Sashe 89
Mar'adam's Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" bani rice ma ya isa amman kadan zaki zuba min ta zuba mata ta ajiye agabanta sannna ta zuba abinda tasan ATA yake so rice and stew da miyar kayan ciki da cowslow ,ta zuba shinkafar a plet dabam haka ma miyar daban tayi masa ta ajiye a gabansa sannan ta zuba nasu ita da nana hauwa'u ta dauka ta wuce."
Ahankali mami take cin abinci amman ATA ko kallon abincin gabansa bai yi ba saboda haushin mami taki kallonsa ballatana yaga faraarta taki furta komai garesa idan zasu hada ido sai ta dauke kanta sosai ya shiga damuwa hankalinsa ya tashi "to me yayi mata da zafi haka ?shi kam bazai ta'ba boye felling dinsa akan maryam ba yadda zuciyarsa bata sonta haka bakinsa bazai qasa furtawa ba sai dai tayi hakuri dashi ."
Ganin yaki ci yasa mami taji babu dadi aranta ta dauki spoon ta sanya cikin abincinsa ta sake tura masa tana tsaresa da idanunta jiki a sanyaye ya sauke numfashi zuciyrasa na sake karyewa allah sarki sweetheart yasan bazata iya dogon fushi dashi ba ,haka ya dinga cusawa cikinsa abinci tana tsiyaya masa ruwan lemu sai data ga ya koshi sannnan ta mike ta soma tafiya ya dago kanshi yana kallon bayanta zuciyarsa cike da tausayinta ya sani cewar tana matukar son maryama ,da wani ne yayi abinda yayi mata koda kuwa acikin ya'yanta ne sai ya hadu da fushinta fiyye da yadda ta dauka dashi amman shi allah ya saka mata hakuri dashi komai zai mata tana shanyewa har ma ta kasa daukar dogon fushi dashi." tashi yayi ya haye saman d'akinsa babu laifi zuciyarsa ta d'an samu natsuwa."
Da misalin karfe hudu na ranar baki suka fara sauka a gidan mami murna a wajen mami ba'a magana ranar a kasalance maryam tayi komai daga karshe ta shige daki ta kwanta ta huta dan ta samu zuciyarta da gangar jikinta su samu natsuwa da suka rasa
tun da taga jama'ar sun fara sauka hankalinta ya tashi jikinta yayi sanyi ."washegari aka fara shirye shirye biki , zaune suke a falon aunty shahida masu gyara jiki nata faman shafa masu dilka ajiki yayinda yanuwa suka zagayesu ana hira daga maryam har nuzla kana kallonsu zaka fahimci suna cikin damuwa da rashin son auren dan fuskarsu kamar zasuyi kuka gidan mami ya sake cika da yan'uwanta har yau friday da zaayi kamu mutane suna cikin zuwa ."
a wani hadadden hall akayi kamu amare sunyi kyau sosai sai dai ango ATA bai je koina ba yana kwance a gida ,bangaren maryam ita kadai ce zaune akan kujerar daaka tanada dominsu dan juyin duniya aunty khadija tayi dashi amman yaki zuwa aranshi yace "ko bikin da yake so ne zaayi bazai je wani kamu ba bare wanda zaa masa na dole ."mrym kuwa juya kai kawai take zuciyarta a jagule bare idan ta kalli hisham da nuzla yadda hisham Ke jefa mata kallon soyayya da kaffa kaffa daita sai taji kamar ta daura hannuwanta duka aka ta saka ihu ko taji saukin zafin da zuciyarta take mata ta sake kallon hisham taga ya makale nuzla sai d'aukarsu hoto ake amman ita nata ango ya wulakantata."
aunty shahida tayi mata duban tsanake nan da nan ta fahimci halin da take ciki ta qaraso inda take zaune tana cewa "Ki kwantar da hankalinki mrym da rashin zuwan adam kema Kinsan halinsa gara rashin zuwansa daya zo ya kunyata mu ta hanyar wulakanta mu amman muddin muna raye bazakiyi bakinciki a gidansa ba."maryam tayi narai narai da idanu zatai kuka "qul karki daga hankalinki bare Kiyi asarar hawayenki da zarar an daura shikenna ya zama naki na har abada a hankali ta dinga rarrashinta har ta dan samu natsuwar zuciya sai dai taji haushi da bakinciki rashin zuwansa domin dai so yake lallai sai duniya tasan irin auren da zasuyi ."
bayan an gama kamu amarya maryam ita kadai a bayan mota direba yajata suka dauki hanyar zuwa gida yayinda hisham da nuzla suke zaune abayan tasu motar direbansu na qoqarin kunna mota hisham ya kafeta da ido sosai Kmr zai cinyeta kafin ya sauke ajiyar zuciya ya kamo hannunta cikin nashi yana kallo yace "Woow my nuzla gsky lallen yayi kyau my wife waya miki shi ?
hade rai tayi sosai tamkar bata ta'ba yin dariya ba a tsawon rayuwarta tana zame hannunta cikin nashi tace "ka tsaya iya matsayinka karka sake ta'ba min jiki dan wannan jikin ba naka bane "na waye "? ya tambayeta yana matsota sosai Kmr zai shige jikinta "tambayarki nake "jikin waye ?"stil dai shiru tayi masa " jibi iwar haka kina cikin gidana watakilla ma muna kwance acikin bargo daya makale da juna "wani kuka ta fashe da shi tana qara matsawa ".
" to to!! shikenan na bari Kiyi hakuri amman dai Kinsan dole zamu kasance tare? tsaki taja ta kawar da fuskarta gefe a haka suka qaraso gida ."mota bata tsaya a koina sai a kofar gidansu bayan motar ta tsaya ta fito hisham ya biyota suka jira yana yi mata magana amman taki kulashi tana qoqarin shiga gida ya riko hannunta daya cikin nashi ta juyo a matukar fusace tana kallonsa shima kallonta yake with a broad smile a fuskarsa sai itace ta dauke kanta tana lissafi yadda zata gudu ta bar shi da wahalarsa ".
"anya kuwa zata iya gudu ta bar iyayenta bayan a yanzu bata iya zuwa koina ta kwana batare dasu ba ?ta tambayi kanta nan take zuciyarta ta bata amsa da" wannan shine mafuta a gareki idan komai ya natsa sai ki dawo wanda zuwa lokacin dole kowa ya hakura ." ta sake kallonsa taga har lokacin ita yake kallo yana murmushi wanda bata san ko na meye ba ."cike da jin haushi ta fix hannuta tana mai bakinciki dan komai ya faru da rayuwarta shine sila shekara da shekaru bata ta'ba tunanin barin iyayenta ba sai a dalilinsa ita kam tsakaninta dashi sai dai allah ya isa da wannan bakinciki ta shige gida ta barshi tsaye yana kallon bayanta ".
Sai bayan data shiga gida sannan ya juya ya wuce kai tsaye wajen ATA ya wuce koda ya shiga parlour'nsa yana tsaye akan dadduma yana sallar magrib bai zauna ba shima bathroom ya shiga ya dauro alwala ya fito ya bisa sallah ,bayan sun idar ya fara tsokanar ATA "ango ango !!amman gsky kai dai anyi dan iskan ango ,wallahi baka kyautawa maryam ba, ka barta ita kadai allah sarki wallahi na tausaya mata, wallahi abokina kabi a hankali ina guje maka ranar da zaka rufta "wani dogon tsaki yaja yana watsa masa harara tare da cewa "ka maida hankalinka jikinka da wannan shirmen da kake yi karka sake min maganar auren nan" hisham yayi murmushi yana cewa "ai hankalina yana jikina nan dai yayita jan ATA."
Nuzla tsaye a dakinta hawaye na zubo daga kwarnin idanunta alokacin da take daukar abubuwan amfanita masu mahimanci tana tuna rayuwar kuncin da iyayenta zasuyi idan suka laluba basu ganta ba ,bayan kamar awa daya nuzla ta fito zuwa babban parlour'nsu koina ta kalla mutane a parlour'n yan'uwan mahaifiyarta gbdy zaune kai tsaye ta shiga dakin hjy salema bata dade ba ta fito ta rasa yadda zaayi ta sake fita dan haka ta koma ciki d'akinta tana tunani hanyar da zata bi ta kubta daga wannan wahallen auren ."
byn Kmr mintuna goma ta sake fitowa har ta kai bakin kofa aunty maijidda tace "ina zaki kuma adaidai wannan lokacin ? Ta fad'a tana kallon agogon dake manne a falon ,nuzla ta dan diririce sannan tace "yaya hisham ne ya kirani yana waje" tana gama jin abinda ta fad'a ta juya tayi d'akin da baki suke ita kuma nuzla ta samu damar fice wa daga gidan gabadaya ."
yan'uwan hjy salema suna ta kikiniyar da hadahadar abincin gobe diner sam babu wanda ya fahimci nuzla bata gidan har karfe goma sha biyu na dare ."Hjy salema dake zaune a bakin gadonta haka nan jikin ta ya dinga mata wani iri ,ta fito ta shiga dakin nuzla bata ganta ba dan haka ta juya ta fito daga dakin tana tmbayr aunty rabi wacce ta kasance diya kanwarta ce "umma bansa inda take ba amman bari na dubata a dakinta "ai daga dakin nata nike bangata ba shiyasa ma na tambayeki ." to bari naje na tmbyi aunty maijidda ko tasan inda taje da sauri ta wuce hjy salema."
A bakin kofar fita daga parlour'n suka hadu da aunty maijidda "Yauwa aunty maijidda ina nuzla ko ta fad'a miki inda zata "eh d'azu tace min zata wajen hisham amman bari na kirata nan ta soma qoqarin kiran layin nuzla sai dai numberta na shiga bata dauka dan haka ta kira layin hisham tana tmyrsa nuzla amsar daya bata yasa ta shigo d'akin hjy salema da mugun sauri ta isketa tsaye cikin faduwar gaba ."
Aunty maijidda batayi magana ba ta cigaba da kallon hjy salema "maijidda ko nuzla ta fad'a miki inda zata ?ta bude bakinta kenan zata bata amsa idanunta suka ci karo da envelop asaman dress mirrow din hjy salema an rubuta wannan sakon na umma da abba ne kallon da takewa envelop din yasa hankalin hjy salema ya kai kanshi "
gabadayansu gabansu ne ya shiga dokawa dan basusan me Ke kunshe a cikinsa ba tun baa kai ga budewa ba hjy salema ta soma furta kalmar "innalilahi inna ilahi rajiun azuci da fili dan ta gama shiga rudani "hannun aunty maijidda na rawa ta dauka ta bude envelop ta soma karantawa a fili hannunta da jikinta na wani irin wara ."
_Assalamu alaikum iyayena nasan aloakcin da zaku nemi ni ku rasa zaku ji babu dadi acikin ranku amman ina mai baku hakuri da neman afuwarku akan halin damuwar da zaku shiga a dalilina na tafe ne adalilin bana son aurena da yaya hisham na fito maku da manufata amman kun kasa fahimtata dan haka na yanke shawarar barinku ba dan raina yaso ba ina sonki ummanah ina sonki fiyyr da komai haka kai ma abbanah ina sonka zanyi kewarku sosai_