← Book details Mar'adam's Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 100

Sashe 2

Mar'adam's Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da misalin karfe biyar na yammacin ranar laraba "Yammata ne su hud'u zaune a cikin wata hadaddiyar mota kirar land cruiser prador ,mutun biyu zaune a gidan bayan ,yayinda biyu ke zaune a gaba akan titi masha dake surelere , humaira dake kusa da mubina ta Ciro wayarta iPhone 12 Pro max acikin jakarta ta soma d'aukarsu snap tana ta'ba kafad'ar mubina dake driving dan ta shigo cikinsu ,mubina tayi murmushi ta dan shigar da fuskarta tare da d'aga yatsunta biyu kana ta maida hankalinta kan tuki ."
tafiyar mintuna ce ta kawosu Apapa  gra suka tsaya a gaban wani makeken get da aka rubuta ABDULLAHI ESTATE  tare da yin hon ,daya daga cikin masu gadin estate din  ya leko adaidai lokacin da mubina tayi  kasa da glass din motar ganin yaran estate din ne ya koma da sauri ya bude .mubina ta danna hancin motarta ta shiga Katafaren  estate din nansu mai d'auke da gidaje  fiye da ashirin  sama da kasa    sai dai acikin gidajen akwai guda daya wanda ya bambamta dana saura wato gidan hjy zulaiheart ."

yanayin gidanta ya bambamta dana saura ne sakamakon marigayin mijinta yafi sauran yanuwansa tarin dukiya kuma ko bayan mutuwarsa yaranta sun cigaba da qawata mata gidanta kullum cikin gyara yake da canza kayan ado na zamani , 'yan aiki  ma sun bambamta dana saura ,yan aiki guda goma sha biyar ne ke  zariyar kula da kowoni bangare na gidanta ,sannan kowannensu sanye da fararen kaya masu ratsin baki .
babu mutun ko daya na cikin ahlin estate din dake tsaye akan kafafunsa domin yin aiki sai dai dan aiwatar da ibada , kowa acikin gidan dan gata ne hatta bakin dake zuwa gidan jin kansu suke tamkar ya'yan wasu saboda mutuntaka na mutanen gida, tsarin gidan hjy zulaiheart   kuwa  kace a gidan turawa ne kowani bangare shirye yaki da kayan alatun na more rayuwar duniya ,haka ma kofar da zata shigar da mutun bangaren hjy zulaiheart  tsare yake da securities guda biyu masu duba jikin mutane koda zaa shigo da wani abun cutarwa .

mubina ta dauki hanyar inda aka tanada domin paka motocin bangaren gidan hjy zulai nan take sauran yanuwanta kuma kawayenta suka hada baki gurin cewa "ya haka kuma ?"Sai data dan marairace fuska sannan tace "dan allah mun dan shiga muga su marsi   kwana biyu bamuga juna ba daga nan ma  sai mu tsaya muyi  sallar magrib da ishai sai kowace ta kama gabanta dake duk suna shiri da juna yasa babu wacce tayi mata mutsu har tayi parking tare suka firfito daga cikin motar suka nufi  hanyar gidan hjy zulaiheart  ,babu wacce ta jira ayi checking  din jikinta ko mata iso shiga ciki kasancewar nan din ma gida ne a wurinsu tunda bangaren danuwan mahaifansu  ne .
sallamarsu maryam da nana hauwa'u suka ji suka mike cike da farinciki suka rungume juna suna wa juna barka da zuwa sannan suka zube akan royal chair's suna tambayar hajiya zulaiheart  "mami tana ciki tana amsa  waya maryam   ta basu amsa zamansu ko cikakken minti biyar basu yi ba sai ga mutun uku cikin masu aikin gidan kowacce sanye da farin kaya da ratsin baki hannunsu rike da tire , tiren na farko lemu da ruwa ne ,sauran biyu din kuwa duk kayan motsa baki danginsu snacks da dambu naman rago , suka gaishesu cike da girma mawa ,suna gama ajiyewa baki abin motsa baki suka Kara gaba suka koma bakin aikinsu .."

"Daga ina haka dan naga alamun kamar fita kukayi ?
"eh ! fita mukai muje birthday din wata abokiyarmu da muka qare karatu tare ne , dawowar mu kenan nace mu shigo kwana biyu bamu ga juna ba inji cewar mubina "ai kuwa mun gode muma kuna ranmu ,wallahi kullum sai nayi maganarku inji cewar maryam , nuzla taí saurin cewa "babu wani maganrmu da Kikeyi ga baki ga hanci amman zuwa ya gagreku kullum kuna gida kunshe kuna faman posting a social media ."
"wannan kuma da sister kike ba dani ba nana hauwa'u ta fada tana murmushi tana kallon maryam , maryam ta kai mata duka ta kauce da sauri tana sake murmushi tana cewa "ai sister daana daura kashi to wallahi data daura nata nifa idan tanayin wani abu har takaici take bani ahankali suke hirar yaushe gamo duk da suna cikin wuri daya amman sukan dauki lokaci basu hadu ba kowa yana nashi wuri ."
Suna cikin hira idanun mubina ya sauka akan tangamemen hoton  mr ATA dake manne da bangon falon yana sanye cikin suit bakake fuskar nan tashi kmr Koda yaushe babu faraa amman hakan bai hana kyawunsa fitowa ba ." ta d'auki sama da mintuna  talatin tana kallonsa Yayinda sauran yan'uwanta suka cigaba da hirarsu, murmushi ne ya subuce akan fuskar mubina wanda bata san sanda tayisa ba , nana hauwa'u ta Kai hannu ta dafa kafadanta tana cewa "ya'akayi mubina kika tsare mana yaya da Ido ko dai ko dai ? a matukar firgice wacce aka kira da mubina ta waigo ta sauke idanunta akan nana hauwa'u tana sakar mata murmushi tare da sauke ajiyar zuciya "wallahi kamar kin sani yar'uwata tunda na taso babu abinda nake so kamar ya adam "inna lillahi kice dai saboda kiga hotonsa yasa kika matsa lallai sai mun fara shigowa nan?inji cewar diyana "kuyi hakuri wallahi yana cikin dalilin saboda na kwana biyu bangansa ba ko wulgarwasa fa ina jin ma kamar baya kasar ko ...."?

wannan furucin da tayi yasa gbdy yan'uwanta suka maida hankalinsu kanta cike da tausayawa  , nana hauwa'u ta dinga kallonta cike da matsanacin mamaki dan tasan mubina da tsatsanin kunya uwa Uba aji dan ta sha ganin yadda takewa samari wulakanci, samari ma yayan masu arziki amman bata da lokacinsu "wallahi nana hauwa'u da gaske Ina son ya adam so Kuma me tsanani da Ina da tabbacin zai aureni da zan ajiye komai na furta masa Ina son shi saboda son da nake masa bana wasa bane, maryam dake zaune kusa da nana hauwa'u tayi murnushi kana tace "zai soki mana amman sai kinyi kmr kina kiyi gsky ,dan wallahi kallon fuskar shi ma abar tsoro ce kullum fuska a hade ga babu mgn mai dadi komai daga nonsense,rubbish, stupid girl ,crazy  girl ,Ke ni gbdy tsoro yake bani bana ko iya kallonsa. suka kwashe da wata  mahaukaciyar dariya suna cewa "shegiyar matsoraciya ,shine  dan iskanci kike bata kwarin gwaiwa taje yaci ubanta ?
"suka sake kwashe da wata dariyar "

Nan hirarsu ta koma ta mr ATA wasu na bawa mubina goyon baya ta fada masa zai amince tunda bai tsaida matar aure ba ,yayinda wasu na nuna mata illar hakan amman ita mubina ko uffan bata furta ba illa dai tana ji Kuma tana sauraronsu daya bayan daya, a natse maryam ta tsurawa mubina Ido "mubina idan kin tabbatar kina son shi shawarata ki cire tsoro dan nasan shi kike ji , ki furta masa in sha allahu zai amince Kuma zai soki tunda duk kin hada abubuwan da zaki sace zuciyar kowani nmj "Kai yar'uwata kina gani zai Soni kuwa ?why not ya Adam zai amince da sauri ma a wannan zamanin namiji ya samu macen dake sonsa kmr yadda kike son ya AD ai babu jiran da zai tsaya yi ,kefa sauraniya ce acikinmu karki ji komai na baki goyon baya dari bisa dari ki ........"
Kiran hjy zulaiheart ne ya katse maryam ta mike da sauri ta nufi d'akin mami ta barsu suna cigaba da tautaunawa byn wasu mintuna hjy zulai ta fito tana sakar musu murnushin jin dadi tana aiyana Ina ma Adam dinta zai daure ya zabi mata a cikinsu kamar yadda sauran yanuwasa sukayi gasu nan masha Allah dan kusan auren zumunci ake yi a family din amman dai zata gwada yi masa magana taga ko za'a yi sa'a ya amince ,suka hada baki suka gaisheta a mutunce ta amsa tana tambayarsu lafiyar iyayensu , anan suka qarasa yini  suna Hira daga wannan hirar zuwa wata hira sai dare suka kama gabansu ."

******
Bayan wata daya 

aka wayi gari akaga gawar mubina agdan qanwar mahafiyarta zainba an kasheta ta hanyar tsoka mata wuka a daidai saitin zuciyarta Kuma aka bar wukar ajikinta ba'a cire ba hankalin family's din abdullahi ya tashi matuka mahaifiyarta kuwa kuka da sambatu take tana cewa daga ziyara shikenan an kashe min 'ya daga ziyara fa ,daga ziyara fa!!  haka ta dinga furtawa har abun yaso zame mata kmr ta zautu saboda ita kadai gareta mace sauran ya'yanta duk maza ne ,sauran yanuwanta sunyi kuka kamar zasu bita lahira maryam kamkame da hannun mubina tana wani irin kuka me ban tausayi saboda akwai sabo me tsanani a tsakaninsu "waye yayi mana haka ?waye ya kashe mana yar'uwa ?an kasheta batare da burinta ya cika na auren ya AD ba sai lokacin mutanen gidan suka San da batun soyayyar da mubina ke yiwa AD batare da bata lokaci ba jamian tsoro suka shiga lamarin suka shiga d'aukar gawarta hoto yayinda daya daga cikin police Ke rike da farar takarda yana rubuce rubuce akan gawar byn sun gama sannan aka cire wukar aka soma kokarin shiryata zuwa makwancinta Inda har lokacin jini bai daina tsiyayya ba."
Chapter 2 · 0% Book details