← Book details Mar'adam's Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 100

Sashe 21

Mar'adam's Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Morning! ta fad'a atakaice tana hade rai
"Hope you had a great night? bansani ba kamar yayi murmushi amman ya maze yana cewa "sweetheart kamshin girkinki  so nice tare da kai hannu zai bude kular gabanta "don't open! shiru yayi tsaye shi bai ajiye murfin ba  shi bai rufe ba ya sake kokarin budewa "I said don't open "kullum aikin  kenan yabon girki amman ..." bai san sanda ya tamke fuska ba ya katseta da sauri "you're worst sweetheart ! naji muje parlour'n tunda ka hanani magana dan ban san abinda ya shigo da kai kitchen ba sai ka gama batawa mutun rai kazo kana salo" ya sake hade rai  sosai tamkar an aiko masa da sakon mutuwa "me nayi km ?"Bansani ba wallahi adamcy idan baka kiyayeni ba to tayi kwafa kawai bai sake cewa komai ba ya juya ya fita daga kitchen din ransa a matukar bace dan yasan akan abinda yayi jiya ne yasa tayi masa haka dining ya qarasa ya dauki cup din tea dinsa da chocolate cake yaci duk da shi din ba mai son zaki bane sosai bai jima ba mami ta shirya masa breakfast "your breakfast is ready "am okay ya fad'a ransa a hade  sannan  ya mike tsaye tun kafin tace wani abu ya fita zuwa haraban gidan ya nufi motar daya bada umarni yana son shiga Range Rover black color driver yajashi suka fita zuwa babban  office dinsa kai tsaye ."

*******

Yauma kamar jiya  maryam tana zaune akan kujerar mr ATA  tare da  saurayinta abbas ta tsura masa idanunta tana kallonsa tana kallon yadda yake  sauke numfashinsa ,muryarsa cike da kasala ya soma fadin "ina matukar  sonki maryam da'ace mutun ya Kan iya  shiga zuciyar mutun ya gani hakika da kin shiga tawa kinga irin zallar soyayyar da nake miki  amman ni nasan bakya sona maryam  kamar yadda nake miki wahalar da kaina kawai nakeyi ."
     "yaushe na furta maka  bana sonka abbas ?Ko na taba furta maka haka ?ta fad'a tana hade hannuwanta wuri daya tana kallonsa" tabbas da zata tsaida mijin aure cikin masu sonta da aure to data tsaida abbas domin kuwa yafi sauran dama dama kuma ya dan kwanta mata arai "yadda tayi shiru tana kallonsa haka shima yayi shiru yana kallonta yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa akanta "me yasa kayi  tunanin bana sonka abbas ?ta katse shirun dake tsakaninsu ta hanyar fadar haka ."abbas !ta kira sunansa ya tsura mata ido kawai "kamar yadda kake sona nima ina jin wani abu akan..."

"Shiiii !"shima ya katseta "sam ban yarda da abinda zaki fad'a ba maryam zuciyar dake son mutun bata banza dashi dan haka karki fad'a min cewar kina jin wani abu akaina dan bakyasona maryam , ban  ma ta'ba ganin soyayyata acikin kwayar idonki ba sau nawa zan kiraki sai kinga dama Kike dauka ?baki ta'ba tunanin ki kirani a duk tsawon lokacin da muka dauka koda kuwa zan shekara ban kiraki ba  , duk wata alama ta soyayya da mutun maryam bakya nuna min hakan kawai ya ishi ne hujja amman ni nasan tabbas ina sonki dan allah karki boye min abinda Ke ran..."

Wayarsa ta soma ringing wanda sanadiyyar hakan ya katseshi ahankali ya dan zame hannu shi ya ciro ya duba dan zabura yayi ganin mai kiransa maryam ta dago ido tana dubansa ya dauki wayar ,bata ji yace komai ba sai "to gani nan ya riko hannun maryam cikin nashi adaidai lokacin da mr ATA Ke qoqarin qarasowa gurin wanda wannan ne karo na farko da hakan ya faru "ki kulamin da kanki na samu wani kiran gaugawa ne amman zanzo dawo zuwa gobe mu qarasa maganarmu ina sonki mar..."giftawar mr ATA ya katseshi tayi saurin zare hannunta dake cikin nashi jikinta na daukar rawa ,abbas ya dan bi bayan mr ATA  da kallo sannan yayi mata sallama ya wuce ya bar zuciyarta cikin tashin hankali."

jiki a matukar sanyaye ta shige ciki yana zaune akan kujera kusa da mami sai dai kana kallon fuskarsa kasan yanayinsa babu alamun rahma bata tsaya ba ta nufi hanyar dakinsu mr ATA ya dago lumtsatsun idanunshi da suka canza kala wanda suka nuna tsantsar bacin ran da yake ciki ya zubawa mami sannan ya fara magana a natse sai dai mgnr tattare yake da 'bacin rai byn kmr mintuna goma  sai ga maryam tare da nana hauwa'u sun shigo daskarewa tayi agun zuciyarta na rawa ,kamar ta juya saboda rawar da jikinta yake sai Kuma ta sanyawa jikinta jarumta ta cigaba da tsayuwa tana sauraronsu ,
"wallahi da tasan yana parlour'n har lokacin bai tashi ba bazata dawo ba batare da bata lokaci ba ta fahimci maganae da  mami keyi akanta ne ."

cikin sanyi jiki ya mike tsaye ya soma taku da kyar fuskarsa har lokacin a murtuke take  ya jingina jikinsa da bangon parlour'n yayinda idanunshi ke kallon screen din wayarsa "wa yace ki sake zama
min akan kujera da wani gardin banza  har kuna taba juna dan ku din tattun yan iska ne ?tayi tsuru tsuru tana kallonsa  hantar cikinta na kad'awa da jin kalmar daya jefesu dashi "wannan shine first and last karki yarda ki sake zama min akan kujeru dan ba dan ke na tanadaisu ba koni sa'anki ne ?"tayi saurin girgiza masa Kai kamar ta durkusa ta bashi hakuri dan ya bar zuciyarta ta hutu sai ta daure taki aikata hakan "ban tanadi kujeruna dan wata gardiya da garden banza su zauna suyi iskanci akai  ba "adamcy ! no sweetheart bari na fad'a mata taji ko auta tayi min wannan ganganci sai na ballata wallahi bare wannan useless din ya fad'a yana nunata da babban d'an yatsa hannunsa" idan mutun ya sake min ganganci nima zan masa ganganci aikin banza kawai zuba masa ido kawai tayi tana jin wani zallar bacin rai na ratsata yayinda tuni hawaye ya soma bin kuncinta "yanzu irin mutumin daake son tayi rayuwa ta har abada kenan ? mutumin da  duk duniya babu abinda ya tsana  kamar ita  burinsa bai wuce ya wulakantata ya tozartata ba  lallai duk yadda zata gujewa wannan hadin zatayi koda kuwa zai zama sanadin rasa rayuwarta ne tun yanzu ma ya kamata tasan abun yi bazata iya ba ,zuciyarta bazata iya   daukar wannan wulakancin ba ta bud'e baki  da niyyar kare kanta kar mami ta dauka maganarsa gsky ce taga tuni har ya  wucewarsa yana jan dogon  tsaki ."

idanuwanta suka ciko da hawaye  cikin rawar murya ta soma "ma..mami wallahi abinda ya fad'a ba gsky ba.."kukan da take ya hanata qarasa maganar nana hauwa'u ta matso kusa daita tare da rike kafadunta
"da Allah meye abun kuka bayan kowa ya San halinsa muje please nana hauwa'u ta janyota suka koma cikin d'akinsu tana rarrashinta "Ina ganin lokacin barina gidan nan yayi zan koma Abuja da zama duk sanda yake gidan nan  bana samun sukuni"wallahi babu Inda zaki idan yayi miki ki daina nuna kina jin tsoro dan hkn da kike nunawa  power kike Qara masa idan yayi miki ki rama duka shekara nawa ya bawa mutune duka fa 9 ne ..?" "naunayen ajiyar zuciya ta sauke "bazan iya daukar shawararki ba sister "manta da wannan maganar yanzu dai ya kuka kare da abbas  ?wallahi ya bani tausayi gbdy na kasa fad'a  masa gskiya sbd ina dan jin wani abu akansa "kenan kina son shi  ?
Ta girgiza mata kai alamun a'a "ina jin wani abu akansa baya nufin ina son shi bane "tunda bakya son ya Adam shi me yasa bazaki bashi dama ba ?"

shiru tayi taki cewa komai "heeeee maryam kiyiwa kanki karatun ta natsu yanzu maza wahala suke karki ga wai iyayenmu nada arzki irinmu wahalar auruwa muke amman Kya kare a auren ya Adam din tunda baki da wanda kike so tana gama fad'ar haka ta d'auki wayarta ta shiga yanar gizo "kisa akawo mana abinci yunwa nake ji sosai ,abincin na fita ci wannan mai dacin zuciyar ya bata min rai " da idanu Maryam ta bita tana jinjina Kai ta d'auki waya ta kira layin kitchen ta bada umarni .
ko cikakken minti biyar ba'a yi ba mutun biyu suka shigo cike da girmamawa suka ajiye tiren abinci da lemun irin wanda suke sha suka juya nana hauwa'u ta bud'e kula ta zuba abinci ta soma cin mrym tana dubanta ."kici abinci mana kin tsaya tunani "jiki a sanyaye mrym ta soma tsukura tana ci tana fargaban sake haduwa da ATA  gara tayi ta gudu tun sakon rashin amincewa aurensa ya Isa kunnensa ya sake  damarar cin kaniyarta koma asani ne tsanar ya qaru"?
Chapter 21 · 0% Book details