← Book details Kwankwason Jimina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 41

Sashe 10

Kwankwason Jimina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tom shikenan babu damuwa. Nagode sosai hajiya Allah ya raba lafiya"

"Ni ce da godiya sosai. Allah yabar zumunci Amin"..

Har kofar gidah malama Hindu ta rakata tana mai kambama dattako irin nata.

Wajen suyar ta je tuni har sun gama ma an saye tas bata ma kai daren ba ranar. Duk dadi ya mamaye su ganin yadda ake tururuwar zuwa sayen awarar tasu..

Nan ta sheda musu yadda sukayi da hajiya qibdiyya ta karkare musu da,

"Idan abbiey dinku yazo zan sanar Masa duk hukuncin da ya yanke sai ayi amfani da shi. Ga katin data bani da number wayarta a baya. Ta saka tawa number a wayarta. "

Duk sukai mata fatan alkhairi da kuma hukuncin da abbiey dinsu zai yanke...

___

*DR. ABUBAKHR DOLLARS DWELLING:HOME/RESIDENCE)*

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_

_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[2/21, 5:42 PM] Hafsaat🧕: _KKJ_

_12_

_✍️:MX_

_ADVERT👇👇_

_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

::::::::::::

_
_NADUKA CRESCENT( APPLE ISLAND)_

(Dr. ABUBAKHR DOLLARS DWELLING/RESIDENCE)

*Ahankali* cike da nutsuwa da kwarewa direban ke tuka babbar motar da hajiya qibdiyya ke ciki a baya mazaunin owners corner....

Kallo daya zaka yiwa motar kasan ba karamin kudi aka sa aka saye ta ba. Mota ce mai nishin kudi. Kyau da kuma tsananin kawatuwa..

Baka ce irin bakin nan mai sheqi a idanu.. babbar mota ce mai kama da land cruiser . Irin Saharan mota dinnan ce wadda ke tafiya ko acikin guguwa ne da tabo. Uwa uba kuma motar bullet proof ce. Ko harbi aka saki akan ta ko gilasan ta babu abunda motar zatayi.

Unguwa ce data amsa sunanta ta manyan masu kudin birnin Naduka... Kaama daga masu rawani na sarauta, Manyan siyasa, Manyan yan boko , Ma'aikatan asibiti wato likitoci, Yan kasuwa da sauran masu farcinan susa..

Wani hadadden daular gidah tamkar a kasashen ketare. Nan direban ya nufa da hancin motar ta su. Hadadden gidah ne fari tas kalar sa. Yayinda gate din gidan jijjigagge shi kuma baki wuluk ne... Tafkeken gidah ne yayi wata unguwar a kauye. Kai ka rantse ba a Nigeria bane gidan. Ganin yadda tun awaje ba ma a shiga cikin gidan ba amman gidan ya hadu kwarai matuka ..

Ga famfuna nan anyi su awaje. Talakawan Naduka zone sunzo sunata dibar ruwan a manyan bokitai da jarkuna..

Hajiya qibdiyya ta dube su ta window yadda suke jere a layi sunata dibar ruwan . Ta sauke ajiyar zuciya kawai cikin zuciyar ta tana mai nanata,

"Allah ka horewa kowa...."

Suna karasawa camerar dake jikin gate din tayi zooming tana scanning motar kafin daga bisani gate din ya bude da kansa. Direban ya shiga da motar ciki.

Mashaa Allahu.... Mai karatu ai kawatuwar gidan ba daga waje yake ba kadai. Ashe akwai sauran kallo a gaba.

Wato cikin farfajiyar gidan ma kadai wata daular duniyar ce. Habawa. Jamaa Allah yayi mana arziki mai amfani wato kudi suna inda suke ..

Wajen motocin gidan ya nufa.. kowacce motar an tanadar mata wuri acikin wata katafariyar katuwar rumfar data hadu fiye da yadda kalmomi zasu bayyana...

Manyan moticine a jere a Kuma fake. Wannan tana bani wuri. Kowacce mai tsananin tsada ce da Kuma kudi Mai yawa.

Direban ya nufi kofa zai bude mata tayi saurin budewa ta futa tana mai daga masa hannu.

Murmishi yayi kawai ya koma baya... Domin ko da yaushe idan sun fita hakan ce take faruwa ko da ya bude mata sai ta saka hannu ta rufe ta kara budewa da kanta. Ta kance masa ya kyaleta ta dinga budewa tana rufewa da kanta ai ba aiki bane. Sangartar Kuma sai tayi yawa. Har mamaki da daure Kai lamarin yake bashi musanman idan suna magana da yan uwansa direbobi dake aikin tuki awasu gidajen yadda matan gidan ke sarauta mai cike da izza. Shi kuwa ko sau daya sai dai bacin rana shima ba fada take yi ba. Amman tunda yake arayuwar sa bai taba ganin mai saukin kai da sanin yakamata ba irin hajiya qibdiyya. Sam batada wulakanci duk kuwa da tarin arzikin da take da shi.

"Sannu hajiya akwai wani aiken ne?"

Ta grigiza masa kai tana mai duba jakar hannun ta. Ta kirgo kudi ta dunkule ta mika masa yasa hannu biyu ya karba,

"Na menene hajiya?"

"Naka ne.,... Aciki na ci awarar dana shigaa kaga ban fito maka da ita ba ka nemi wata awani wajen idan ka gani ka saya hakki ne."

Ya girgiza kai da sauri Yana mika mata kudin yace,

"Hajiya wahalar ta Isa wallahi, bugu da Kari ma kuma wallahi a koshe nake nak. Kuma kudin da kika bani da safe ma ban Ida kashe su ba wallahi. "

"Rike rabon ka ne. Nagode..."

"Ni ne da godiya hajiya Allah ya saka Miki da mafificin alkhairin sa. Ya biya Miki bukatin ki na alkhairi duniya da lahira Amin"

"Aamin... Jam'an..." Har tayi gaba zata shiga cikin gidan sai Kuma ta juya,

"Malam Liti...."

Da sauri ya amsa Yana takawa inda take,

"Naam hajiya..."

"Wannan matar me awara..."

"Eh hajiya Ina sauraron ki"

"Yan Ina ne su? Dama can tana awara bamu sani ba?"

Malam Liti ya girgiza kai da sauri cike da girmamawa yace,

"Gaskia ba Yan nan Naduka bane ance daga baya suka dawo. Amman basuda matsala yadda naji mutane na maganar. Kusan matar da mai gidan nata ma anfi yabon su kwarai matuka. Ance sudin mutanen arziki ne. Wani abun ne hajiya?"

Tayi saurin girgzia Kai tana murmushi tace

"A'ahh ba komai malam Liti. Tanada kirki ne sosai. Ga yaranta masu tarbiyya sosai wallahi.."

"Mashaa Allahu.. haka akace kam"

"Tohm dama. Kaga tafiyar Indo me aiki an dau lokaci. Yaran nan basa cin abincin malama Talatu. Basariya Kuma tayi kankanta. So na dai yi kuskuren harshe zance ko ko gandoki ne"

"Idan na fahimta kina nufin me awarar ta dinga zuwa tana yiwa su junior abinci?"

"Eh"

"Kuma har kin gaya mata?"

"Eh... Nayi sauri ko?"

"Eh to Amman insha Allahu nasan babu matsala zata amince.."

"Wallahi na yaba da hankalin ta ne. Ga shi tanada tsafta mashaa Allahu"

"Allah yasa adace hajiya"

"Aameen Yaa Rabbi. To sai gobe In shaa'Allahu "

"To hajiya ahuta lafiya. Allah ya saka da alkhairi "

"Aameen " ta amsa kasan makoshi .

Ta shige cikin gidan ta cikin wata babbar kofa mai nauyi da ado ajikin ta. Harda madanni na kararrawa da yar camera dake haska fuskar wanda yazo.

Bakinta dauke da sallama. Ta shiga ciki tana mai zare mayafin jikin ta,

"Wash Allah na..." Ta furta ahankali tana dafe kugunta,

"Sannu da zuwa Mami..." Cewar wata yarinyar daga gani maai aiki ce... Ta Sha uniform fari da dankwali baki.

"Yauwa sannu basariya. Kina lafiya?"

"Alhamdulillah Mami... A kawo ruwa?"

"Eh maza kawo mun. Nagode"

Yarinyar tatafi dasauri ta dakko ruwa da kofi akan tray ta ajiye agaban Mami.

"Amatsa kafafun naki yanzu"

"Yauwa yar kirki. Basariya tah. Allah ya miki albarka kinji"

Basariya tayi murmushi cike da jin dadi ta kamo kafafun hajiya qibdiyya tana matsa mata kafafun da har sun dan kunbura ma saboda tsananin ciwo. ...

"Su Hayfa sun dawo kuwa?"

"A'ah ai da sauran lokaci."

"Okay eh Allah ya dawo dasu lafiya" ta fada tana kallon agogon hannun ta. Ta tsiyayi ruwan a kofi tana sha..

Yayinda basariya ta cigaba da matsa mata kafafun ahankali tana mata sannu...

*NADUKA ZONE*

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_

_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
Chapter 10 · 0% Book details