← Book details Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 31

Sashe 23

Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana komawa gida babu ɓata lokaci ta ɗora girki,white rice ta dafa da miya taji kifi,ta san shine favourite ɗin Khalees,ta tsala wanka ta sanya sexy English wears ta zubo da kitson attachment da tayi bayan ta,tayi wa fuskar ta light make up ta zauna tana danna waya tana taunar chewing gum,a lokacin ana ta sallar Isha'i amma ba ta ita take ba

Tun lokacin take jiran dawowar shi shiru,har tara shiru,goma shiru,sai hankalin ta ya fara tashi,ta É—auki waya ta fara kiran shi,amma switch off,hankalin ta ya fara tashi,don sai lokacin ta tuna cewa ya É—auki jakar kaya,ai bata san lokacin da ta É—ora hannu aka ba ta kama gunjin kuka,faÉ—i take "na shiga uku na lalace,asiri na ya tonu"

Kafin washegari da safe wasu ƙuraje masu ruwa da mugun wari suka feso mata a dukkan ilahirin jikin ta,ga ƙaiƙayi da raɗaɗi da suke mata,da ta kalli kanta a madubi ita kanta sai da taji ƙyanƙyami, bata taɓa shiga matsanancin tashin hankali da masifa irin wannan ba,ta koma bata da aiki sai kuka da tunanin mafita

***** ***** *****

Ta nutsu sosai a gidan Auntyn ta Nusaiba tana jin daɗin rayuwar ta,yau kwanan ta shida kenan a US, Rayuwar su sukeyi ciki ita da Aunty nusaiba da yaran ta Amra da Ajmal,sai auta Adnan,gaba ɗaya ta manta da wani abu wai shi ɓacin rai ko damuwa

Affan kuwa koyaushe yana hannun ƙanin mijin ta Safwan da Allah ya ɗora masa ƙaunar yaron,shi kanshi Affan yanayin san Francisco ya karɓe shi yayi fresh abin shi

Suna zaune a parlour suna kallon wani American film,yaran duk basa nan sun tafi makaranta,hatta Safwan ya fita aiki, Deeja ta ɗago ga kalli auntyn tata tace cikin shagwaɓa"Aunty"

Cikin kulawa Aunty nusaiba tace"ya dai auta?"

Deeja ta zauna daga kishingiÉ—ar da tayi tana kallon ta tace"Aunty na ganki Amma banga Yaya Yusuf ba"

Murmushi aunty Nusaiba tayi tace"inna bata gaya miki baya US ba?"

"Ta gaya min,amma kuma ai bazaki rasa sanin inda yake ba ko?"

"Eh!yana tokyo,a can yayi karatu kuma ya fara aiki,yau kwanan mu sha shida da dawowa matar shi ta haihu,yaushe kike zuwa?"

Da mugun zumuÉ—i Deeja tace"ko yau a shirye nake wallahi"

"Lallai kam,to be ready next week in Sha Allah zamu tafi,amma muna dawowa zan nema miki admission ki yi masters É—in ki idan kin yarda"

"Yeah Aunty!na yarda, wallahi dama na so É—orawa kawai ban samu dama bane"

"Okay,in Sha Allah idan muka dawo sai ki É—ora karatun"

Murna Deeja ta rinƙa yi har da tsalle,Aunty nusaiba sai kallon ta takeyi tana murmushi

Satin ta biyu a ƙasar suka cale zuwa ƙasar Japan,tun a airport taga yayanta Yusuf,sai da gaban ta ya faɗi da ta ganshi,don babu in da ya baro mahaifin su sai hasken fata,da gudu taje ta rungume shi tana hawaye,ya rungume ta yana shafa kanta,kafin ya ɗago ta yana kallon ta da murmushi,yace"Are little sister?

Kin girma fa! lokacin da muka bar ki You was just a little girl"

Murmushi Deeja tayi tana nuna masa Affan da ke hannun Aunty nusaiba tace"yanzu nima gashi na dire little baby"dariya sukayi daga shi har matar shi hanan da ke rungume da Æ´ar babyn su safna

Farin ciki iya farin ciki kam Deeja ta shige shi,taga soyayya ta ga kulawa daga kowanne angle, Yusuf ma daina fita aiki yayi,kullum yana tare da Æ´an uwan nashi ana ta shan raha da hira,ga matar shi mai kirki da barkwanci

Satin su É—aya a Japan suka tattara suka koma US,Deeja taji tamkar su kar su rabu,amma hakan bai hana ta farin ciki ba

Satin su uku da komawa Deeja ta fara ɗaukar lecture a Cambridge University cikin farin ciki da nasara,karatun nata yana gara mata yadda take so,don taji sauƙi ma Aunty nusaiba ta samar mata Nanny da zata rinƙa kular mata da Affan,ƴar ƙasar Uganda, dattijuwa mai tsafta

***** ***** *****

Babu irin cigiya da neman da Khalees da Imran basu yiwa Deeja ba,gidajen rediyo da na tv babu in da basu kai cigiya ba, Khalees har wani ɗan ƙaramin hauka yayi,ya zabge ya rame ya fita hayyacin shi,ko abinci baya iya ci sai Imran ya lallaɓa shi yake shan yoghurt ko tea,yanzu haka ma ya janye shi zuwa Lagos don abin nashi ya fara yawa

Suna zaune a ɗakin hotel ɗin da suka sauka,waya ce a hannun Khalees ɗin ya ƙurawa hoton su shi da Deeja idanu,sunyi kyau a hoton dukkan su sunyi murmushi,sunyi hoton ne a wani lokaci da suka shirya zasu je gaida Hajiya yace mata"ƴan matan Abdul kinyi kyau fa"

Tayi murmushi tana masa hararar wasa tace"don kar nace ka chanja kar ƴan mata suyi min shigar sauri shine kayi riga malam masallaci?ko baka san ka fi Ni kyau ba?"shine yayi dariya ya janyo ta yayi musu hoton suna dariya,suka hau musu akan wanda yafi kyau,ƙarshe sai da suka ɓata lokaci suka fita, dukkan hotunan Deeja da ke wayar Nadiya ta goge su,wannan ne kaɗai saboda son hoton da yakeyi ya ɓoye shi Nadiya bata ganshi ba

Imran da ya shigo yanzu ya tsaya yana kallon yadda hawaye ke zubo masa yana kallon wayar shi,yasan abinda yake kallo don wannan hoton shine abokin hirar shi,abincin shi, walwalar da duk wani farin cikin da ya rage masa, tabbas ya jinjina irin son da Khalees yakeyiwa Deeja,ya ƙarasa inda yake yayi tapping kafaɗar shi,ya ɗago a sanyaye yana kallon shi,ya samu waje a gefen shi ya zauna

Cikin kwantar da murya yace"Ni kam Khalees why not mu koma gida mu tuhumi matan mu kan batun Deeja,nasan Umaima bazata iya ɓatar da Deeja ba,amma nasan idan Nadiya ta aikata wata ɓarnar musamman wadda ta shafi umaiman zata gaya mata,so definitely indai sune suka ɓatar da ita idan muka tuhume su zamu samu hint"

"Kana ganin hakan mafita ce?"a cewar Khalees yana kallon shi

"In Sha Allah,mu jarraba hakan"

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 32

"To shikenan,muje"

A ranar Imran ya yankar musu ticket suka dawo Kano,a gidan Imran suka sauka,ko mintuna talatin da sauka basuyi ba Imran É—in ya É—ebo Æ´an sanda suka shiga suka fito da umaima da ke ta gunjin kuka,dama already ya tura wasu gidan Khalees, sai da aka tafi dasu sannan suka shiga cikin parlourn gidan suka zauna jugum,an rasa mai yin magana a cikin su

Turo ƙofar akayi da karfi,da sauri suka kalli ƙofar, Ma'aruf ne,yana zuwa ya shaƙe wuyan rigar Imran ya hau zazzaga masa masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba,babu abinda bai kira shi ba,matsiyaci,butulu,maci amana,wanda bai san ciwon kanshi ba,a ƙarshe ya kaɗa masa warning cewa ya nemo masa ƴar uwar shi ko ya ɗauki duk matakin da ya ga dama akanshi,sannan ya juya kan Khalees da shima ya zuba masa idanu kamar yadda Imran ɗin yayi yace

"Ka bani mamaki Abdul,ban taɓa tunanin za'a haɗa kai da kai a cutar da wani wanda yake da alaƙa dani ba,zuwa yanzu nasan waye kai,na gode"yana gama bayani ta take ƙafar Imran ya juya ya fice daga parlourn

Shiru ya ratsa parlourn,Imran ya sunkuyar da kanshi ƙasa, Khalees kam ya rasa mai ya kamata yayi ma,duniyar baki daya tayi masa wani irin ƙunci,da wanne zai ji?da ɓatan Deeja da yaron shi ko da laifin da wasu suke ɗora masa,a sanyaye ya miƙe yana goge ƙwallar da ta cika idanun shi,da sauri Imran yace"ina zakaje?"bai amsa ba ya nufi ƙofa,da sauri Imran ya riƙo hannun shi yana faɗin"I'm sorry gaskiya bazaka fita a wannan halin ba"

Cikin sanyin murya yace"gidan mu zan koma,wajen Hajiya ta"

"Okay bari nazo na mayar da kai,don bazan bar ka kayi driving a wannan halin ba,bai sake magana ba ya samu waje ya zauna, Imran ya shiga don É—auko makullin mota

** ** **

Babu irin wuyar da su Umaima basu sha ba don su faɗi in da Deeja take,amma basu faɗa ba saboda basu sani ba,ga Nadiya da take fama da jinya,cikin wannan halin Khalees ya aikowa da nadiya takardar saki,da ƙyar dai ƴan uwan ta suka samu suka karɓe ta, Umaima tayi kuka sosai,ta ji inama ace tana da wani a kusa da ita nata,dama Najeeb ne ya ɗauko ta daga ƙauyen su, kasancewar bata da iyaye sai ya mayar da ita gidan su,amma ya mayar da ita tamkar matar shi

Yanzu kuwa ta sani bata da gata,bata san yadda rayuwa zatayi da ita ba

***** ***** *****

Lokaci guda Deeja tayi kyau tayi ƙiba,ta zama abin burgewa, hankalin ta ya kwanta sosai,amma dai tana matuƙar kewar mijin ta Khalees,ko ya yake zuwa yanzu bata sani ba

Tsawon shekara guda ta É—auka tana karatun ta kafin ta kammala, result ya fito tayi murna sosai ganin sakamakon yadda yayi kyau,a lokacin ne hankalin ta ya koma gida,sai taji sam bata kyauta ba abinda tayi,don haka ta shawarci auntyn ta kan cewa tana son komawa Nigeria

Aunty nusaiba ta kalle ta tace"tuntuni ya kamata ace kin je ko da da ziyara ne,amma bazan matsa miki ba, shiyasa na ƙyale ki,yanzu dai ki bari sai nan da three weeks sai mu tafi gaba ɗaya,nima Ina son naje na ga ƴan uwa na"

"Su Aunty masu Æ´an uwa,to Allah ya nuna mana dai"cewar Deeja tana dariya

Itama dariyar tayi tace"ameen,ko kin É—auka ke kaÉ—ai ake so?"

Kafin lokacin yazo Deeja ga ƙasa,sai ƙirga kwanaki takeyi,ranar tafiya Deeja sai zumuɗi takeyi,su Aunty suna ta tsokanar ta suna dariya

A gidan baba Prof suka sauka,basu sanar da zuwan su ba,amma anyi Sa'a yawancin jama'ar gidan suna nan,ganin Deeja ya haifar da sowar murna da farin ciki,don kowa ya cire rai daita,duk da har zuwa lokacin ana saka ta a adduoi,Aunty Bintu ma satin su biyu kenan daga dawowa daga Syria,bata samu shigowa gidan ba sai yau,ashe dai ta taki Sa'a

Fauwaz ne ya kira Ma'aruf, Khalees da Imran da basa nan,bai gaya musu abinda yake faruwa ba,sai da suka zo kusan a tare,Imran ya riga su shigowa,yana zuwa Ma'aruf ya shigo,bai kai ga fitowa daga mota ba ma Khalees ya shigo,sai dai har kwanan yau Ma'aruf baya yi musu magana,don haka ko da sukayi masa sallama ma tsallake su yayi ko kallon su baiyi ba,suma suka bi bayan shi zuwa cikin gidan
Chapter 23 · 0% Book details