Sashe 1
Matar Khalees Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*****Matar khalees*****
âœï¸Alkalamin Nusaiba ibraheem rimi(Nusy bee)
بسم الله الرØÙ…ان الرØÙŠÙ…
Part 1
Matashiya ce wadda bazata gaza shekaru ashirin da biyar zuwa da bakwai ba, kyakykyawa ce wankan tarwada,tana sanye da golden lace riga da zani,ta yafa babban mayafi tun daga kanta,cikin takun ta na nutsuwa ta nufi bakin motar ta dake ma'ajiyar motoci ta kamfanin nasu
Muryar barrister Zee taji tanayi mata magana, Barrister Zee matar engineer Jabir wato mammallakin kamfanin,waigowa tayi fuskar ta cike da faraa ta qarasa kusa da zee suka tafa da raha irin ta qawaye, zee ta dube ta tace
"Su DEEJA manyan mata!sau hudu Ina shigowa kamfanin nan bana samun ki,yau ma Allah ya taimake ni"
Deeja tayi murmushi sannan tace"to zee me zan zauna nayi bayan na gama aiki na?dole na rinqa komawa da wuri,kin san É—an rigimar nawa fa"
"Gaskiya kam deeja,ai rayuwar Sai haquri kawai"a cewar Zee
"Uhm!hakane,ni bari na wuce gida,Sai mun sake haɗuwa"a cewar deeja tana ƙoƙarin bude motar ta
"Okay!ki gaida gida"a cewar Zee,sannan ta juya ta nufi cikin kamfanin
Kamar yadda ta Saba yau ma bata tarar da KHALEES a gidan ba,hakan bei bata mamaki ba,Kai tsaye bandaki ta fada tayi wanka,bayan ta fito kaya kawai ta zura tayi sallah sannan ta zauna a gaban madubi ta fara kintsa kanta
Muryar engineer khalees taji,da alamu ya dawo,ta Dan saurara,ga dukkan alamu waya yakeyi,Don haka batayi gaggawar fitowa ba,ta cigaba da abinda takeyi,tana jinshi ya shige dakin shi
Bata fito ba Sai da ta kammala Shirin ta tsaf,cikin riga da skirt na lace orange colour,tayi kyau sosai,kanta Babu Dan kwali Sai mayalwacin gashin ta da ta tufke da ribbon kalar kayan jikin ta,Kai tsaye dakin khalees É—in ta nufa
Da sallama ta shiga,yana zaune a bakin gadon yana latsa waya,ya amsa batare da ya kalle ta ba,bata damu ba ta zauna gami da fadin "sannu da dawowa"
Sai da ya bata lokaci sannan ya amsa da "yauwa"
Batayi zuciya ba,don idan da sabo ta saba,tace"na hada maka ruwan wanka fa"
"Naji"ya bata amsa har yanzu idanun shi Yana kan wayar shi
Ta ƙara da cewa "na Kai maka abincin dinning ko na kawo maka nan?"
Wannan karon ya dago ya dube ta,amma duban wulakanci yace"duk yadda kika gani,Kinga malama surutun ki ya ishe ni"
Batayi fushi ba,Don ta Saba da halin shi tace " I'm sorry"bata jira amsar shi batayi waje
Sai a lokacin khalees yabi hanyar da tabi da kallo na ƴan daƙiƙu Kamar wani Mai nazari,zuwa can yaja ajiyar zuciya kafin ya miƙe ya nufi banɗaki
Tana zaune a falo tana danne danne a laptop É—inta ya shigo falon,yadda yayi sallama batare da ya kalle ta ba haka itama ta amsa batare da ta kalle shi ba,bai damu ba yace
"Ina abincin nawa?"
"Gashi can na kammala shirya maka a dinning"ta bashi amsa,har yanzu kanta na ga laptop É—inta,hakan bei dame shi ba ya nufi dinning set din ya zauna,ya zaro waya ya kama latse latse
Ta tabbatar bazei taba serving kanshi ba,hakan ne ya Sanya ta miƙewa ta nufi dinning ɗin tayi serving ɗin shi,yana ta danne dannen shi har ta kammala,tana kammalawa ta wuce ta cigaba da aikin ta
Deeja kenan,MATAR KHALEES!duk tarin ƙalubale da damuwowin da ta haɗu dasu a rayuwar ta hakan bai hana ta neman na kanta ba,Kuma tana matuƙar kama kanta a duk halin da ta riski kanta
A shirye take tsaf cikin doguwar riga light blue Mai adon duwatsu,ta naɗe mayafin rigar a kanta,cikin sauri take gudanar da Shirin ta don ta ɗauko hanyar makara,a main parlor ta riski khalees,batayi jinkirin gaishe shi ba Amma ko kallon banza bata Samu ba,Sai ma gyara agogon shi da ya cigaba dayi yana tafiya a cikin isa irin yadda ya saba,bata ƙara bi ta kanshi ba ta ɗauki hanyar waje abinta
"Ina zuwa?"taji muryar shi
Juyowa tayi cike da mamakin tambayar rainin hankalin da yayi mata,Ina zuwa kuma?bai san tana fita ba dama?Amma Sai ta daure tace
"Wajen aiki zan je"
Sai da ya bata lokaci sannan ya kalle ta
"Anyway!yau duk inda 1:00 pm tayi ki tabbatar kina gida,ki shirya Mana abinci don zanyi baƙi"yana Kai wa nan ya kewaye ta ya fice batare da yaji ta bakin ta ba
Itama rufa Masa baya tayi suka fito zuwa harabar gidan,shi ya nufi motar shi ƙirar BMW,ita Kuma ta nufi motar ta ƙirar anaconda
Tuƙi takeyi Amma tunani fal ranta,ƙwalla na neman zubo mata,amma tana ƙoƙarin dannewa,gaba ɗaya rayuwar ta tun tana ƴar ƙaramar ta take haɗuwa da wahalhalu dabam dabam,zata iya cewa bata taɓa jin daɗin rayuwar ta ba,a fili ta furta
"Gaskiya duk wanda ya rayu babu uwa to da sauran shi a farin ciki"
Ta tuna ummu,uwar riƙon ta, Imran masoyin ta,ga khalees mijin ta,hajiya uwar mijin ta,da su farida ƙannen shi,duk mutanen nan Babu wanda take jin daɗin shi
Jin ƙirjin ta ya fara motsawa ya Sanya tayi gaggawar kawar da wannan tunanin a ranta,domin ko da wasa bata ƙaunar ciwon zuciyar ta ya tashi
Ƙarfe takwas saura minti biyu ta shiga office ɗinta,an gyara shi tsaf, ta nemi waje ta zauna ta harɗe yatsun ta ta tokare haɓar ta gami da yin Shiru,tamkar Mai yin nazarin wani abu,ba komai take tunani ba illa mafita a rayuwar ta,ta kasa gane mei mutane suke nema da rayuwar ta,musamman mijin ta da ta kasa gane kanshi,duk hanyoyin da take tunanin masu bullewa ne tabi amma babu nasara,gaba ɗaya kanta ya kulle,gata ba ƙawaye ta cika ba Koda ace tana da ƙawayen surutu bai dame ta ba,balle har ta sanar wa wani taji sanyi
Abban ta ne ya faÉ—o mata a rai,a lokacin da yake raye shine abokin shawarar ta,bata manta wata rana a lokacin da tana gidan Imran, wani zuwa da tayi gida yaga yanda ta rame yace
"Khadija,ko da Baki gaya min halin da kike ciki ba nasan kina cikin matsananciyar damuwa,nasan cewa ke mai haƙuri ce,amma Ina so ki sani shi haƙuri baya yawa Sai dai yayi kaɗan,don haka ki cigaba da haƙuri Allah Yana tare dake"
Tace"babu komai abba in Sha Allah zaka same ni Mai biyayya,bazan baka kunya ba"
Allah yayi miki albarka"a cewar abban nata
Doguwar ajiyar zuciya ta ja bayan ta dawo daga tunanin daidai nan taji an ƙwanƙwasa ƙofar,ta bada izinin a shigo
Sa sallama sakatariyar tata ta shiga,ta amsa fuska a sake,a ladabce sakatariyar tata tace
"Madam oga na neman ki"
"Okay gani nan fitowa"ta bata amsa
Tana fita itama ta miƙe ta fice zuwa office din MD ɗin nasu
Batayi mamakin ganin khalees a office É—in ba,sai dai yadda beiyi mata kallon sani ba itama haka,ta samu waje ta zauna,bayan sun gaisa ya dube ta yace"madam ya ake ciki game da aikin da na baki?"
"Ai na kammala tun jiya"
"Okay idan babu damuwa É—auko mini su"
"Okay sir!"ta fada gami da miƙewa ta nufi hanyar fita daga office ɗin
Jim kaɗan ta dawo riƙe da takardu a hannun ta,ya amsa ya duba,ya kalle ta da murmushi yana fadin"very nice madam"
"Thank you sir!"inji ta
Wasu takardun ya miqo mata a files yana fadin "ga wani aikin nan da fatan Shima zai kammalu da wuri"
"In Sha Allah"ta fada gami da amsar takardun ta nufi waje
Sha biyu da rabi daidai ta miƙe ba don ta kammala aikin ba sai don umarnin khalees,Amma dai dai taci ƙarfin aikin,ta miƙe ta fito don rufe ƙofar office ɗin,sukayi sallama da sakatariyar ta ta nufi motar ta ta tayar ta ɗauki hanyar gida
#Nusy_bee
*****Matar khalees*****
âœï¸ Nusy bee
Page 2
Cikin sauri tayi wanka tayi sallah sannan ta shiga kitchen,farar shinkafa ta ɗora da miya sannan ta tayi papper chicken ɗin ta lafiyayye sannan tayi coconut juice,duk a cikin Abinda bei kai awa ɗaya da rabi ba ta kammala,ta jere su a dinning,cikin sauri sauri ta gyara ko'ina ta sanya turare gidan ya ɗauki ƙamshi,ta koma ɗakin ta tayi wanka ta shirya zuwa riga da skirt na atamfa ta ɗaura ɗankwali akanta ta zauna a bakin gadon tana mayar da nunfashi
Ta kai mintuna goma a zaune tana chatting taji sallamar su,sai da gaban ta ya faɗi saboda jin Muryar shi,tabbas shine ba amsa kuwwa bane,da sauri ta miƙe ta leƙa ,ga mamakin ta har da Yaya fauwaz,da sauri ta koma ta faɗa kan gado,gabanta yana dukan uku-uku,kanta ya fara sarawa,cikin rawar murya ta furta"wannan mummunar sakayyar taka ta ishe ni haka Imran"
Wayar ta ce ta katse ta,da sauri ta duba, khalees ne,ta san kiran me yake mata,da sauri ta janyo hijabin ta ta sanya ta miƙe ta nufi falon
Da sallama ta shiga,dukkan su suka ɗago suka amsa,a kallon da tayiwa Imran ta gano tsantsar mamakin da yake yi,wanda bata raba ɗayan biyu mamakin ganin ta a matsayin MATAR KHALEES yake yi,ita dai batayi ƙasa a gwiwa ba wajen gaishe su ba,su shida ne, banda yaya fauwaz da Imran,sai ragowar su huɗu da bata san su ba,suka amsa cikin fara'a, fauwaz ya dubi Khalees cikin tsokana yace
"Iyyeeee!ashe kaine kayi wuf da ƴar ƙanwar tamu shine ko mu sani?"ya dubi deeja yace"Dijangala ba'a sanar mana ba ko?ko da yake nasan fushi akeyi damu ko?"
Tayi É—an murmushi tace"I'm sorry banyi gayyata bane,Kuma yazo a gaggauce shiyasa"
"Babu damuwa, Allah ya sanya alkhairi"inji shi
Ta wuce kitchen tana fadin"ameen,na gode"
Cikin Æ´an mintuna ta gama halarto musu abincin,sannan ta juya ta shige É—akin ta
Tana kwance tana jiyo hirar tasu sama sama, zuciyar ta na suya,tunani takeyi me ya haɗa Imran da Khalees?wace iriyar mu'amala ce ta haɗa su?ko dama can sun san juna?kai bei zama lallai ace sun san juna ba,don da ace sun san juna Imran zei taɓa bata labarin shi watarana,amma bata taɓa jin labarin shi a bakin Imran ɗin ba,to me haɗin su dashi yake nufi?
"Tabbas da wata ƙulalliya a ƙasa!"ta faɗa da raunin murya,idanun ta na kawo ƙwalla
Ta É—aga hannun ta sama tace "ya Allah ga bayin ka nan,idan har da wani abu suke nufi na Allah ka tseratar dani,su kuma ka ganar dasu"
Tayi saurin goge hawayen da ya taru a kwarmin idanun ta suke ƙoƙarin zubowa,wayar ta ta janyo ta buɗe data suka cigaba da hira da aunty kiyya akan bikin Yasmin