Sashe 40
Mar'adam's Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani dogon ajiyar zuciya umma ta sauke cikin fargaba ta tashi zata wuce har ta juya maryama tayi saurin riko hannunta cikin nata "umma ! ta kira sunanta muryarta na rawa cak umma ta tsaya tare da juyowa fuskarta da tausayawa itama maryama mikewa tayi cikin tsananin tashi hanakali ta rusuna kasa ta daura hannuwanta a saman kafafun umma cikin raunin murya ta fara mgn Kmr zatayi kuka "umma nasan Kinsan komai daya faru da iyayena dan allah karki boye min gskyr dana sanki daita "
umma ta zare hannuta ta sake juyawa "umma Kodai mu din bata hanyar sunah aka haifemu bane ?"
Umma ta juyo da sauri tana dubanta qirjinta na dokawa da karfin gaske "maryama ta gyada mata kai kana ta cigaba da mgn "duk yadda muke da aunty duk shakuwarmu da soyyyar da take nuna mana ta kasa fad'a mana haka kema gashi umma zaki wuce ki barni byn kece kika bukaci kisan damuwata .
"Nasan kinsan komai daya faru ki fada min mu san matsayinmu wata killa ma shine dalilin da yasa muke ganin tasko acikin gidan nan dan girman allah umma karki boye min abinda yafi komai mahimmanci arayuwarmu ki fad'a min na rabu da nauyin dake daskare da qirjina ta qarasa mgnr cike da sheshekar kuka ."
Girgiza kai umma ta shiga yi ta dawo inda take tsaye ta kamota ta zaunar daita akan kujera tana kallonta cike da tausayawa kusan mintuna ashirin sannna ta numfasa tana cewa "ku din ba shegu bane ku din yan halak ne" naunayen ajiyar zuciya maryama ta sauke tana kamo hannu umma cikin nata "kinsan kowani d'an adam da yadda yake kar'bar gaddararsa . wasu mutane basa gane rayuwa duk yadda allah ya rubutawa bawa babu wanda ya isa ya canza maka ita,ita qaddara kuma tana fadawa bawa daidai da yadda allah ya hukunto masa qaddara bata san talaka ba bata san mai kudi ba ,qaddara ce da rabonku ta nisanta mahaifiyarku da yan'uwanta yan'uwanta sun kasa kar'ban qaddarar data fad'a mata amatsayin su na muslimai amman mgn ta gsky ku din yan halak ne sai dai akwai yan'uwanki da'aka samesu bata hanyar aure ba .."
nan take jikin maryama ya kama rawa tmkr mazari ta tsaya tana kallonta tana assessing maganarta umma ta damke mata hannu gam cikin nata tana kallonta tana jin yadda jikinta Ke rawa tamkr mazari , maryama tayi imani bancin a zaune take da ta tabbatarwa kanta kafafuwanta bazasu iya d'aukar ba, da zuwa yanzu ta zube kasa."cikin kyarrrma wasu hawaye masu zafi suka shiga turereniyar zubo mata tana jin wani zafi a qirjinta mara misaltuwa cikin ikon allah allah ya bata ikon furta kalmar "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun shi tayita furtawa tana maimaitawa still jikinta da zuciyarta na rawa ."
Umma ta kalleta cikin sarewa ta cigaba da magana "wannan qaddara ce maryama km kowani bawa da tashi irin kalar qaddarar bata wuce Kan kowa ba , ki godewa allah da yasa ta hanyar aure aka sameku bilkisu na bani tausayi matuka kullum idan na kalleta sai na zubar mata da hawaye , da gatanta da komai tana rayuwa tmkr bata da kowa ,tana rayuwa cikin kaskanci alhalin bata cancanci haka ba tunda taji an samu wasu babu aure taji komai ya tsaya mata cak hatta shi karan kanshi labarin taji ya fita kanta ."
Mahaifiyarki haifaffiyar wannan gari ce anan aka haifeta aka haifi iyayenta ke hatta kakaninta ana aka haifesu sune asalin yan kasa "Idan mutun ya shigo jahar lagos din nan ya tmbyi family's din alhj rafi'u giwa to babu wanda bai san mahaifinta ba ."mahaifinta ko nace dangin mahaifiyarki gbdy masu arziki ne ."mahaifinta alhj rafi'u giwa yana da mata hud'u kinga kenan suna da yan uba a qalla guda talatin sai dai bazan iya kawo miki sunansu ba ina dai jin Aisha , hauwa wacce suke kira da jiddah abakinta gbdy a gidansu bilkisu ce auta a mata sai kannenta biyu maza dake binta daga kanta mahaifiyarta bata sake haihuwar mace ba haka ma sauran bangaren matan sun daina haihuwa wanda hakan yayi sanadiyar da soyayya mai karfi ya shiga tsakaninta da mahaifinta da yan'uwanta gbdy kowa yana sonta kasancewarta auta a mata "
gabadaya yan'uwan bilkisu masu kudi suka aura daga wanda yake london sai wanda yake Canadá ko American ,mafi yawa daga cikin yan'uwanta suna wata kasa daga maza har mata idan kuma anan ne zaki iske su cikin VI ita kadai ce ta auri talaka marashi ,dan gbdy asalin mahaifinki talakawa ne idan aka cire abban sadam wanda yake da d'an rufin asiri dan yana da gidan bread da kowa ya dogara dashi amman basu da komai ."
"bilkisu ta taso cikin gata da soyayya da kulawar iyaye tun daga tasowarta har zuwa girmanta duk abinda take so shi takeyi ta taso cikin soyayyar iyaye dana yan'uwa kowa yana sonta sannan ta taso da farinjin samari acikin family's dinsu kasancewarta kyakkyawa hasalima kyawun jikinta kika d'auko fuskarki ce ta mahaifinki amman km shi din ma baki dauko farinsa ba dan shi fari ne sol tmkr bature kmr yadda kike ganinsa a hoto ." kowa na sonta da nuna mata soyayya ,acikin masoyanta akwai mubarak dake mutuwar sonta, mubarak cousing dinta ne da ubansa da uwarta uwa daya uba daya kuma shima mahaifinsa mai kudin gaske ne km shi kadai suka haifa ,bilkisu na da shekara shabiyar a duniya alokacin tana ss 1 a secondary school alokacin mahaifiyarta da mahaifin mubarak sukai alkwarin aure a tsakanin yaransu dan mubarak din zai yi tafiya zuwa american qaro karatu , sun bar mgnr atsakaninsu idan ta gama karatunta na secondary sai ayi musu aure ."
mahaifinki ussein adam shima asalin haifaffen garin nan ne haka iyayensa sun kasance su takwas ne a wajen iyayensu mata hud'u maza hud'u umar ,fatima ,gali saadatu ,nazifi fadeela Kmr yadda kikasani , hassana da ussein ne auta ."
yana da shekara ashirin da takwas a duniya ya fara aiki a gidansu bilkisu ta sanadiyyar abokin abban sadam abdulwahab wanda shi gadi yake a makotansu ." mahaifinki ussein ya kasance direban ne gidansu bilkisu wanda Ke kaita school , idan lokacin tashi yayi ya koma ya d'aukota duk inda zata shike kaita hussein ya kasance mutun ne mai tsananin kirki gashi kyakkyawa aji farko illarsa dai shi din ya kasance talaka ne mai son jin dadi arayuwarsa km yana harka da yammata da shaye shaye sai dai bai ta'ba barin gidansu bilkisu sun san da zaman wannan halin nashi ba a boye yake yi saboda tsira da aikinsa ."
Maryama ta runtse idanunta tana jin wani tuttukin bakinciki a zuciyarta. ta d'aura kanta akan cinyar umma ko zata samu sausaucin zugin da zuciyarta take ,dan tun baaje koina ba ta fara datasanin jin labarin iyayenta , mahaifinta manemin mata ne ga shaye shaye a iyan nan ma kad'ai ta raina kanta ta sake yarda su din marasa gata ne ."
" tun farkon ganin bilkisu da ussein taji ya burgeta daman shi Allah yayi masa farinjin mata dan atarihinsa bai ta'ba cewa yana son mace ba dan har prouding yake , wannan yasa ya qara samun kusanci daita sosai , duk abinda taci sai ta rage masa idan zai kaita school ta bashi tun abun yana bashi mamaki har yazo ya daina bashi mamaki ya ajiye abun amatsayin ita din mai alkhairi ce , shima kma yana kulawa daita sosai dan hatta murfin mota kafin ta fito ya fito ya bude mata sannan idan sun iske an gama assembly zai tabbatar da ta shiga class akan idanunshi sannan zai juya ya koma gida ,ga iya bada labari, ussein ya iya bada labarin da zai saka mutun nishadi amman fa ga wanda yake da mahimanci a wajensa duk wannan yana cikin abinda yasa bilkisu ta sake sakewa dashi , shiyasa kullum bata da magana sai na fadar kirkinsa a wajen iyayenta wanda har hakan yasa iyayenta suke son batunsa tana sa ayi masa alkhairi na mussaman kullum da irin kyautar da take sa ayi masa ."
haka rayuwa tai ta tafiya mubarak na kiranta a waya amman sam bata bashi lokacinta yayinda wata irin shakuwa mai karfin gaske ta shiga tsakanin ussein da bilkisu lokacin da ta kai shekaru sha bakwai ta fahimci ba shakuwa bace kawai a tsakaninsu soyayya ce mai karfi wanda shima zuwa lokacin ya kamu da matsanancin soyayyarta ta yadda ya kasa hakuri sai daya zaunar dani ya fad'a min ciwon dake zuciyarsa yace zai yi qoqarin ya boye nashi domin itama bilkisu ya fahimci irin son da take masa bazai ta'ba barin wannan soyayya ya tabbata a tsananinsu ba domin dai yasan tafi karfinsa tafi karfin aurensa ita din ba sa'ar
aurensa bace babu ta yadda zai sameta arayuwarsa ."
"Nima na karfafa masa gwiwa ya danne abinda yake ji akan bilkisu na nuna masa bambamci dake tsakaninsu daita samun auren irinsu akwai wahala duk da babu yadda allah baya al'amarinsa shi yayi talaka kum shi yay mai kudi nace yayi addua sai allah ya kawo masa sauki da mafuta , amman alokacin ya sheida min zai ajiye aiki ya nemi wani still dai nice na hana na bashi kwarin gwiwa ya cigaba da aikinsa ya dai rage sakar mata fuska da kusanci daita ."
yana cikin wannan halin kwatsam bilkisu ta bayyana masa soyayyata da fari yaki amincewa hakan yasa ta shiga damuwa mai tsanani har rashin lfy ta kwanta batare da iyayena sun san akanshi take ciwon ba wanda ta kai har dakin daaka bashi a gidan take biyosa tana kukan ya amshi soyayyarta "ya zaunar daita ya fad'a mata gsky soyayya atsakaninsu ba abu ne mai yuwu wa ba duba da matsayinta da nashi , kuka take tana nuna masa babu wani bambamci a tsakaninsu dashi duk abu daya ne a wajen Allah da kalamai masu sanyaya zuciya da soyayya tasa ussein ya amince tunda daman shima yana sonta ranar daya amince aranar yan gidansu suka ga ikon allah domin dai bilkisu ta warke daga rashin lfy da take suka fara gudanar da soyayya ."