← Book details Kwankwason Jimina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 41

Sashe 31

Kwankwason Jimina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya Isa dakata da wannan wa'azin kurman da kake don ba saurara nake ba. Da fari kana magana yo wancen akurkin dakin ai sai da ya tabbatar dan Adam ba zai iya kwana aciki ba ko da kuwa rai daya ne bare yace zai moriyar sa shine ya jefe ni da shi. Su kansu kiwon dakyar suke nunfashi saboda azabar zafi da duhu ba ai wundo ba a dakin haba haba dan Allah... Kana maganar awara awarar banza awarar wofi Allah ya kwashewa waken soya ma albarka Auwalu, . Kana maganar suna kyautata mana to ba dole su kyautata ba kudin yafendo ne data bayar ya handame don kuwa sata yayi yasa tayi masa kyautar dole. Dake Kai zakara ne sai da tsaba ya saye ka da kananun kashin kudin da yake maka ya rufe maka baki baka iya ganin lefin sa . Wannan kai ya dama. Na fada na sake fada ba yaran da zai zauna mun agidah wallahi. Muna karime Karime to abincin da zamu ci kullum na rai hudu dakyar zaka karo mana wasu hudun? Tukun nama aina zasu kwana? Wannan gidan Mai kama da turken agwagwi. Muma bai ishe mu ba bare Karin wasu mutanen Na gama magana Allah . Ba dan da yar da zasu zauna mun " tana karasa maganar ta shiga daki ta bugo kofar.

Bappah Auwalu yayi shiru ya kasa cewa komai. Babban abunda yafi daure masa kai da Yan uwan sa uwa daya uba daya ke wajen basu tanka sun tsawatar mata ba, Amman ba wani abun mamaki bane tunda sun ki amincewa su rike yayan kanin su uwa daya uba daya .

"Allah ya kiyaye hanya idan kun tafi. Na bar ku lafiya Allah yabada ladan taaziyya mungode"

Ya saka kansa ya fuce ya bar su zaune... Suka gama maganar da zasu yiyyi suka hada Yan kudin hannun su suka zura a takardar envelope suka saka masa a bayan kujerar da ya tashi
.
Daya bayan daya suka dare suma batare da sunji kunyar abunda suka aikata ba na kin daukar 'ya'yan kanin su uwa daya uba daya...

Ashir yana kallon kowannen su ya shiga motar sa ya tafi, ta cikin windon dakin sa.. yakumbo aminatu ma direban ta yazo daukar ta ta shiga mota tatafi.

Rayuwa kenan dama wasu dangin basayi da iyalin ka sai kana raye idan ka rasu kabar iyalan kama juya musu baya suke..

Lalle bango majingina ya fadi. Allah ya jikan Bappah junaidu da malama Hindu. Ya Kuma raya musu yaran da suka bari, Ashir, Ashfeef , Nawraah da auta Amnah.

Sabon shafin rayuwa suka bude mai ban tausayi da ban tu'ajjabi....

_Assalamu alaikum... HGL CHARITY FOUNDATION. Na neman temako me hamsin me dari ko sama da haka ko da kayan abinci ne zaa dafa a tallafawa abawa mabukata da sukayi azumi a wannan wata Mai abarka..._

_idan kudi zaa bayar ga asusun banki na opay 9044191709. Haka zalika idan kayan abinci zaa kawo zaa zo tarauni dake unguwar Kano sai akira number opay dincan dake sama_

_zaayi abincin azumi, kosai da Kuma kunu. Wani lokacin harda kankara ta ruwan sanyi ma da za rabawa mabukata masu buda baki.._

_kofa a bude take da dik Wanda zai taimaka. Allah yabada saa ya hadamu a ladan duka amin_
[3/7, 2:50 AM] Hafsaat🧕: _K'K'J_
_(M/W/S)_

_✍️:MX_

_39_

:::::::::

_ADVERT👇👇_

_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_

:::

**Dawowar sa kenan daga bakin tashar motar unguwar su ta Naduka zone. Ya shiga gidah bakin sa dauke da sallama. A matukar gajiye yake baki daya jikin sa ciwo yake tamkar ana kwankwatsar kashin sa.

Ya bude parlorn ya shiga yana doka sallama. Amnah ce zaune akan kujera dauke da kofi a hannun ta.

Ta amsa sallamar tana murmushi. Kasancewar akwai shakuwa sosai tsakanin ta dashi. Kusan shi ya reneta tun tana zanin goyo har girman ta.

"Amnah nah"

"Hamma" Ta kira sunan sa tana murmushi.

"Sai ke kadai? Suna Ina?"

"Adda Nawraah ta na kitchen hamma Ashfeef kuma baya nan"

"Me kike sha ne baki rage mun ba?"

'kunu ne Hamma. Gashi na rage maka" ta mika masa kofin

Ya girgiza kai yana komawa kusa da ita ya zauna yana kai hannun sa kan goshin ta,

"Ya jikin naki?"

"Da sauki hamma"

"Toh sannu kinji? Allah yabaki lafiya mai dorewa Amnah"

"Aamin Hamma"

Bakar ledar dake aljihun gefen rigar sa ya janyo ya sunceta. Yana dubanta yace,

"Kinci abinci?"

"Na koshi Hamma"

"Ah ai bazeyiwu ba. Jeki ce Adda nawrah tabaki plate. To zakici biredi?"

Nanma ta grigiza kai tana mikewa tsaye tace,

'ga kunu nasha. Na koshi"

"Toh jeki kice ta baki plate"

Tayi hanyar kitchen zata kira Nawraah sai ga fitowar nawraahn "

"Ah hamma yaushe ka dawo?"

"Ba dadewa kenan na shigo. "

"Sannu da dawowa hamma. A kawo abinci?"

"Aa barbabincin nan cikina ya cushe ban dai ruwa kawai, ki taho da plate"

"Tohm Hamma"

Kitchen ta koma tana yan zikirinta labbannata na motsawa ahankali . Ta dakko plate da ruwa ta kawo masa ta durkusa ta mika masa ya karba,

"Allah ya shi miki albarka"

"Aamin Hamma. Wa iyyakum"

Ya karasa shan ruwan kenan sai ga shigar Ashfeef parlorn ya dawo daga filin ball.

Ya tsaya suka gaysa da Hamman na su sai Kuma ya wuce bandaki. Wanka yayi ya sauya kayan sa zuwa na gidah ya koma parlor ya zauna shima

Ashir ya nannade takardar naman ya zazzage naman akan tray. Ba wani mai yawa can bane. Amman yankan su nada girma ya debi manyan tsoka da yawa ya mikawa Amnah

'kin dora akan abinci. A Zuba Miki ko da biredi zakici uhm?"

"Zanxi da bread"

"Yauwa Ashfeef Miko mata bread idan da akwai"

"Suaran sa kenan dazu na cinye Kafin na gama abinci wallahi." Nawraah ta amsa shi tana langabar da Kai

'okau ba damuwa Ashfeef huta ka karno bread anan shagon naga Yan majalisa fal dawowata dana aika Nawraah,

"Ah zan karbo Hamma. Ai ban gaji sosai ba"

"Rike ungo ban naka ne. Nawraah kema ungo naki." Ya daddanka musu nasu kasan naman yana karkade hannun sa

"Hamma Kai fa?" Nawraah ta tambaye shi cike da tausayin sa

Ya girgiza kai yana kauda shi yace,

"Yana yankawa Ina ci. Kaki damu" ya bata amsa da haka

Sarai tasan bawani naman dayaci sanda ana yankawa. Wannan dabiar tasa ba zai taba sauyawaba. Kusan kullum hakane ke faruwa. Ko abinci ne bai Isa ba zai ce su cinye shi a koshe yake..

Ganin irin kallon da suke masa su ukun yasa ya kakaro murmushi don tabbatar da su yace,

"Gyaran wata mota mukai babba. Ta gyaru sosai shine mutumin da aka gyarawa dayazo karba yaji dadin gyaran sai yayi mana alkhairi"

"Allah sarki Hamma. Allah ya kara daga ku ya inganta ku"

"Aameen. Jam'an"

Ashfeef ya fita ya sayo biredi. Haka suka gaggand'a da abinci suka ci. Dare yaja suka kwanta..

Ashir na tsaye tsayin daka akan su. Kwata kwata baya samun hutu ko na minti. Kullum Yana aikin da zai rufawa kansa dana Yan uwan sa asiri.

Idan yaga ana gini zai cire kayan sa. Yaje ya musu lebura ya debo musu ruwa su biya shi ko bulo, Idan yaga gidan Mai yayi datti ya shiga ya share a biya shi.

Yaje gareji nanma yayi gyaran mota ya Kuma wanke ta a biya shi. Ahakan Kuma duk da haka idan fenti aikinsa ya taso yana zuwa yayi shi da Ashfeef

Ya yinda Nawraah ke kula da gidan tana dawainiya da kanwar ta su marar cikakkiyar lafiya wato Amnah...

Nawraah tana yin kitso akan mutane daya daya haka. Da haka suke hada yan kudaden su rufawa junan su asiri mashaa Allah...

_Assalamu alaikum... HGL CHARITY FOUNDATION. Na neman temako me naira hamsin me naira dari ko sama da haka ko da kayan abinci ne zaa dafa a tallafa abawa mabukata da sukayi azumi a wannan wata mai albarka..._

_idan kudi zaa bayar ga asusun banki na opay 9044191709. Haka zalika idan kayan abinci zaa kawo zaa zo unguwar tarauni dake garin Kano sai akira number opay dincan dake sama_

_zaayi abincin azumi, kosai da Kuma kunu. Wani lokacin harda kankara ta ruwan sanyi ma da za rabawa mabukata masu buda baki.._

_kofa a bude take ga duk Wanda zai taimaka. Allah yabada saa ya hadamu a ladan duka amin_..
[3/7, 2:50 AM] Hafsaat🧕: _K'K'J_
_(M/W/S)_

_✍️:MX_

_40_
_Assalamu alaikum... HGL CHARITY FOUNDATION. Na neman temako me naira hamsin me naira dari ko sama da haka ko da kayan abinci ne zaa dafa a tallafa abawa mabukata da sukayi azumi a wannan wata mai albarka..._

_idan kudi zaa bayar ga asusun banki na opay 9044191709. Haka zalika idan kayan abinci zaa kawo zaa zo unguwar tarauni dake garin Kano sai akira number opay dincan dake sama_

_zaayi abincin azumi, kosai da Kuma kunu. Wani lokacin harda kankara ta ruwan sanyi ma da za rabawa mabukata masu buda baki.._

_kofa a bude take ga duk Wanda zai taimaka. Allah yabada saa ya hadamu a ladan duka amin_..

:::::::::

.... Suna zazzaune baki dayan su a parlorn su. Nawraah na koyawa Amnah karatun alqur'ani tana kara mata ayoyi biyu kamar ko da yaushe na daga surar da suke...
Chapter 31 · 0% Book details