← Book details Kwankwason Jimina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 41

Sashe 6

Kwankwason Jimina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga can kofar corridor Kuma kitchen ne da karamin store dinsa aciki. Sai yar farfajiyar tsakar gidan su mai shuke shuke da wasu kujeru guda biyu tsofi ne na gidan da suka taso da wani dan teburi a tsakiyar su. Sai wajen ya hadu ya bada ma'ana sosai.

Daki daya daga ciki duake yake da gado da drawer harda mudubi. Nan ne yake a matsayin dakin bappah Auwalu da Mai dakin sa.

Sai daki Mai kallon sa Kuma na Ahmad ne yayan layla Wanda tsaran shekarun nasu ba yawa. Kasancewar dukkanin su Yara ne basu mallaki hankalin kansu ba. Hakan yasa bappah Auwalu Cewar dakin ya zama na Ahmad Amma yar katitar Layla na gefe sai ta runga kwana.

Mahboub yace yaci girma ya bar mata dakin. Shi zai rika fito da katifar sa parlor Yana kwanciya. Domin shi yafu kaunar parlorn ma acewar sa...

"Nawraah"

"Uhm.. Layla"

Kamo hannun Nawraah Layla tayi suka shiga parlorn suka zauna...

Kawu Auwalu yafuto daga kitchen daya shiga Shan ruwa Yana murmushin ganin su. Fuskar sa akan Dan uwan nasa yace,

"Junaidu ne? Ku karaso ku zazzauna mana"

Bappah junaidu ya durkusa har kasa Yana gayda yayan nasa. Bappah Auwalu ya amsa fuskar a sake

"Ka koma kan kujerar ka zauna Dan Allah. "

Daya bayan daya su nawrah suka shiga gayshe shi ciki harda mahaifiyar su data durkusa itama sosai cike da ladabi da biyayya ta gayshe da wan mijin nata.

Ya amsa musu fuska a sake duka...

"Layla Ina umman na ku?"

"Tana daki "..

"Je kice mata ga bappan ku nan sunzo da su nawrah kice ta taso su gaysa."

"Ah idan ta kwanta a kyale ta . Ma sake dawowa mu gaysa a tsanake inshaa Allah"Cewar malama Hindu.

"Aa ataso ta dai... Yanzun ta tashi daga nan anan na barsu dasu Layla.. jeki kirata ke"

Layla ta mike tana yamutsa yatsunta ta nufi dakin mahaifiyar tasu.

Ta Dan bubbuga kofar Kafin ta saka Kai ta shiga bakinta dauke da sallama,

Tana shiga ta tarar da ita akan gado tana zaune tana kallon kofar,

"Ummy bappah ne ke Kiran ki yace kizo su bappahn nawrah sunzo.."

"Naji ... Kema can daya Mai abun haushi sai kice Mai Kai na na ciwo haka ba sai an taso ni ba"

"Yo hakuri"

"Je ki"

Layla ta fita tana kakaro murmushi tace,

"Wai tana zuwa"

"Ko a kwance take ne na shiga na dubata?" Malama Hindu ta tambayar,

"Aa fa "

Fitowa tayi daga daki tana bude baki tamkar gonar auduga tache,

"Gajiya ce ta mamaye ne shine na Dan kwanta ko zan ji dama. Bappan su Ina wunin ku? "

"Dama nace ko jiki ne? Sannu ya kike ji yanzu?" Malama Hindu ta tambaye ta,

"Alhamdulillah naji dama sosai .."

"Sannu Allah yakara afuwa"
Cewar bappah junaidu

"Aamin bappan su "

Daya bayan daya su nawrah ma suka gayshe ta cike da ladabi Kai kace wasu sabbin baki ne daga wajen bayan dazu suka rabu amman saboda tsananin tarbiyya tun sanda suna yankin bunza ma haka suke gaisuwar safe da ta rana data dare daban cike da ladabi da dinbin biyayya...

Ki nunnuna musu yadda akayi jeren ko nusaiba? Cewar mijinta bappah Auwalu.

"To bappansu Mai zasu gani anan gidan. Amma dai muje. Nan din fa iya kasa ne bamu da sama" malama nusaiba ta fada tana mikewa tsaye

Basuyi mamakin kalamanta ba don ba ranar ta fara ba. Don haka malama Hindu tace,

"Haba bappah ai munsan gidan kamanta duk tare mukai komai? Ai ana tare muma komawa zamuyi mu Dan sake kikkintsa inda ya kamata"

"Yo ai dake musanman tunda ku gidan sama ne daku. Ga bene ko'ina fala fala babu matsatsi ba kanara Nan ba da dakuna biyu ne jalllin jal"

Malama Hindu batayi magana ba murmushi kawai tayi ta mike tana kamo hannun Amna autar ta.

Bappah auwalu kunya ta sake dabaibaye shi tamkar kasa ta tsage ya fada haka yake ji.

Cikin kakaro murmushi dayafi kuka ciwo yace,

"Junaidu kaga an zuba tumakin da Yan kajin fa mashaa Allah. Allah ya saka maka da alkhairi ya kara arziki. Nusiaba kin sake Masa godiya kuwa?"

Malama nusaiba tana soso kasan gashin ta ta cikin dankwali tace,

"Sosai ma. Mungode kwarai . Nan gaba ma kawak sai a bige a shigo da shi cikin nan gidan muma ya zama dakuna uku kamar su"

Bappah A. ya saka yatsa a baki ya ciza Takaici ya sake gauraye Masa wuya da ilahirin jikin sa baki daya ji yake tamkar ya hau nusaiba Mai dakinsa da bugun tsiya ya bude kofar Yana cewa,

"Muje ka gani junaidu... Allah dai ya bar zumunci ya saka maka da alkhairi"

"Aamin** suka amsa baki daya Banda nusaiba da ke tabe baki

Dan dakin abun kiwon sika nufa. Dauke da tumakin biyu da akuya daya sai kaji zasuyi goma.

"Kagani ko ? Wallahi kamar Dan su aka Gina shi komai da komai ya yi mashaa Allah"

"Gashi nan kam Allah yasa albarka Amin"

"Aamin Aamin"

"Laaa ga kwai Ina so..." Amnah ta fada Hadi da shiga cikin dakin ta dakko Kwan kajin har biyu.

"Jeki ajiye*

"A bar mata Mana ai na uwar ta ne" bappah Auwalu ya fada Yana wa nusiaba murmushi.

Ta kakaro murmushin yake tana cewa,

"Dauki mana Amnah... A soya Miki Kona dafa Miki kici kinji?"

"Nagode" Amnah ta fada da sauri tana gudu

"Sannu da miskri Allah ya bar zumunci ya kara arziki su zama garke" malama Hindu ta dubi malama nusaiba tana mata godyar kwai data bajwa Amnah

Daga nan kuma suka koma nasu gidan bayan sun musu sai da safe. ... Malama nusaiba tabu bayan su da kallo tana Mai tabe bakin ta ta koma cikin gidan nasu tana jera tsaki..

"Kul kika sake daukar abunda baa baki ba baa ce Miki gashi ba kinaji na ko?"

"Eh... Bazan sake ba ammeiy kiyi hakuri" Amnah ta bawa mahaifiyar tasu hakuri

"Ya wuce... A dafa Miki ko a soya? "

" A soya"

"Yauwa... To jeki parlor ki zauna kinji idan aka soya sai a kawo Miki"

Amnah ta koma parlor da sauri ta zauna akan kujera tanata murna. Malama Hindu ta nufi wajen kwanuka ta dauki wani Dan karamin mazubi ta fasa Kwan aciki

Kallo daya zakai nata kasan ita din mahaifiyar su nawrah ce duba tsananin kamar da suke yi da yaran nata duka. Duk kuwa da sun dauki kamannin mahaifin na su ma ciki harda tsawon sa da gashin hirar sa Zara Zara masha Allah...

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_

_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[2/17, 2:20 AM] Hafsaat🧕: *_KWANKWASON JIMINA!!_*
_(MAI WUYAR SHAFAWA)_
🦩🦯🦾

_✍️: MX_

*_ZAFAFA BIYAR 2024_*

_vip pages na arewa👇_
*_arewabooks:mssxoxo_*

*_paid page :09_*

______

  Muhammad Junaid hamidniyya shine cikakken asalin sunan mahaifin su Nawraah... Kuma shine 'da na karshe ga marigayiya yafendo. Haka zalika karamin kani ga su Bappah Auwalu.

Hindu Musa shine sunan mai dakin sa kuma mahaifiya ga su nawrah da sauran yan uwanta.

Hindu da Junaid yan uwane wanda ke karkashin inuwa daya ta zumunta. Kuma aka hada auren su auren zumunci wanda yayi dadi. Don shekaru da yawa kenan tunda aka yi hadin auren su gashi har sun Tara iyalin kansu. Baa taba jin fadan su ba ko cacar baki.

Auren su ya kasance Mai Dadi Mai tattare da sirri domin ko yaji Hindu Bata taba yi ba. Duk kuwa da kowanne aure ana samun sabani don tsakanin harshe da hakori ma ana sabawa don haka Koda sunyi fadan babu Wanda ke jin kansu ko da kuwa iyayen su. Su kan shirya kansu su sulhunta. Hakan yasa Ko a dangi ake kwatance da su idan zaa kulla auren zumunta ko idan ana jan kunnen sabbin ma'auratan akance da su suyi koyi da iyayen su Yakumbo Hindu da Bappah junaidu...

Da mahaifiyar Hindu Marigayiya Yagwalgwal Fatime Domin ita ta Dade da rasuwa tun ana goyan Nawraah, da Kuma  Marigayiya yafendo mahaifiyar junaidu yar wa da yar kani ce..

Don haka iyayen su Kanwa da Yaya ne wadanda iyayen su suka fito tsatso daya...

Kasancewar tsatson na su larabawa ne na yankin Lebanon gefe daya kuma suka hada zuri'ah Mai tarin yawa daga fulanin yankin bunza ta hangar auratayya. Hakan yasa zuriyar tasu ficewa gaba saboda tsananin kyawun su da dabi'unsu na nagarta. Masu dinbin tarin arzuka Kafin mahara su Kai wa yankin sumame suka kwakushe masu tattalin arzikin su cikin Kashi uku ba Kashi biyu...

Allah ya azurta Hindu Musa da Junaid hamidniyya da Yara Kadan masu tarin albarka,

Ashir shine babban Dan su, Sai mabiyin sa Ashfeef , Sai Kuma Nawrah sai autar su Amnah shikenan su hudu. .Maza biyu mata biyu

Hakika junaidu da Hindu sunyi wa yaran na su tarbiyya sosai da sanin yakamata Dan ko a yaran dangi ana yabon su saboda tsananin biyayyar su da sanin yakamata..

Suna kiran yan uwan iyayen nasu wasu da Bappah wasun su Abu kaza, idan bangaren mata ne sukan Kira su da yagwalgwal kaza ko yadukko, ko Maamaa tamkar yadda larabawa ke kiran iyayen su.
Chapter 6 · 0% Book details