← Book details Kwankwason Jimina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 41

Sashe 23

Kwankwason Jimina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummyn ta karba tana cusa ta a jakarta ta hannu ... Tana kambama jarumta irin ta Nawrah tun tana karama. Lalle idan ta girma za'ai mace mai kamar maza....

Nawrah ta futa daga gidan taje titi ta hau mota ta koma gidah. Yayinda malama Hindu ta koma cikin kitchen din duk abunda da suke ashe Dr bintu na hango su... Ba dai ta jiyo maganganun da suke..

Jikin malama Hindu na rawa ta shiga aikin data sakata ta dama kunun tazuba a flask

"Hajia na karasa"

"Hindu"

"Naam"

"I don't care da rantse rantsen da kike Amma Allah idan naji magana daya ta fita wallahi sai kinyi mamaki"

"Wace magana hajia nace ba abunda naji"

"Ni dai na gaya miki"

"Inshaa Allah hajia. Ni ba zamma Kara aikatau ba wallahi daga yau da yardar Allah, na tuba dan Allah kiyi hakuri ki gafarce ni" ta durkusa kasa tana hada hannuwan ta

"Shikenan jeki sai da safe"

Hindu ta mike dasauri jikinta na rawa ta zura takalman ma wari da wari ta saka..

Tana futa Alhaji Sambaso ya mike zai fita shima,

"No Alhaji please "

"Kin aminta da ita.. ba ita ce mai aikin su ba kafin tafiyar su waje"

"Dan Allah ka kyaleta nasan ba zata fada ba"

"Okay ni ba wajenta zani ba"

"But am...

"Nace miki ba wajenta zani ba. Refreshing brain na kawai zanyi zan dan fita yanzu ba nisa zanyi ba ita kuwa ai nasan ta hau mota ta tafi ma"

"Shikenan sai ka dawo"

Fita yayi wajen gidan ya dau motar sa ya fita daga cikin gidan a hankali yake tafiya yana hango malama Hindu tana tafe tana waiwaye tana tafiya atsorace...

Tunani dankare cikin kirjinta, wannan wace iriyar rayuwa ce haka? Dama zaman cin amana suke da su? Lalle duniya abar tsoro ce... Wayar dake gurin ta ce ta fara kara mai gidan ta ne wato bappah junaidu ta dauka muryarta na rawa ta saisaita kanta tace gata nan zata dake yanzu inshaa Allah...

Daman titin yayi dubu ba street lights sun mutu..Salati ta fara yi tana karanta la'ilaha illa anta subhanaka jnni kuntu minazzalimin..

Alhaji Sambaso ya kara gudu zuciyar sa na kuna,, wato har ta fara kiran waya tana fada kenan? ya tashi kanta tana komawa gefen bishiya ya hadata da bishiyar ta daga sama can ta fado kasa tim kamar ba mutum ba ..

Ya arce dagudu ya hau babban titi. Sai bayan yan mintina tukun sannan mutane sika taru tana numfashi dakyar,..aka lalubo waya ajikinta aka Kira number data amsa Kira karshe ta bappah junaid da nawrah tayi saying da abbiey ban da nan suka kira shi suka gaya masa hankalin da ake ciki.
.
Suka nufi gidan da ita wani mutumi ya temaka aka kaita kasancewar ummyn tanata magana da kyae kan akaita gidah

Ana kaita baki daya yaran sukai kanta sunata ife ife da adduoi. Daga na suma rankaya asibiti

Likitoci sukai kanta aka saka mata oxygen kasancewar numfashin ta ya fara sarkewa.

Likitocin sunata kokarin bata temako, Bayan wani lokaci, Likita on duty ya fito daga emergency ward yana zare facemask dinsa ya dubesu kansa a kasa .

Ashir ya karasa kusa dashi yana girgiza kafadar sa,

"Ya jikin ummyn wani abun ake bukata? Jini? Kudi? magani? Me kuke so?"

Likitan ya girgiza kansa bayan ya sauke katuwar bahaguwar zuciya yace,

"Sai dai muyi hakuri Allah ya mata rasuwa...babban dadin kuma ta cika da kalmar shahada Alhamdulillahi....

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_

_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

[3/1, 1:57 PM] Hafsaat🧕: _K'K'J_
_(M/W/S)_

_✍️:MX_

_26_

:::::::::
    *Dukkanin* su a tare ji da ganin su suka dauke na 'yan wasu daki'kai...

Ji ka ke timmmmmm... Bappah junaidu ya fadi wanwars a kasa sumamme ..

Likitan yayi kansa. Ashir ya shiga bubbuga kansa a bango... Yayinda Amnah ke duban su duka tana hawayen itama duk kuwa da karama ce ainun. Ashfeef ya rike hannun ta shima yana rera kukan sa ahankali

Nawraah ta sulale daga jikin bango ta yi zaman dab'as na yan bori...Ta saki marayan kuka mai tsuma zuciyar duk wanda ya saurara....

"Ummy.... Wayyo ALLAH na ummy" Ta shiga maimaitawa tana bubbuga hannuwanta a kasa.

Bappah Auwalu yana tsaye daga bakin kofar dakin bawa marasa lafiya na gaggawa temako inda aka shigar da Bappah junaidu da yayi doguwar suma suna bashi temako don ya farfado.

Nusaiba na gefe tana girgiza kai... Mutuwar Hindu kwarai matuka ta girgiza ta. Hawaye suka shiga zirarowa daga idanun ta ..

Su Layla suka karasa asibitin itada Ahmad... Ganin su suka yi cikin yanayi marar dadi...

Jikin su yayi sanyi. Layla ta karasa wajen Nawraah dake kuka sosai kamar ranta zai fita ta zauna a kusa da ita tana kallon ta,

"Nawraah..... Meya faru? Meya samu ummy? Operation ake ma ta? Ko ciwon ne ya kara tsamari?"

Nawraah ta girgiza mata kai tana zubar da hawaye. Ta saka hannun ta ta share hawayen tace da ita, cikin rawar murya,

"Ummy ta rasu"

"Inna Lillahi wa inna ilaihi raji'un... Ummyn?"

Fashewa tayi da kuka sosai itama ta saka tafukan hannuwan ta akan bakin ta. Ahmad ma ya fara hawayen yana girgiza kansa cikin dimaucewa,

Har tsakiyar dare Bappah Auwalu ya futa ya kawo musu burodi dakyar ya tsawatar musu suka sha da ruwa. Wasa wasa har akayi asubah sukaci sauran burodin...

Wata nurse ta futo daga ciki tana duban su... Kowanne cikin tashin hankali. Bappah Auwalu ne kawai yake kokartawa yana kukan zuciya,

Ta karasa kusa da shi tana masa sallama. Ya amsa ta yana sharce hancin sa da hankici,

"Mashaa Allah an samu ya farfado mun masa allura saboda ya samu nutsuwa . Ita kuma marigayiya idan akwai motar da zaa sakata aciki to idan babu munada kurkura mota ta haya sai a sakata aciki, dubu biyar ne kudin kaiwa"

Ya kada kai yana sanya hannu acikin aljihu zai zaro kudin Nusaiba dake gefe tana duban su ta karasa da sauri,

"Menene ?"

"Kudin motar da za'a saka Hindu aciki ne zan biya meya faru?"

"Har nawane kudin?"

"Menene haka sai? Dubu biyar ne mana "

"Yanzu dubu biyar din zaka kwasa ka bayar?"

"Bakida hankali Nusaiba wallahi bakida hankali "

"To ai gaskia ne. Shi ya bayar mana.... Dubu biyar dinnan idan ka kwasa ka bayar ya zamuyi da sayen taliyar...?"

Dogon tsaki yayi ya girgiza kai cike da takaicin maganganun ta yace,

"Zaki matsa ko sai na hanbare ki?"

"Hanbareni halin naka zaka nuna a bainar jamaa hanbare ni Auwalu"

Kudin ya kirga da sauri ya mikawa nurse din ta koma ciki.

Ya bar Nusaiba a tsaye tanata banbamin mita. Ya nufi wajen Ashir ya riko shi

Ashir din ya fashe da kuka. Bappah Auwalu ya riko shi ya rungume shi tsam a jikinsa

Ashir ya shiga rusgar kuka tamkar karamun yaro yana kiran sunan mahaifiyar ta su

"Ummy... Ummy"

"Dan Allah ku dai na mata kuka, ku dai na zubar mata da hawaye. Addua take bukata yanzu ba zubar hawayen ku ba. Soyayyar kadai da zaku nuna mata yanzu addua ce. Sai tafi bukatar ta. Kuyi hakuri dan Allah. Uhm munyi rashi kam . Allah ya gafartawa Hindu ya kyautata namu zuwan. Bar kuka Ashir dan Allah kaji? Alhamdulillah jikin mahaifin naku ma ya farfado yanzu nurse ta fada. Kuma zamu kai gawar gidah don a sallace ta.,"

"Wayyo Allah na. Ummy na wayyo Allah " Nawraah ta shiga nanatawa tana cigaba da hawaye.

Bappah Auwalu ya shiga wajen da aka rufe gawar malama Hindu da wani yadi shudi baki daya ya rib'e ya koma kalar jini. Saboda tsananin jinin dake futa daga jikinta har yanzu. Tun sanda aka kawo ta. Daman bayan likitocin sun yi gwaje gwajen su angani ta samo karaya takwas. Hudu a kwibi. Biyu kafafun ta daya hannun ta. Yayinda dayan Kuma gefen wuyan ta. Sai internal bleeding shima data samu. Sai Kuma jini daya taru a kwakwalwar ta. Sai ciwo a gefen goshin ta da aka mata dinki har zuwa lebenta. Domin fuskar ta ma ta rabe gidah biyu. Da sauran ciwuka Wanda ba zasu kirgu ba don da tayi rai ma ba lalle ta cigaba da moruwa ba, kasancewar spinal cord dinta ma ya tsinke.

Bappah Auwalu ya saka hannu ya toshe bakin sa da tafin hannunsa alokacin daya shiga dakin yaga an lullube Hindu har kanta. Dankwalin data saka a kanta shi aka rufe fuskar ta. Tabbas kayan data saka ne dazu da ta je gayshe su.

Kwakwalwar sa ta shiga tariyo masa ashe dama bankwana take musu na tafiya tamkar wasiyya? . .

Wani siririn hawaye ya silalo masa ya sharce da bayan hannunsa sa.

Tsayawa yayi aka gama cike ciken da zaai na takardu kasancewar irin wannan idan aka kawo marasa lafiya ranga ranga haka magashiyan, To police na shiga cikin case din.

Don haka anyi dikkanin abunda ya dache daga karshe maaikatan suka Kai gawar malama Hindu cikin mota yar kurkura aka saka ganye agaba da bayan motar

Ballah Auwalu ya tattara kan su baki daya yaje su tafi gidah zaa yiwa malama Hindu wanka a sallace ta...
.
Bappah junaid da allura ta sake shi ya dubi Karin ruwan da ake masa ya fizge shi da karfi ya mike Yana dafa bango ya fita
Chapter 23 · 0% Book details