← Book details Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 31

Sashe 27

Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Afra ta kalli Deeja tana ƴar dariya tace"ai kuwa sai naje,idan na gagara ai kuna da ƙarfin goyo ni"sukayi dariya su duka,Afra ta miƙe ta ɗauki mayafin ta, Deeja ta goya little Deeja, ta kalli Umaima tace"da me za'a lulluɓe ta saboda sanyi?"Umaima ta ɗauko ɗankwalin atamfar ta ta miƙawa Deeja, Deeja tace"wannan ai bazai yi ba,akwai showel ɗin Affan a mota,bari nayi amfanin dashi"

"Ni kam zan ce yayi yawa ma ban tambaye shi ba,banga kinzo dashi ba"a cewar Umaima

"Yana wajen ubanshi,da yake na yaye shi"ta ƙarasa faɗa tana ficewa daga ɗakin,su Umaima suka biyo bayan ta

A bakin motar ta suka same ta tana ƙulle showel ɗin da ta ɗauko,sosai take tausayin yaran saboda bata da wasu kaya masu yawa,hulunan ta guda biyu ne kacal,kuma su ma ba masu kauri ba,rigar sanyin ta guda ɗaya ce,ta dubi umaima tace"muje kasuwa kawai,akwai abinda nake son siya"babu musu suka wuce kasuwar a ƙafa,don babu nisa

Suna shiga kuwa sukayi Sa'ar ganin shagon kayan sakawa na manya da na yara,kai tsaye Deeja ta nufi can ta siyo kayan jarirai da diapers masu yawan gaske,sannan ta siyo dogayen riguna da undies sannan suka fito,cefane sukayi mai kyau,duk yadda Umaima ta so biyan kuɗin Deeja bata saurare ta ba ta biya,suka ɗebo kaya niƙi-niƙi sukayo gida

Shinkafa jollof da kifi Umaima ta dafa musu, sai haÉ—iyar yawu takeyi don zata iya cewa rabon ta da kifi ta manta,bayan ta gama ta É—ora ruwan wankan little Deeja a É—an murhun

Bayan Isha'i bayan sun gama cin abinci Deeja tayiwa little Deeja wanka ta sanya mata ɗaya daga cikin sababbin kayan sanyin da ta siyo mata ɗazu har da hula da safa,ɗan ƙaramin baby net ɗin da ta siyo ta buɗe ta sanya ta a ciki,don dama ƴar ƙarama ce sosai,watan ta huɗu amma ko wata ƴar wata biyun ta fita girma, Deeja ta lulluɓe ta tana tapping bayan ta a hankali har bacci ya ɗauke ta,tayi mata addu'a ta tofe tada ita ta mayar da net ɗin ta rufe ta ɗago tana kallon su Afra da Umaima da suka zuba mata idanu suna kallon ta

Murmushi tayi tace"ina matuƙar son ƴa mace,amma na godewa Allah da ya bani namijin ma,yanzu gashi na kuma samun macen"Umaima tana murmushi tace"idan zaku tafi ki tafi da ita na bar miki,nasan zatafi samun ingantacciyar rayuwa a hannun ki fiye da hannu na"Deeja tayi murmushi kawai

"Bayan wasu mintuna Deeja ta kalli Umaima ta fara magana cikin kwantar da murya"Umaima,da ace Imran baya buƙatar ki a rayuwar shi da saki uku zai yi Miki kamar yadda yayi min,ranshi ya ɓaci ne,amma har yanzu yana sob ki,irin soyayyar da Imran yayi miki I don't think it can be vanish a dare ɗaya,sannan ki goge dukkan abinda ya faru,ki ɗauka irin taki kaddarar kenan,baki san abinda Allah ya rubuta miki ba,don haka gobe tare dake zamu koma,akwai sabuwar rayuwar da take jiran ki a Kano,da ke da takwara ta"

Umaima ta girgiza kai tace"Deeja ki barni kawai na cigaba da rayuwa ta anan,bani da inda yafi nan"

"Wannan ba mai yiyuwa bane Umaima,ko kinji daÉ—in rayuwar da kikayi har haka da kike fatan ta wa Æ´arki?ko kinsan abinda zai faru gobe?so kike itama ta tashi tana jin haushin ki kamar yadda kike jin haushin magabatan ki?"

A sanyaye umaima ta girgiza kai tace"a'a, idan zaku tafi ku tafi da ita,ku tambayi baban ta idan yana so sai ku bashi,idan baya so kuma na bar miki"

Duk da cewa jikin su a sanyaye yake sai da suka kama dariya, Deeja tace"umaima akan takwara ta nake magana fa,ba jaka ko ɗan kunnen ki ba"Umaima ta wara idanu tace"na sani mana,nima akanta nake magana"suka ƙara fashewa da dariya, Afra har da riƙe ciki, Deeja tace"lallai na yarda da abinda ake cewa akan ɗan fari,amma a hakan kuke cewa kun fi mu wayo"itama Umaima dariya tayi tace"kema kinsan ƴan fari sun fi auta wayo"Deeja tace"ga evidence na gani"daga nan suka shiga tsokanar juna suna dariya,soon ta manta da damuwar da take ciki

Washegari da safe Deeja ta kalli Umaima fuskar ta babu wasa tace"Umaima ki haÉ—a dukkan ababen ki masu muhimmanci,zamu wuce Kano in less than one hour"

Kallon ta Umaima tayi,zatayi abinda ta saba wato musu,amma ganin yadda Deeja ta É—aure fuska alamar ba wasa sai tayi shiru,a sanyaye ta janyo jakar Ghana must go É—in ta ta fara jera kayayyakin ta, wadanda duk yawanci na little Deeja ne,Afra ta taimaka mata, Deeja kuma ta shirya little Deeja ta goya ta

Bayan sunyi wanka Deeja ta fito da dogayen rigunan da ta siyo,ta ɗauki ɗaya ta basu ɗaiɗaya,ta Deeja light blue,tayi mata kyau sosai,ta hau sosai da chaculate skin ɗin ta,ta Afra blue Black ce, kasancewar tafi Deeja haske itama Tata tayi mata kyau,ta Umaima maroon colour,Wai don ma yau da taɓa ta fatar tayi ɗan duhu,amma da yake kyan na nan da ta shirya sai gata ta fito a umaiman Imran ɗin ta, Afra tace"awwwn!naga manyan mata anan", Deeja tayi murmushi tace"dama kyan akwai wanda aka adanawa na Musamman,sai yanzu zai bayyana"Umaima tayi murmushi tana girgiza kai tana ƙoƙarin ɗaure dogon gashin ta

Yau da shagali🤗 Deejan Khalees da umaiman Imran sun haɗe kai sun bar mu🥺oho dai mu ma biye muku zamuyi mu haɗe kai🙈

#Nusy_bee

*****MATAR KHALEES*****

✍️Nusy bee

Page 37

Wajen ƙarfe goma na safe suka fito don tafiya gida,babu yadda Deeja batayi da Umaima ba tayiwa mutanen gidan sallama ba amma taƙi,da ta matsa mata ma kuka ta fashe mata dashi,sai kawai ta ƙyale ta,ta saɓa little Deeja a kafaɗa,wadda tayiwa kwalliya da overral ta ɗora mata doguwar riga mai kyau da hula har da Safa,ta lulluɓe ta da sabon showel,fari tas sai ɗaukan idanu yake

Tafiyar awanni uku da rabi ya kawo su kano,kai tsaye ƙaton shopping mall suka nufa,anan su Afra suka ga yadda ake haukar siyayya,ashe ba komai Deeja tayi a taura ba,don sai ta ta cika Boot taf da kayan little Deeja masu tsada,da kayan wasa,na Umaima da ta siya a backseat ta zuba su,ta fara biyawa gidan fauwaz ta sauke Afra sannan ta ɗauki hanyar gidan ta na Na'ibawa

A falo suka zube suna hutawa, Umaima sai kallon gidan takeyi don ya burge ta sosai,Deeja ta miƙe ta shiga kitchen ta samo musu drink ta zubo akan ɗan plate da glass cup ta kawo ta zuzzuba musu a cup

Suna sipping a hankali Deeja ta kalli Umaima tace

"Nan gida na ne,zaki zauna anan,duk abinda kike buƙata zan saka a kawo,ranar asabar idan Allah ya nuna mana zan kawo miki wadda zata taya ki zama da aikace-aikace,that same day kuma zan kai ki islamiyya ki cigaba da karatun kina addini,ranar Monday kuma in Sha Allah zan kai ki don kiyi registration na JAMB"

Umaima ta buÉ—e baki da zummar yin magana kuka ya kubce mata,cikin kuka ta fara magana

"Deeja ban san da me zan biya ki ba,haƙiƙa a dukkan rayuwa ta babu wanda yayi min rana ya sanya na ji Ni a mutum kamar ki,na gode Allah ya saka miki da mafificin alkhairi"

Ta sauko daga kan kujerar da take zauneta durƙusa ta kama ƙafafun Deeja,wadda tayi shiru kawai tana kallon ta,tace

"Don girman Allah Deeja ina roƙon ki ki yafe min abinda nayi miki,don Allah ki roƙar min yafiyar Imran da duk wanda na cutar,na...."Deeja ta toshe mata baki tana girgiza kai cikin ɗaure fuska tace"indai kin san idan nazo kuka zaki rinƙa yi min gwara ki gaya min kar na sake wahalar da kaina na dawo"da sauri ta share hawayen ta tace"na daina in Sha Allah"Deeja ta ɗan yi murmushi ta dafa kafaɗar ta tace"don Allah ina so ki manta da duk abinda ya faru a baya kiyi facing new life ɗinki,ki ɗauke ni a matsayin yayar ki da kuka fito ciki ɗaya,wadda a kowane hali sai dai ta ƙaurace miki na ɗan lokaci,amma bazata guje ki ba,don haka ki kwantar da hankalin ki ki manta da baya,ki goge shi a ranki,you are starting a new life,wadda a cikin ta babu Najeeb,babu Nadiya,babu talla,babu ƙuncin rayuwa,babu kaɗaici da kewa,in Sha Allah very soon komai zai wuce"tana gama magana tayi mata side hug ta miƙe ta ta ƙarasa kan two sitter da ta kwantar da little Deeja, yarinyar sai kallon juyawar fanka takeyi tana ƴan wasannin ta,babban ɗan yatsan hannun ta ta zurmuƙa shi a baki, Deeja ya durƙusa tana shafa fuskar ta tana murmushi tace"to Angel,zan tafi,i will miss you so much, much luv sweetheart"tayi kissing ɗin ta a goshi da kumatu,sai wulla ƙafa takeyi tana dariya, Deeja ta waiga ta kalli Umaima tana murmushi tace"to maman takwara,sai Saturday"bata jira amsar ta ba tayi sauri ta fice ganin umaiman tayi wani irin sanyi

Ai kuwa ranar asabar É—in Deeja ta dawo da wata mace dattijuwa,zata kai 47-48 years, sannan ta É—auki umaima suka je wata makarantar matan aure,ta gama mata komai suka dawo gida

A ranar ta sa aka ƙaro kayan abinci masu yawa,sannan ta bawa Umaima tsadaddiyar waya da makullin tsadaddiyar mota, Umaima bata taɓa tsammanin zata sake tuƙa mota a rayuwar ta ba,duk yadda taso kar tayi kuka ta kasa sai da ta fashe da kuka tana rungume Deeja ta kasa magana, Deeja na goge mata hawayen tace"ki shirya jibi zakiyi registration ɗin JAMB"

Umaima ta ƙara goge hawayen ta tace"amma lokaci bai ƙure min ba kuwa?ina nufin a karatun"

Deeja tace"shekarun ki nawa?"Umaima tace"I'm turning 25 next month"wani kallo Deeja tayi mata tace"dudud nawa kike,har Æ´an 60 years ma karatu sukeyi ballantana ke haihuwar kwanan nan,c'mon malama ki koma makaranta,don wannan karatun shine best pride É—in ki,kar ki kuskura kiyi wasa da opportunity É—inki na karatu"Umaima ta gyaÉ—a kai cikin sanyin jiki ta kama hannun Deeja tace"na gode sosai, Allah ya saka miki da mafificin alkhairi"Deeja bata daÉ—e sosai ba tayiwa umaima sallama ta tafi bayan ta gama wasa da takwarar ta,amma ta dawo ranar Litinin,a motar umaiman suka je sukayi registration na JAMB
Chapter 27 · 0% Book details