← Book details Kwankwason Jimina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 41

Sashe 13

Kwankwason Jimina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta rurrufe ko'ina sannan suka haye sama dakin su .. sai data fara lekawa dakin su Nawrah suna bacci sannan ta shige nasu dakin bakinta dauke da sallama...

"Ko kana bukatar wani abun abbiey?"

Bappah junaidu ya matsa kusa da ita ya kamo hannuwanta cikin nasa yana murzasu ahankali. Idanuwan sa cikin nata yace,

"Bana bukatar komai Hindu.... Ke kadai kin ishe ni... Ke kadai nake bukatar kasancewar ki matata agare ni a Koda yaushe .. kin zarce matsayin duk wani abunda kike tunanin zai kere ki.... "

Tayi murmushi kanta na mata girma ta dashare hakora sosai tace,

"Godia nake abbieyn su..."

"Ki fadi sunana mana daga ni sai ke ne fa... Junaidun naki Kuma?"

Hindu ta sake sakin wani tattausan murmushin da ta saka bappah junaidu Kai hannunsa kan kumatun ta yace,

"Kinji......?" Yaja ji..... Din sosai ta yadda Hindu sai data kasa danne yanayin daya sakata tace,

"Junaid .... Junaidu.... Junaidu na..."

Bappah junaidu dadi ua sake mamaye shi. Sunayen datake Kiran sa kenan lokacin suna saurayi da budurwa da aka saka ranar auren su kafin ayi auren idan yaje zance yana ce mata,

"Hindu... Hindunah.... Hindatuna tawa ni kadai ..." Ya tuno bayan yana mai sake fada ahankali a kuma rarrabe

Ta sake murmushi tana cusa fuskar ta a akan cinyar sa tace,

"Kai abbieyn su har kasa na fara kunyar ka.."

"Kunya....? Ni Kuma yau?"

Ya tambaye ta yana daria sosai.

Itama dariyar tayi ...ya saka hannuwan sa biyu ya dago fuskar ta. Ya tallabo fuskar sosai yana duban ta,

Ya kai kansa saitin fuskar ta dab da dab suna shakar numfashin juna .. Ya samu kansa da Kai bakinsa kan saitin tsakiyar gashinta ya sakar mata sumba..

"Allahumma barik ....."

"Wa iyyakum ...."

"Hindu....."

"Naam...."

"Da farko Kafin na baki amsar hukuncin da muka yanke akan maganar aikin ki zuwa gidan Dr .... Inaso ki bani nutsuwar ki sosai .."

"Ina sauraron ka Junaid... Allah yasa muji alkhairi"

"Tohm aameen ya rabbi.... Alkhairi nema.. da farko dai kinga a kudaden da yafendo ta babbamu anyiyyi guzuri akazo Kuma kashin kudin nan garin ba irin na bunza bane.nan birni ne sosai kudin komai anan Naduka ya ninka na bunza sau uku... Ko ba haka bane?"

"Haka ne abbieyn su.."

"Dukkanin ku kunsani ke da Nusaiba da sauran matan su bappah sani. Kudin da yafendo ta bari don ayiwa yarannan kidimar karatu da Wanda zaa musu idan sun tashi aure sun Kare anyi haka?"

"Hakane abbiyen su"

"Tohm... A dawo kan namu kasafin kudin. Kinga anawa kudin da gado na da Wanda yafendo tabani ta karamun dasu nayi gidan nan na Kuma tattara nake harkar kasuwancin nan da su ciki sune dai na tsakura ba yawa na baki kike awarar nan. yaran nan maza Kuma suke fenti idan an samu dama. Ake biya musu kudin boko da arabi matan ma ake biya musu kudin islamiya ko?"

"Wannan haka yake abbiyen su. Ai kowa ya sani Allah dai ya saka maka da alkhairi..."

"Aameen dukkan mu .. To kinga a abunda ake samu kema da Wanda kika bayarwa da Wanda yaran nan musamam Ashir ke kawowa duka kokari muke a taru a rufawa juna asiri. Abunda ya rage mun na boye kawai wannan ajiyar ce... Zaki dakko mun ita da safe inshaa Allahu... "

"Allah dai ya kara horewa Amin... Amma abbiyen su me zakayi da wannan ajiyar dakace ka tanade ta ne saboda nan gaba idan da rai idan auren Yara ya tashi..."

Bappah Junaid ya sauke nannauyar ajiyar zuciya mai turiri ya sake kamo hannuwanta yace,

"Babban uzuri neya taso... Kuma ba aro zan bada su ba kyauta zan bayar. Inshaa Allah Allah zai hore mana agaba... Kinji?"

Taso tambayar sa menene sai Kuma ta danne kawai ta daga masa kai. Don tasan koma menene tsakanin sa neda dan uwan sa. Don haka batasan shiga lamuran yan uwantakar su inde ba ance mata gashi gashi ba...

"Hindu ....." Ya sake kiran sunan ta..

"Naam.."

"Tunanin me kike ne?"

"Bakomai abbiey..."

"Kinga ki kwantar da hankalin ki ba wani abu bane. Gidan bappah Auwalu ne yake yoyo sosai baki daya katangar sai an canza ta .. wasu kofofin suma sun lalace sai ya sauya. To kinsan Nusaiba ta saka shi agaba wallahi. Ransa ba dadi sai dana tilasta masa sannan yake fada. Yace na tayashi neman inda zai samu bashi. Kuma kinga Hindu hannun ka baya rubewa kace zaka yanke ka wullar ko? Dan uwana ne bazan iya zuwa wani wajen na aro masa kudi ba bayan ni inada shi ni ne zan share masa hawaye tunda ni ne dan uwansa dake kusa yanzu... Shi yasa nace zan duba Masa acikin mutane zuwa da safe.. Amman ni ba aro zan bashi ba kyauta zan bashi. Nasan Allah bazai hana mu ba nan gaba. Dama shi ya bamu... Ko kuwa?"

"Hakane abbiey ka gama magana. Allah ubangiji ya saka maka da aalkhairi.. Allah yabar zumuncin ku. Ya biya maka dukkanin bukatin ka duniya da lahira. Allah Kuma ya kara arziki ya bude maka kofofin alkhairi Amin... Hakika Kai dan uwane na gari ne mai share hawayen nasa Yan uwan ko da kuwa shi nasa idanun rufe suke da damuwa. Allah ya iya maka abbiey. Amin"

"Aamin Hindu ... Tare da ke .. Allah ya Miki albarka. Nayi dacen mata tagari a duk halin dana tsinci Kai na Hindu bazan taba mancewa da alkhairin ki gare ni ba... Allah ya saka Miki da gidan aljanna. "

"Aameen abbiey..."

"Sai maganar zuwa gidan Dr abubakhr dollars... Shin againiki ke akan kankin kanki babu takura kiyi aiki a karkashin wasu tunda ba taba yi kikai ba? Kada kiga ko sabuwar rayuwar da muka tsinci kanmu aciki a haka zamu dauwama kike tunanin kaskantar da kanki kiyi aikatau a biya ki.. don rufin asirin mu"

"Ko kadan abbiyen su... Kuma kasan ni Ina son dukkanin abunda ya danganci fannin girki. Da ba girki bane bama bana tunanin zan karbi aikin gaskia"

"Hakane.... Kuma mun yi magana da bappah Auwalu. Shima yace a nemi yarjewar ki tukun dukkanin yadda Kika yanke yayi. Idan kin amince zamuyi to muna murna idan bakyaso nanma muna murna da fatan alkhairi.. me kika zaba? Wanne hukuncin ne yayi miki"..

Malama Hindu ta dan nisa can tache,

"Na amince abbieyn su ....zanyi aikin"

"Toh Allah yasa hakanne nafi alkhairi , Allah ya dafa Miki yasa ki fara a sa'a"

"Allahumma Aameen abbiey"

Haka sai adaren ranar suka kusa raya rabinsa da hira. Daga nan sukayi alwala sukayi sallar dare kana sukabi lafiyar katifa suka kwanta bacci ya dauke su...

Sai da malama Hindu ta dauki kwanaki biyar tukun sannan ta kira hajiya qibdiyya tace mata ta amince. Hajiya qibdiyya tayi murna kwarai matuka tace mata zata aiko a dauketa da safe inshaa Allahu .. ai kuwa haka akayi da safe wata zungureriyar mota hadaddiya tazo ta dauki malama Hindu har kofar gidah zuwa gidan da zata fara aikin abinci na iyalan Dr. Abubakhr dollars.....
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_

_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[2/24, 12:58 AM] Hafsaat🧕: _K'K'J_
_(M/W/S)_

_✍️:MX_

_16_

:::::::::

Dr. ABUBAKHR DOLLARS DWELLING/RESIDENCE:

  Malama Hindu na bayan mota, Ya yinda kanta ke kallon window na mota tana duban gidajen layin masu matukar kyawu Ma shaa' Allah ..

Malam Liti ya karya kan mota ya shiga gidan, Yayin da malama Hindu taga gate din ya bude da kansa motar ta shiga ciki....

Kasa boye mamakinta tayi har sai da ta waiwaya ta bayan motar ta sake duban gate din ya koma ya rufe da kansa...

Ta bude murfin motar ta futa bakinta dauke da addua... Sanye take cikin doguwar riga ta atamfa mai dogon hannu... Ta saka wadataccen hijabi kalar kayan na ta.

Hannunta rike da yar karamar jakarta da wayarta me torchlight aciki sai charbi da take ja..

"Yauwa, Bismillah! ga kofar da zaki shiga nan..." malam Liti ya nuna mata kofar da zata shiga ciki

"Tohm, Nagode." Ta dan kakkalo harabar gidan cikin ranta tana yaba kyawu da tsaruwar komai na wajen tun ma bata shiga cikin ba. Don a iya motar da aka zo daukar ta kadai tasan ba karamin gidah zata jebah..

"Mashaa Allah ..!" Ta fada ahankali alokacin da ta zare kafafunta daga cikin takalman data saka ta taka wani lallausan welcome carpet da kafafun ta suka lume ciki saboda tsananin laushin sa.

Ta sadda kai kasa ta dubi dan karamun carpet din da ke shimfide a bakin kofa an rubuta masa welcome da manyan baki..

Sake doka wata sallamar tayi bayan wadda tayi ta karasa shiga ciki tana mai nanata wa a karo na uku .

"Waalykm Salam" wata dattijuwar mata ta amsa mata daga wani daki data leko da fuskar ta.

Malama Hindu ta kakaro murmushi tache,

"Ina wuni?"

"Lafiya kalau... Ina zuwa"

Malama Hindu ta nemi jikin bango ta tsaya tana dan kallon cikin babban parlorn da mai karatu zai iya fasalta shi da aljannar duniya.

Ya hadu karshen haduwa, Domin babu ce kawai babu a parlorn nan duk inda hadadden parlor ya Kai na manyan attajiran masu kudi parlorn nan ya kai. Don ko acikin manyan masu kudin ma ba kowanne bane zai yi dace da gidan sa ya samu kayan dake cikin parlorn .
Chapter 13 · 0% Book details