri,haka Allah yaso dake,ki sani duk mutumin da kika ga Allah yana ta jarabtar mutum ta Allah yana son shi,don haka ki cigaba da haƙuri, akwai lokaci,ki saurari zuwan yaran kawai,ko me zasu yi kar ki kula su,ki kama kanki kawai,in Sha Allah zaki ga ribar abin, kuma ma Allah na tuba abin kwana nawa ne? 'yan mata ne fa,aure zasu yi"
Jikin Deeja yayi sanyi,taji sauƙi a zuciyar ta, cikin wata kasalalliyar murya tace"in Sha Allah aunty kiyya zan kiyaye"
"Well!yaushe zaki zo bikin ne?ko sai anzo dab?"
Murmushi mai sauti Deeja tayi,tace"Kai aunty!Sai kace wani gari dabam?"dariya aunty kiyya tayi tace"sai mun ganki dai"
"Okay na gode aunty kiyya"
"Nima na gode"sukayi sallama
Ai kuwa bayan kwana biyu ta dawo daga aiki ta samu motar su fareedan a harabar gidan,sai da gaban ta ya faÉ—i,amma da yake mace ce mei kamar maza sai ta dake,ta shiga falon da sallama
Dukan su suna zaune sun kunna TV suna kallo,suka ɗago suka kalle ta suka watsar,ta nuna kamar bata san sunyi ba,tace"sannun ku da zuwa"da ƙyar jannat ta amsa da cewa
"Yawwa kema sannun ki"bata damu ba ta kewaye su ta shige É—akin ta,tana jin Farida na jan dogon tsaki,amma ko kallon sashen da take batayi ba,ta shige É—akin ta
Bayan tayi wanka tayi sallah ta fito ta nufi kitchen,bisa mamakin ta sai ta tarar babu abincin sai warmers É—in nata da akayi mata wancakali dasu,ta shiga bin ko'ina da kallo, girgiza kai tayi kawai, sannan ta fara kwashe kwanukan tana tattare su a water sink,ta wanke su tas ta maida su ma'ajiyar su sannan ta share kitchen É—in sannan ta É—ora jollof É—in Talia,don tasan Khalees yana hanya, gashi kuma babu abinda zasu ci ita da Khalees É—in
Cikin azama ta dafa talia jollof da kifi taji kayan lambu, cikin ƴan mintuna gidan ya ɗauki ƙamshi,ta haɗa lemon mangwaro ta sanya a fridge,ta ɗibar wa su Farida itama ta ɗiba,ta zubawa Khalees nashi a warmer ɗin shi
#Nusy bee
*****Matar Khalees*****
âœï¸Nusy bee
Page 4
Babu komai a fuskar ta ta miƙa musu,ko kallon mutunci bata samu ba,itama bata damu ba,ta ɗauki nata ta shige ɗakin ta
Sanda Khalees ya dawo tana jin su,suna ta hira da ƙannen shi,bata kula su ba sai da taji ya shiga ɗakin shi,da alamu wanka zai yi,ta fito ta jere kayan abincin a dinning area,ta shiga ɗakin shi don yi masa sannu da zuwa
Har lokacin Khalees yana banɗaki bei fito ba,ta zaro masa kaya marasa nauyi na zaman gida ta ajiye masa a bakin gado,tana gamawa ta miƙe ta fice daga ɗakin
Tana cikin ɗakin ta taji Muryar shi,ta fito tayi masa sannu da zuwa,ta sha mamakin amsawar da yayi fuska a sake, amma bata bar hakan ya bayyana akan fuskar ta ba,kuma ta alaƙanta hakan da wanzuwar su Farida a falon,don ta juma da kula cewa basa iya kawo mata raini a gaban shi
"Idan ka shirya ga abincin ka nan a dinning"ta faÉ—a cikin kwantar da murya
"Dama shi na fito nema,bari in ci tukunna"ya nufi dinning É—in,ita kuma ta koma cikin É—akin ta
Da daddare suna zaune a cikin É—akin nashi ta dube shi cikin kwantar da murya tace"am dama Ina son yin wata magana da kai"
Ya É—an kalle ta sannan ya maida kanshi fuskar wayar shi yace"ina sauraron ki"
"It is better ka ajiye wayar nan,don kafi fahimta ta ko?"ta faÉ—a cikin kwantar da murya
Wani matsiyacin kallo ya watsa mata sannan yace"ashe?har kina da maganar da take da muhimmancin da zata sanya ni ajiye waya?"ya faÉ—a har yanzu idanun shi na kan fuskar wayar shi
Shiru tayi bata ƙara magana ba,shima shirun yayi, tsawon lokaci ganin bata da niyyar magana sai ya kashe data ɗin shi ya dube ta yace"ya ake ciki ne?"wacce magana ce take tafe dake?"
Shiru tamkar bata ji ba,sai da ya maimaita tambayar, cikin kasalalliyar murya batare da ta kalle shi ba tace
"Dama kan batun bikin ƙanwa ta ne"
"Ehen,me kike so nayi miki?"ya faÉ—a yana kallon ta
"Kasan tun ana igobe ko jibi za'a fara bikin nake so naje,to yanzu yaya zan yi da su Farida?"
Da sauri ya kalle ta cikin mamaki,yace "su Farida mana"
"Eh su Farida mana"ta bashi amsa tana kallon shi
Cike da mamaki ya gyaÉ—a kai sannan yace"to nono zaki basu kenan?"
Kallon shi tayi cikin mamaki tace"a'a ba batun haka bane,bei dace ace mun bar su a gida ba su kaÉ—ai, Hajiya ma bazata ji daÉ—i ba,amma idan babu matsala sai in tafi É—in"
"Babu"ya bata amsa a taƙaice,sannan ya juya ya kwanta,itama kwanciyar tayi,duk da ba bacci takeyi ba,kawai nazarin rayuwa takeyi
Washe gari basu tashi daga bacci ba sai da ta kammala girki,tana ji Khalees yana tayi musu faɗa,ita dai sauri takeyi don ta tsani makara a rayuwar ta,kunun gyaɗa ta dama da ƙosai sai plantain da miyar ƙwai,sai wainar ƙwai da chips,sai ruwan Lipton
Ko da Khalees baya yaba mata a fili,yana matuƙar jinjina baiwar iya girki, tsafta da hikima da Allah ya bata,gashi sam bata gajiya, kullum cikin hidima dashi take ko da ace zai kashe ta kuwa
Suna cikin cin abincin ya kalli Farida yace"yau ƙarfe nawa kuke da lecture?"ta amsa"nine zamu shiga lecture"
Ya kalli Jannat yace"ke kuma fa?"
Ta amsa "by 12:pm"
"Good!"ke Farida, kafin ki fita daga gidan nan ki tabbatar kin gyara wajen nan ki wanke kwanuka,ke kuma Jannat ki tabbatar kin yi girkin rana kafin ki bar gidan nan,okay?"
Hukuncin nashi yayi masifar bawa Deeja mamaki,amma sai tayi kamar bata sauraron su,sai cin abincin ta takeyi a nutse, lokaci lokaci tana kallon haɗaɗɗen agogon hannun ta gudun kada lokaci ya ƙure, Farida da Jannat suka dubu juna cikin tsananin kaɗuwa da al'ajabi,sannan suka kalle shi a tsorace,suna raya ya raina musu hankali ma,ya ɗebo su daga gaban Hajiya,don kawai ya basu wahala
Farida itace tayi magana cikin rawar murya"yaya ina da excuse"
"Wanne excuse kenan?"ya tambaya batare da ya kalle ta ba
"Zamuyi group meeting yau kafin mu shiga lecture,Kuma rashin halartar shi zai iya jawo min matsala"
Shiru yayi yana cin abincin shi a nutse,ita kuwa Farida addu'a takeyi a ranta Allah ya sanya ya bar ta ta fita amma ina! addu'ar ta bata karɓu ba,don cewa yayi
"A haƙura da group meeting ɗin,tunda anayi,kuma watarana ma za'a ƙara yi, shikenan ko?"
Shiru Farida tayi tana cika tana batsewa,dama ita Jannat ta daÉ—e da sanin halin yayan nasu,,kaifi É—aya ne,idan ya faÉ—i abu,to abun yake nufi , shiyasa bata tanka ba
Deeja kam shiru tayi tamkar bata san me yake wakana ba,tana kammala cin abincin ta ta É—auki jakar ta gami da yi musu sallama ta fice daga falon
Ranar bata dawo da wuri ba sai wajen la'asar, Saboda meeting da sukayi,a falo ta same su a zaune sun cika sun batse,falon kaca-kaca ta ko'ina,koda tayi sallama ma babu wadda ta amsa,sai Farida da ta kalle ta cikin fitsara tace"Malama har da zuwa a wani daÉ—e saboda kin bar bayi ko?to ga gidan ki nan,ki gyara abinci,girki kuma iya mu yamu muka yi,don haka ruwan ki ne kiyi abinda ya dace ruwan ki ne ki bari"
Ko kallon banza bata samu daga wajen Deeja ba,hakan ya ƙona ran Faridan, Deeja bata kula ba ta shige ɗakin ta
Wanka tayi ta É—auro alwala don yin Sallah,tana shirin tada kabbarar Sallah kenan ta jiyo faÉ—an Khalees akan rashin gyara gida da basuyi ba,bata kula ba ta tayar da sallar ta,sai dai tana jin irin rashin mutuncin da yakeyi musu da dukan da yayi musu,cikin sauri ta idar,da gudu ta nufi falon tana faÉ—in"I'm sorry Khalees,nice nace su bari zan gyara fa"
Khalees ya kalle ta na wasu daƙiƙu,bei ce komai ba ya juya ya bar falon,itama Deeja haka ko badan komai ba,ta bar falon don watsatstsen kallon da suke jefa mata
Haka rayuwar gidan ta cigaba da tafiya tsawon kwanaki shida, gaisuwar arziƙi bata haɗa su da su Farida,shi kuma Khalees ya kallafa musu yin aikace-aikacen gidan idan suna gidan
Ganin wahalar bazata ƙare ba ne ya tilasta musu guduwa, Hajiya na zaune sai kawai taga sun shigo,ta sha mamaki ƙwarai da gaske,don da kansu suka yanke shawarar komawa gidan ɗan'uwan nasu,da ta tambaye su dalilin dawowar tasu suka ce sun gaji da wahalar da yaya Khalees yake basu, Hajiya bata matsa musu ba,don dama su suka so komawar
Tafiyar su Farida ya faranta wa Deeja ba kaɗan ba,a ƙalla ko ba komai ta samu sakewa,kuma ɓacin ranta ya ragu,domin shi Khalees ta sani in dai ba harkar shi ta shiga ba ranta bazai ɓaci ba
**** **** ****
Ƙarfe biyar na yamma suka ji announcement na cewa jirgin su ya sauka,cikin nutsuwa suka sauko daga jirgin,ɗauke da kyawawan yaran su Mee'ad da muneeb,kai tsaye waje suka nema suka zauna, sannan ta kirawo aunty Bintu tare da shaida musu isowar su, aunty Bintu tace gata nan
#Nusy bee
*****MATAR KHALEES*****
âœï¸Nusy bee
Page 5
Cikin abinda bei wuce mintuna sha biyar ba aunty Bintu da babbar ƴar ta intisar mei kimanin shekaru goma sha bakwai suka iso, cikin murna mai yawa intisar ta rungume meema tana faɗin"wow! aunty meema you are highly welcome, gaskiya munyi missing ɗin ku da yawa"ta dubi hafeez fuskar ta ɗauke da murmushin farin ciki tana faɗin"uncle hafeez yau a gari?ai munyi tsammanin mutanen Malaysia sun riƙe mana kai"
ÆŠan murmushi hafeez yayi sannan yace"ina!kuna raina intisar,kawai time ne baya samuwa,amma kuma ai auntyn ku tana zuwa ko?"
"Eh haka ne,to yanzu dai kuzo muje gida, Mamie na ta shirya muku delicious and wonderful dish"
Mima ta wuce gaba tana faÉ—in"kuzo muyi sauri,a gajiye nake ni"suka É—unguma suka shiga motar,aunty Bintu taja suka tafi gida