← Book details Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 31

Sashe 30

Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama Bilki tace "sunan dai gashi nan gashi nan dai,yana kama da hama,don Ni hama ma nake ce mata hankali na kwance"Deeja tace"ko dai UMAIMA?"mama Bilki tace"wallahi haka sunan yake? tabbas haka sunan yarinyar yake"

Deeja ta sunkuyar da kai tana jin wani iri,batayi aune ba ta ji hawaye ya ciko idanun ta,a sanyaye ta É—ago ta kalli Umaima wadda already hawaye ya fara zarya akan kuncin ta,kafin tace komai Umaima ta fara magana cikin kuka

"Amma baku kyauta min ba,wannan itace soyayyar da kuka nuna wa mahaifiya ta bayan babu ita a raye?kuka raye amma kuka bar ni rayuwa tana walagigi dani,na koma tamkar marainiyar da bata da asali?"saukowa tayi daga gefen gadon da take zaune,da rarrafe ta ƙarasa gaban su ta haɗe hannayen ta tana kuka mai sauti tana faɗin"meyasa?don Allah meyasa?a sanadin watsar da rayuwa ta abinci ya gagare ni, sutura ta gagare ni, ballantana ilmi na boko ko na addini,babu wanda zanyi shawara dashi,babu wanda zan kaiwa kuka na, azzalumai suka shiga rayuwa ta sukayi ya ƙwallo dani,don Allah laifin me nayi na cancanci wannan hukuncin daga gare ku? meyasa kuka rinjayar da ƙiyayyar mahaifi na akan soyayyar mahaifiya ta da kukeyi?"a haukace ta miƙe tana gunjin kuka tayi waje,ta bar su da bin ta da kallo, Mima tsabar shock bata san ma ta zauna ba,idan ta fahimta kenan ita da Umaima cousins ɗin juna ne

Deeja ce ta girgiza kai tana kallon su yadda suke bin umaima da idanu cike da mamaki,a takaice tayi musu bayanin rayuwar da umaima ta fuskanta har zuwa sanda ta É—auko ta a garin su, Mima sai kallon Deeja takeyi ta kasa magana

Mama bilki da inna haleema kuwa fashewa sukayi da kuka,mama bilki ta miƙe batare da tayi magana ba ta zaro wayar ta ta soma neman babban yayan su wato abban Mima

Ita kam Umaima backyard ɗin gidan ta nufa ta zauna tana kuka mai motsa rai,babu abinda yafi mata ciwo kamar yadda taga suna rayuwar su cikin farin ciki da ƙaunar juna,amma ita sun banzatar da tata rayuwar da ta tunda har zina tayi da auren ta saboda rashin gata sai ta sake rushewa da kuka

Mima ta kalli Deeja cikin sanyin murya tace"abin mamakin deejo,wai ashe yarinyar nan cousin sister ɗi na ce?"ɗan murmushi Deeja tayi tace"ikon Allah kenan leemo"Mima ta juya tana kallon little Deeja da ke ta wasannin ta akan gado hankalin ta a kwance,sai ji tayi tausayin yarinyar ya kamata,ta matsa bakin gadon ta ɗauko ta tana kallon ta tana murmushi,ga ƙwalla a idanun ta,suna haɗa idanu yarinyar ta fara dariya, Mima ta rungume ta hawaye na zubo mata

A ranar mahaifin Mima ya dawo bayan maghriba,da sai gobe,amma dalilin issue ɗin Umaima ya bar abinda yake yazo,zuwa lokacin da ƙyar Mima da Deeja suka lallaɓa umaima ta taso daga backyard suka kai ta ɗakin amaryar da za'ayi bikin ta shukra suka kwantar da ita,don da kafewa tayi bazata koma gidan ba tafiya zatayi,tana shiga kuma ta nemi waje ta kwanta, sallah kawai ke tayar da ita, little kuwa tuni ta fita lamarin ta ko kallon ta batayi Allah ya sa yarinyar akwai haƙuri, Mima ta dama mata cerelac ta bata,da ta fara rigimar bacci kuma tayi mata wanka ta goya ta har tayi bacci,ta kwantar da ita

A lokacin ragowar yayyen Mima ma sun hallara,Aunty aziza, Aunty Na'ima,da Yaya mukhtar da shi ma baya ƙasar yana UK,sai Mima da amaryar da ke gidan ƙanwar yadikko Inna salame,sai ƙannen abban su Mima,banda inna haleema da mama bilki,akwai baffa Tahir,mama fati,sai autan su,wanda innale take bi,wato baffa mukhtar

Sai da suka kammala haɗuwa sannan Alhaji kabir wato abban su Mima yace a kira masa Umaima,Aunty aziza da Mama bilki ne suka shiga ɗakin shukra in da Deeja ke zaune a wajen ta,jikin ta ya rine da zazzaɓi,da ƙyar da suɗin goshi Deeja ta samu ta sha shayin da ta haɗa mata ta bata magani,da Imran ya kira Umaima a waya ita ta daga tayi masa bayanin abinda yake faruwa, kam yayi farin ciki sosai,yayi tayiwa Deeja godiyar ta silar ta duk wani cigaba yake ta samun su,ya ƙara da cewa shima zai shigo,ita dai Umaima tana jin su, kasancewar a speaker Deeja ta saka wayar,amma bata tanka ba

A wannan halin su Aunty aziza suka zo kiran umaima,tana ganin su ta sake fashewa da kuka, Cikin fusata Deeja tace"amma kinyi min alƙawarin bazaki sake kuka ba, wallahi sai in ƙyale ki in kama harkar gaba na"Umaima tayi saurin goge hawayen batare da tayi magana ba ta miƙe ta bi su zuwa parlourn

Da sallama suka shiga,ta gaishe su cikin girmamawa,suka amsa suna kallon ta,ita kuwa kanta a ƙasa ta kasa kallon kowa,har yanzu hawaye na ƙoƙarin zubo mata amma tana dannewa

Alhaji Kabir yayi gyaran murya ya bude taro da addu'a,bayan ya gama ya fara jawabi

"Kamar yadda muka sani shekaru ashirin baya mun rasa autar mu maimunatu,ko nace innale,mun so tilon Æ´ar ta ta dawo hannun mu amma mahaifin ta da dangin shi suka nuna sun fi mu iko da Æ´ar, dalilin haka muka bar musu Æ´ar su wanda shine mafi girman kuskuren mu

A yau ga yarinyar innale ta dawo gare mu amma kuma maimakon mu kasance cikin farin ciki sai akasin hakan dalilin irin rayuwar da ta samu kanta a ciki"a taƙaice ya basu labarin Umaima,da yawan su sai da sukayi kuka,wanda ya sanya Umaima fashewa da wani sabon kukan, Alhaji Kabir ya cigaba"don Allah muna roƙon ki Umaima,da kiyi haƙuri abinda ya faru ya faru,a irin soyayyar da mukayiwa autar mu banda ƙaddara da jarrabawa babu abinda zai hana mu dawo da ke cikin mu,kar ki saka a ranki wai mun girmama ƙiyayyar mahaifin ki akan soyayyar da mukayiwa mahaifiyar ki,sam!mu bamu ƙi Aliyu ba,abinda zai je ya dawo muka guda,gashi kuma mun tarar

Definitely dangin mahaifin ki sun fi mu ƙarfi akanki, lokacin da mahaifin ki ya rasu da kusan watanni biyu Na tura Tahir don ya ɗauko ki,amma sai wan mahaifin ki yace bazasu bamu ke ba,idan ma muka cigaba da bibiyar ki sai kotu tayi mana tsakani,hakan yasa nayi tunanin zasu kula da ke na ƙyale ban sake bibiyar lamarin ki ba,amma kuma komai na rayuwar bawa a rubuce yake,babu wani bawa da ya isa ya sauya ƙaddarar ɗan uwan shi ko tashi,bazamu iya sauya ƙaddarar ki ba Umaima,so erase off damuwoyin da ke ranki ki manta da ɓacin rai,dama rabon haihuwar ki da jarrabawar da zaki fuskanta yasa innale ta auri Aliyu,amma definitely bamu so innale ta aure shi ba,don sanda ya haife ki ma bata kai 17 years ba, lokacin ma makaranta takeyi ta auri mahaifin ki,gashi shi baiyi karatu ba,don ma yayi ƙoƙari da yayi enrolling ɗin ki,kiyi haƙuri Umaima kinji? dukkan mu muna son ki,muna ƙaunar ki"

Sosai Umaima taji relief a ranta,kusan kowa na parlourn sai da ya bata haƙuri ya gabatar masa da kanshi,ita dai sai bin su takeyi da idanu tana jan ajiyar zuciya, fuskantar ta gaji ya sanya Mima tayi musu sallama ta kama hannun umaima suka koma ɗakin shukra

Ita ta haÉ—a mata ruwan wanka tace ta shiga wanka, Deeja dai na gefe tana kallon su,har yanzu ji takeyi kamar a mafarki wai Mima da Umaima cousin sisters ne

Mima da Umaima cousins 🤔Nima dai naji kamar a mafarki 😴

#Nusy_bee
*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 40(last page)

Bayan Umaima ta fito sababbin kayan bacci Mima ta bata,sai da ta gama shirya wa sannan umaima ta kawo mata abinci

A sanyaye ta girgiza kai tace"na sha tea ai"

Mima tace"amma dai kin san shayarwa kike ko?kuma yau through out banga kinci wani abin kirki ba,c'mon malama kin ci abinci,nan ɗin gidan baban ki ne,raɓe raɓe ya ƙare kuma"Umaima tayi murmushi ta karɓi abincin ta fara ci

Mima ta zauna gefen gadon tana kallon Deeja da tayi sakare tana kallon su,ta fashe da dariya, Deeja tace "bazan kula ki ba,nasan magana kike nema"

Mima tana dariya tace"really deejo,gani nayi kin zama kamar wata tsuntsuwa da aka figewa gashi aka saka a ruwan sanyi"Deeja ta yatsina fuska ta kuma cewa"ba fa zan kula ki ba leemo,don yanzu sai ki saka min tension"

Mima tayi dariya tace"bari na kira injin miya shi nasan zai kula ni"babu shiri Deeja ta kama dariya tace"wallahi leemo kin raina min miji,meye kuma injin miya?"

"Eh saboda shi a ƙani na ne"a cewar Mima tana kallon Deeja a ɗage

Deeja ta ja tsaki tace "leemo baki da kunya wallahi,mutumin da a haihuwar kaji ya haife ki shine ƙanin naki?"

Mima ta tafa hannu tace"ai ya faÉ—o tunda ya auri Æ´ar autar mu"

"Ke fa waÉ—annan watanni taran jin su kike kamar shekaru É—ari tara"ba Mima ba,ita kanta Umaima da ke kallon su cikin burgewa sai da ta É—an yi dariya

Gyara zama Mima tayi akan daddumar da ta shinfida akan tiles ta kalli Umaima da ke zaune gefen gado tana cin abinci a hankali tana kallon su,Mima tace "idan an ƙare biki zan kai ki gidan mama iyami,itace wadda ta riƙe mahaifiyar ki

Kafin maman ki tayi aure kullum aikin mama iyami tace innale tayi kaza tayi kaza,kuma ana cewa za'a yi mata faÉ—a zata kama kuka tana faÉ—a wai don an ga bata girma da uba ba,komai tayi mata sai dai ace Allah ya kyauta

Lokacin tana siyar da kayan yara su carbin malam,tsami gaye,aya,ɗan tamatsitsi,to yawanci Aunty innale ke cinye riba har ta taɓa uwa,idan taga babu tayi ta faɗa,a gaban idanun ta kuwa muƙus take tayi ta zare idanu

Akwai lokacin da ta soya aya mai gishiri da daddare ta kwashe a ƴar langar ta, suna ta hira da baffa Tahir,sai ga Aunty innale tayi sallama ta dawo daga makarantar dare,tana gani tace"ah!yau mama ta tuna aya kenan"ta cika hannu ta watsa a baki,tana tauna tace"kwana biyu mama bakiyi aya ba,tayi daɗi"ta ƙara cika hannu ta watsa a baki ta sake cewa"gishiri yaji"sannan ta cire hijabin ta ta saƙale, baffa Tahir yace"auta ba magana?"ko kallon shi batayi ba tace "ina wuni"tayi shigewar ta,yana kallon mama iyami ta miƙe da sauri
Chapter 30 · 0% Book details