← Book details Kwankwason Jimina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 41

Sashe 28

Kwankwason Jimina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya daga hannu cikin tsantsar tashin hankali da tsana ya shararawa masa mari

Alhaji Sambaso ya rike kuncinsa, Yana duban bappah Junaid daya sake daga hannu zai kauda masa wani , Alhaji Sambaso ya jinginar da shi a jikin baranda, bappah junaid ma ya tattake ya buga shi da kofar.

Alhaji Sambaso cikin hazalar fushi ya cakumi wuyan bappah junaid ya hankada shi da karfunan barandar.

"Kashe ni zakai? Nima ka mar yadda ka kashe matata?"

Alhaji Sambaso ya saka hannu, Yana rufe bakin bappah Junaid dayaki ya sake cakumar sa. Alhaji Sambaso ma ya riko tasa yana sake cakomar rigar sa yace,

"Shashasha"

"Kai ne shashasha, Mugu, Azzalumi...."

Garin riko shi zai naushe shi ya hankada shi. Bappah junaidu ya fada kasa ji kake 'Timmmmm

Kamar kara ya fada, Take kansa ya fashe bai shura ba ya mutu awajen alokacin....

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_

_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[3/5, 7:07 PM] Hafsaat🧕: _K'K'J_
_(M/W/S)_

_✍️:MX_

_34_

:::::::::

Rufe bakinsa yayi da sauri, yana zare idanuwa jin muryoyi suna kururuwa daga waje lalle da alama mutumin ya mutu....

Tun sanda mutumin ya shigo dama yayi hanzarin danna recording kiran na video call da sukeyi....

Alhaji Sambaso ya saka hannunsa ya shafo kasan keyar sa, Yana rufe bakinsa da tafin hannun sa....

"Naga kaman labarai kake kalla ko? Bari na kashe na sake kira yanzu nima zanyi abune?"

Ya jiyo murya daga cikin laptop. Dama bai katse video call din ba? Ai baki daya ya manta.

Ya dafa teburin yana kallon sa ta cikin system din yace

"Dama baka kashe ba? Me kake nufi da labarai? Ka saurari maganganun da nake fada ne?" Alhaji Sambaso ya tambaye shi cikin tsananin tashin hankali

Ya girgiza kansa yana bashi amsa da

"No da naga Jana kallon labarai ne kome. Magana sama sama sai na tashi na shiga bandaki fitowata kenan kuma naga kaman da kanta ma muna waya"

"Ka tabbatar abunda ka sani kenan?"

"Eh mana... "Ya kakaro daria ya sake cewa,

"Futsari na tashi nayo ma sai na tsaya na karba parcel dina da aka kawo yanzu"

"Oh okay. To shikenan zamuyi magana, yanzu zamu shiga meeting ne " ya katse kiran yana rufe laptop din baki daya..

Zagayawa yayi ta kofar baya emergency exit dinsa wanda ba kowa bane ya sani a kamfanin ya fita ta ciki ya koma kasa...

Nan da nan maaikatan wajen suka fara taruwa akan gawar bappah junaidu....

Da sauri wasu maaikatan suka nufi ofishin nasa suka bude baya ciki. Aka dudduba bayan ko'ina

Nan suka shiga fara kiraye kirayen wayar sa. ... Ya fito daga cikin wani guri a kasan kanfanin da suke kira da lodge .

Daki ne da parlor da bandaki inda manyan maaikatan suke shiga su huta.

Nan ya futo daga ciki yana mitssika idanu,

"Ah ranka ya dade ashe baka cikin ofishin na ka?" Cewar wani leburan kamfanin daya nufe shi yan yana tambayar sa. Duk sauran maaikatan suka yayyabe su.

Alhaji Sambaso ya saka hannu yana rufe bakinsa alaman hamma ce tataho,

"Alhaji ayi hakuri amaana afuwa, Ashe hutawa ma kake"

"Wallahi kuwa bansamu bacci bane gaba daya nache bari na dan huta. Bayan tafiyar Alhaji ateeks"

"Ranka ya dade wani mummunan labarin ne ya faru"

"SubhanAllah Allah yasa muji alkhairi meya faru kuma?"

"Wani ne ya fadi daga barandar ofishin ka...

Kafin su karasa maganar da suke. Alhaji Sambaso ya katse su cikin buda baki yace,

"Ba dai junaidu ba da yazo duba gyaran da zaa mun a barandar"

"Allahu Akbar kabiran. To shine... Bawan Allahn nan yazo dazo yake tambayar mu wajen ka muka nuna masa ofishin ka . Dama bakuwar fuska ne kam. Amman daya nuna katin ka dinnan nasan babban bako ne shysa ma muka kyale shi ya shiga. Ashe ashe ajalinsa ne ke kiran sa. Kuma akwai tsani fa a bayan kofar bai duba ba kenan ya taka karfen dama karfen ai girgidi yake"

Alhaji Sambaso farin ciki ya taho masa ya danne don kar su gane. Ba kadan ba yaji dadi da daya ji daya a cikin maaikatan yace dama karfunan barandar suna girgidi..

Wucewa yayi gaba tamkar Wanda yake cikin tsananin tashin hankali .mutanen suka rufu akansa sam ba dadin ganin gawar ma ta bappah junaid. Aka dakko kyalle aka rufe shi.

Alhaji Sambaso ya sanya aka kirawo ambulance nan da tazo aka fara wucewa aasibiti aka gyara shi sannan aka kira gidah da number Ashir dake cikin wayar ta bappah junaidu.

Nan ake sanar dashi zaa kawo gawar mahaifin su ya fado daga benen barandar me tsananin tsayi ya rasa rayuwar sa yanzu ma gasunan akan hanyar motar kwana kwana sun biya ta asibuti an gwada gwaje likitoci sun tabbatar ya rasa ransa..

Ashir baki daya dama suna zazzaune a parlor ne. Ya na tsaye wayar ta fadi daga kunnen sa yana salati

"Menene Ashir? Menene ?"

"Hamma menene?"

"Ashir Ashir menene?" Bappah Auwalu ya shiga girgiza kafadun Ashir. Ashir yana zubar da hawaye duk tsananin dauriyar sa jikin sa na rawa yace,

"Abbiey ne..."

"Abbieey din. Meya same shi meya samu junaidun?"

"Bappah.... Abbiey ya ra su... Abbiey ya rasu bappah "

"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un.......

Bappah junaidu ya ambatada da karfi gwiwoyin sa sun gaza daukar sa ya zube awajen ya fara kuka sosai tamkar karamun yaro ...

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_

_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[3/5, 7:07 PM] Hafsaat🧕: _K'K'J_
_(M/W/S)_

_✍️:MX_

_35_

:::::::::

Nawraah na sama ta sakko rike da bokiti a hannun ta da kaya aciki. Tana murmushi tana taka kafafun benen tana sakkowa tace,

"Hamma! Yau ni ma na rigaka Ina son na samu lada.... Na wanke kayan abbiey daya cire jiya. Yana dawowa zan gaya masa"

Tana sakkowa ta tsaya tana duban su. Yadda sukai cirko cirko masu kuka nayi masu salati nayi.

"Menene?" Ta tambaye su jikinta a sanyaye ..

Duk sukayi shiru suna kuka sosai. Ta karasa kusada da Layla ta dafa kafadarta,

"Meya faru ? Eh? Menene? Wane ne ba lafiya ko wani abun ne na daban?"

Layla ta daga fuskarta sharkaf da hawaye ta saukar ta akan Nawraah tace,

"Bappah ne?"

"Bappah sani Bappah salisu ko bappah Auwalu? Meya same su bappahn?"

Layla ta sake girgiza mata kai tache,

"Bappah junaidu?"

"Bashida lafiya? Wani abun ne ko? Daman yadda kwana biyu abbiey yake yi nasan bashida lafiya. Me akace ya same shi?"

"Nawraah. Abbieyn ku Allah ya masa rasuwa"

"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un..." Ta fada da karfi ta zube awajen a sume.

Sukai kanta da sauri. Bappah Auwalu ya saka aka kawo ruwa aka yayyafa mata. Ta farfado da kyar tana wani irin sauke numfashi mai nauyi tamkar zata shide..

"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un... Bappah Auwalu ku tasheni daga baccin da nake.. wai abbiey ya rasu? Abbiey fa kukace? Abbiey ya rasu fa kukace? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un. Wannan wane irin wasa ne? Layla meyasa zaki ce abbiey ya rasu akan wane dalilin abbiey zai rasu eh?" Ya karasa fada tana sakin dariya harda tafa hannuwa tamkar sabuwar marar hankali, can kuma ta saki kara mai razana ta fashe da wani irin kuka tana birgima.

"Wayyo Allah na. Abbiey. Wayyo Allah na! Wayyo Allah na Ummy. Wai abbiey shima shikenan ya rasu ya bar mu? Abbiey ya tafi shima? Ummy ma tarasu fa? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un. Waya kashe mana abbiey? Kashe abbiey sukai. "

"Kiyi hakuri Nawraah babu Wanda ya kashe junaidu kinji. Lokacin sa ne yayi. Kinaji daga wajen aiki ne wai a karfen baranfa ya taka shine ya fado rai yayi halinsa sun akai shi asibiti ma ance ya cika. Yanzu sun taho kawo shi gidah. " Ya karasa fada mata shima yana sake barkewa da wani kukan

Baki daya sai suka bude shafukan kuka. Nusaiba daga can gefe tayi shiru itama kanta a kasa. Hakika mutuwar kanin mijin nata junaidu ta razananta kwarai matuka. Agubi agubi anyi musu mutuwa biyu kenan ajere ba daukar lokaci.

"Shikenan Hamma bamuda iyaye? Abbiey da ummy sun rasu? Shikenan bamuda sauran gata ko Hamma? " Ashfeef ya fada yana girgiza kai.

Ashir ya katse hancinsa Yana goge hawayen fuskar sa yace,

"Ga mota can inaga sune..."
Chapter 28 · 0% Book details