← Book details Kwankwason Jimina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 41

Sashe 39

Kwankwason Jimina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakika ahalin Hamidniyya sun shiga dimuwa wadda ta kere duk yadda alkalami zai fasalta. A gub'i a gub'i sun rasa rayuka hudu ... Daga kan kaka, Uwa, Uba zuwa 'Da wato marigayi Ashir ... Marigayiya yafendo, Marigayiya Hindu, Marigayi Junaidu, da kuma marigayi Ashir.

Kuma dukkanin su ba wasu lokaci mai tsawo aka dauka na tazara tsakanin rasuwar ta kowanne ba.... Lalle bawa ya kamata ya koma ya tuba ga ubangijin da ya halicce shi. Domin shi din buwayi ne gagara misali. Mamallakin kowa da komai ...

Dakyar likitoci da maaikatan asibitin bangaren sashen suka tausashe su duka tun daga kan Bappah Auwalu zuwa Amnah .suka saka su a mota suka mayar da su gidah dauke da ledar da ragowar naman gawar marigayi Ashir ke ciki...

Aka wanke shi aka nannade shi a likafani. Haka dan tsakuren sauran naman nasa sai ya zama kamar jariri ne ya rasu aka nade shi...

Akayi masa sallah aka kai shi gidan sa na gaskia wato makabarta gidan kowa... Ba tazarar kaburarruka tsakanin kabarin marigayi Ashir dana iyayen sa marigayi junaidu da marigayiya Hindu...

Ashir ya samu mutane, Mutane sosai da sai ka dauka wani babban maaikacin gwamnati ne ya rasu, ko wani babban dan siyasa ko kuwa mashahurin dan kasuwa ne..

Ba ahalin Hamidniyya Lebanon ko ince ahalin marigayi junaidu su Nawraah ne kadai suke alhini ba. Baki daya mutanen Naduka zone suke alhinin rasuwar Ashir.

Ya samu yabo sosai daga bakunan mazauna yankin Naduka zone, Dana unguwar da sike da ma yan layin su, da wajen aiyukan sa. Bangaren lodin tasha, Da na gangaren wajen wankin mota, Da inda yake leburanci idan ana gini... Magina sun shiga dimuwa wanda suka san shi. Da ma masu fenti Wanda suke harka daya...

Banda tarin mutane da suka zo daga yankin bunza da rasuwar tasa ta riski kunnuwan su. Sun shiga dimuwa sosai.

Haka zalika Ashir ya samu jamaa da suka dinga biyan duk wasu bashikan da ake binsa... Suka koma harhada yan kudade suka ce a bawa yan uwan mai rasuwar Allah ya gafarta masa ya kai masa ladan Amin.

Haka aka dinga zuwa ana taaziyya. Saboda kowa yayiwa marigayi Ashir shaida ta kirki, Babu ruwan sa da shiga harkar da ba tasa ba, Yana mutinta kowa ga ladabi da biyayya, Bai taba fada da kowa, Kuma kowa nasane, komai kankantar aiki inde halal ne zaiyi a biya shi. Don haka kowa yake shedar sa ana masa addu'oin halayen sa nagari su bishi Allah ya haskaka makwancinsa.

Haka aka share makoki... Duk wannan Kwanakin da akai ana makoki. Hankukan kannen marigayin sun tabu sosai tamkar zararru wadanda basa hauka. Don kuwa magana ma sai an tsawatar musu da fada da magig sannan sike yi

Sun koma haka haka gwara Ashfeef da Amnah ma. Amman Nawraah mutuwar ta daketa sosai. Don har karin ruwa ma sai da akayi mata na leda biyar .

Sun Sha zazzabin na rashin lafiya sun kwanta ciwo dukkan su. Abun ya tayarwa da mutane hankali musanman bappah Auwalu da ya Dan sayi alawa ya Kai islamiyar kusa da su yace arabawa Yara akuma yi addua dan Allah Allah ya sanyawa Yan uwan Ashir su Nawraah hakuri da dangana Ameen..

Sannan ya sake sawa aka musu saukar karatu na alqur'ani. Shi ma Kuma ko da yaushe a sallah da bayan yayi karatu, Yana yi musu adduoi Yana gayawa Allah kan ya farfado da zukatan Yan uwan marigayi Ashir

Sai da suka dau dogon zango sosai Kafin su farfado. Amman duk da haka ba wata magana suka cika yi ba daga uhm sai uhm uhm kawai. Kullum cikin Nawraah take. Bappah Auwalu yayi yayi amma Ina ta kasa hakuri kullum sai tayi Kuka sosai idan ta tuno da shi kadai ne dama ya rage musu tamkar shine mahaifi da uwa agare su. To gashi shima an wayi gari Allah daya fi su kaunar sa ya dauke abun sa.

Maganganun Ashir su nata dawo mata Kai. Daman wasiyya yake musu duk maganganun da yake fada a baya.tamkar yasan mutuwa zaiyi kullum cikin yi musu nasihar rayuwa yake Yana kara Dora su akan hanya madaidaiciya.

::

Toh haka rayuwar ta cigaba da tafiya ta kowanne bangare na cikin sashen littafin.

Ko'ina ana samun sauyi na rayuwa wani na dadi wani akasin haka.

A yanzu dai babu wadanda duniya ta sauyawa ta kuma juyawa baya fyace su nawrah da suka sake zama abun tausayi. Sun rame baki daya sun jeme.

Gashi makarantar tamkar da aka basu gurbi gini har an fara karatu basu taba zuwa ba saboda alunin rashin Dan uwan na su. Layla ma taki yadda taje ita kadai sai da Nawraah. Nusaiba ta daketa ta kyareta amma kmadagas layla tace ita gaskia sai da Nawraah zata fara zuwa jami'ar.

Hakan kuwa akayi sai bayan kwanaki hamsin da uku da rasuwar Ashir tukunna sannan Nawraah ta hakura zata fara zuwa jami'ar. Kasancewar bappah Auwalu ya zauna ya sake mata nasiha Mai ratsa jiki da jikinta yayi sanyi ya karkare yace,

"Dukkanin wadandan abubuwan agaba zasu wuce inshaa Allah. Haka rayuwar take wucewa yake kamar baayi ba nawrah. Kuma akace wai mutanen kirki Allah ya ke saukewa. Bayaga haka sanin kanki mahaifan ki da dan uwan ki mutanen kirki ne na kwarai. Duk inda mutanen kirki suke masu Kuma su junaidu sun zarce. Kuma wallahi Allah ba zai barku haka ba. Akwai jin dadi agaba da yardar Allah. Domin Allah shi kadai ya barwa kansa sani Nawraah. Tabbas munyi rashi. Amman Allah dayafi mu son su ya karbe su Nawraah. Sai mu fawwala lamuran mu gareshi. Da yardar Allah Nan gaba sai kinyi dariya . Zakiga komai ya wuce. Addu'ar mu kawai sike bukata musanman taku da kuke Yaya agsre su haka zalika Ashir yake Yaya agare ku..Allah ya gafarta musu kinji? Ki shirya goben Dan Allah kuje kinji? Ki dau hakan a ranki ki saka daga gobe kin shiga wata sabuwar rayuwa wadda acikinta ne komai zai yi sauki na matsatsi kinji? Allah ya muku albarka"

"Allahumma Aameen Bappah. Inshaa Allahu zanje"

"Yauwa haka nake son ji. Mashaa Allah. Bari naje nan layin baya na dawo"

"To bappah sai ka dawo"

Fita yayi daga dakin nasu. Ta juyar da Kai tana duban Amnah dake. Bacci ta sake ramewa itama baiwar Allah duk sai Kashi baki daya sun mokade.

Mikewa tayi ta nufi baya tayi futsari kasancewar akwai rariya da famfo awajen ta dauro alwala ta dakko sallaya ta shimfidah tana sallah. Kan Allah ya shiga lamuran sun ya musu zabi nagari adukkanin abubuwan da suka saka agaba na rayuwar su Allah Kuma ya jikan iyayen su da yayan su. Ya gafarta musu. Jamia Kuma da zasu fara Allah yasa suje a sa'a Amin"

Haka ta daga hannuwa sama bayan ta idar tanata kwarara adduan daga nan juna ta dakko alqur'ani ta zauna tana karantawa. Hawaye ya shiga diga daga idanun ta rayuwar su ta baya kawai take tunowa lokacin da dukkanin su suna raye yadda rayuwar tasu ke tafiya ahankali cike da farin ciki. Amman yanzu duk sun rasu, rayuwar tasu ta jima cikin dinbin bakin ciki da ya mamaye farin cikin su na baya ...

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_

_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[3/10, 12:23 PM] Hafsaat🧕: *_KWANKWASON JIMINA!!_*
_(MAI WUYAR SHAFAWA)_
🦩🦯🦾

_✍️: MX_

*_ZAFAFA BIYAR 2024_*

_vip pages na arewa👇_
*_arewabooks:mssxoxo_*

_*BOOK ONE*_

_paid page :50_
_(FINALE/KARSHE)_

____

*Zafi* ake yi sosai astagfirullah. Gashi babu window a dakin nasu. Dan Amnah ma da wando take kwanciya kawai. Kusan kwana Nawraah take a zaune tana mata fiffita. Gashi ciwon ta kwana biyu ya motsa ya lafa ya dawo yakeyi.

Duk yan kudaden da aka raba musu na ragowar gadon su baki daya har na wajen marigayi Ashir duk akan rashin lafiyar Amnah yake tafiya. Saboda lalurorin ta masu cin kudi ne...

Bappah Auwalu yayi yar buga bugar da zai yi ba wani kudi da yake samu. Wanda ya dan samu din Nusaiba sai ta kwace tace yara ba lafiya su Ahmad zata saya musu magani....

Ko da yake maganar zaa fasa wundo a dakin dasu Nawraah suke. Haka nusaiba a ranar tun safe ta dinga tijara har dare tana dire tsallan albarkar wallahi babu mahalukin da ya Isa ya fasa mata wundo . Ai dakin mallakin ta ne halaliyar ta ne din haka Bata amince ba.

A ranar tsabar bakin ciki sai da Bappah Auwalu ya jera mata marika har biyu a kuncinanta ta dafe kuncinta tana duban sa,

"Ka mareni Auwalu?"

"Na mareki nusaiba. Kiyi abunda Zaki. Haba mace sai kace zazzauciya ? Aradun Allah wani mai tabin kwakwalar ma yafi ki sanin abunda ya Kamata. Ace ke kwata kwata ba digon tausayi a ranki? Ke fa uwa ce. Kin haifa gasunan agaban ki. Baki tsoron ayiwa naki haka?"

"Okay baki zaka mana kenan ni da yaran? To ni na haife su da Kai na kenan? Kai ma ai jinin ka ne. Ko ka ki, ko ka so su, su din da baka son su dai sune 'yayan ka na cikin ka wadancen yayan dan uwan ka ne"
Chapter 39 · 0% Book details