← Book details Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 31

Sashe 31

Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanda Aunty innale ta gama shaunin ta a ɗaki ta fito ta samu waje ta zauna tana faɗin"wai!yau fa na gaji da yawa,malamin da ke mana karatu bai zo ba,wani ɗan takura aka turo mana"daga nan ta matsa kusa da kwanon,shi dai baffa Tahir ƙoƙarin danne dariya yakeyi,mama iyami kuma ta ɗauke kai tana sakace haƙuri,Aunty innale ta faki idanun su ta watsa a baki,ai da mugun sauri ta fito dashi tana tofarwa,wai ashe Inna juye ayar tayi ta zuba bushashshen kashin awakai a kwanon ta ajiye shi a inda yake, shiyasa baffa Tahir yake ta danne dariya,yanzu kuwa a bayyane ya kama dariya har da ƙyaƙyatawa"ita kanta Mima mai bada labarin dariya takeyi ballantana Deeja da Umaima, Mima ta cigaba"ai kuwa Aunty innale ta kwanta tana burgima tana ihu,mama iyami ta ɗauko kwanon ayar ta dire mata,ta zauna tana aikin lallashi,da ƙyar ta haƙura,kuma bayan ta haƙura mama iyami ta kora baffa Tahir da bulala

Lokacin da ta fitar da baban ki wai ita aure take so,kakar mu yadikko tace bata yarda ba,sai da mama iyami ta daina mata magana,a ƙarshe dai haka akayi auren Aunty innale da ƙananun shekaru,don har ta haife ki bata cika 17 years ba"Deeja tace"gaskiya dai Aunty innale akwai rigima,wai!"

Mima tace"ai auta ce,banga abin mamaki anan ba"Deeja tayi kamar bataji Mima da ke dariya ƙasa-ƙasa ba, Umaima kam tayi dariya tana kallon Deeja,don zuwa Yanzu itama ta gane Deeja bata son sunan autan nan

Hirar su suka cigaba da yi suna tsokanar juna,ko da Umaima bata saka musu baki amma tana nishaÉ—antuwa,har dare ya kusan raba basu sani ba

Washegari akayi event ɗin da ba'a samu anyi jiya ba,babu ƙarya sunyi kyau sosai, dama dukkan su gwanayen kwalliya ne, Umaima dai a lokacin taga dangi taga ƴan uwa,ko'ina ta zaga sai taji ana ga ƴar innale,amma fa rayuwar ta abban Mima ya hana tayar da batun,don yaga umaiman tana shiga damuwa,a ranar ta sake sosai,tare suka fita da ita da Deeja da Mima sai yaran su,kuma tare suka dawo gida

Washegari ta kama É—aurin aure,bayan an É—aura Imran ya kira Deeja a waya,itace tayi masa iso babban parlourn gidan ta kawo masa abinci da drinks,sannan ta kira Umaima da suke zaune da Æ´an matasan matan family É—in,har da intisar Æ´ar gidan Aunty Bintu,sai kallon Umaima takeyi da mamakin abinda ya kawo ta,itama umaiman kallon ta takeyi tana son tuna inda ta santa,babu wanda ya yiwa wani magana dai

Suna ta hira a ɗakin ya cika da hayaniya Deeja ta shiga,janyo hannun Umaima tayi ta dauko mata mayafi tace"mu je,mijin ki yana neman ki"bata jira amsar ta ba ta ja hannun ta suka nufi parlourn baƙi,tana zuwa bakin ƙofa ta saki hannun Umaima ta koma ciki

Da sallama Deeja ta shiga,Imran yana zaune akan two sitter ya ɗago daga danna wayar da yakeyi ya kalle ta yana murmushi,duk da dauriyar da ta koya kwanaki biyu saida taji ta karye,suna haɗa idanu ta fashe da kuka,da murmushi ya taso daga inda yake zaune ya ƙaraso kusa da ita ya kama hannayen ta yana faɗin"yanzu gaba ɗaya kin zama cry cry baby,abu kaɗan sai ki kama kuka"sai ta ɗaure fuska ta fizge hannayen ta tana huci,ƴar dariya yayi ya sake kamo hannayen yana faɗin "sorry Please,don Allah ki manta da komai Umaima,kamata yayi a ce kina cikin farin ciki,kar kiyi wa Allah butulci,ki godewa Allah wanda ya juya miki rayuwa daga ƙunci da damuwa ya canja miki zuwa ganiyar farin ciki,just move on kinji mon amé sóuiré?"kwanciya tayi a hankali akan ƙirjin Imran,ya sanya hannu ya kewaye ta,a hankali ta furta"Deeja tayi min komai a rayuwa,me zanyi na biya ta?"

"Ki riƙe ta da kyau,ita ɗin alkhairi ce ga duk wanda ya raɓe ta"umaima tayi murmushi batare da tace komai ba

Anyi biki lafiya an kai amarya É—akin ta, washegari Deeja ta dawo Kano ta bar Umaima a azare,Mima ta raka ta ta zaga dangi sosai,ta ga soyayya ta ga gata,wanda ya goge mata duk wani tabo da ciwo a ranta,kwanan ta biyu da dawowa Bauchi sukayi wa dady sallama suka dawo Kano

** ** **

Cikin sauri take shirya little Deeja,Imran ya leƙo yana faɗin"Madam You are wasting my time"

"I'm sorry gani nan"ta kama hannun little wadda yanzu babu inda bata zuwa da ƙafar ta,suka fito

Sai da suka shiga mota ta kalle shi tana faÉ—in"wai ina zamu je ne?"batare da ya kalle ta ba yace"ziyara mana"

Tafiyar rabin awa ta kawo su asibitin shi da ya gina,aka buÉ—e shi sati uku da suka gabata,bayan sun isa parking lot suka fita zuwa cikin asibitin

Kai tsaye ɓangaren Male wards suka nufa, Umaima tayi matuƙar firgita da ta ga Imran a kwance a wani ward,male nurses na ta gyara shi da alamu ma babu abinda yake iya yiwa kanshi,a guje ta juya zata fice daga ward din Imran ya riƙo ta,ta fashe da kuka cikin fitar hayyaci,bai ce mata komai ba ya ja ta suka fice daga ward ɗin

A reception suka tsaya,ya riƙe mata hannu gam,don sai ƙoƙarin tirjewa takeyi tana son fizgewa ta fice daga asibitin, Imran ya riƙo ta sosai yana ɗago haɓar ta yana kallon ta,cikin kwantar da murya yace"is okay Umaima,calm down,ki nutsu zamuyi magana"batare da tayi magana ba ta daidaita nutsuwar ta tana share hawayen ta

Ya kalle ta sosai yace"ban kawo ki nan wajen ba don kiyi kuka ko don ki tayar da hankalin ki,i bought you here don ki sake fahimtar rayuwa"

Cikin mai motsa rai Umaima tace"bana bukatar sake ganin shi a rayuwa ta,shi ya raba ni da farin ciki na,shine ya sa na kware muku baya,shine ya hana ni sukuni ya raba ni da dukkan walwala ta,ya guje Ni a lokacin da na rasa komai,bana son ƙara ganin shi kuma bazan taɓa yafe masa ba"

Tausayin ta ya kama Imran,ya sa hannu yana goge mata hawayen yace"You need to forgive him Umaima, rikon bashi da amfani musamman yadda rayuwa ta juya muku ku duka,kika koma matsayin da yafi nashi ɗaukaka,shi kuma ya mayar dashi matsayin da yafi naki ƙasƙantuwa,ki yafe masa,ko ba komai albarkacin yafiya muke ci baki ɗayan mu,ba don yafiya ba da yanzu kina taura kina rayuwa da ƴa ta ɗaya tilo wadda bansan ta ba,ba don yafiya ba da Ni da ke bamu haɗa kai da family ɗin mu ba,ba don yafiya ba da Yanzu ina rayuwa cikin kewar ki da rashin ki,kema haka,the most beautiful part ba don yafiya ba da yanzu baki san maternal relatives ɗin ki ba"

Murmushi tayi tana share hawayen ta tuno da Deeja da tayi,wadda a yanzu ita da Khalees basa ƙasar,a cewar su sunje honeymoon ɗin da basu samu sun je ba a farkon auren su

"Now forgive him wife"cikin sanyin murya tace"na yafe masa"

"That's my girl"ya faÉ—a yana murmushi yaja kumatun ta,sannan ya kama hannun ta suka nufi ward É—in da Najeeb yake

A bakin ƙofa ya tsaya,ita kuma ta shiga ciki tana kallon yadda gaba ɗaya ya lalace ya ƙwanjale,sai hawaye yake tun shigowar su ta farko

Murmushi mai ciwo Umaima tayi tana kallon Najeeb,cikin sanyin murya tace"sannu ya jikin?"

"Ki yafe min Umaima"a cewar shi cikin kuka

"Na yafe maka,ko babu komai silar ka nasan Imran kuma nasan Deeja,waɗannan mutanen sunyi min komai a rayuwa,duk da abinda kayi min ka bani gata,ka bani ilmi,ka bani mijin aure da nake alfahari dashi,na yafe maka"kuka ya ci ƙarfin ta,har Yanzu tana jin ciwon yadda Najeeb ya wulaƙanta mata rayuwa ya mayar da ita kamar matar shi, musamman yanzu da tayi ilmin addini sosai tasan hukuncin hakan

Tsayar da kukan tayi tace"ina Nadiya?"

Cikin shaƙewar murya yace"nadiya ta rasu watanni bakwai baya,bayan ta sha jinya"

"Allah yaji qan ta,itama na yafe mata"a cewar Umaima,ta juya cikin sanyin jiki ta fice daga ward É—in

Imran ya tako inda Najeeb yake yana murmushi,yace"Finally,komai ya wuce,kuma kamar yadda Umaima tace ne,a sanadin ka muka san juna,we are grateful for that,a sanadin ka na rabu da Deeja,banyi bakin ciki ba saboda Allah ya rubuta Deeja ba mata ta bace, MATAR KHALEES aboki na ce,ka jefa min tsanar ta,amma bakayi laifi ba saboda nine na zamo wawa har na bari aboki yake wasa da tunani na,na barshi a hakan ƘADDARAR MU CE(my next novel), Allah ya baka lafiya"yana kai wa nan ya fice abin shi, Najeeb ya bishi da kallo yana hawayen nadama mara amfani

BAYAN SHEKARU BIYAR

Abubuwa da yawa sun faru, Najeeb ya rasu shekaru uku da suka wuce, Umaima ta gama karatun ta cikin nasara, Deeja ta buɗe companyn ta nata na kanta,a yanzu Umaima ce M.D a companyn, Afra da fauwaz sun koma Columbia da zama baki daya, Deeja ta sake haifar yara biyu, babbar mai sunan Mamie babba,sai ƙaramin mai sunan mahaifin Khalees, Umaima ta ƙara haifar mace an saka mata sunan mahaifiyar su,Afra ƴan biyu ta haifa mata,ɗaya sunan mahaifiyar ta,ɗayar kuma sunan Deeja, lubaisa ma yara biyu ta haifa,babbar mace sai ƙanin ta namiji, zakiyya ma ta haifi mace ta saka mata sunan Deeja,Mima ma ta haifi ɗan ta namiji a Malaysia an saka masa sunan mahaifin mijin ya hafeez,wato Abdulhakim

A yanzu rayuwar family ɗin ta zama abin sha'awa,ko da Umaima da Mima take da alaƙa,kuma yanzu sun daidaita,har da Imran ma,amma ta ɗauki Deeja a matsayin uwa da ta rasa,yaya da bata da ita,sun haɗe kansu baki daya,zaman lafiya ya wanzu sosai, kowace tana rayuwa cikin farin ciki da kwanciyar hankali tsakanin ta da mijin ta

TAMMAT BIHAMDULILLAH 🙏

Anan na kawo karshen littafi na na MATAR KHALEES wanda Ni Nusaiba Ibrahim Rimi (Nusy bee)na rubuta,kuskuren da nayi ina roƙon Allah ya yafe min,abinda na rubuta mai amfani kuma ina roƙon Allah ya sa ya amfani al'ummar mu

Ina matuƙar godiya ga waɗanda suke yi min likes da comments,kune kuka bani ƙwarin gwiwa har nazo wannan matakin🤗ban manta da waɗanda har zuwa na musamman nakeyi don ganin comments ɗin su ba😁 jidda da Juliet,akwai sharhi da ƙarin bayani, Allah ya bar mu tare Allah ya saka muku da alkhairi baki daya

Sai mun haɗu a littafi na na gaba ƘADDARAR MU CE

#Nusy_bee
Chapter 31 · 0% Book details