← Book details Kwankwason Jimina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 41

Sashe 21

Kwankwason Jimina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shysa a har kullum ake son ka kalki na kasa da Kai kada ka kallo na sama da kai lalle idan ka kalla na kasa da Kai Wanda ka fishi komai tanan zaka Kara godewa Allah da rahamar da yayi maka. Nawraah wasu suna nan basu da matsugunin da zasu zauna Ina nufin gidah.. wasu basu da abincin da zasuci bara suke. Nawraah wasu suna nan kayan da zasu saka ma basu da shi sutura tayi karanci Nawraah. Wasu Kuma suna asibuti ma sai dai a kwantar a tayar basusan Wanda ke kan su ba. Wasu ma hankali ne basu da shi a zare suke suna kwana a bola. Nawraah lafiya kadai ma idan Allah ya barka da ita wallahi babban arziki ne. ... Ki kasance cikin hamdala ga mahaliccin ki shi Kuma zai ninka maki bukatin ki inshaa Allah"

"Inshaa Allahu ummy"

"Yauwa Nawraah,,, mace ce ke sai kiga Allah ya daga ki ya Kai ki gidan wani hadadde Wanda baki taba zaton samu ba Allah ne kadai yabar wa kansa sanin wayasan gobe. Kuma inshaa Allah khair"

"Hakane ummy.. nagode sosai da tunatarwa"

Suna tsaye a bakin kofar tun da suka danna door bell dai baa bude musu ba sai da Nawraah ta sake saka hannu ta danna madannin tukun sannan bayan yan mintina wata matashiyar budurwa kamar Nawraah tazo ta bude musu kofar

Ta sakala earpiece a kunnenta kana jiyo karar sautin wakar da take ji.. Sanye cikin kananun Kaya riga da wando kanta ba dankwalii ta yi parking gashin nata.

Wani hadadden babban parlor ne mai girma sosai yana dauke da saitin kujeru har biyu . Yayi matukar kyau parlorn kudi yayi aiki agidan domin komai Mai tsada ne sosai.

Yarinyar data bude musu kofar wadda kallo daya zakai mata kàsan yar gidan ce dubada wani zama da tayi akan doguwar kujera ta cigaba da karkada kafa tana bun wakar da take sauraron ta earpiece.

Can sai ga wata mata fara irin fararen ne don yarinyar ma data bude irin farar nance haka. Sunada kyau ba lefi . Irin buzayen nanne yan nijar

Matar ta dashare baki tana duban su tace,

"Dan Allah ku zauna... Malama Hindu ko?"

"Eh ni ce ce. Barka da rana mun same ku kalau?"

"Alhamdulillah..."

"Ina wuni?"
Nawrah ta gayshe ta

"Lafiya kalau yammata"

"Uhm lily kawo musu ruwa please"

"Mommy ni fa ba Mai aiki bace. In kawo musu ruwa Ina Dela take takawo musu mana?"

"What nonsense coman get up. Ki dakko harda lemo ki kawo"..

"Wallahi a koshe ma muke hajiya"

"To kinji sun koshi ma" yarinyar data kira da lily ta fada. Hadi da komawa ta gyara zamanta tana harde kafafun

"Bari a kawo kayan. Ah ai dole kusha ruwa malama Hindu...takanas daga gidan kawata ai dole a karramaka . Sunana Dr. Bintu... Ke dama nasan naki hajia qibdiyya ta fada wannan ce bansan sunan taba. Yar ki ce?"

"Eh yata ce... Nawraah"

"Mashaa Allah... Sunan Mai Dadi Mai kyau kamar jta tubarkallah. Ga yata can Ilham muna ce mata Lily . Sai babban 'dana Marwaan... Lily zo ga kawa na Miki"

Lily ta juya ta dube su duka a shekeke ta tabe baki tana girgiza kai,

"Not my type.... "

Dr. Bintu ta mike ta shiga wani daki tana kwada sunan,

"Dela.. Dela"

Da alama Mai aikinta ce don da sauri ta futo daga kitchen,

"Naam hajia"

"Zo ki fito da kayan nan duka please .."

"Tohm hajia yanzu kuwa"

Suna dai zaune suna kallon sarautar Allah dela ta fito da wasu manyan buhubuna dauke da kaya kaka kala.

"Kunzo da wayar ki? Ku fara dauka*

"Eh. Nawraah daukar mata"

Nawraah ta mike tana daga kayan daya bayan daya tana daukar hotunan su wasu budiyoyin su take yi.

Dela aiki ya kachame mata tamkar zatai hauka tazo tana cewa Dr bintu tuwo yayi ruwa gashi ko miyar bata hada komai ba.

Malama Hindu dake jin su tace,

"Bari na zo na kama Miki ko miyar ce"

"Kai harda wahala ayi haka?"

"Bakomai hajiya"

Malama Hindu ta futa tabu bayan dela suka je kitchen din. Nan da nan dama miyar kuka ce.

Malama hindu ta hada komai da zata tanada gata da saurin aiki ta fara hada miyar nan.

Baa dau wani lokaci Mai tsawo ba kitchen din ya fara tashin kamshin Miya. Nan da Nan ta gama ta ta zuba a food flask ta dauraye hannun ta ta koma inda Nawraah ke daukar hoto da bidiyo din . Suka kammala daukar

Yayinda suka lissafa Hadi da irga kayayyakin da suka haura guda biyu iri daya suka rarraba su Kashi biyu. Kowanne nawrah ta rubuta ta wayar ta ajiye.

Suna gamawa sukai mata sallama zasu tafi.. Ta bawa Malama hindu dubu biyar ta Kuma bawa Nawraah riga da skirt na cikin kayan sabbu.

Suka mata godia suka tafi. A mota malama hindu ta curo dubu daya tabawa malam Liti Dakyar ya karba yana shi mata albarka.

Nawraah ta saka aka sauketa agidan su Kuma suka wuce. Malama Hindu ta kaiwa hajia qibdiyya wayar ta Kuma nuna mata alkhairin kayan da Dr bintu ta baiwa Nawraah. Da ita kanta data Bata dubu biyar ta nuna nata ta Kuma karin tabawa malam Liti dubu daya.

Tayita yiwa hajia qibdiyya godia. Dakyar ta tsaya taci abinci aka Kuma zuba mata wani a kwanon ta.

Hajia qibdiyya ta dauki wayar bayan ta kwashe komai ta hada da chajar ta mikawa malama Hindu Wanda saboda tsabar farin ciki har kukan dadi ta saki...

:::;

Washegari malama Hindu dataje yiwa hajia qibdiyya sallama Nan take sheda mata ai Dr bintu ta kira waya tanata yaba mutinci da iya girkin malama Hindu ta kuma roki alfarmar tunda futa qibdiyya zata tafi haihuwa waje yaranta biyu Kuma zasu yi jamia. Zatayi hutu acan sosai Kafin ta dawo tana rokon Dan Allah malama Hindu ta rika zuwa tana mata abinci saboda Mai gidan ta ya yaba kwarai da miyar da tayi yanata santi..

Dakyar malama Hindu ta amince dubada yadda hajia qibdiyya keta rokon ta...

Nan sukayi sallama da su har yaran na ta da zaa Kai makaranta, junior da Hayfa. Yayinda anees Kuma zaiyi hutu tare da hajia qibdiyya zasu huta idan ta haihu har zuwa wani dan lokaci Kafin su dawo.

Har hawaye malama Hindu da hajia qibdiyya sukayi saboda tsananin sabon da sukai da juna, malama Hindu tana katse hawayen ta tace,

"Nagode hajia .. da dukkanin tarin alkhairin ki gare ni Allah ubangiji ya saka Miki da mafificin alkhairin sa ya bude Miki kofofin albarkar sa. Ya raya Miki zuri'ah ya shriya su tundaga kuruciyar su har gidan su. Allah Kuma ya sauke ki lafiya Amin. Dan Allah idan na Miki wani lefi Wanda nasan da Wanda bansani ba dan Allah ki yafe mun.Allah ya KADDARA saduwar mu ya hada fuskokin mu da alkhairi Amin"

"Ni ce da godia Hindu Allah ya daga Miki yaran ki duk kuwa da kin mun rowar ganin su Kuma bakimin lefi ko daya ba Hindu. Sai ma ni da nasan tabbas na Miki Dan Allah ki yafe mun"

"Ku gafarce ni hajia.abubuwan ne sai ahankali, Amma inshaa Allahu har sai kin gaji da ganin su ma. Ni ke Zaki aurar da su ma. Saboda ki yafemun "

"Inshaa Allahu Hindu. Allah ya yafe mana gaba daya"

Hajia qibdiyya ta rungume Hindu jikinta sukai sallama suna daga mata hannu suka shiga mota direba oga emaka yaja suka tafi.

Yayinda ita Kuma ta shiga motar malam Liti ya sauketa agidah.

Satin ta daya agida Kafin daga bisani Dr bintu ta fara Aiko direban ta yana daukar malama Hindu tana zuwa tana abinci Yana dawo da ita...

Da wannan suka cigaba da rayuwar su.sabo sosai ya shiga tsakanin malama Hindu da Dr bintu. Itaxe yiwa mijin Dr bintu abinci Kuma ya aminta da abincin sosai yana masa Dadi don har kyautar kudi yake bayarwa ayiwa malama Hindu

Wanii lokaci takan tafi da Nawraah don ta tayata wasu aiyukan na gidan aikin nata...

Ranar wata asabar da yammaci.....

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_

_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[2/29, 2:02 PM] Hafsaat🧕: _K'K'J_
_(M/W/S)_

_✍️:MX_

_25_

:::::::::

*Ranar* wata asabar da yammaci... Malama Hindu nata sauri kasancewar Dr. Bintu tace mata kada tazo da safe ta bari da yamma tazo tayiwa mai gidan nata girki zai ci da daddare ba zai samu cin na ranar ba saboda wani meeting da yake da shi,

Don haka malama Hindu ta karasa aiyukan da zatayi a gaggauce.. Ta zura hijabin ta tanata sauri ta sauka kasa.

Duk yaran suna nan har da Layla yar gidan Bappah Auwalu tana zaune a kan kujera mai cin mutum biyu tana yiwa Amnah kalaba kanana a kanta.

"Ummy tafiyar za ki yi yanzu ji rani.?"

"Eh Nawraah kilama na so na makara."

"Bari na saka hijabi na nazo"

"Ai Nawrah baki gaji ba? Da kin zauna yau"

"Aa zanje"

"Tohm.shikenan shiryo da sauri"

Malama Hindu ta karasa fada tana zama akan hannun kujera ta dubi Ashir tache,

"Hamma dan Allah idan abbiey dinku ya dawo ga abincin cin sa nan a food flask na saka a kasan kantar kitchen. Idan yanason shayi kuma akwai ganyan shayi acikin kwanon nan na kan freezer."

"Tohm ummy inshaa Allah."
Chapter 21 · 0% Book details