← Book details Mar'adam's Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 100

Sashe 18

Mar'adam's Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

murmushin gefen baki yayi wanda yafi kuka ciwo yana girgiza Kai "impossible babu wannan macen a fad'in duniya da zata ce bata son ni Adam wallahi ta raina muku hankali ne sannan tayi balain rainaku ni ko giyar wake ta sha bazata ta'ba fada min haka ba , numfashi ya sauke a maganarsa ta karshe sannan ya mike tsaye ya zuba hannuwansa duka cikin ajihun wandonsa ya soma taku kamar baya son taka kasa yana k'okarin barin parlour'n a matukar fusace har ya Kai bakin kofar fita ya tsaya cak batare da juyo ba "abar maganar nan a tsakankanimu banason sweetheart tasan komai zan san abunyi .."
"Da dai ya fiyye maka ka ajiye wannan shegen girman kan naka ka fuskanceta da kanka wata Killa zata yarda "inji cewar aunty shahida " ai ni idan na fuskanceta umarnin kawai zan bata Kuma dolenta tabi umarnina koda kuwa mutuwa zatayi yana gama fad'ar haka ya k'arasa ficewa  daga parlour'n bai tsaya jin abinda zata ce ba .

girgiza Kai sukayi a tare "kinji ba aunty , kinji abinda yake cewa ko ?"wato shi bazai rusunar da kai ba, Komai ta karfi zai yi byn ita mace yar rarrrashi ce ." Allah dai ya shirya AD yasa ya gane kuma ya wanke masa wannan zuciyar tasa aunty shahida ta fad'a . bedroom din hajiya zulaiheart suka shiga suna qoqarin danne damuwarsu dan karta fahimci komai a hankali suka dinga nuna mata babu wata matsala sunyi mgn da maryam kuma ta amince "masha Allah "Kai alhamdulillah amman naji dadi Allah yayiwa rayuwarsu albarka wannan aure Ina son shi Ina qaunarsa Ina farinciki dashi yanzu sai a sanar da baba babba  shi kuma ya nemi sauran yanuwansa aje neman aurenta gurin saidu ko ? "wannan haka ne amman ki dan tsaya tukun kinsan halin 'yan kayanki muna son ya dan saki jiki da mrym din su samu fahimtar juna sai ayi maganar aure hjy zulaiheart ta gyada Kai tana murmushin jin dadi  "wannan ma shawara ce  mai kyau Allah ya daidata tsakaninsu dan mrym bani da matsalata daita , nan sukayita biyewa hjy zulaiheart dan basa son tasan abinda ke faruwa ta shiga damuwa , domin kuwa muddin tasani akwai gagarumin tashin hankali a gidan ."

"Yana shiga d'akinsa zariya ya soma yi daga farkon d'akin zuwa karshe ya kasa zama kamar wanda yayiwa sarki karya can ya tsaya cak yana jan tsaki har lokacin mamakinta yake dan yasan aunty shahida baza ta'ba fad'a masa qarya ba daya qaryatata cikin zafin nama ya soma balballe botiran gaban farar rigar dake sanye ajikinsa ya cire sannan ya zame ash three quarter din da yake sanye dashi ya shiga toilet yana sake jan tsaki ya kunnawa Kansa ruwa yana jan numfashi da rarrashin zuciyarsa tare da son karyata zuciyarsa akan jin haushin maganar yarinyar shiru yayi ruwan na sauka ajikinsa " dole yana bukatar saita kanshi dan ya samu damar tarwatsa zuciyarta cikin ruwan sanyi ban da ma hauka da jakanci irin nata Ina ita Ina shi Adam ai sai dai darajan iyaye ?

shi da yake da mace kamar  princess yarinyar da ta samu kyakkyawan mazauni a zuciyarsa me zai yi da mai jiki kamar na turkey, abinda batasani ba da abashi mace irinta gara ya kare rayuwarsa babu aure yana cikin toilet ya dinga jin sautin qarar wayarsa bai fito ba sai daya samu natsuwa sannan ya fito d'aure da white towel iya gwiwarsa ya tsaya gaban mirrow yana karewa kanshi kallon tsab sannan ya sauya kaya riga armygreen da wando baki kafafunsa sanye da takalmi fari sol ya zauna shiru akan kujera duk yadda yaso ya cire damuwar rashin son shi da'akace mrym batayi abun ya cutura wani irin zabura yayi ya mike  ya kwashi wayoyinsa ya fito zuwa haraban gidan Inda security da escort dinsa ke faman safa da marwa suna ganinsa suka hau kikiniyar bud'e masa bayan mota suna furta" barka da fitowa ranka ya dade ya shiga ya zauna fuskarsa a hade batare daya amsa ba direbansa yayi saurin shiga mazaunin direba "aka bude makeken get din gidan ,motor daya da direba da wasu escort sukayi gaba sannan motar da Mr ATA ke cikin sai daya a bayansu suka bar gidan suna hawa kan titi kira ya shigo wayar direba sai daya nemi izini agurin A
Mr ATA sannan ya d'auka mgn daya ya katse kiran Tare da tmbyr mr ATA"ranka ya dade Ina muka nufa ne ? "gdn mb ya fada ataikace yana kallon gefe titi zuciyarsa na zafi ,tafiya mintuna kadan sukayi suka k'araso ikeja gra a kofar gidan suka ja suka faka suka yi saurin firfitowa suka zagaye motar da Mr ATA yake ciki ,daya daga cikinsu ya bude masa murfin mota , masu gadin gidan muhd bello na ganinsa suka fara rawar jikin da kokarin kawo gaisuwa.

" Kai tsaye ya shiga gidan batare da neman iso ba waje ya samu a rumfar dake ajiye da kujera na alfarma dake haraban gidan ya zauna ya d'aura kafarsa d'aya akan d'aya wannan ya rigada ya zame masa jiki no matter how ya zauna sai ya d'aura kafa daya a kan d'aya , hannunsa daya ya d'aura a kan table yayinda wayarsa ke manne da kunneshi yana neman layin MB cikin kankanin lokaci ya bayyana a gabansa ."sai da gabansa yayi mugun bugawa hankalinsa ya tashi da ganin yanayin Mr ATA , ya zauna kusa dashi yana kallonsa "Lafiya friend na ganka haka kmr kana cikin damuwa ?"

shiru yayi masa zuciyarsa na zafi da tafarfasa kmr zata kama da wuta "please talk to me friend what's wrong with you ?"yin duniya mr ATA yaki magana shiru Shima yayi yana kallonsa zuwa sanda mai aikinsa ta k'araso rike da tire dake d'auke da ruwa da lemuka masu sanyi tun kafin ta k'araso ya amsa a hannunta dan yasan yadda mr ATA ya tsani ganin fuskokin masu aiki ya ajiye akan table ita Kuma ta juya da sauri .ta kasan idanunshi yake kallon yadda take daga ka'fafunta haka nan ya tsinci kanshi da kallon every step of her  zuciyarsa na quna ."
MB ya tsiyaya masa ruwan ya mika masa "Kar'ba ka sha ka dan ji sanyi ATA ya numfashi ya sauke numfashi kana ya nuna masa kan table "ba ruwa nazo sha ba MB wai har ni wanan stupid monkey din zata ce bata so ......?"yayi maganar yana nuna qirjinsa da d'an yatsansa .

a matukar firgice MB yace "who's she ?"wannan monkey revenble person din mana har ni zata ce bata so? " is a lie she just say it "ka natsu plz nifa ban ma fahimceka ba amman duk da haka nasan babu macen da zata ce bata sonka "wannnan yar iskar yarinyar diyar kanin sweetheart dake fama da danyen jiki kmar daga alhalin china aka samota yayi maganar a tsawace yana dukan table din gabansa nan take tire da glass cup suka tarwatse MB bai tsaya bi ta kansu ba ya riko hannuwansa duka cikin nashi dan gbdy zuwa yanzu ya fahimci ko wa yake nufi  "calm down ATA ba fushi yakamata kayi ba soyayya haka take kayi hakuri ka natsu musan abunyi tunda kaji kana sonta yanzu shawo kanta bazai yi mana wa......"

MB yayi saurin katse maganarsa sakamakon wani mugun kallon da ATA ya  watsa masa yana zare hannuwansa dake cikin nashi "nace maka Ina sonta ne ? MB yayi saurin girgiza masa kai alamun a'a "to me yasa kace Ina Sonta ?wai naga kamar ka damu ne" "to bana Sonta kuma har abada bazan sota ba Koda kuwa tazamo mata agareni wallahi bazan sota ba kai bancin darajan sweetheart bazan ta'ba iya aurenta ba, bugu da kari ni mallakin princess ne ba kowace mace ba ,Ina son yarinyar  nan MB Ina zaka nemo minta ?na saka 50 billion ga duk wanda ya nemo min ita ka taimakeni abokina ka tayani nemota wallahi muddin na auri yarinyar nan zan cutar da zuciyata sannan zan cutar da yarinyar mutane dan bana son mace irinta bazan yi mata adalci ba bazan iya italic ba  ."

"Is okay ATA Ina iyakar kokarina wallahi amman zan qara ya kife kanshi akan table kmr wani karamin yaro zuciyarsa na zugi da rad'adin bakinciki "kayi hakuri friend ka sanyaya zuciyarka maryam bazata kika ba sai dai ta furta hakan ne adalilin yadda kake mata amman ni zan sameta muyi magana kune da kune da fahimta nasa zata fahimceni km zata yarda da au.. ."karka yi MB ka barta kawai kar Allah yasa ta amince  "no no !! baza'a yi haka ba ai ba saboda ita ba darajan sweetheart zata ci, kasan yadda ta damu kayi aure , hakuri kawai zakayi  a shawo kanta " ai bana sonta  MB , ta'ba kaji yadda qirjina yake bugawa ,km  yana bugawa ne duk akan yarinyar mafarkina tunda na fara mafarkinta ban sake samun natsuwar zuciyata ba burina na ganta na mallaketa " yayi mgnr yana furzar da iska tare da kamo hannun MB ya kai daidai saitin zuciyarsa dake beating very fast .

" ban taba jin soyayya ba irin wanda kake wa yarinyar nan " "wallahi ni kaina nakan zauna Ina wannan tunani MB ban taba gajiya da tunaninta ba daidai da second daya soyayyarta bata raguwa sai ma karuwa ya karasa maganar tare da yin shiru qirjinsa na dokawa da matsanacin karfin gaske".
maganganu masu sanyi MB ya dinga rarashinsa dashi har zuciyarsa ta dan yi sanyi a karshe yace "ka rage tsanar yarinyar nan ATA saboda baka da hujja tsanarta kabi umarnin mahaifiyarka kawai ku rabu Lafiya ita irin wannan tsanar idan ta juyi zuwa soyayya abun ba'a magana please aboki kabar komai a hannuna zan san abun yi ".
Chapter 18 · 0% Book details