← Book details Kwankwason Jimina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 41

Sashe 34

Kwankwason Jimina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ashir yayi murmushi yana grigiza Kai yace,

"Dan Allah kayi hakuri bappah Amman wallahi bazan iya dawowa gidan nan da zama ba tabbas gaskiyar Aunty yayi mana kadan"

"Yauwa Ashir kaji yace gaskiyar ta. Yo mu kanmu Ina gidan nan zai dauke mu bakidayan mu"

"Zan mugun saba miki nusaiba Allah kuwa. Ashir....

Kafin bappah Auwalu ya karasa maganar dazai Ashir ya katse shi ta hanyar zube gwaiwoyin sa akassa yace,

"Dan Allah kayi hakuri bappah. Ka dubi girman Allah ka saurari abunda Zan fada. Kuma dan Allah ka amince da abunda Zan fada din. "

"Inasauraron ka Ashir"

"Bappsh gidan nan wallahi ba zai dauke mu ba yayi kadan wallahi Anty tayi gaskia. Na biyu dama wallahi bada niyyar zaman agidan nan muka biyo ka ba yau din. Dama akwai tsare tsare. Da nake akai na.kayi hakuri yau din na amince akan dare yaja zamu kwana anan, Amman daga gobe inshaa Allah ba zamu sake kwana ba. Zamu samu waje kusaa da nan din. Idan Allah ya amince na mun samu kudaden da zamu biya wancen mutumin shikenan sai mu karbi gidan bappah mu biya shi. Dan Allah karma ka ki amincewa bappah. Idan kaki amincewa akwai matsala. Dan Allah Kai ne mahaifin mu albarkar ka muke nema" ya rike kafafun bappah Auwalu ya faraa hawaye dumin su na diga a kafar bappah Auwalu.

Sunkuyawa bappa Auwalun yayi ya riko hannuwan Ashir yace dashi,

"Shikenan na amince Ashir. Amman sai idan inda aka samu din anan zagayen layin yake ko nan yankin idan baa samu ba to gaskia ban amince ba. Haka zaku dawo nan mu cigaba da rayuwa tare watarana ma duk mutuwa zamuyi ashir. Dan Allah Nima Ina rokon wannan alfarmar kaji?"

"Shikenan bappah. Na amince"

"Yauwa ko kaifa Allah yayi muku albarka kaji? "

"Aaameen bappah wa iyyakum"

Nusaiba sai Harare hararare take bappah Auwalu yasa ta dakko zannuwan gado Ashir da su Ahmad sukayi shimfida a parlor suka kwanta.

Nawrah da Amnah da Layla Kuma suka kwanta a adakin layla. A haka sukayi bacci kowanne da abunda zuciyar sa ke saka masa....

Ashir da asubah ya futa tunda akayi sallah Bai dawo gidah ba. Ya sayi biredi wajen takwas na safe da madara da sukari ya Kai musu duka gidan suka ci

Nan ya shiga neman gidan haya kain dana in anan yankin.. Amma Allah cikin ikon sa baa dace ba. Gashi Ashir bayason ketare maganar manya don haka ya cewa bappah baa samu ba . Ya Kuma nemi gafarar sa daya barsu su nema a unguwar kusa da su. Bappah Auwalu yace sai nan gaba amman ba yanzu ba.

Tunda nusaiba ta jiyo su ta fara hauka kamar sabuwar tabi. Har da fashe fashe na kofuna tana nanawa kanta wuka zata kashe kanta kan lalle Auwalu ya zabi daya ko ita ko su.

Ganin haka yasa Ashir yace da kannen nasa su tashi su dakko kayan su duka suka fito. Bappah Auwalu ya biyo su Yana hawaye,

"Dan Allah Ashir karku yanke mana zumuntar mu ku nake kalla naga kamar junaidu don Allah . Kayi hakuri ka janye maganar ka ni ku na zaba ba ita ba. Ita tamkar riga ce da zan cire na sako wata haka take awaje na. Aurota nayi ,Dan haka iya rabuwa da ita na auro wata ku kuwa Yaya na ne bazan iya taba yanke zumuntar mu ba har gaban abadan. Jini ya wuce gaban komai"

Ashir Ya goge hawayen sa Yana rasa Mai zace Duk suna tsaye cirko cirko da akwatinan su a hannu...

_ADVERT👇👇_

_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
[3/8, 8:20 PM] Hafsaat🧕: _K'K'J_
_(M/W/S)_

_✍️:MX_

_44_

:::::::::

"Zamu iya kwana nan Bappah..." Ashir ya fada yana nuni da dan dakin da Bappan su ya bawa nusaiba take zuba kiwon ta . Tamkar akurkin kaji.

'ah haba ahsir. Ya za'ai rai na dan Adam ya iya zama nan? Ai ba zeyiwu ba"

"Allah Bappah zai yiwu. Zamu zauna har ya zuwa sanda zaa samu dan waje na kamawa anan yankin. Idan har zuwa nan da yan lokacin dana bari ya cika bamu samu ba. To kayi hakuri ko da awani unguwar ne zamu kana waje mu koma. Kuma zumuncin mu har aljanna inshaa Allah. Haka na dai yanke bappah .. Daurewa zai ayi"

"Ashir ka kalli dakin nan kuwa."

Nusaiba dake binsu dadi fam ranta ta nufesu tana murmushi,

"Kalau daki yake. Tumakan kawai zaa janye. Kajin Kuma a mayar da kejin su gefen can haka daga ciki ai yayi"

Bappah Auwalu ji yake tamkar ya Kai mata gula aciki ya hanbare ta baki daya. Cike da takaici yace,

"Bar nan nusaiba"

"Naje Ina? Ko ka manta mallaki na ne nan din? Ai na wa ne"

"Mahaifin su ne dai ya baki kada ki manta. Ke butuluce wallahi Allah"

"To daya banu yanzun ai nawa ne ko na baka ta rabaka da kayan ka. Allah na tuba nan din dan ya bani har wani abun birgewa ne...

"Da kata anty.ya isa hakaa. Kada ki tabo abbiey ko ummy. Maganar ta tsaya akan mu please." Ashir ya katseta Yana kada Kai.

Bappah Auwalu ya juya ya dankara mata harara,

"Ai ga irin ta Nmnan" ya fada Yana Jan dogon tsaki ya dubi Ashir yace,

"Amma da sharadin zaayi gyara sosai acikin sa da sauran su. Don daii ka hadamu da babban bango ne kace Allah bazan iya musu ba. Amman kasani har cikin raina banji dadin kasancewar ku anan dakin ba wallahi Allah ne sheda. Dakinda ake saka kiwon tumaki da kaji daa harda zomaye ma ace dan Adam ne zasu kwana acikin sa?"

"Bakomai bappah Allah. Mungode hakan ma ta mana kokarin"

"Kokarin me bayan mahaifin ku nema ya bata ba wai kudi ta saka ta saya ba"

"Kuma dai ai ba roka nayi ba da zaka ce haka. Allah na tuba dakin da kiwon da duk mutuwa suka dinga y kamar an canfa shi. Ni dai ga daki nan nace su zauna aciki ba Kuma kyauta na bayar ba ban amince Kuma ayi wani fàshe fashe ko gine gine acikin sa ba batare da izini na ba gaskia. "

Tana gama magana ta koma ciki kamar Zata tashi garin,

"Kifi ruwa gudu ma nusaiba. Aikin kawai" bappah Auwalu ya fada Yana hararo bayanta data tafi

Ashir yayi gaba Yan uwan na biye da shi abaya aka bude dakin. Ba lefi Yana da Dan girman sa. Sai dai kofa ce kawai babu window a dakin. Sai kashin tumaki Dana kaji da kazanta dai sosai.

Ashir ya kade hannunsa yana duban nawrah yace,

"Muje keda Amnah . Idan muka gama zamu kira ku. Sai anyi gyara sosai"

"Hamma zan tayaku"..

"Aa jeki zauna da amnah"

"Toh shikenan Hamma Allah ya bada sa'a"

"Aamin"

Tafiya tayi ... Ashir da Ashfeef da Ahmad da b. Auwalun suka fara kaude kauden kayan wajen zasu gyara nusaiba ta leko tana kiran Ahmad.

Tunda ta kiraa shi bappah Auwalu ya girgiza kai kawai don ya tabbatar Kiran sa tayi ta hana shi aikin.

Ai kuwa suna fita ta rufe shi da fada,

"Dan uban ka a wannan kurar,wannan shekararren akurkin dakin da ba bil adama ke kwana aciki ba kaje ka baje hanci kana tayasu aiki. Wuce muje gidah. Kuma wallahi ka sake ka fito sai na ci haka kaza ta uban ka"

"Kai umma"

"Zakaa wuce ko sai na sharara maka Mari"

Ciki ya nufa,Yana kananun mita. Ta shiga ta rufe kofar harda mukulli ganin haka yasa nawrah rike hannun Amnah suka koma can gefen famfo suka zauna.

Sannu ahankali suka fara gyara dakin suka wanke shi. Ya bushe suka saka katifun da suka rage akayan da basu sayar ba.

Suka raba dakin biyu da labule. Rabi daya na Ashir da Ashfeef. Dayan Kuma Nawrah da Amnah sai yama tamkar ciki da parlor don sai ka daga labulen zaka Isa wajen su Amnan.

Suka jajjera Yan abubuwan su da suka taho dasu. Suka jinginar da akwatunan su a gefe .

Ashir ya kunna karatun alqur'ani awayar ummyn su dake wajen sa tun da suka fara aikin har safiya sai da wayar ta kare karaf sannan ya kashe...

Haka rayuwar tasu ta cigaba da garawa. Da safe zai sayo biredi ya Kai gidan bappah auwalu suci gaba daya. Da Rana ma Dan kudin da suka samu da Ashfeef zasu auno taliya yar aune ko shinkafa su bawa nusaiba ta dafa...

Dare ya zama safjya, safiya ta zama rana, Rana ta zama yammaci yammaci ya koma dare lalle Allah buwayi ne gagara misali.

-------

Zaune suke baki daya a parlorn su bappah Auwalu wasu a akasan kujera wasu Kuma akan kujerar.

Tun ba su yarda suna zuwa ba. Har dai suka saba saboda takurawar da bappan nasu yake musu kan lalle su je su zauna ayi hira.

Duk abunda ake cewa nusaiba sai dai
ta yamutsa fuska. Tana jinsu. Sai data mula ta sha iska tace...

_ADVERT👇👇_

_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_

_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_
Chapter 34 · 0% Book details