← Book details Mar'adam's Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 100

Sashe 32

Mar'adam's Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty tayi shiru tana duban maryama yanayinta kamar kazar da'aka tsamo cikin ruwa gaba daya alamu sun nuna gajiya a tattare daita amman dan karfin halin irin nata take boye mata damuwarta , hawayen da suka cicciko acikin kwarnin idanunta tayi qoqarin maidawa tana danne damuwarta saboda farinciki diyarta ."
ahankali ta dauke kwayar idanunta aKan tilon diyarta zuwa wani bangare dabam tana tunanin rayuwa da abubuwan da sukai ta faruwa daita ta sha wahala arayuwarta shiyasa batason maryama ta sha wahala irin wanda ta sha ,wannan aikin da aunty salma kesata yana matukar ta'ba zuciyarta domin ko ita da tayi sanadiyyar zuwanta duniya bata sakata aiki haka koda tace zatayi ma bata yarda ta bar mata tayi ita kadai sai dai suyi a tare amman bata da yadda zatayi da rayuwata dan bazata iya hanawa ba "tabbas bata da yadda zatayi kuma bata isa ta hanata ba tunda zaman gidan ya zame mata dole dan bata son rasa yaranta kuma bata son ta koma ga danginta ." tayi maganar a kasan ranta .

maryama ta kalli mahaifiyarta duk da bata san me ya canza yanayinta ba amman tasan meke yawo acikin kwakwaluwarta ta matsota sosai tana jijiga Aunty wacce tayi nisa cikin tunanin rayuwa "meke damunki Aunty ?firgigib ta dawo haiyacinta tana dubanta duba mai tattare da damuwa tana cewa " babu abinda Ke damuna princess " ta fad'a tana mai jin tausayinta domin dai duk halin da suka tsinci kansu aciki itace sila, itace silar janyowa ya'yanta rayuwar wahala wacce bata kamacesu ba duk wani abu daya faru da ya'yanta itace ta janyo masu adalilin zunzurutun Kaunar data nunawa mahaifinsu ya janyo mata rasa komai domin ta zabi
Mahaifinsu ta bar danginta wanda yasa kowa acikin danginta yaji babu dadi akanta."

"me yasa kowa ya tsanemu acikin gidan nan ?" bayan mahaifinmu da granny da umma da abba babu mai qaunarmu acikin gidan nan gashi abba ya rasu ya barmu kamar yadda mahaifinmu ya barmu why Aunty ?me yasa basa qaunarmu ? "Me yasa suka tsanemu ko kin yi masu wani laifi ne ?ina son nasan abinda ya kawo wannan kiyayyar ?shiru kawai Aunty tayi tana dubanta dan bata da abinda zata fad'a mata domin kare kanta maryama yarinya ce da bata wuce shekara ashirin a duniya ba but she's smart in ance smart ana nufin mutun wanda ya kasance mai tsananin hankalin da kwakwaluwa tare da kaifin baseera sannan yarinya ce mai fadar gsky komai d'acinta zata fad'a she's very shap akan komai dan wani lokaci har mamaki take bata idan tayi wani abu kanta naja sosai fiyye da yadda take tunanin tasan muddin taji ta zabi mahaifinta ne akan iyayenta yasa dangita suka juya mata baya tabbas zata fad'a mata gskyr data kasa amsa daga ahlinta "Ina danginki suke Aunty ?ta jeho mata tambayar data nemi bugar mata da zuciya tana mai d'aura kanta a saman cinyarta ."

tsura mata ido tayi tana kallonta kafin daga bisani tace "suna nan ! "suna nan amman me yasa bakya zuwa inda suke kamar yadda Aunty salma keyi ?"babu komai "ta bata amsa atakaice tana jin wani tuttukin bakinciki acikin ranta mai tattare da damuwa "Aunty karki ce babu komai lallai akwai dalili akwai abinda yasa bakya son zuwa inda suke har yasa bamu sansu ba ,mahaifiya mahaifi yan'uwa duk ba abun wasa bane domin suna da matukar mahimanci arayuwar mutun ."

Naunayen ajiyar zuciya aunty ta sauke tana sake tsura mata ido "dan baki san abinda suka aikata gareni bane maryama shiyasa zaki fadi haka ta fad'a hk a zuciyarta " ahlinki suna da matukar mahimanci sannan suna da hakki akanki most especially iyaye yana da kyau a dinga basu hakinsu domin hakan zai samarwa mai yi kwanciyar hankali ,meye acikin duniyar da babu albarka iyaye acikinta ?yadda kike iya hakurin rashin zuwa ga iyayenki bazan iya barinki daidai da second daya batare dana daura kwayar idanuna akanki ba saboda qaunar da nake miki ina sonki aunty fiyye da komai dake cikin duniyar nan dan haka Kiyi qoqarin kije garesu nasan suma zuciyoyinsu na cike da kewarki da qaunarki tunda kika haifeni na girma na kai wannan shekarun ban ta'ba ganin ranar da kika shirya kika ce zakije ga ahlinki ba , kullum muna cikin dangin dady cikin kaskanci da wulakanci ya kamata ko sau daya ne muje domin nima ina son ganinsu ina son ganin danginki zaki je ga ahlinki ? tayi mata tmbyr tana mai tsura mata kyawawan idanunta masu matukar kyau ."

Kusan minti goma aunty bata amsa mata ba har sai data sake maimaita abinda ta fad'a sannan tace "to maryama zanyi qoqarin zuwa." ta fadi hakan ne ba dan zata aikata hakan ba sai dan abar maganar ta wuce "da gaske kike Aunty zaki ga ahlinki ? murmushi tayi mata domin bata son damuwarta dan ta fahimci yau din nan tana cikin damuwa ."

maryama ta rungumeta tsam tsam ajikinta tana mai jin dadi "naji matukar dadi Aunty ina son ganin ahlinki nasan habib ma zai ji dadi yaushe zamu je ? ta fad'a tana zare jikinta daga na Aunty yayinda idanunta Ke kallonta aunty tai shiru tana dubanta hakan nan ta tsinci kanta cikin farinciki wanda tasan maryama ce sila tana matukar son farincikin yaranta murmushinsu murmushinta ne haka zalika damuwarsu damuwarta ce tana matukar qaunarsu fiyye da komai dake cikin duniyar nan dan sune iyayenta yayyaenta kannenta komai nata daman tasha yin addua ko a can baya Allah ya bata ya'ya masu albarka wadan da zasu maye mata gurbin yan'uwa."

"aunty !
Ta kira sunanta cikin sanyayyar muryarta mai tsananin kashe jiki a duk sanda tayi mata magana da wannan muryar tana tuno mata da mahaifinta ko habib da ya kasance nmj bai dauko sanyin muryar mahaifinsu ba sai ita "na'am my princess ta amsa tana dubanta tana saurararta "a ina danginki suke zaune ?"tayi mata tmbyr fuskarta na nuna farinciki."

"suna zaune acikin garin nan" "cikin garin nan ? maryama ta maimaita abinda mahaifiyarta ta fad'a cike da mamaki Aunty ta gyada mata kai alamun" Eh!wani sabon mamaki ya sake cunkushe zuciyar maryama "suna zaune a gari daya amman duk tsawon wannan shekaru bata taba zuwa dasu inda suke ba bare su sansu gashi ta zauna tana rayuwa cikin kunci da babu tamkar wacce bata da kowa acikin duniyar nan ,numfashi ta janyo da kyar ta fesar a hankali kafin ta bude bakinta da kyar "yaushe zamu je wurinsu ?".

"karki damu sarauniyata in sha allahu zamu " cike da farinciki maryama ta kai hannunta ta dauki remut tana mai kunna tv tare da maida hankalinta Kan program din daake yi a tashar galaxy tv tana mai jin farinciki da natsuwar zuciya "Aunty zan so naji ranar da zamu na soma lissafa kwanaki "canza fuska tayi batare datai auni ba kafin daga bisani ta kawar da kanta gefe dan karta fahimci damuwarta dan gbdy ta soma neman natsuwarta ta rasa bazata iya zuwa garesu ba ,haka zalika ya'yanta ma bazasuje ga danginta ba most especially mahaifiyarta ta barsu har abada kamar yadda suka barta zata karasa rayuwarta a haka cikin kunci ."

a qalla sun dauki mintuna goma zaune suna duban tv babu wanda ya sake yunkurin cewa komai
Kafin ahankali cikin sanyi jiki maryama ta mike daga kwanciyar da tai akan cinyar mahaifiyarta ."Aunty lokacin sallah yayi bari naje nayi sallah gashi ina son na danyi zane kafin na kwanata ga bacci da nake jin yana fixgata tamkar zan fadi ni zan shiga ciki sai da safe dan gabadaya yau ko gurin umma bazan shiga ba idan sakina ta shigo kice mata na shiga bacci dan bazan sake fitowa ba allah ya bamu alkhairi ."tana gama fadar haka ta juya ."

har tayi taku biyu Aunty ta dakatar daita ta hanyar kiran sunanta "princess!
Ta dan tsaya tare da waigowa "abinci fa ? maryama ta dan yatsina face dinta tana ciza gefen lips dinta sannan ta girgiza mata kai alamun "a'a ! "to amman karatun jarabawa ya kamata kiyi ba zane ba ko gobe baku da exam ne ? muna da shi zanyi karatu sannan na d'an yi zanen sai na kwanta " "kiyi karatu da kyau maryama Kinsan a final year kike, ni da son samuna ne da kin bar zanen nan har sai kin gama karatu " karki ji komai Aunty duk zan iya Kiyi min addua da fatan samun nasara ."

Aunty ta sauke numfashi tana cewa "allah ya bada saa yayiwa rayuwarki albarka "Ameen sai da safe "
"okay to shikenan allah ya bamu alkhairi "Ameen ! ta sake juyawa tana rausaya tamkar zata karye dan rashin jikin da Allah ya bata , har sai da Aunty taga ta shiga cikin d'akinta sannan ta dauke idanunta daga kallon bayanta ."

Tana shiga dakin bayi ta shiga tayi wanka hade da dauro alwala ta fito cikin sanyi jiki tana goge gashin kanta da towel tana goge jiki tana mamakin abinda yasa mahaifiyarta bata son zuwa ga danginta alhalin suna gari daya ,"me yasa haka? " zata so tasan dalilin dayasa bata son zuwa garesu da wannan tunanin ta saka doguwar rigar bacci fara sol har kasa ta qarasa inda take ajiye sallaya ta dauka ta shimfida ta kai hannunta ta dauki zumbulelen hijab dinta ta saka ta kalli gabas a natse ta tada sallah ."

byn ta idar ta mike ta cire hijab ta ajiye a gefen gadonta ta zauna akan kujera kwaya daya dake dakin wanda gabansa dan qaramin table ne mai dauke da tarin textbook da fararen takardu na zanenta ta janyo textbok daya daga ciki sannan ta zaro farar takarda kwaya daya ta ajiye a gabanta ta soma karatu tana joting kusan mintuna talatin sannan ta rufe ta maidashi inda yake ta sake zaro wata takarda ta ciro pencil da kayan aikinta ta fara zane wanda ya kasance abinci ruhinta a duk lokacin da zaka ga maryama a natse zaka ganta kuma akan aiki idan bata makaranta boko tana islamiyya idan bata islamiyya tana Kan aikinta na Architect wanda dashi take samu take taimakawa mahaifiyarta batayi karatu akanshi ba kawai baiwa ce daga allah ya bata babu abinda bata iya zanawa tun tana qarama take Zane dashi ta girma ."
Chapter 32 · 0% Book details