← Book details Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki Local reading mode
READING PART 9 OF 31

Sashe 9

Kururuwar Shaidan Wasa Farin Girki · about 8 min read

Chef Rehman ya koma bedroom da fuska a ɗauri. Ya zauna kan kujerar gyefin gadu ya jawo laptop ɗinsa. Amma duk abin da ya ke hoton tsoron da ya gani a fuskarta da yadda ta firgita yadda take hawaye da yadda ta saki tray ya dawo masa a rai.

Sai ya lumshi kyawawan Eyes ɗinsa zuciyarsa na bugawa sai ya miƙe tsaye da fuska a ɗauri ya koma gaban mirror idosa sunyi jajir kamar wota jawo kofin coffee ɗinsa ya sha sai ya fitar da iska a hankali.

“No…. Me kake tunani haka ne Rehman wannan aljanar yarinyar na tsaneta duli na nesanta kaina da ita kar inye mata abin da ban shirya ba.

A daren nan

Zysha ta kwanta amma barci ya gagara zuwa duk lokacin da ta runtse ido sai ta hangu yanda idon Rehman a gabanta ya yi jajir kamar wuta.

Ta rufe kanta da bargu tana rawar sanyi duk da babu wata iska sosai a ɗakin. Sai ta fara karatu addu’o’I cikin sanyin murya.

Amma kafin ta rufa da suratu fatiha karu na uku, sai ta ji wata iska mai sanyi ya hura cikin ɗakinta fitilar ɗakin ta yi dum! Ta yi ƙasa kamar zata mutu.

Zysha ta ƙara rike bargon jinta tana kallon kofar idonta firgice. A hankali saita ji kamar wani yana tafiya da kafa amma babu kowa acikin ɗakin.

Zuciyarta na bugawa ta fara ambaton sunan Allah da karfin hani.

*”A’uzubillahi minash shaiɗananirra jim….*
*Bissimillahir rahamanir rahim….”*

✨✨✨✨Daular masarautar Egypt

Da ɗan tsawa papa ya fara magana da harshen Egypt.

“Mother shin kin mata wacece munika a gurina? Ta zauna dani a lkcn da kowa ya ke gudana ba kalar tsanar da bata fuskanta ba duk sabu da ni ko kin manta cewa nima musulmin ne ?”

Dago idonta da suka yi jajir ta zuba masa a zuciyarta tana tsinewa mamie kasan cewarta musulma.

Ya yunƙura zai sake magana afsana ta yi wani irin tari da sauri ya karasa gurinta kumfa na fita daga bakinta.

Hankalin papa ya yi ƙululuwar tashi. Yana riƙe da hannun afsana da bata motsi. Hawaye na zubu masa kamar ruwan sama.

Mamie kowa gaba daya ta fita daga hayyacinta, tana kiran sunan ƴarta da karfi.

“AFSANA! Ki tashi my sweetheart! Don Allah ki buɗe idonki….”

Wani irin tsoro ne ya lulluɓe zuciyar papa yana tuna kalaman wata tsohuwa da take zuwa masa a farki ta ce duk wata masifa da zai gani daga matarsa musulma ce ta jawo. Da sauri ya kawar da zancen daga ransa.

Knocking ɗin ɗakin aka yi doctor ya shigo da sauri hannunsa da kayan aikinsa.

Ya ƙarasa ya duba afsana ya ɗora mata stethoscope.

Bayan wani ɗan lkc fuskarsa ta nuna rashin kwanciyar hankali.

“Yallaɓai”. Doctor ya faɗa cikin taushin murya
Amma da nauyi,” al-amarin nan ba ƙaramin abu bani alamu na nuna ba ciwon zuciya kaɗai bane akwai…. Akwai wani abu da ke faruwa da ita wanda baya cikin kimiyya ba”.

Papa ya zaro ido a rikici:

“Wani abu kuma? Wani abu ka ke nufi doctor?”

Doctor ya ɗanyi shiru, ya dubi mamie wadda ta ke kuka har tana rawa jiki.

Sannan ya ce:

“Wallahi kamar an saka mata wani kariya ne na tsafi ko wani abu da bamu fahimta ba.

“Saboda duk wani magane da muke mata baya aiki abin da kawai zai iya ceto shi ne addu’a da kuma neman taimako gurin ƙwararrun malamai.

Mamie ta ɗaga kanta da sauri idanunta jajir:
“Na gaya maka dama wallahi wannan ba cutar asibiti bace. Wani makircin shaiɗan ne papa baka sun ka yarda….”

Kafin papa ya yi magana sai ga wata ƙara daga ta tashi daga gyefin gadun afsana. Afsana ƙwatsam! Ta buɗe idonta amma idon ba kamar na ɗan Adam banu___jajaye ne kamar wuta.

Saita fara magana da muryar da ba a taɓajin jin irinta daga bakinta ba.

“ Na faɗa muku… baku isa hanani wannan yarinyar ba domin ba taku bace!”.

A lkc ɗaya suga wani haske ya cika ƙofar window aka wata inuwa mai suffar maci ta bayyana tana kallonsu tana dariya.

“Na dawo ta ce da yarin Egypt” afsana ba taku…. Bace tawa ce”.

A firgice mamie ta rungume yarinyarta tana kuka tana karantu addu’a da karfi. Papa kowa ya faɗi da sauri yana neman taimako.

Matar ta ɓace ɓatt tana wata shaiɗaniyar dariya.

Afsana na rawar kunne da wata irin murya ko papa bai taɓa jin irinta ba cin murya mai kauri.ta ce

“Kunyi tunanin zaku hana ni? Ko kunyi tunanin addu’arku zata yi tasiri a jikina? To kunyi kuskure dumin kowa na faɗa muku afsana yarinya ta ce tun kafin ku haifita na ɗauki ai nihin ruhinta tun ranar da kuka kawota duniya….”

Mamie ta saki fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai saurari tana ƙara rungume yarinyarta sosai tana karanta suratu fatiha cikin rawar murya.

Idon papa ya cika da hawaye, yana kallon yarinyar da yake so fiye da komai amma yanzu ta zama kamar wani abu mai ban tsoro.

Doctor kuwa ya ruga ya fita daga ɗakin da gudu yana kurma uban ihu! Dumin wannan yafi ƙarfin zuciyarsa.

To jama’a littafin KURURUWAR SHAIƊAN ya fara ce da wuta dan yafi ƙarfin zafi da haka nima na ajiye alƙalamina dan abin nema yana sun ya fi ƙarfin zuciyata

Karku manta ku danna like kuyi comment ƴan amana️
KURURUWAR SHAIƊAN

*Book 1 free ne [2025] novel ️*

HYPERLINK "https://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30https://chat.whatsapp.com/GMguONdwRnw5KiIfxpKquJ" https://whatsapp.com/channel/0029Vb6QGRg6WaKl7oWkqq30https://chat.whatsapp.com/GMguONdwRnw5KiIfxpKquJ

Story & writing
By

*ZULFA M TUKUR*

(Zufee baby shalelen momma)

Ƙarƙashin jagurancin ƙungiyar….️

بسم الله الرحمن الرحيم

اللهم صل على محمد....

Page 13

Doctor kuwa ya ruga ya fita daga ɗakin da gudu yana kurma uban ihu! Dumin wannan yafi ƙarfin zuciyarsa.

Afsana ta fara dariya wadda ke futuwa da ƙara kamar ana haɗa Muryar yara da kuma Muryar tsohuwa. Dukan window ɗin ɗakin suka fara girgiza, fitulu suka fara ƙift-ƙift, kamar zasu fashe.

Mamie ta ƙara ruɗewa cikin kuka:
“Ba zan taɓa barin ki ba! Koda kuwa zaki kashe ni, afsana ni dake duk abu ɗaya ne!”

Kwatsam afsana ta ɗago hannunta ta riƙe wuyan mamaie da karfin da bai kamata yarinya ƴar ƙuruciya ta yi ba. Mamie ta fara ƙoƙarin yin tari, tana rawar jiki amma duk da haka taƙi sakinta.

Papa dake durƙushe a ƙasan carpet ya fice daga firgicewa ya ruga da gudu ya riƙe hannun afsana yana ƙoƙarin kwace mamei daga hannunta. Amma da ya duba cikin idonta sai yaga ba asalin ƴarsu bace wata muguwar halittace ke sarrafata.

“Afsana! Sweetheart! Nine papa! Ki tuna mu duka muna son ki….don Allah ki dawo gare mu!”.

Wani irin ihu mai ban razana ya fito daga bakin afsana ɗakin yay wani irin girgiza kamar ƙasa zata tsage. Bayan ihun ta faɗi kan mattress cak komai ya tsaya shiro sai tari mai mugun karfi da ya sarƙeta tayi laƙwas kamar wadda aka kashe mata karfin jiki.

Mamie ta saki kuka, ta rungume yarinyarta da ƙarfin gaske tana cewa:
“ ya Allah ka kare min ƴata daga sharrin su!”

Papa kuwa ya tsaya dafe da bango zuciyarsa na harbawa kamar zata fito. A ransa ya fara tabbatarwa:
Wannan al’amarin akwai sarkakiya acikinsa sabu da me wannan tsohuwar dake tsanata neda mamie duli akwai saka hannunta ya zama dole in gano wannan sirrin kafin in rasa komai.

A wannan lokacin wata murya ta bayyana, akunninsa shi kadai:
“Kayi sauri JAPHETH lokaci yana ƙurwwa….
Afsana zata ɓace idan baka tsayar da ita ba”.

A firgice ya fara dubi-dubin ɗakin ya mayar da hankalinsa kan afsana ko itace tay maganar amma sai yaga afsana bata numfashi da alamaa dai ta sake sumewa mamie na tsaye tana buga kanta da bango sai dirzar kuka take.

Hankalin papa ba karamin tashi ya yi ba a wannan ranar yay sauri ya dakatar da ita ya zaunar da ita yana lallashinta tari da ɗaukar mata alƙawarin zai wayo karshin al’amarin.

Shiru ne ya biyo baya saiga ƙarar wayar papa banza yay da wayar dan halin da yake ciki bazai iya magana da kowa ba.

Ƙarar wayar ce ta fara isarsa ya miƙe ya ɗauko wayar *number ba suna* da tsoro ya ɗaga wayar.

Ƙara wayar ya yi a kunninsa Muryar mace mai kauri ta cike wayar cikin yarin Egypt.
“Japheth har yanzu baka gane ba? Tun farko nayi gar-gaɗi matar da ka aura musulma bazata haifar maka da ɗa mai gadun mulki ba, sai dai ta lalatar maka da jinin ka”.

Papa ya matuƙar firgita dan ya gani muryar ita ce wannan *tsohuwar da ta shake mamie a baya*.

“Me kike so daga gurin mu? Me yasa kike sun hallakar min da afsana? Ita ƙarama ce bata da laifin komai!”

Yay maganar da rawar murya.

Tsohuwar ta yi dariya”laifi? A’a Japheth. Ita afsana ce ita ce silar laifin da kakanta ya aikata. Ka manta? Uban ku ya karya alƙawari tun shekarun baya da ya aura maka musulma Kuma kaima ka musulunta, uban ku ya rusa asirin da akawa masarautar. Don haka duk jinin da ya fito daga gare ku to bana ku bane. Dole ne ya mutu!”.

Sakin wayar papa ya yi jikinsa yana ƙarƙarwa. Ya joya ya kalli mamei da ta ji labarin ta sanƙame idonta yay jajir.

Da ƙyar ta buɗe baki ta ce:
“Ka ji ko?tun farko ban samu farin-ciki da aurin nan ba. Daga baya na ɗauka soyayyarka zata kareni ni da yarinyata ashe ni ce asalin matsalar ka”.

Ta fashe da kuka. Papa ya riƙe hannunta ya ce cikin tsananin damuwa:
“A’a! karki saki tunanin haka. Kin sani bana jin tsanar ki duk duniya bani da masoyi face ke. Dan haka ki daina ɗaurawa kan ki laifin da ba saka hannunki aciki, amma yanzu ya zama dole mu nemo babban malamin da zai bawa afsana abin da zai karita daga sharrin su kafin wannan tsohuwar ta ɗauke ta daga gare mu”.

Kwarai mamie ta gamsu da kalamansa kuma ta fara jin nutsuwa a ranta. Shiru sukayi jugum-jugum suna jiran farkawar afsana.

Wani irin iska mai sanyi ya ratsa ɗakin fitila ta yi tsalle kamar zata fashe sai suka ji muryar tsohuwar ta saki bayyana amma acikin bango, tana dariya.
Chapter 9 · 0% Book details